🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
🅿️—–58
Bayan an ɗauke Amina daga cikin akwatin waɗanda ake tuhuma
Ta tsaya cak
Idanunta suka sauka kan Barrister Suhail
Hawaye ne kawai ke zubo mata
Ta kasa furta ko da kalma ɗaya
A hankali ta taka zuwa gabansa
Ta haɗe hannayenta waje guda, kuka mai tsuma zuciya ya hana ta furta abin da ke bakinta
Ta rasa kalmar da ta dace ta gode wa wannan bawan Allah da ya jajirce wajen kare ta
A ganinta, ko ta yi masa godiya har tsawon rayuwarta ba za ta biya masa wannan alheri ba
Da ƙyar ta buɗe baki cikin rawar murya ta ce
“yaya Suhail nagode"
a yadda tayi kira sunan sa sai yaji kamar iman ita kadai ce ke kiran sa a haka
Ta share hawayen da suka cika fuskarta kafin ta ci gaba
“Nagode da ka ceci rayuwata"
“Nagode da ka sake ba ni damar rayuwa cikin ’yanci, ba tare da mutane suna kallona a matsayin matar da ta kashe mijinta ba.”
Ta yi shiru na ɗan lokaci, ta haɗiye wani irin kuka mai zafi
Sannan ta ɗaga idanunta da suka yi ja saboda kuka ta ce
“Wallahi sau da yawa ina jin kamar mutuwa ce kawai mafita a gare ni"
“Amma ban taɓa fatan mutuwa da wannan mummunan zargi a kaina ba.”
“Na yi ta roƙon Allah Ya bayyana gaskiya kafin ranar da zan rufe idona har abada, domin ina jin a jikina rayuwata na gab da ƙarewa"
Gaba ɗaya Suhail ya yi tsit
Kallon Amina kawai yake yi
Da farko ya yi zaton firgici da wahalar da ta sha ne suka sa take wannan maganar
Sai dai da ya ga yadda take magana cikin nutsuwa da cikakken hankali, ya fahimci cewa abin da take faɗa daga zuciyarta yake fitowa.
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali, sannan ya ce
“Amina, ki gode wa Allah kafin ki godeman sannan Mahaifiyar ki tayi kokari sosai a kanki"
“Ni kuwa, aikin da Allah Ya ɗora mini kawai na yi"
A dai-dai wannan lokacin mahaifiyar Amina ta ƙaraso da sauri
Ta durƙusa gabansa tana ƙoƙarin kama ƙafafunsa
Da sauri Suhail ya kama hannunta ya ɗaga ta tsaye
“Haba Hajiyame kike ƙoƙarin yi haka?”
Cikin kuka ta ce
“Nagode Barrister Allah Ya saka maka da Aljannatul Firdausi"
Murmushi ya yi
“Amin Mama"
“Sai ku ci gaba da gode wa Allah. Shi ne Ya ba mu nasara"
“Sannan ya kamata ku tafi kada dare ya yi"
Amina da mahaifiyarta suka yi masa sallama cike da farin ciki
Sama’ila ma ya ƙaraso
Ya miƙa masa hannu suka gaisa
“Barrister, Allah Ya saka da alheri Da ba kai ba da gaskiya ba ta bayyana ba"
Suhail ya yi murmushi
“A’a, Sama’ila Kai ne jarumin wannan shari’a Da ba ka yi ƙarfin halin fitowa ka faɗi gaskiya ba, da har yanzu Amina tana gidan yari"
Ya ciro kuɗin mota ya miƙa masa
Sannan ya ba shi lambarsa
“Duk lokacin da ka ji kamar rayuwarka na cikin haɗari, ka kira ni kai tsaye"
Idanun Sama’ila suka cicciko da hawaye
bai taɓa haduwa da mutumin kirki irin Suhail ba shiyasa har ransa ya kauna cesa basan komai sai yadda ya mu'amallacen sa duk da matsayin su ba daya ba amman suhail ya jasa a ciki
“Na gode Barrister"
Daga nan kowa ya kama hanyarsa, zuciyoyinsu cike da farin cikin nasarar da Allah Ya ba su.
⸻
A gefe guda kuwa
Jaru sai ihu take yi
“Ban kashe kowa ba!”
“Wallahi ban kashe kowa ba!”
Amma babu wanda ya saurare ta
Jami’an tsaro suka kai ta inda aka tsare Salisu
Da aka buɗe ƙofar cell ɗin aka tura ta ciki
Salisu ya miƙe a firgice
“Tsohuwa Me ya kawo ki nan?”
Cikin kuka Jaru ta ba shi labarin duk abin da ya faru a kotu
Shiru ya yi na wasu daƙiƙu.
Sai ya kalleta da idanu cike da baƙin ciki
“Kin ga bala’in da kika jefa mu a ciki?”
“Tun farko ke kika kawo wannan muguwar shawarar"
Jaru ta dafe ƙirji
“Salisu ni kake faɗa wa haka? Ai saboda ku na yi komai"
A fusace ya ce
“Ƙarya kike, munafuka!”
Jaru ta zaro ido
“Salisu! Ni kake kira da munafuka?”
Ya matso kusa da ita
“Wallahi, faɗa miki munafuka ma kaɗan ne"
“Ke ce kika lalata rayuwarmu.”
“Kin haifi yara fiye da goma, amma babu ko ɗaya da ya tashi cikin tarbiyya"
“Wasu ’yan daba ne, wasu barayi ne, wasu ’yan shaye-shaye ne, matan ma kowacce ta kama gabanta"
“Duk wannan kuwa saboda gazawar da kika yi wajen rainonmu da bamu tarbiyyar data dace"
“Wallahi Allah Ya isa tsakanina da ke"
“Ba zan taɓa yafe miki halin da kika jefa rayuwata a ciki ba"
Kuka ya ci ƙarfin Jaru
Ta fashe da rusa kuka a tare
Amma Salisu bai saurare ta ba
Cikin fushi ya mare ta mari lafiyyayu har biyu
“Ni ne zan yi kuka, ba ke ba!”
Ihun Jaru ya sa jami’an tsaro suka yi saurin shigowa
Nan take suka raba su zuwa cells daban-daban
aka kulle Salisu shi kaɗai
Ya jingina da bango
Hawaye suka fara gangarowa daga idanunsa
A karon farko cikin rayuwarsa
Ya gane cewa nadama ba ta da amfani idan hukunci ya riga ya ƙure
Suhail na barin kotu ta ya kama hanyar gida Allah Allah yake ya koma ya fadawa iman an saki Amina har ta koma garin su
a kofar gida ya bar motar ya shiga ciki babu kowa a falo sai karar Ac da tv
ya nufi dakin iman tana kwance kan gado tana game lokacin zuwa lokacin bikin duba agogo a zuciyar ta tana tunanin ko an gama Shari'ah
taji karar kofa duban takai ga Suhail dake shigowa fuskar dauke da murmushi da sauri ta miƙe ta ajiye wayar
"yaya Suhail,an gama Shari'ar"
gefen fuskar ta ya dan riƙe a hankali ya ce"done and dusted yanzu haka Amina ta kama hanyar garin su she is free"
bata san lokacin da ta rungume sa ba tare da fadin"i know my husband can did it well congratulation Sweetheart for wining the case"
ta jima haka kafin ta raba jikin sa da nasa tare da rufe fuskar ta da tafin hannu daga karshe ma ta shige bandaki
suhail ya girgiza kansa yana murmushi
ya koma dakin sa
Bayan Amina da mahaifiyar ta sun iso garin tsauni...........
share
like
comment
khadywrite👌ta kuce