A Weekend To Remember
by @zahrabmrs
Washegari da safe bayan sun gama breakfast , Anty Zaheera ta yanke shawarar su fita da Tadala ɗan yawon Abuja kafin ta koma gida .Bayan kusan rabin awa, motarsu ta shiga harabar Millennium Park suka fito iska mai sanyi da ƙamshin ciyayi suka tarbe su, Wurin Cike da mutane wasu suna picnic, wasu outing,ga yara sai wasan su suke ,tadala kuwa jinta tayi a new world .
mardiyya pls muje ki rakani na hau lilo ,mardiyya tayi rolling ido da girman ki zaki hau lilo tadala ?muje mu hau tare tadala wai ita idan an barta ta zama big girl tafi Karfin hawa lilo Ameerah ta fada Tana Jan hannun Tadala ,mardiya na biye dasu Akan ta zama photographer dinsu ,ita dai Tadala bata taba Jin dadi irin na Yau ba ,she has so much fun ,lilona Kala Kala ta hau dan watakila daga Yau bazata kara samun Dama irin Wannan ba
Bayan Sun sauko mardiyya ta masu hotona Kala Kala daga karshe sukayi selfie su ukun Na ɗan lokaci ta manta da komai .zaheerah na gafe tana kallonsu Yarinyar tana da wani irin kyau da natsuwa , tayi kama da wacce bata taɓa samun damar jin daɗin rayuwa ba sai Yau
Suka hada ido da tadala, zaheera ta Kira ta hannu Tadala ta karaso fuskar nan Kamar gonar Auduga .Yauwa tsaya na dauki ki hoto ,Tadala ta gyara tsayuwarta zaheera ta dauke hotona Kala Kala
Anty Nagode sosai ban taba hawa irin wanna lilon ba tunda nake a rayuwata ,Wanda muke hawa agadez irin na karfe ne Wanda ake tura mutum Tadala ta fada Tana tuno da kuruciyart ta ,Zaheera ta numfasa kar ki kara min godiya Tadala ,duk abinda twin yake so Nima Ina daukar sa da mahimanci so kar ki ji komai ,yanzu dai koma Wajan sisters dinki maza suna jiran ki
tadala na tafiya direct ta bude WhatsApp number kamal ta Nemo Twin ❤️short video da pictures din Tadala ta tura masa
A daidai lokacin Alhaji Kamal yana zaune a study ɗinsa yana duba wasu takardu Wayarsa ta yi ƙara ganin daga twin ne yayi saurin buɗe saƙon Wani murmushi ya bayyana a fuskarsa ba tare da ya shirya ba,hotonan tadala ne harda short videos
Ya ajiye takardun da ke hannusa ,so looks so happy a hotonan ,reply yayiwa zaheera Mi dahlia looks so happy zaheera all thanks to you ,within seconds tayi masa reply yeah she looks happy Kamar ta dawo waje na da zama Keda sadiya ba ruwana Nagode for the pictures talk later .
Pictures din da suka dauka Ameerah ta ɗora shi a WhatsApp status tare da rubuta
Weekend with our beautiful Agadez sister ❤️sosai
Gidadon Katsina mansion
Kuna tana kwance a falon Mommy tana duba status har tazo kan Ameerah cousin Kamar yadda tayi saving tana budewa cak ta tsaya Idonta Kamar gizo yake mata ,ta sake duba na gaba ,still dai tadalan ce dasu Ameerah ,wani wawan tsaki taja Mtswwww Shegiya kawai ,Mommy Falmata ta ɗago kai daga littafin da take karantawa Kuna wa kike zagi ?Yaya Ameerah ce ta saka hoton yarinyar nan a status ,Wace yarinya ?Kuna ta turo baki Tadala mana Kamar wata celebrity ,Falmata ta girgiza kai bana son maganar mutane,na hanaki gulma kin ƙi ko?Watarana zan zubar miki da haƙora saboda wannan ɗabi’ar taki yarinyar nan ba ta yi miki komai ba , karatu tazo allow her rest pls ganin yadda mommy ke fada ,kuna tayi gum da bakinta dan yanzu ba karamin Aikin mommy bane ta make ta
Bayan sun gama zagaye park din , Ameerah ta riƙe hannun Tadala ,Kin yi min alkawarin zaki gidana Nima ki min weekend
inshallah zanzo yaya Ameerah Zan sa mardiyyah ta kawo ni
naji Ana kiran sunnana me nayi ?mardiyyah ta karaso rike da Affan din Ameerah a hannunta,Ameera ta kalle ta gulmar ki muke Tadala ki daina biyewa yaya Ameerah gidan ta zata koma ta barni ta dake nice Dahir dai jealousy is that you speaking sosai Ameerah mardiyyah suka birge Tadala yadda suke tsokanar juna amma kuma Akwai respect tsakanin su
A daidai lokacin wayar Zaheera ta yi ƙara twin Ina hanyar zuwa daukar mi dahlia gobe da school
Sun koma gida befi da mintuna talatin ba sai ga baƙar motar Alhaji Kamal ta danno Kai already tadala ta shirya kayanta jikinta a sanyaye take Sam bata son tafiya
Sanye yake cikin shadda sai ƙyalli yake Kamar Sabon Ango ,duk Sun hallara a falo dan kwana biyun nan Sun Saba da tadala daya Bayan daya yaran suka gaishe shi harda Tadala ,idanunsa suka sauka kan ta annurin dake Fuskarta dazu ya gushe ,take Shima yaji mood dinsa ya canza
Zaheera tayiwa su Ameerah inkiya da ido daya Bayan daya suka watse a falon aka bar tadala da dady
muryarsace ta katse shirun ,me ke damunki ne you look lost din tots ?Bana son komawa gida nafi son nan gidan yafi dadi ta fada Kamar zatayi kuka ,Shi Kansa ya Lura she’s lonely a gidansa dan apart from Ahmad ba Wanda yake ganin yana kulata .kar ki damu Indai gidan zaheera duk sanda kika son zuwa awaisu zai dinga kawo ki Kinji ko ?hakan kuwa ba karamin faranta mata rai yayi ba
Har bakin mota yan gidan suka rakasu
Tadala mun gode sosai da ziyara ki gaishe da sadiya ga sakon ki nan a Bayan mota sai na kara ganinki,godiya Tadala tayi ta shiga mota ta zauna a driver’s seat,Alhaji kamal ya kunna motar suka dauki hanya ,jefe jefe suna dan taba hira A daidai lokacin wayarta ta fara ringing Mansoor Calling ba tare da bata lokaci ba ta daukaAllôMansoor Muryar Mansoor ta fito cike da annashuwa Comment vas-tu ma chère?(Yaya kike, masoyiyata?)Tadala ta yi murmushi Je vais très bien. Et toi?
(Ina cikin ƙoshin lafiya. Kai fa?)Très bien. Tu me manques beaucoup Ina lafiya sosai,Ina kewarki ƙwarai.)haka ta biyewa mansoor suna ta hirar soyayya hankalin ta kwance dan tasan dai alhaji kamal ba Jin French yake ba
Ba zato kawai taji ya taka burki da Karfi ,ajiyar wayar tayi ta kalle shi a tsorace ,daddy Lafiya ?Meke faruwa
Fuska ba walwala yace ba komai ,ya cigaba da tuki ,bata taba ganin sa a yanayi irin haka ba ,muryar Mansoor ya dawo da ita daga duniyar tunani Je viendra au Nigeria un jour pour te voir (Wata rana zan zo Najeriya domin ganinki.)Tadala ta yi murmushi D’accord(To shikenan.)
A wannan karon Cikin nutsuwa, ba tare da ya kalle ta ba Alhaji Kamal ya ce Tu parles un très bon français Kin iya Faransanci sosai.)Tadala ta daskare ,Ya ci gaba da kallon hanya ,Je comprends tout ce que vous dites (Ina jin duk abin da kuke faɗa.)ji tayi Kamar ta nutse Sabida kunya,ta saki jiki sai fadawa mansoor kalaman soyayya take cire wayar tayi a mute Ta yi saurin cewa wa MansoorJe te rappellerai plus tard.
(Zan sake kiranka daga baya.)Ta kashe wayar Shiru ya mamaye motar bayan wasu daƙiƙu, cikin sanyin murya tace Ashe kana jin French daddy ?Ya ɗan kalle ta a Paris nayi degree Dina na biyu ba Wanda ya Kara magana har suka Isa gida ,kowa da tunanin dake ransa ,alhaji kamal ji yake Kamar zuciyarsa zata buga yadda Tadala ta zage Tana soyyayah da wani ,ga kalaman da take fadawa mansoor Wanda be taba jinsu a wajanta ba ,suna isa gida ko Kallonta beyi ba ya fice daga motar tare da mikawa awaisu key ,Kafin ma ta karaso falo har ya haye sama ,Tana Jin sadiya na masa magana be amsa ba gabadaya jikin tadala yayi sanyi ,tsaf sadiya ta chaje katuwar ledar ta tadala tace anty Zaheera ta bata tarkacen Kaya ne na mata kala kala ,sadiya ta tabe baki Anjima ki shiga ki nunawa dr kar kice Nina aiko ki
kowa ya hallara a babban teburin cin abinci. Falon ya cika da hayaniyar yaran gidan, Safa da Marwa suna gardama kan wani abu, Zahra da Ahmad na duba abu waya
Kuna Tana gefe as usual alone ,Sai dai wuri ɗaya ne babu kowa Kujerar Daddy.
Tadala ta lura Tun zuwanta gidan, ba ta taɓa ganin yayi missing zuwa dining ba
Falmata ta ɗan ɗaga kai ta kalli kujerar, sannan ta ɗauki wayarta ta kira shi ,Bayan ringing biyu ya ɗaga ,Hellobabban mutum
Na’am, Madam ,Muna dining fa Kowa ya hallara ,Ba zan samu fitowa ba kuci abincin ku kawai ,Falmata ta ɗan gyara zama Lafiya kuwa? Kaina ne yake ciwo kaɗan ta ɗan yamutsa fuska sannu babban mutum ,a aiko maka da magani?
A’a Zan ɗan huta ne kawai
Okay to a huta lafiya ta kashe wayar ta ɗaga kai ta kalli sauran nYace kansa ne yake ciwo ,Dr. Mariya ta ajiye spoon ɗinta Alhaji da ciwon kai? Gskia muje mu duba shi ,ban yarda iya ciwon kai bane maybe baya so ya daga mana hankali ne ,ta mike ta nufi sama ,nan take Falmata da Sadiya suka mara mata baya
Tadala ta bi su da ido tun a hanya ya canza
Allah yasa dai ba ita ce dalilin ciwon kan nasa ba .
Kuna ta jingina da kujera tana kallon Tadala Wani irin murmushi ne fuskarta ,Murmushin da bai kai zuci ba,Uhmm An je wajen su Yaya Ameerah ana ta shishigi Tadala ta ɗago ta kalle ta batace komai ba ,Wai shi mutum dole sai ya saba da ’yan gayu? Ba wanda ya ce Kala a dining din ,Zahra ta ɗan kalleta ta san yanayin ‘yar’uwarta addu’a take kada ta fara halin nata
Tushin mutum dai… hamada ne ,baa canzawa tuwo suna ,a gama a koma inda aka fito ,Kalmar ta faɗi a falon kamar an jefa dutse cikin ruwa ,yaran gidan ba Wanda yayi magana dan tsoran kuna suke bata da mutunci,Tadala bata San sanda ta zabgawa kuna harara ba ,Kina min habaici alhali babanki yana kwance saboda ni har ya kasa cin abinci ta ayyana a ranta ,kawai ganin kuna tayi a gabanta Ke!” Tadala ta ɗan firgita
Ni kk harara? Tadala ta girgiza kai A’a…ba dake nake ba ,Kafin ta rufe baki kawai taji tass Mari ya sauka kunci ta Tadala ta dafe fuskarta Ba ta ma gama fahimtar abin da ya faru ba tasss…..Mari na biyu ya sake sauka ,Dan ubanki! Ni kike harara? A gidan ubana kinzo cin arziki ki kawo min raini ,ta shake wuyan tadala ,Amal ,yusra da Ahmad suka miƙe tsaye ,Haba yaya kuna cewar Amal ki sake ta mana ,matsa Kafin na juyo kanki tunda ba dake nake ba ,Amal taja da baya ,twins kuwa ko mosti basuyi ba daga zaunen da suke ,ganin kuna taki sakin tadala Ahmad kawai ya haye sama
Umma tana cikin duba temperature ɗin alhaji kamal ,ƙofar ɗakin ta buɗe da ƙarfi Ahmad ya shigo a guje Daddy!”ya Kira Alhaji kamal yana haki ,Me ya faru? Ahmad sadiya tayi saurin taro shi ,Yaya Kuna… ta mari Anty Tadala! Ta na dukanta ,yaron be rufe baki ba alhaji kamal har ya nufi kofa Umma ta ce, “Alhaji, ciwon kan— Ina yayi fice Matan ma suka bi bayansa
A falon ƙasa Har yanzu Kuna tana riƙe da Wuyan Tadala ,Tadala kuwa tsaye take cikin mamaki halin kuna , hawaye sun cika idanunta
SAKETA, MAIMUNA Muryar Daddy ta cika falon ,Kuna ta juya ta ganshi a tsaye Fuskarsa a ɗaure ,Ta saki Tadala a hankali
Hannun Tadala yana kan kuncinta ,Alhaji Kamal ya ji kamar shi aka mara Ya kalli kuncin Ya ga alamar yatsun hannu ,wani irin abu ya motsa a ƙirjinsa.
Ya kalli Tadala Meye ya faru?Ta buɗe baki
Amma babu murya Sai kawai ta girgiza kai.
Ya juya ga Kuna ,me ta miki kika mare ta harda Shaka ?shiru tayi bakin ta ya mutu ,tambayar ki nake maimuna sau nawa kika mare ta ?Kuna ta haɗiye yawu sau biyu
Falon ya sake yin tsit Ya kalli Tadala ,Je ki rama ta kalleshi a tsorace D… Daddy?
Na ce ki rama tagirgiza kai da Sauri aa dady na yafe mata ,Wani irin abu ya sake motsawa a zuciyarsa ganin tsoran kuna a Idonta , ya juya ga kuna ,Tass ya tsinke mata Mari Kafin ta farfaɗo Tass ya kara mata na biyun ?Kuna ta dafe fuskarta Idanunta suka cika da hawaye ta kasa yarda ,Daddy…Ya mare ta?A gabansu?
Alhaji Kamal ya zuba mata ido ,Wani irin rashin tarbiyya ne wannan? Da kk shaketa , da me za ki yi? Kasheta za ki yi?Kuna ta fashe da kuka ,Wallahi baki yi halin mahaifiyarki ba Sam ba ki yi halinta ba
Kukan Kuna ya ƙaru ,ya Kara nuna da yatsa Ban haifi ɗan da zai fi ƙarfina ba Maimuna.
Ki ba ta haƙuri ,Kuna ta yi shiru lalle ma daddy ita zata ba Tadala hakuri ?Talk, young lady,wani irin kuka ta fashe dashi mai tsuma zuciya Falmata ta Kira sunanta
Maimuna…Kuna ta ɗago ganin kallon da mommy take mata yasa ta shiga taitayinta
Ta kalli Tadala Daƙyar ta ce Ki… ki yi haƙuri Tadala ,Daddy ya Kalli kuna one last time Sannan ya ce You’ll still be punished
Yajuya ya kalli Tadala sau ɗaya Kuncinta yayi jajir ,be ce Kala ya juya ya nufi sama.
Amma zuciyarsa Har yanzu ba ta huce ba.
Duk suna tsaye kamar an dasa su Sadiya ko kallon tadala batayi ba ,itafa yadda sadiya ke nuna mata ko in kula na bata mamaki Kamar ba wajanta tazo ba
Ba marin da Daddy ya yi mata ne ya fi mata ciwo ba Abin da ya fi mata zafi shi ne…A gaban kanneta ya mare ta kuma Sabida Tadala tunda take rayuwarta, Daddy be taba ɗaga mata hannu ba Ta ɗaga kanta a hankali Idanunta suka sauka kan Tadala.
Wani irin tsanar Tadala ya mamaye ta Numfashinta ya fara fita da sauri ,Ta goge hawayen da ke fuskarta ,Sannan ta nuna Tadala da yatsa Wallahi… wannan marin da Daddy ya yi mini saboda ke, sai ya zama miki masifa da bala’i Gaban Tadala ya faɗi.
Kuna ta matso kusa da ita Kin ji na rantse miki,za ki ga abin da zan miki Shegiya! Yar talakawa
Kuna Zahra ta kira sunanta a firgice Amma ko kallonta ba ta yi ba Idanunta na kan Tadala ,Ta nuna Sadiya da hannu ,Mami, kin kawo mana masifa cikin gida! Muna zamanmu lafiya kin je kin ɗauko mana annoba Sadiya ta zaro ido ,Kuna rashin kunya zaki min ?Ta ci gaba da magana kamar ba ta ji ba In sha Allah, ke ma zuwanta sai ya zama sanadin tashin hankalin ki
KUNAAAA falmata ta daka mata tsawar dayasa ta firgita ,Ba kasafai Falmata ke fushi haka ba Ta taka zuwa gabanta
Maman Twins ɗin kike wa rashin kunya haka?Kuna ta buɗe baki Mommy ni—
Yi min shiru ,Falmata ta juya ta kalli Sadiya.
ke kuma kina tsaye kina jinta, Baki sumar da ita ba ?Sadiya ma ta rasa abin cewa Abin ya ba ta mamaki Ta san Kuna tana da saurin fushi, amma ba ta taɓa ganin ta kai haka ba Falmata ta sake kallon ’yarta
Kin dai ji Daddy ɗinki ya ce ba ki yi halina ba
Hawayen Kuna suka sake zuba ,Falmata ta girgiza kanta Wallahi sam ba haka nake ba
Can wajansu Zaheera kika gado wannan baƙin halin ta juya zuwa ga Tadala ta sassauta fuska ta kalli yatsun da suka bayyana a kuncin Tadala Wani irin tausayi ya kamata ,ta shafa kumatun Tadala a hankali Ki yi haƙuri, Tadala Hawayen da Tadala ta daɗe tana riƙewa suka gangaro.
Ta girgiza kai A’a, Mommy…ba komai
Falmata ta sake shafa kuncinta Hakan ba zai ƙara faruwa ba Zan wa tufkar hanci Tadala ta sunkuyar da kai
Falmata ta juya kama hannun Kuna da ƙarfi Har sai da ta yi yar ƙaramar ƙara Mommy…kin matse min hannu Jan kuna take da Karfi Mommy, hannuna…Na ce mu je ko ?a wannan lokacin, ba wanda zai ce budurwa mai shekaru ashirin da uku ce yadda momy ke janta
Sadiya ta juyo kenan taga dr mariya na ending video call baki sake take kallon ta tasan ba Wanda zata Kira in ba Ameenatu ba ,wanna gulma har Ina ?Kenan duk abin nan da ke Ameenatu na kalla a video call ?
Allah wadaran irin halin dr
Har Daki sadiya tabi tadala ,fuska ba walwala ta kalle ta ,kisan matsayinki Tadala Kina wuce iyaka fa ,Nasan Haka kawai kuna bazata mare ki ba na tabbata wani abun kike mata ,bata jira amsar tadala ba ta fice tare da banko kofar
Dakin twins ta Nufa ,Mami bakya ganin Kamar daddy ya zake da yawa ?safa tace tana kallon sadiya Murmushi sadiya tayi Naji dadin hakan ,Yau biki ga bakin Dr ya mutu ba ,tasan yadda daddyn ku kullum yake mana warning duk fadan da zamu muku Banda duka amma Yau gashi da kansa ya Mari kuna Sabida cousin Dina ,ko yanzu Sun San hubby baya wasa da duk wani lamari na sadiya ,Dr ta bace a falon mamaki ya sumar da ita .Marwa tace Nidai na gaji da ganin tadalan nan wallahi tayi ta gama ta Kara gaba
Tadala tana kwance a kan gadonta, sam barci ya ƙi zuwa Duk lokacin da ta lumshe ido, sai ta ga fuskar Daddy lokacin da ya ga Kuna tana shake ta, call dinsa ne ya shigo ,Muryarsa ta fito a ɗaya gefen a hankali kamar wanda baya son magana ,biki bacci ba ?Yanzu nake shirin yi ,hope dai Marin be sa miki ciwon kai ba ?aa dady be samin ba Nagode ,Kada ki sa abin nan a ranki Kinji ?ToDaddy ,Kuma kada ki ji tsoron kowa a gidan nan Duk wanda ya yi miki laifi, ki faɗa mini Zan dauki mataki ,Ta lumshe idanunta.
Wani irin tausayinsa ya ratsa ta ,bawan Allah he’s trying he’s best to see her happy
Ina … wannan abu ba zai yiwu ba ,Idan yau kaɗai abubuwa suka kai haka, me zai faru idan suka ji maganar aure? Ba zata zama sanadin rikici a gidansa ba ta ayyana a ranta
Uhmm daddy Dazu ance baka da lafiya me ke damu Ka ?Ciwon Kai ne amma da sauki
Daddy Ka daina over stressing kanka kaji?kuma Ka dinga samun Hutu da bacci sosai
To Mi dahila Nagode da tunatarwa inshaAllah I will abide Ki huta,Gobe kina da lectures
Ta jinjina kai kamar yana ganinta To, Daddy good night ,Goodnight, Mi dahila I love you .
ta sauke wayar a hankali ,Watanni shida…”
Zan ci gaba da playing ɗin Daddy har sai watanni shidan sun cika Daga nan… komai zai ƙare.