The cresent moon 🌙
by @zahrabmrs
Zumar Hamada
Page 18
Kwanaki suka ci gaba da tafiya Tadala ta koma cikin tsarin rayuwarta na makaranta da gida Da safe tana zuwa lectures, da yamma kuma ta dawo gidan Gidadon Katsina ta kulle kanta a É—aki tun da abun nan ya faru tsakaninsu da kuna ,ta kara kame kanta
Yauma suna zaune da farida a ƙarƙashin wata bishiya bayan sun gama lecture ɗinsu na yamma daf da magrib Iska mai ɗauke da ɗan sanyin ƙarshen Sha’aban tana kaɗawa, yayin da ɗalibai ke ta kai-komo a harabar makarantar Farida ta turo baki Wallahi Ina cikin damuwa kawata , Tadala ta kalleta damuwar me kike ciki haka faridata?Farida ta sauki numfashi Wancan mutumin mana
Wane mutumi? Mr. Silent mana Tadala ta yi murmushi Nawaf kenan ? Eh! Fa tun ranar ban sake ganinsa ba ,Na je club sau uku Ko alamarsa babu,har Manager na tambaya ya ce bai dawo ba Kuma ba ni da numbersa abun takaicin kenan .ki kwantar da hankalin ki zai dawo Wataƙila aiki ne ya tare shi Farida ta ja tsaki Aiki ne haka? Kawai ya ɓace? Ta ɗora haɓarta a tafin hannunta ,Ban ma san dalilin da ya sa nake ta tunaninsa haka ba ,Tadala ta yi murmushi Kin fara sonsa ne ,Farida ta zaro ido Ni? A’a! Ba soyayya ba ne ,Tadala ta ɗan ɗaga gira
To me ce?Farida ta buÉ—e baki, shiru tayi rashin sanin amsar da zata ba Tadala tsaki ta kara ja ,Ni ma ban sani ba ,Kya ji dashi dai farida ki gama kunbiya kunbiyar ki
wasu ɗalibai suka zo wuce ta gefensu An ga wata!”An ga wata!
Cikin daƙiƙu kaɗan, harabar makarantar ta kaure da farin ciki ,tadala ta daga kanta sama ,Ba ta iya ganin komai daga inda take, amma murnar da ke fuskar mutane ta isa ta sa zuciyarta cika da wani irin farin ciki .Gobe za a fara azumi Ramadan ya sake dawowa Alhamduillah ,daga nan ko wacce ta nufi gida
tun bayan abin nan ya faru alhaji kamal ya ƙara mai da hankali sosai kan Tadala Kullum sai ya nemi wata hanya da zai sa ta farin ciki sometimes ya aiko mata da littattafan Accounting da ba ta da su, Wata rana ya sa aka kai mata kayan ciye-ciye daga wani restaurant har school ,Watarana kuma ya kira ta kawai ya tambaye ta yadda lectures ya kasance ,Yana ƙoƙarin tabbatar mata da cewa ba ita kaɗai ba ce he’s always with her
Yau tana dawowa daga makaranta ta yi mamakin yadda gidan ya cika da hayaniya.
Ma’aikata na ta kai-komo Ameenatu ma tazo suna ta hira da amal a Wajan lambu ta hango su Bayan Sun gaisa da Malam Awaisu, ta dan tsaya dan tambayar sa me ake a gidan haka ,dan tasan ba inda zata samu labari, Ahmad yaje Zaria Hutu shekaranjia ya dawo ,Dama a Wajan sa take samun labarai ,mal awaisu ya fada mata ay khalifa ne ya dawo dazu Bayan fitar ta makaranta ,Ba tare da ta yi tunani ba ta juya kai tsaye zuwa part ɗin Umma ,da sallama ta shiga ,ta hango khalifa da bakar jallabiya ,sai da gabanta ya fadi ganin irin yadda yake kama da daddy ,Ina yini umma muryar tadala ta katse masu hirarsu ,Ah lalle yau kece a part dinmu ?dr Mariya ya washe fuska,zauna zauna Tadala Ah! Princess of Agadez cewar khalifa yana zama a dayar kujerar
Ina yini khalifa ya hanya?hanya Alhamduillah Yau dai na ganinki ido da ido Ina yawan ganin ki a status din yaya Ameerah da ,mommy (zaheerah)yusra maza ki kawo yayarki snacks dr Mariya ta aiki yusra wacce ke kwance a 3 sitter
hira suka fara da khalifa Ya tambaye ta yadda makaranta take, ko ta saba da Abuja ko akwai abin da take buƙata Umma tana murmushi tana kallonsu ay badan tadala da khalifa age mates bane data hada su aure ta tabbata Alhaji zai yadda
Bayan ɗan lokaci Tadala ta miƙe ,To zan tafi sai wani lokacin ,Khalifa shima ya mike
Ki dinga shigowa part É—inmu hira Gidan nan na kowa ne
Insha Allah ,Tana jiyo dr mariya na cewa ba sai sadiyar ta barta ta shigo ba
Tana fitowa corridor É—in, ta ci karo da Sadiya ta zuba mata ido Tadala.
Na’am Anty
Har kin fara shiga part ɗin kishiyoyina ba tare da izinina ba ?Tadala ta dan ruɗe A’a… na je gaishe da Khalifa ne Malam Awaisu ne yake gaya mini ya dawo ,Khalifan kanin uwarki ne ko na ubanki?Tadala ta ɗaga kai da mamaki Chan ta girgiza kai A’a kiyi hakuri maganar fiza ce ta fada mata Ki je ki yi karatu kawai ,Ki jure komai zaman gidan sadiya sai da Kai zuciya nesa
Ta tuna semester uku kacal suka rage mata
Ta tuna Uma Ta tuna Papa kawai ta haÉ—iye komai watarana sai labari ta ayyana a ranta
Ki yi hakuri, Anty Insha Allah ba zan sake ba ta kara fada ganin sadiyar Kamar zata kai mata duka ,Sadiya ta kalleta na wasu daƙiƙu tayi kwafa ta dan bangaje tadala
ta tsaya ita kaÉ—ai a corridor Wani irin kaÉ—aici ya rufe ta Tun zuwanta gidan nan Ba ta da kowa Twins É—in Sadiya ko hira ba sa yi da ita Sadiya kuma ta hana ta zama a main falo ba tare da wani dalili ba A mafi yawan lokuta Tana kulle kanta ne a É—akinta Ba TV
Ba wani abin nishaÉ—i Ahmad ne kaÉ—ai wani lokacin yake shigowa ya yi mata hira ko ya ba ta labarin abin da ke faruwa a gidan A wannan lokacin ta ji kewar gida Ta ji kewar Agadez Ta ji kewar zama a tsakar gida tare da Uma ko Aghali , duk da kuwa rayuwarsu cike take da talauci amma a kalla Akwai Farin ciki
Ramadan ya sauka a gidan Gidadon Katsina cikin wani irin yanayi na farin ciki da albarka Tun daga ranar farko, gidan ya canza gaba ɗaya Ana tashi sahur daga kitchen sai ƙamshin abinci kala Kala da kayan marmari Da yamma kuma, idan lokacin buɗa baki ya yi, gaba ɗaya iyalan gidan kan taru a babban dining dik dai Tadala ba ta taɓa jin kanta a cikin taron ba a ware take Tana zuwa ta ci abinci cikin ladabi, ta yi sallama ta koma ɗakinta Sai dai mutum ɗaya bai taɓa mantawa da ita ba
Daddy ,kallonsa kadai yana wadatar da ita
Kullum sai ya Kira ya tambaya Mi Dahlia, yaya azumin yau?Alhamdulillah, Daddy.”
Wani lokaci ya ce Kin sha ruwa sosai jiya da sahur dazu naga Kamar zaki sume ko kuma yace Kar ki yi karatu da yawa kina azumi
Duk ƙananan abubuwan nan Suna sa zuciyarta yin wani irin bugawa ,Indai caring ne daddy ya cire tuta Abinda mansoor be iya ba kenan
Yau bayan buÉ—a baki Tadala na fitowa daga kitchen da cup É—in ruwa a hannunta, caraf suka haÉ—u da Kuna a corridor ,ina sane da ke, Tadala Ban manta abin da kika yi mini ba
Wai Akan maganar marin nan ne?ba momy ta mana sulhu ba ? Kuna ta matso daf da tadala ta mata wani kallon kaskanci ,zakiga sulhu ganin idonki Shegiya yar talakawa ,Jin motsin shigowa yasa kuna saurin matsawa daga jikin Tadala tare da fita daga kitchen din gabadaya
Kwanaki suka ci gaba da gudu har An kai azumi na goma A daren ranar ne, bayan an sha ruwa Tadala ta fara jin hayaniya daga falo Ana dariya ta ɗan leƙa daga ƙofar ɗakinta ta ga ma’aikata suna kai gifts
Fitowa tayi dan taga me ke faruwa Ahmad ya ganta Anty Tadala! Ya naga biki shirya ba ?ina zamu Ahmad?Kin manta ne? Yau birthday ɗin Yusra? Oh…Bata ma sani ba
Yusra, autar gidan ta cika shekara goma sha bakwai ,ta sake jin hayaniya daga sama ana sauko wa Ahamd ya kalleta ,je ki shirya mu tafi mana ,zuwa Ina Ahmad ?Birthday dinner mana Kafin ya ƙara maganAmeenatu ta karaso anci gayu ga wani karamin veil Kamar ba matar aure ba ,nanny na biye da ita da yaronta ,Ta kalli Ahmad naji kana cewa ta shirya badai dinner kake nufi ba ?Ita nake nufi mana Anty Ameenatu zaa barta ita kadai ne a gida ?fuska ba walwala ta kalle Ahmad ,to babu inda zata ,iya Yan gida ne kawai zasu outing ɗin Ba ma buƙatar outsiders Ahmad ya yi shiru gabadaya kunya ta kama shi ,khalifa Wanda karasowar shi kenan yaji abinda yar uwar tashi ta ke fada ,Don’t be mean sis Haba ke kuwa ya juya wajen Tadala ,shirya Mu tafi Kinji ?Tadala ta yi saurin girgiza kai
A’a, Khalifa ku tafi kawai ba damuwa
Ya É—an É—aure fuska Why?
Zan yi karatu ne Ya san ƙarya take yi
Amma bai ce komai ba ,ta kalli Ahmad tace ka fadawa yusra nace Happy birthday to her Khalifa ya kalleta na wasu daƙiƙu ya fice Ahmad ma yabi bayansa
Alhaji Kamal da matansa uku suna zaune a cikin motar da za ta kai su dinner Ba su san abin da ya faru a cikin gidan ba tunda Sun Riga yaran fita shi kuwa dady be San Mi Dahlia” ita kaɗai ta rage cikin gidan Gidadon Katsina ba. 💔
Tana shiga ta dauki wayar ta hau TikTok comments din mutane take karantawa ,Tana saka pics dinta da vidoes amma masu mutunci har na picnic duk tasa
page É—inta ya fara É—aukar hankali sosai. Followers É—inta sun kai 50k, abin da har yanzu ke ba ta mamaki ,Ta yi É—an murmushi.
Allah mai canza rayuwa Daga yarinyar Agadez mai mafarkin shiga jami’a…Yanzu dubban mutane suna bin shafinta
Bayan ta gaji da TikTok, sai ta koma google tana duba wasu abubuwan da suka shafi assignment ɗinta Can da ta gama…
Ta ɗaga kai Shiru Wani irin shirun gidan ya dauka Ta cire earphones ɗinta Sai a lokacin ne ta tuna cewa gaba ɗaya gidan babu kowa ,duk suna restaurant ana ci gaba da birthday celebration din Yusra.ta kalli ƙofar ɗakinta ta haɗiye yawu tare da rungume pillow tunda take ba ta taɓa zama ita kaɗai a irin wannan katafaren gida ba ,Tsoro ya fara kama ,Kodai BQ zata ne Wajan su bintalo ?
A can restaurant kuwa ana ta hotuna Yusra
tana tsakiyar tebur ga cakes a gabanta Daddy ya É—aga kai Idanunsa suka fara yawo Wani abu yake nema Mi Dahlia Bai ganta ba Ya sake kallon entrance gani yake Kamar an taho da ita maybe Tana mota taki shigowa ne Ya É—an daure fuska ya kalli Ahmad ,Ina bakuwar mamin Ka ?Ahmad ya kalli Ameenatu ,Khalifa ma ya É—ago kai
Daddy… ai bata zo ba
Me ya sa? Baku fada mata bane ?Khalifa ne ya yi gyaran murya Ta ce zata yi karatu ne
Daddy ya ɗan zuba masa ido Akwai wani abu da suke ɓoyewa dan ya Lura da yadda suke musayar Kallo
Bayan minti kadan daddy ya fita da niyar waya ,tana kwance wayarta ta yi ringing, ta duba screen Daddy Calling…Da sauri ta ɗaga Hello… Mi Dahlia Kina jina ?eh dady Ina jinka ,Kuka kike? Ta goge idanunta A’a
Mi Dahlia Me ya faru? Cikin rawar murya tace Tsoro nake ji daddy ,Tsoron me kike ?
ni kaɗai ce a gidan Wani ƙaramin murmushi ya subuce masa To me ya sa baki biyo su ba?Ameenatu tace dinner ɗin iya na yan gida ne… ba sa bukatar outsiders
Fuskar Daddy ta canza ,murmushin nasa ya kau haka tace ?Eh… amma ba komai ay gaskiya ta fada
kin kusa zama matar babansu ay daga nan kin zama yar gida babu zancen outsider kuma tadala tace Daddy… ni dai kamar abin ba zai yiwu ba, A rude ya ce
Why?Meyasa kike tunanin haka?Saboda abin da Ameenatu ta yi miki yanzu ?To zan É—auki mataki
A’a!” Dan Allah kar ka yi magana ba haka nake nufi ba
Haka ya cigaba da mata hira Bayan wasu mintuna ya ji fara ta hamma Barci kike ji?Kadan ba ,To kwanta Ta kwanta ta rungume pillow
Daddy…
Hmm?
Kar ka kashe wayar ,Wani Abu ya ya ratsa zuciyarsa Ba zan kashe ba
A hankali ta lumshe idanunta Bayan wasu mintuna numfashinta ya sauya Ta yi bacci
ya yi shiru na wasu daƙiƙu Har yanzu wayar tana manne a kunnensa, yana jin saukar numfashinta a hankali ,kashe wayar yayi da niyar komawa restaurant din yana juyawa yaga Khalifa Tsaye a bayan sa hannayensa a cikin aljihun wando, idanunsa a kansa