ALIYU HAYDAR

Chapter 16

by @nieemartullah

Da yamma bayan Jay ta dawo daga wurin aiki suka shirya ita da Munarh akan zasu je airport dakko dad.

makullin mota ta dauka suka yi ma mom da Ummi sallama sannan suka fita,a hanya suna tafiya suna hirar abubuwan da suka faru a baya suna ta dariya har suka qarasa airport.

Suna shiga cikin airport din jirgin su dad yana yin landing,don haka basu dade ba suka hangi dad janye da suitcase din shi.

Inda yake tsaye Jay ta qarasa tace welcome home dad,hugging dinta back yayi yace thank you Jay how is work ?kalan tausayi tayi da face dinta tace work is so stressful dad,I'm even thinking of resigning ta fada tana dariya.

Dariya shima yayi yace toh waye zai kula da asibitin?ko  haka za'a barshi ba'a kula da shi? 

What i mean is that zan dena zuwa aiki regularly, kallonta kawai yayi ya girgiza kai bai ce komai ba sai da suka kusa qarasawa inda tayi parking tace dad close your eyes i have a surprise for you.

Zai yi wata magana tace dad please,sai bai ce komai ba ya rufe idon,sai da suka je bakin mota tace you can open your eyes now.

Akan Munarh dake tsaye a jikin mota tana murmushi ya bude idanun shi at first bai gane ta ba sai da ya qara kallonta sannan ya juya ya kalli Jay yace wannan ba Maimunatu bace?

Gyada mashi kai tayi alamun ita ce,rasa ma me zaice yayi kawai yace Allahu Akhbar, indeed God is great.

Durqusawa tayi tace barka da yamma dad, ya hanya?Alhamdulillah Maimunatu ya kike?lafiya qlau, barka da dawowa,yawwa,daga haka suka shiga cikin mota suka dauki hanyar komawa gida............................


Hello Layla,Hafsat ta fada bayan Layla ta daga kiran da tayi mata.

Bayan sun gaisa Hafsat tace ina jin zan fita daga cikin harkar ki ne gaba ki daya,ke kike da matsala amma nike bin kanki akan neman mafita? toh na gaji tunda baki dauki abin da muhimmanci ni zan cire hannu na daga ciki.

An fada maki nade qafa ake a zauna saboda kin samu Sooraj a hannunki?.

Baki san cewa yan uwan shi zasu iya zamar maki barazana ba?.

Ga kuma wannan yar iskar yarinyar da yace zai aura,kin san ita yanxu me zata shirya idan ta lura ya dena zuwa wurinta?.

Shiru tayi bata ce komai ba har sai da ta gama fadin duk abinda ta fada sannan tace ke matsala ta dake gaggawa.

Ba wai nayi shiru bane saboda na manta,na bari ne ita ta gama duk wani shiri da zata yi idan ma tana da wani shiri,mu kuma daga baya kinga sai mu rusa duk wani shiri da tayi.

Jin ta fadi haka yasa Hafsat tace toh shikenan na dauka ai mantawa kika yi don na san halin ki da shiririta.


Dariya tayi tace toh ba mantawa nayi ba uwar masifa daga haka suka cigaba da hira.......................................................


Da dare bayan an gama dinner mom ta samu dad a dakin shi yana duba wasu yan takaddu,zama tayi a gefen shi tace ashe aiki kake yi gashi kuma da zuwa nayi muyi magana.

Ture takaddun da yake aiki dasu yayi ya riqe hannunta cikin nashi,massaging it gently yace kar ki damu family over everything,work can wait.

Murmushi tayi tace dama Sadeeq ne yace yana so a bashi rana iyayen shi suzo a nema masa auren Jay.

Murmushi yayi shima yace masha Allah,ai dama haka muke fata kira man ita.

Waya ta dauka ta kira ta tace tazo parlour dad yana kiranta.

Yan mintuna kadan tayi sallama,aka bata izinin shiga sannan ta shigo ta nemi wuri a gefen qafafun dad ta zauna.

Tace dad gani,kallonta yayi for some seconds sannan yace tambayar ki nake son yi tace toh dad.

Wannan yaron Sadeeq da mamanki tace yana son zai turo iyayen shi suxo nema mashi auranki ke kika bashi dama?

Shiru tayi for almost a minute sannan ta bude baki da qyar tace eh.

Murmushi yayi yace toh ba damuwa,kafin iyayen nashi suzo zanyi bincike akan shi sosai in shaa Allah.

Shi kuma ki fada mashi ya sanar da iyayen shi ranar Saturday da yamma sai suxo.

Qasa ta qara yi da kanta sannan tace toh in shaa Allah zan fada mashi.

Shafa kanta yayi yace shikenan tashi kije Allah yayi maki albarka ameen tace sannan tayi masu sai da safe..................................


Juyi safiyyah take tayi akan gado amma ta kasa bacci, tafi minti hamsin da kwanciya amma bacci ya gagari idanunta.

A hankali ta sakko daga kan gadon ta shiga toilet,alwala tayi ta fito ta dakko dadduma ta shimdida ta hau kai ta fara sallah.

Ita  kanta bata san iya kar sallolin da tayi ba,sai da taga lokaci ya ja sosai sannan tayi sallama ta daga hannayenta sama tace.

La ilaha illallahu wahdahu la sharika lah, lahul-mulku wa lahul-hamd, wa huwa 'ala kulli shay'in qadir. 

Allahumma inni as'aluka bi-anna laka al-hamd, la ilaha illa Anta, Al-Mannan, Badi'us-samawati wal-ard, Dhul-Jalali wal-Ikram, Ya Hayyu Ya Qayyum.

Ni mai laifi ce ya Allah,ni mai tarin zunubai ce, amma kuma kai mai gafara ne,Allah kayi mana alqawari cikin suratul Zumar,

Qul yā 'ibādiyal-ladhīna asrafū 'alā anfusihim lā taqnaṭū min raḥmatillāh, innallāha yaghfirudh-dhunūba jamī'ā,innahu huwa al-Ghafūru ar-Raḥīm.

Allah ka yafe man,na bari san zuciya da rudin shaidan sun kusa kaini ga halaka.

Kaico na dana watsar da tarbiyar da aka yi man na bi son zuciya.

Allah na roqeka ka yafe man ta qarasa fada tana kuka.

Ta bude baki zata cigaba kuka yaci qarfinta sai durqusar da kanta tayi aka sallayar ta cigaba da kuka.......................………..


Zaune yake akan couch a study room dinshi da drawing materials akan table.

Wani contract aka bashi na ginin wani company amma da ya dora pencil da nufin zana wani abu hankalin shi gaba daya zai bar wurin.

Ganin ya kasa yin komai yasa ya rufe materials dinsa na zanen da system dinshi  yace i need some fresh air.

fitowa yayi daga study room din ya wuce dakinshi,wayar sa ya dauka yayi dialling wata number bayan an daga yayi magana sannan ya kashe.

A gurguje yayi wanka ya fito ,bayan ya fito ya shafa lotion dinshi sannan ya dakko rough white pattern cargo-pockets shorts ya saka sannan ya dakko black armless shirt na company Nike ya saka,Ludovica suede loafers ya saka sannan ya dauki wayoyin shi da makullin mota ya fito.

Tunda ya hau kan titi bai tsaya ko ina ba sai a Lagos Polo Club,dake ikoyi.

Bayan ya qarasa wurin yayi parking motar shi, ya dade zaune a cikin motar kafin ya fito.

Yana fitowa ya wuce ciki,suka gaisa da few staffs dake wurin kafin ya wuce wurin dokin shi.

Yana zuwa wanda yake kula mashi da dokin yace barka da zuwa ran ka ya dade yawwa iliyasu an gama shirya Rumi?

Ya tambaya,eh yallabai tunda ka kira kace zaka zo  na shirya shi,tohm ba damuwa.


Helmet dinshi ya bashi ya saka sannan ya qarasa inda Rumi yake.

Qosasshen doki ne Kyakyawa baqi,hannu ya dora akan wuyan shi yana zagayawa dashi,ai kuwa sai ya dan motsa kafadunshi alamun ya gane shi murmushi yayi yace kayi missing dina ko Rumi?.

Yana gama fadin haka yayi adjusting helmet din ya hau kan dokinshi ya ja siddin dokin ya fara tafiya.

Zaune take ita da friend dinta sunxo kallon race kaman ance ta daga idonta ta hango shi yana gudu akan doki.

She don't know she was staring at him until her friend nudge her.

What are you staring at?ta tambaya.

Ina guy din nan da muka taba haduwa dashi a Bococho beach har nace maki mun qara haduwa dashi an airport din Abuja?

Eh what about him?

Shine fah na gani ya wuce yanxu akan doki.

Let me go and meet him,kin san how badly i want to see him.

Let me get going kafin na rasa dama ta,ok sai kin dawo.

Adjusting silk vintage scarf din dake kanta tayi ta nufi inda HAYDAR yake.

Tun daga nesa ya hango ta tana tahowa inda yake, kuma ya gane ta amma sai yayi kamar ma shi kadai ne a kaf fadin wurin.

Tana zuwa inda yake tace excuse me,ko arziqin kallo bata samu ba hakan bai dameta ba ta cigaba i don't know if you remember me,we met in Bococho beach few months back.

Ganin yaqi cewa komai yasa tayi murmushin yaqe tace and then again at Nnamdi Azikiwe airport in Abuja.

Nan ma bai ce mata komai ba, actually ta cigaba tana murmushin yaqen this is the third time I've seen you. 

At this point, I'm starting to think fate is trying to tell me something.

Irin kallon baki ma da hankali yayi mata sannan ya bar wurin ba tare da yace mata qala ba.

Banda ta taba ji yayi magana an airport da zata iya cewa kurma ne shi.

Haka nan ta koma wurin friend dinta ba tare da ta nuna mata komai ba but deep down she's disappointed.

Yana shiga cikin motar shi yayi letting out a sigh of relief sannan yayi reverse ya dauki hanyar da zata maida shi gidan shi...........….


Meemarh ce zaune a downstairs tana kallon TV bayan ta gama breakfast.

Tana zaune tana ta jiran taga fitowar Billy amma shiru.

Dakin Billy ta shiga ganin har rana tayi amma bata fito ko breakfast tayi ba.

Tana shiga ta tarar da ita akan gadonta riqe da wayarta,tana ganin Meemarh ta aje wayar tace welcome Meemarh.

Bata amsa ba ta kai hannu kan goshinta ta taba amma taji babu zafi sai tace what's wrong with you sweetie?

Nothing is wrong with me Meemarh,ok but why didn't you come down for breakfast?

Bata amsa ba tace please Meemarh allow me to visit my friend's house.

Gane dalilin da yasa taqi sakkowa taci abinci,ranta ne ya baci bata san lokacin data daka mata tsawa ba.

Ta kira ta da ai nihin sunan ta tace BILKISU!BILKISU!BILKISU!.

Sosai ta firgita da irin kiran da Meemarh tayi mata hakan yasa ta rakube a jikin gado.

Bata lura da halin da Billy ta shiga ba ta cigaba da cewa i repeat myself you are not going anywhere.

Sai bayan ta gama fadan ne sannan ta lura da yanda Billy take ta zare ido ta rakube a jikin gado.

Sai a lokacin itama taji babu dadi,qarasawa tayi kan gadon ta riqeta tace I'm sorry sweetie.

Shiru tayi  tana kallonta bata dai ce mata komai ba,itama shiru tayi sai kuma tace ok i will let you go but on one condition.

Jin tace haka yasa tayi murmushi tace what condition Meemarh?

You must say you want to visit your friend's house in hausa.

Dariya tayi tace ok,Meemarh please je ina so my aboki house.

Bata san lokacin da ta fara dariya ba tace gaskiya sweetie I will hire someone to teach you hausa.

You are terrible in speaking it,zaman Canada ya bata man ke.

Oya get ready i will ask the driver to take you there.

Rungumeta tayi tace thank you so much Meemarh.

Murmushi kawai tayi ta girgiza kai ta fita daga dakin.

Qasa ta sauka tasa mai aikinta ta fada ma driver dinsu zai kai Billy anguwa.

Tana zama ko minti biyu bata yi da zama ba sai ga Billy ta fito shirye cikin wata baqar abaya tayi rolling veil din a kanta tana riqe da channel bag a hannunta.

Abinka ga farar ce gashi ta saka baqin abu,sai tayi kyau sosai Meemarh na ganin tace tabarkAllah Masha Allah.

You look good sweetie hugging dinta tayi tace thank you so much Meemarh.

Best mom ever,tana gama fadin haka tace bye see you later.

Girgiza kai kawai tayi ganin har ta fita,tana fitowa compound ta tarar driver dinsu yana jiranta.

Gaishe da ita yayi cikin girmamawa itama ta mayar masa da gaisuwar.

Suna hawa kan titi ya juyo ya kalleta yace where are we going to ma'am?.

sai a lokacin ta tuna bata san anguwar su Jay ba hakan yasa ta dakko wayarta daga cikin handbag dinta tayi dialling number Jay.....................................................