BIYU A ƊAYA

Chapter 3

by @barista

BIYU A ƊAYA 


***
YOTA 13 
Team of FIVE INK legends 

Dedicated to my love Nimcyluv Sarauta 👸🏻


Page 3

Tana isowa ɗakin Dr Waahab ɗauke da basket dake ɗauke da breakfast nasa, ta turo ƙofar tare da sallama shiru ba'a amsa ba, ta ƙaraso ciki, sanyayyen ƙamshin room freshener ne ya daki hancinta, ga sanyin AC da ya haɗe da ƙamshin ya bada wani yanayi na musamman. Ta ajiye basket ɗin tabi ko'ina da kallo tana sake karewa ɗakin kallo, a hankali ta sauke numfashi ganin ko'ina fes ba datti komai an ajiye a inda ya dace.

 Ta kurawa photo Dr Waahab dake maƙale jikin garu idanu, sanye da kayan likita yayi matukar kyau.....

"Ashfat"

Ta tsinkayi muryarsa kamar daga sama, saurin juyowa tayi ta daidaita nutsuwar tare da cewa 

"Ya Waahab breakfast na kawo maka na tadda baka nan"

Ya sauke numfashi ya zauna bakin bed yana cire agogon hannunsa sa ya ce

"Thanks"

Bai sake cewa komai ba daga wannan, ya cire agogon ya ajiye akan bedside ya ɗago ya kalleta tayi saurin cewa 

"Kana buƙata wani abu ne"

"A'a"

Ya faɗa a takaice, taja jiki ta fice, ya cire rigar jikinsa, ya rataye a hagger ya ɗauko basket da ta ajiye ya buɗe, a hankali yake duba abin da ta girka masa, jollof na macaroni ne wanda yaji kifi da ganye, kaɗan ya zuba a plate sannan ya haɗa tea da ruwan zafin da ta kawo cikin tea flask, a nutse yake ci yana kuma kurɓan tea har ya kammala ya ɗan huta kaɗan sannan ya dawo kan bed ya kwanta har ya lumshe idanunsa sai kuma ya buɗe su ya kalli photon sa dake maƙale jikin garu ya tuna shigowar shi yaga Ashfat ta kurawa photo idanu ko me take kallo oho ya sauke numfashi a hankali ya rufe idanunsa nan da nan bacci ya ɗauke sa...


******************************

GHANA

Zaune suke kan dakali, da alamu nan ne wajen zaman su, saboda ganin yadda suke wasa a wajen hankali kwance, babu ruwansu, yara ne kusan su 11, maza 6 mata 5. Manya basu wuce 4 ba a cikin su. Ƙaramar cikin su ce ta taso daga inda take zaune ta soma takowa zuwa bakin Titi, ganin haka yasa wasu daga cikin su kiran sunanta da ƙarfi 

"Aicha! Aicha!"

Hakan ya janyo hankalin jama'a da dama waɗan da suke harkokin su ta wajen.

 Jin muryoyi da ihu yasa ta tsaya daga tafiyar da take yi, ta juyo ta kalli inda muryoyin ke tashi da mamaki taga yara ne, tabi inda suka maida hankalinsu suke kallo, ta hango yarinya ce wacce ba zata wuce shekaru 4 ba tayo kan Titi ga mashin Ocada yayo ta inda yarinyar take, cikin saure da hanzari ta iso inda yarinyar take ta ɗauke ta daga wajen zuwa gefen Titi ta kalli fuskar yarinyar kyakkyawa da ita black beauty an tufke gashin kanta da ribon duk da ba tsawo ne dashi sosai ba.

Kura mata idanu Aicha tayi tana kallon fararen idanun wacce ta ɗaukota daga kan Titi. Ganin fuskar a rufe take yasa Aicha kai hannu zata buɗe niqabin amma kuma bata bata damar yi ba, har sauran ƴan'uwanta suka iso, Aicha ta gudu ta bar inda matar take zuwa wajen yan'uwanta da suka tsaya suna ganin mace me rufaffiyar fuska, ta mik'e daga tsugunno da tayi ta kallesu itama, a hankali ta sauke numfashi za tayi magana kuma sai taga sun ruga a guje zuwa kan dakalin da suke zama, daga nesa suke kallon ta, mamaki ƙarara ɗauke kan fuskarta, me kuma su ke yi anan ɗin? Nan ai gefen hotel ne me suke yi a wajen? A hankali ta koma da baya ta tari machine ta hau yaja suka bar wajen.......

*****
Kasancewar yau sun yi customers da yawa a restaurant yasa bata samu damar hutawa ba, duk ta gaji ga rashin isasshen bacci da bata samu ba a daren jiya, har ciwon kai ya saka mata, basu huta ba sai wajajen azahar sannan ta samu ta fito ta wuce ta ɗauro alwala ta iso ta wuce wani ɓangare daga cikin restaurant ɗin saboda gabatar da sallah, a nutse ta idar da sallah tayi addu'a ta shafa, nan ta jingina da jikin garu tana sauke numfashi tare da hamma yunwa take ji tun safe bata sanya komai a cikinta ba, gashi ba daman ta taɓa na restaurant yanzu Alaja sai ta ce zata cire a albashinta.

Lalubo jakarta tayi ta fiddo da biscuit ta soma ci sai da ta gama ci ta fito ta tsugunna ƙarƙashin fanfo ta kunna tare da sanya tafukan hannayenta biyu tana tara yana zubowa tana sha, sai da ta gusar da ƙishin ruwan da take ji sannan ta dawo inda ta idar da sallah ta ɗan kwanta tana sauke numfashi a hankali ta lumshe idanunta nan da nan bacci ya sace ta....

"Bilqees!"

Alaja ta faɗa da ƙarfi ganin tayi ɗaiɗai tana sharɓan bacci ganin bata farka ba yasa ta iso wajen tare da danna mata duka a baya nan da nan ta tashi, tare da waro idanuwa ganin Alaja ne yasa ta mik'e tsaye tana mamakin baccin da tayi daga kwanciya....

"Bacci ki ka zo yi ko aiki?"

"I'm sorry Maa aiki ne ya kawo ni"

"To ya zama na ƙarshe da zan tadda kina kwance har ma da bacci, sallah kawai na amince ki zo nan ki yi bayan ita ban lamunci komai ba"

Tana jin raɗaɗin bugeta da Alaja tayi ta amsa da 

"Ok Maa"

"Ki wuce ki ɗauki abincin Alaji Muktar ki kai masa"

Daram ƙirjinta ya buga, ta ɗan waro idanuwa waje tare da cewa 

"Hotel?"

"Eh hotel, da a masallaci za ki kai masa?"

Ta girgiza kanta alamun a'a, ta sake daka mata tsawa 

"Ki wuce mu tafi"

Tabi bayanta suka nufi kitchen an kammala shirya komai cikin food carrier ta ɗauka duk jikinta a sanyaye ta ce

"Majada ki raka ni mu kai mu dawo"

Majada dake tsaye tana zare idanuwa saboda ganin Alaja ta ce

"Mu je"

"Ita kaɗai za ta je ai aikinta ne, ko aikin ki ne Majada? I said, is it your turn?"

Majada cike da tsoro ta girgiza kanta alamun a'a, Bilqees ganin haka yasa ta fito jiki a sanyaye, me yasa a duk lokacin da aka yi customers a hotel ita Alaja ke aikawa, kuma ta san da wannan abin da akwai hatsari. 

Ta fito bakin gate ta sallake titi ta shige cikin hotel ɗin, gateman ya santa saboda yawan kawo abinci da take yi bai yi mata magana ba ta shige kai tsaye room number da ta gani jikin food carrier ta nufa tana isowa ta yi nocking kusan sau uku sannan taji alamun motsin buɗewa, ta ɗan ja da baya ta tsaya.

Ya buɗe ganinta a tsaye yasa ya ce

"Menene?"

Ganin babban mutum ne yasa ta ce

"Abinci na kawo maka daga Alaja restaurant"

Ya jingina kai, ya dawo ciki, hakan yana nuni da ta shigo, kamar ba zata shigo ba amma ta daure ta shigo ta ajiye food carrier ta juya zata fito taga yana ƙoƙarin kulle ƙofar da mamaki da kuma kaɗuwa ta ce

"Ka manta ne? Ban fita ba kake ƙoƙarin rufe ƙofar"

Da mamaki yake dubanta sama da ƙasa ya ce

"Are you serious?"

"Ban gane ba? Ka buɗe na fice"

"Kada ki raina min hankali mana, za ki ce ba a faɗa miki komai ba, ai ko ba a faɗa miki ba kin san me ake yi in kun kawo abinci"

Cikin rashin fahimta ta ce

"Ban gane ba, me ake yi?"

"Determine"

"Cut it out"

Murmushi yayi ya zauna bakin bed tare da cewa 

"Wanka za mu fara daga nan na samu nutsuwa dake sai na ci abinci"

Jikinta ya soma rawa, ta ce

"Kindly, let me go"

"Ke kada kiga ina bin ki da laluma kada ki raina min hankali, za ki ce Alaja bata faɗa miki komai ba, i think she already clarified everything"

"Ban gane ba, me ku ka kulla a kaina?"

"Infact na bada kuɗin abinci da kuma na wanda zan huta dake"

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, hasbunallahu wa ni'imal wakil. Wa ka baiwa kuɗin?"

"Oh! ashe kuna sane da Allah ku ke bushashan ku"

"Kai Alhaji mukhtar bani bace"

Da mamaki kuma yake sake dubanta ko da gaske ba ita ɗin ɓace, shi ya ce ta turo masa da zazzafar yarinya, ya ce

"Kenan waccen tana hanyar tahowa?"

Da sauri Bilqees ta ce

"Eh"

"To ai sai ki yi min bayani"

Ya buɗewa Bilqees da sauri ta fice jiki na ɓari har ta iso ƙofar restaurant ta sami guri ta zauna, tana sauke numfashi, lallai Alaja ta cika mara imani wato bayan wannan harka ta abinci da take yi har da na ƴan mata, no wonder shiyasa take nan² dasu...

"Bilqees have you returned?"

Tayi saurin ɗagowa ta kalli Majada dake tsaye tana tambayar ta, ta miƙe tare da cewa 

"Yanzun nan shigowa ta"

Suka jero zuwa ciki, suka wuce corido suka zauna Majada ta ce

"Nawa ya baki?"

"Waye?"

Cewar Bilqees tana kallon Majada, tare da tambayar ta don bata fahimce ta ba, murmushi tayi tare da cewa 

"Alaji mukhtar"

Ta waro idanuwa waje ta ce

"Me kike nufi?"

"To ni dai ban ce ki bani ko sisi daga cikin kuɗin ba, nima gobe zan kwashi rabona kowa ya ci kuɗin sa"

A razane Bilqees ta mik'e tana nuna Majada da yatsa bakinta yana rawa ta ce

"Kina aikata abin da na tadda yau ɗin nan kenan?"

Murmushi Majada tayi ta ce

"Yeah wato kema kin yi, so perfect....

"Majada!"

Bilqees ta faɗa da ƙarfi tare da yin baya ta ce

"Kina mu'amala da mazinata? Waɗan da basu san darajar kansu ba balle kuma naki"

"Hold on Bilqees, kina nufin duk wannan tsawon lokacin da muke tare mu ke kuma aiki a ƙarƙashin Alaja bata taɓa ciniki dake ba?"

"Enough Majada, ki dakata kuma ki yi gaggawar barin nan wajen, zan iya yin hauka"

"Bilqees menene haka? Ai duk mu da kika gani har mun yi nisan da bama jin kira, ana maganar kuɗi....

Kan ta ƙarisa Bilqees tayi saurin chakumota ta wuyar rigar ta tana haki idanunta sun yi ja, ta ce

"Kune kuke janyo mana zagi, ashe ba laifin kowa bane da suke kiran duk wanda yake aiki a ƙarƙashin Alaja da karuwai, kun ɓata mana suna kun cuce mu"


"Bilqees"

Cewar Alaja da ta iso wajen, ganin abin da yake faruwa kuma abin da bata taɓa ganin Bilqees tayi ba sai ya bata mamaki tare da cewa 

"Ki cika ta, zauna mu yi magana, menene? ya aka yi kika baro hotel ɗin da wuri?"

Bilqees sabar ɓacin rai da tashin hankali ma ta ƙi zama ta tsaya a tsaye tana kallon Alaja tana ci gaba da fassarata ta ko wane yanayi....

Da sauri Majada ta bar wajen, Alaja ta mik'e tare da dafa kafaɗan Bilqees ta ce 

"Why you're so worried?"

"Alaja kin karɓi kuɗi kin sayar da jikina wa wani ƙato, me hakan yake nufi?"

Murmushin ƴan duniya Alaja tayi tare da cewa 

"Oh really! that's what makes you so angry?"

"Alaja me kike so damu me muka yi miki? You are playing a game with our lives"

"Lower your voice Bilqees, don't raised it on me, I'm your mom and rayuwar ki a hannuna take, dole nayi yadda nake so dake, ya zama dole ki yi min biyayya"

"I'll end it"

Dariya sosai Alaja tayi tare da cewa 

"To ya za ki yi da uwar ki dake kwance wacce bata iya tsinanawa kanta komai ba, balle kuma ta taimaka miki? Ya za ki yi da kuɗaɗen da nake bin ku? In da yadda za ki yi sai mu gani"

Tana faɗin haka tayi ciki, tabar Bilqees a tsaye cikin tashin hankali, tunowa da tayi da Mamarta na kwance babu lafiya ga kuma tulin kuɗaɗe da Alaja take binsu yasa ta tsugunna kan gwaiwowinta ta saki kuka, sosai take yi, tana jin ƙuna da tsanar Alaja har cikin ranta. 

Ta mik'e tare da ɗauko jakarta ta fice daga cikin restaurant ɗin ta wuce gidansu dole su nemi mafita ita da Mamanta.........


******************************

Nigeria 

 Maiduguri KIRAWA'S FAMILY.


Ashfat a lokacin da ta fito daga ɗakin Dr Waahab ta koma kitchen ta taimaka musu suka fita da breakfast ɗin suka jere kan dining, sannan suka sanar da Ammie sun kammala, Ammie ta fito ta duba komai yayi daidai ta ce

"Ina naku?"

"Hauwa ta ce

"Yana kitchen yanzu za mu ɗauko mu kai ɗakin mu a cen za mu yi breakfast"

"Hakan ma yayi, Hajiya Binta ma bata ji daɗi ba,  in kun idda breakfast ɗin sai ku je side nata ku yi mata ya jikin"

"To Ammie"

Sun amsa mata, sannan suka tafi kitchen suka ɗauko nasu abin karyawa suka wuce ɗakin su acen suka karya, bayan sun kammala ne kowacce ta watsa ruwa suka shirya suka fito, za su wuce ɗayan bangaren dake cikin gidan.

A palour suka tadda iyayen su na karyawa, Ammie mahaifiyar Ashfat da Teemah, da Mamie mahaifiyar Dr Waahab da Hauwa da Alhaji Waseem KIRAWA (Daddy) mahaifin Dr Waahab da Abbie Alhaji Shareef mahaifin Suhaima da kuma Alhaji Musa da suke kira Abba shine mahaifin Ashfat da Teemah...

Cikin girmamawa suka tsugunna suka gaida iyayen nasu, suka amsa sannan suka wuce ɗayan side ɗin. Nan ma suka tadda iyayen su maza suka gaida su sannan suka shige ciki anan suka tadda kusan ƙannensu na ciki suka gaida Hajiya Binta tare da yi mata ya jikin. Ta amsa nan aka hau gaishe² a cen su kayi zaman su.


*********
A hankali ya buɗe idanunsa, ya ɗanyi miƙa ya tashi ya zauna mamakin bacci da yayi me nauyi, ganin kusan la'asar gashi azahar ya wuce shi yayi sauri ya sauƙo ya faɗa toilet ya watsa ruwa ya ɗauro alwala ya fito ya zura jallabiya ya hau kan dardumar sallah ya idar da azahar yana kan addu'oi aka kira la'asar don haka ya mik'e ya idar sannan ya mik'e a nutse ya shirya cikin ƙananan kaya, yayi matukar kyau sai ƙamshi yake yi, ya fito ɗauke da side bag da wayarsa a hannu da key mota, sai da ya shige wajen Mamie yayi mata sai da safe zai wuce wajen aiki yana da night duty, tayi masa addu'a sannan ya wuce ya fito parking space ya buɗe motar sa ya shiga, ya tada ta, ganin Sa'eed yana ƙarasowa ne yasa ta dakatar da motar yana zuwa ya shiga tare da cewa 

"Dr sauke ni a hanya mana"

"Ok ina motar ka?"

"Tana wajen gyara, ta ishe ni ma kawai canzata zan yi"

"Ai kayan Bature ba guarantee, musamman ma kayan ƙarfe, abin da za mu yi shine ka sai da wancen tun da tafiya zan yi kuma zan ɗan kwan biyu sai kayi amfani da nawa motar"

"Haka ma za ayi likita kawai zan ce mechanic ɗin ya nemo wanda zai saya kawai a wuce wajen"

"Ya Waahab"

Suka jiyo Muryar Ashfat daga waje ta ɗan rage tsawonta tana kallon Dr Waahab ta window motar, Ya Sa'eed ya ce

"Kin ga fita za mu yi, kuma ba hanyar ki za mu bi ba"

"Nope Ya Sa'eed daman abinci na kawo wa Ya Waahab ne, ko zai tafi dashi office"

Sauke numfashi Dr Waahab yayi, a hankali ya ce

"Ashfat bani da lokacin da zan nutsu na ci kawai ki bari"

Jikinta yayi sanyi, Ya Sa'eed ya ce

"Sanya masa a seat na baya, in ya samu nutsuwa sai ya ci"

Ta saka ciki, tare da cewa 

"Ya Waahab sai ka dawo"

Ya ɗan kalleta ya ce

"Thank you"

"To mun ji, ni kuma kura ta cinye ni ko to lafiya kalau zan dawo"

Dariya tayi ta ce

"A'a Ya Sa'eed kai ma sai ka dawo"

Dr Waahab yaja motar suka fice, sun ɗan yi nesa Dr Waahab ya ce

"Habu mechanic zan kai ka?"

"Eh likita nafi gane aikinsa"

"Ni kuma Jibrin mechanic na fi so yayi min aiki"

"Uhm likita ka fahimci wani abu kuwa game da Ashfat?"

"A'a ban gane ba, sai dai kwana biyun nan kamar ta damu dani"

"Babu tantama son ka take yi"

"A matsayin Yaya ko menene?"

"A'a so na soyayya wanda ake yi na mace da namiji"

"Uhm bani da lokacin wannan, in ma aure take so ga maza a family"

Dariya Ya Sa'eed yayi, ya ce

"Ai ta san dasu ta zaɓe ka"

"To gaskiya ni ban shirya aure ba har sai mommy ta sami lafiya, kuma ko da zan yi aure ba zan auri matan family ba"

"Me kake nufi, yan'uwanka ne fah?"

"Bana son hayaniya da yawan ƙorafi gwanda na auro daga waje na kawo ta nan ɗin ya fi min kwanciyar hankali"

"Tab ai ko Alhaji babba ba zai amince ba, don kana daga cikin waɗan da ya lissafo su  wanda za su auri ƴar family koda bayan ransu ne ku kula da KIRAWA'S FAMILY"

"To malam mun iso sai kuma gobe da safe"

Murmushi Ya Sa'eed yayi ya fito tare da cewa 

"Allah ya kai mu, godiya nake likita"

Shima murmushi yayi, ya wuce Maiduguri Teaching hospital (TH).....



Comments and share fisabilillah