6. Feelings
Gaba ɗaya hankalin shi na kan laptop ɗin da yake ta faman latsawa irin na ƙwararrun mutanen da suka iya keyboard. Bayan kamar rabin awa yayi shutting down laptop ɗin tare da rufe murfin ta, ya ɗauke ta daga kan cinyoyin shi sannan ya ajiye kan karamin table.
Ya miƙa hannu ya dauki wayar shi dake kusa. Whatsapp ya shiga a lokacin da ya lura messages ɗinda yake dasu nada yawa.
Cikin messages ɗin akwai saƙonni na mata daga ƙasashen waje da kuma nan Nigeria da suke damunsa da sunan soyayya.
Wassu a cikinsu suce mishi yana da kyau sosai ya auresu, wassu kuma suce mishi zasu iya ɗebe masa kewa idan ya kasance tare dasu, banda masu tambayar shi ya tura musu hotunan shi.
Dalilin hakan yasa yake da layin kira daba sannan na social media daban.
Ya buɗe messages masu muhimmanci a cikinsu ya karanta tare da yin reply, sauran kuma ya barsu. Ya shiga duba status uploads har yakai na Hasina, ya fara viewing pictures ɗinda tayi uploading. Duk hotunan birthday ɗinta ne da tayi jiya.
Hoton farko Hasina ce tsaye a gaban cake ɗinta. Tayi kyau sosai. Ya kalla yayi murmushi tare da faɗin, “My princess.”
Ya wuce hoto na biyu yaga ita da ƙawayen ta ne sunyi group hug suna dariya. Sai yaga kamar ya hango Maryama a cikin su.
Hannun shi dake riƙe da wayar ya tsayar na ɗan lokaci kafin ya sake dubawa da kyau.
Ita ɗin ce.
Wani irin nutsatstsen yanayi yaji ya ratsa shi a hankali.
Ya ɗauki ɗan lokaci yana kallon hoton sannan ya wuce na ukun. Hasina ce da Maryama suna cute smiling. Najib ya kalli Maryama a hoton. Kyakkyawa ce sosai, ya faɗa a zuciyar sa.
Doguwar yatsarsa yasa akan screen ɗin wayar don kada hoton ya wuce, yana mai sake kallon Maryama. Tayi shigar atamfa tayi dauri mai kyau, kwalliyar fuskarta baiyi yawa ba.
Murmushi ya sakar daya tuna abinda ya faru tsakanin su. Sam bai lura da ita ba har yakai ga sukayi karo da juna, kuma ya tabbata cewa itama bata lura da shi ba.
A jiya daya ganta yayi mamaki sosai. Bai taɓa zaton zai sake ganinta ba dalilin rashin sanin ita wacece. Yana ganin fuskarta yasan tabbas itace yarinyar daya gani a dinner ɗin bikin abokin shi Habib.
Farin ciki haɗe da mamaki, sune suka mamaye shi a lokacin. Tun ranar daya fara ganin ta yaji wassu feelings ɗinda zai iya cewa bai taɓa ji akan wata 'ya mace ba. Sau tari yayi tunanin hanyar da zai sake ganin ta, hanyar da zai san ita wacece, sai gashi Allah ya sake haɗasu.
Wani sabon mamaki yaji sanda Hasina ke ce masa ai Maryama ita ce ƙawarta da take yawan bashi labari a waya.
Ya tuna ya fara tozali da ita ne a wajen dinner lokacin da ta wuce inda yake zaune har ta isa table ɗin data zauna. Yana sane da lokacin da ta ɗauko wayarta ta fara recording video har zuwa sanda tasan da zamansa a gurin.
Yaso ace yaje ya sameta,
yaso ace sunyi magana da juna.
Amma hakan bata faru ba dalilin introducing ɗinshi da Habib yayi da wata ƙanwarsa, Hauwa.
Bai san ya kwashi lokaci yana kallon hoton Maryama a screen ɗin wayar shi ba sai daya ji yatsarsa ta fara masa nauyi. Screenshot yayi, hoton Maryama ya koma gallery cikin wayarsa sannan ya fita daga Whatsapp ya duba lokaci.
Karfe sha biyu daidai na rana ya nuna a screen ɗin wayarsa. Tun asuba daya dawo daga masallacin harabar gidansu yake ɗaki yana aikin bacci, sakamakon raba dare dayayi kamar yadda ya saba saboda gudanar da aiyukan sa.
Yunwa kuma baya wani jinta saboda yaci abinci cikin dare tare da coffee daya haɗa ya hauro dashi. Shiyasa ko breakfast baiyi ba yaci gaba da baccin sa har sai daya farka.
Ya miƙe ya shiga wanka sannan ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya. Yau ne ya kamata ya fita cikin gari ya haɗu da abokansa kamar yadda suka saba aduk sanda ya dawo gida Nigeria.
Key ɗin motoci biyu ya ɗauka, ɗaya na motar daya kai Maryama gida ɗayan kuma na wata motar. Ya zubawa key ɗin motar daya kai Maryama idanu.
Da alama yarinyar tana da kunya sosai.
Yana sane tana son yin magana sanda zai kaita gida a daren jiya amma ta gagara furta cikakkiyar jimla.
Yasan adress ɗin gidansu Maryama ne daya tambayi mahaifiyar shi kafin ya fito ya kaita. Yayi hakan domin ya rage fargaban dake tsakanin su, domin tabbas yaga alamar tana feeling awkward sosai.
Da tunanin ta ya fice daga ɗakinsa yayi ƙasa gurin mai wanke musu motocin gidan. Da zuwansa ya damƙa wa mai wankin mota key ɗin motar daya fita da ita jiya da daddare sannan ya koma cikin gida yayi sashen iyayen sa ya gaishe dasu.
Ɗakin mahaifin sa ya fara zuwa sannan ya shiga na mahaifiyar sa. Bayan sun gaisa Hajiya Bilkisu ta dubi ɗanta.
"Yanzu Najib haka zaka yi ta raba dare kana aiki? Yau ma bakayi breakfast ba kuma nasan yanzu fita zakayi ba tare da ka tsaya kaci na rana ba. Nikam wallahi kana sani cikin damuwa."
Cikin ladabi yace, "Ummi kada ki rinƙa damuwa akan hakan. Nakan ci abinci cikin dare idan nasan zanyi aiki. Kinga ai yunwa bazai dameni ba. Bana so aiki yamin yawa ne shiyasa nake ragewa kafin na koma."
"Yaushe zaka koma?"
"Maybe next week."
"Ka ƙara ko da sati biyu mana, ai kaga ka kyauta min sosai ko? Sannan ga Ramadan ma zai dawo cikin kwanakin nan, gida zai cika kuma zan kasance cikin farin."
Najib yayi jim sannan yace,
"Toh shikenan Ummi. Just for you."
Hajiya Bilkisu tayi murmushin jin daɗi.
"Yauwwa ko kai fa? Allah ya maka albarka." Ya amsa mata da ameen.
"Batun aikin ka kuma Sai kayi haƙuri mataimakin ka ya rinƙa tayaka daga can Canada duk da nasan kafi so kayi yawancin aikin. Kaga ai zaka ɗan samu hutu.
Don gaskiya bana son rashin baccin ka da kuma rashin yin breakfast tare damu."
Ya murmusa yace, "To Ummi, hakan za'ayi. Zan canza na fara yi da sassafe. Idan na gaji ban gama ba zan bari sai washe gari. Wassu ayyukan kuma sai a rinƙa tackling daga can.”
"Yauwwa ɗana nawa na kaina, kana faranta min rai sosai.” Sukayi dariya. Sai tayi jim, alamar tana son ƙara faɗan wani abu. Najib yayi shiru yana kallon ta yana jira.
“Sai kuma batun auren ka…,”
Najib ya runtse idanu yayi dariya mai sauti ciki ciki a lokacin da faffaɗan kafaɗunsa ke motsawa.
“…akwai 'yan mata 'yan uwana masu kyau sosai daga Maiduguri.”
“Umm?” Yace ya ɓude idanun sa tare da ɗago gira.
“Ya kamata ka zaɓi ɗaya daga cikin su ayi muku aure. Akwai Jamila, yarinyar tanada hankali sosai, ga kirki. Zaka fi dacewa da ita."
Yasan dama zata kawo maganar aure, don sau tari takan kawo masa maganar a waya. Bare kuma yanzu da gashi gata.
"Ummi, zamuyi wannan maganar wani lokaci kiyi haƙuri."
Ta kalle shi cikin damuwa. "Najib na damu da kayi aure. Kaga idan kayi aure zaka samu canji da rayuwar aikin nan. Ko da yaushe priority ɗinka aiki.
A duk sanda kayi aure ka tuna kana da iyali, zaka sauƙaƙe ma kanka kada wani abu ya shige maka lokacin kulawa da kuma kasancewa tare da iyalin ka.
Sannan na kwaɗaita da naga 'yan jikanu na suna wasa. Ya kamata ka rinƙa sauraro na idan ina maka maganar auren nan."
Najib yayi ajiyar zuciya.
"Ummi ki daina damuwa akan wannan. Ina kula da kaina sosai, kuma Inn shaa Allah zanyi aure nan bada daɗewa ba. Bana so naji kina cewa kina cikin damuwa."
Ta dube shi cikin rashin yarda.
Nan bada daɗewa ba?
To ko da wasa bata taɓa jin labarin yana da wata budurwa ba. Ai idan ba haɗashi tayi da wata ba sai yayi mata tawaye.
“Toh shikenan..., yanzu ina zaka?"
"Zani mu gaisa da abokai nane. Daga can zanci abinci. Kada ki damu Ummi, bazan zauna da yunwa ba."
Ya mike daga zaman dayayi a carpet ɗinda ke shimfiɗe ƙasan floor sannan ya mata sallama ya fice. Yana fita waje yayi rumfar parking na motoci yana duba motar da ƙaramar remote ɗinta ke hannun shi.
Yafi son shiga motar daya bayar a wanke amma yasan mai wankin motar bazai gama yanzu ba shiyasa kawai ya ɗauki key ɗin wata motar. Ya danna remote ɗin a lokacin da motar tayi ƙara. Yana shirin shiga yaji ana fadin,
"Rankaya daɗe! Rankaya daɗe!!”
Ya juya yaga mai wankin mota ne yake zuwa inda yake cikin sauri mai haɗe da gudu. Yana isowa daf dashi ya fara cewa,
"Allah taimake ka. Allah ja zamanin ka dan gidan Alhaji." Najib ya dube shi yace,
"Ameen ameen. Ya dai lafiya ko? Na ganka a tafe cikin sauri. Wani abu ya faru ne?”
"Rankaya daɗe babu wata damuwa. Dama wannan 'yar sarkar ce na tsinta cikin motar daka bani na wanke. Ina cikin wankin motar na hango ka zaka fice shine nace bari nayi maza na kawo maka."
Mai wankin mota ya miƙawa Najib ƙaramar sarƙa, Najib yasa hannu ya karɓa. Sarkar hannu ce mai kyau da dauƙan ido. Kallo ɗaya zakayi kasan asalin zinari ne.
Sai yaga kamar ya taɓa ganin sarkar a wani guri. Ya ɗan tsaya yana tunani.
Wayarsa ya ɗauko daga front pocket ya buɗe ya shiga screenshots. Yana duba hoton farko yaga tabbas sarƙar ce zagaye a hannun Maryama data dafa Hasina.
Ya dubi mai wankin mota dake tsaye a kusa dashi, kayan jikin sa ya ɗan jiƙe, fuskarsa ɗauke yake da faffaɗan murmushi a lokacin da haƙoran sa da suka ɗan rine suka baiyyana.
Najib ya ciro da wassu ‘yan kuɗaɗe daga wallet ɗinshi ya miƙa masa.
Cikin zumuɗi ya karɓa tare da yin godiya bila adadin sannan ya wuce yaci gaba da aikin sa. Najib ya saka sarƙar hannun cikin jeans pocket ɗinshi sannan ya shige mota yayi cikin gari gurin abokan sa.