ALIYU HAYDAR

Chapter 17

by @nieemartullah

Ya na yin parking ya ga  motar zannur a parking lot alamun ya zo gidan,wa ni sanyi ya ji a ranshi da ma he's looking for someone to rant to,ya na buɗe qofar parlour ya ga zannur zaune a kan kujera ya na danna waya.

Babu gaisuwa babu komai yace "wai meyasa wa su matan nowadays ba su da kunya? su na mantawa da qimar su da darajar su ta 'ya'ya mata ne? can you imagine yarinyar nan da muka haɗu da ita a airport na qara haɗuwa da ita yau,she even has the guts to approach me,ta na yi man magana kaman wani sa'anta.

Dariyar da bai shirya yin ta ba ya yi,ya ce and kai kuma mai kace mata?ganin ya maida shi ɗan iska ya sa ya yi tsaki ya zauna akan kujera yana kaɗa  qafa,gefen shi ya zauna yana cigaba da dariya, kawai yana imagining scene din ne.

Tsaki ya qara yi ya ce joke aside,I'm not in the mood to play zannur,ganin how serious he is ya sa ya dena dariyar ya ce ,alright amma me kace mata da tayi maka magana?kallon banxa yayi mashi yace kana tunanin zan kula tane?mata masu aji ma ban kula ba sai wannan da nake mata kallon mara sanin qimar kanta ita zan kula?.
Soyayyar gasiya ɗaya ce kuma na riga da na bada ita,babu wani sauran space da ya rage a cikin zauciya ta da zan iya qara bawa wata 'ya mace, naso Hazely so irin wanda bazan iya qara yi ma wata irin shi ba kuma har qarshen rayuwa ta ba na fatan na qara son wata ya mace idan ba hazely ba,ita kadai zuciya taso,ita kaɗai zuciya ta za ta so,kuma ita kaɗai za ta cigaba da so har qarshen numfashi na.

Yanayin yadda yayi maganar da karyayyiyar murya kaman me shirin yin kuka ya ba ma Zannur tausayi, hakan ya sa yayi keeping serious face ya ce meyasa ba za ka qara tunkarar ta a karo na biyu ka yi mata magana ba?.

Murmushin da ya fi kuka ciwo ya yi irin wanda duk wanda ya gani yasan ciwo ne ake qoqarin danne shi da murmushi,ya ce ina ganin kaman duk duniyar nan babu wanda ya kai ni sanin halin hazely,ko mamanta bana jin ta kaini sanin cikakken halayyar ta,ba za ta taba amincewa ba,ko da kuwa soyayyata za ta za ma ajalin ta.

Na bar ma Allah komai don yafi ni sanin abinda ya da ce da ni,kuma Allah ba ya sabon aiki duk wa ni abu da ka ga ya faru dama a rubuce ya ke zai faru tun kafin ma nazo duniyar nan don haka ka dai na ɗaga hankalin ka.
Rasa abinda zai ce ya yi don haka ya girgiza kai ya ce Allah ya shiga cikin al'amarinku.Ameen ya ce suka canja wata hirar....................................

Qarfe sha biyu da yan mintuna driver ɗin ta ya yi parking a dai dai in da Jay ta bata address din, horn suka yi ma maigadi ya fito ya buɗe masu, bayan driver ya ga ma dai dai ta parking ɗin ta fito.

Entrance ɗin gidan ta nufa,ta na zuwa qofar parlour ta danna doorbell,aunty Naja ce ta buɗe mata qofar ta bata hanya ta na mata sannu da zuwa,murmushi tayi tace thank you, ta ga kamar welcoming din ta take yi.

Kujera ta nuna mata tace ta zauna,sannan ta ce wa za'a cema ya yi baquwa?sheqeqe ta tsaya tana kallonta don bata gane me ta ce ba,murmushi ta qara yi ta ce I'm sorry,i did not understand what you said.

Aunty Naja ta ce toh wannan jikar turawa ce bari na kira mata aunty sai ta tambayeta,kallon Billy ta yi ta nuna mata stairs alamun ta na zuwa, jinjina mata kai Billy ta yi.
Ɗakin  Jay ta je ta yi knocking,bayan an ba ta izinin shiga ta shiga ta gaida Jay da Munarh da ke zaune suna hira,mayar ma ta da gaisuwar su ma su ka yi,murmushi ta yi ta ce toh aunty kun yi baquwa, ban dai san wurin wa ta zo ba ta na nan a qasa ina jin dai jikar Elizabeth ce.

Dariya Munarh ta yi ta ce kai aunty,wai jikar Elizabeth, ita ma dariyar ta yi ta ce eh mana,ai na yi mata hausa amma na ga kaman ba ta jin hausa sai turanci take yi,murmushin gefen baki Jay ta yi ta ce toh aunty Naja bari nazo.

Kimono ta ɗora akan wandon three quarter da T-shirts din da ke jikin ta, sannan ta fito.

Ta na sakkowa ta ga Billy zaune a kan kujera, bude idanun ta ta yi da alamun mamaki ta ce wallahi I thought you are joking,when you asked me for the address.

Dariya Billy tayi ta ce Laa, I'm not joking. I'm even on the road when I asked you for the address.

Hugging din ta Jay tayi sannan ta zauna a kujerar da ke gefen ta ta ce welcome sweetie,murmushi ta yi ta ce thank you aunty Jay.

Aunty Naja ce ta fito daga kitchen riqe da tray ta dora ruwa da snacks akai,aje shi tayi a kan centre table ta ce ashe ma wurin ki tazo aunty dariya Jay ta yi ta ce baquwa ta ce aunty Naja,sannan ta juya ta ta fi.

Billy ce ta kalli Jay ta ce is mummy around?so that i will go and greet her.

Ohh mom let me call her.

Sama ta wuce yan mintuna kadan sai ga su sun dawo tare da mom.

Kujera mai zaman mutum ɗaya ta zauna a kai, ɗan zamo wa ta yi daga kan kujerar da take zaune ta ce good afternoon maa.

Mom da tunda ta fito parlourn take kallon Billy tace afternoon dear how are you?.
I'm fine maa.

Gyada kai tayi tace glad to hear that.

Bayan ta ɗan zauna for some minutes ta yi excusing kan ta ta tashi ta koma ɗakin ta.

Amma tunda ta koma ɗakin ta ta ke ta tunanin inda ta san fuskar don tabbas ta san me irin fuskar,ko kuma ta yi mata kama da wadda ta sani..........................................................

Sadeeq ne ya sami baban su a parlour,gaishe da shi yayi sannan ya zauna.

Kallon shi mahaifin shi yayi bayan ya amsa gaisuwar ya ce baba na ya aiki? Alhamdulillah Abbah,dama akan maganar da kayi min ne four days back.

Gyada kai ya yi ya ce ina jinka.

Dama munyi magana da ita ne take fada min baban nata ya dawo kuma har ma ya bada ranar asabar a ranar da zaku same shi.

Jinjina kai ya yi ya ce Masha Allah, asabar dai ta jibi? Ya tambaya.

Eh Abbah ita.

Toh Masha Allah bari na kira su iyayen naka sai na sanar da su.

Miqewa ya yi ya ce toh Abbah ni zan dan fita, jinjima kai ya yi ya ce a dawo lafiya.

Hira aka yi sosai tsakanin Jay da Billy har Munarh ma ta sakko ita ma aka yi da ita,lokacin da yamma ya yi ta ce a kira mata mom ta yi mata sallama.

Ɗakin Mom Jay ta je ta ce mata Billy za ta tafi ta zo suyi sallama,ɗakin ta ta wuce ta ɗebo chocolate da yawa ta zuba a cikin gift bag.

Sannan ta sakko bayan yan mintuna kaɗan sai ga mom ita ma ta sakko.

Murmushi ta yi bayan ta sakko, Billy ta dan sunkuya tace i'm going mom.

So soon?

Murmshi ita ma ta yi ta ce  I have to go if not Meemarh will never allow me to come again.

Jinjina mata kai ta yi tace she has her reasons. Wata decorated paper bag ta miqa mata ta ce greet her for me.

Karɓa ta yi ta ce thank you so much mom.

Murmushi ta qara yi ta ce it's my pleasure.

Jay da Munarh ne suka fita raka ta a compound suka ga driver ɗin da ya kawo ta yana zaune a cikin mota yana jiran ta.

Hugging Jay ta yi ta ce thank you so much aunty Jay it's nice spending my evening with you.

Hugging na ta back tayi ta ce same here sweetie.

Gift bag din hannun ta ta bata ta ce it's not much.

Karɓa tayi ta qara yi mata godiya sannan driver ɗin ta ya ja suka bar gidan.

Kuka ta cigaba da yi mai taɓa zuciyar me sauraro, tana ta tuna abubuwan da ta ringa aikatawa,tana ta addu'ar Allah ya yafe mata,locaci ta duba taga qarfe uku da minti bakwai na dare,tasan a irin wannan lokacin momma ta tashi tana qiyamul layli don haka ta dauki wayar ta tayi dialling number ta.

Ringing biyu Momma ta daga ta yi sallama da qyar Safiyyah ta iya buɗe baki ta amsa mata,da damuwa tace Safiyyah lafiya na ji muryar ki a haka? Me ke faruwa? Ko ba ki da lafiya ne? Ta jero mata wannan tambayoyin.

Shiru Safiyyah ta yi ta kasa cewa komai da farko, sai kuma ta ce don Allah Momma ki yafe man,ina cikin damuwa wallahi na kasa samun kwanciyar hankali.

Daga dayan bangaren Momma tace ni na san kina cikin damuwa Safiyyah amma ya zan yi tunda kin qi faɗa man damuwar ki?

Momma ba wai na qi fada maki bane,a'a ban san ta ina zan fara bane,amma yanxu ya zama dole na fada maki,saboda bani da wata mafita.

Amma ba magana bace da za'a yi a waya,gobe in shaa Allah zan dawo gidan sai muyi magana.
Kin san ba na son yawo,jiya kin zo gobe ma ki ce zaki dawo? Ki bari zan zo gidan naki da kaina gobe in shaa Allah.

Toh ta ce mata sannan ta kashe wayar.