Zumar Hamada 🍯 🏜️

Unspoken

by @zahrabmrs

Zumar Hamada 

Page 19

Tun bayan daren nan a club…Nawaf bai sake zuwa ba, ba  saboda aiki ya yi yawa ba, kuma ba saboda ya manta da ita ba ,Sai dai duk lokacin da ya yi niyyar fita sai fuskar Farida ta faɗo masa Baya son sata a ransa it’s not healthy Gara ya nisance ta shine mafi alkairi ,sau biyu yana ɗauki key ɗin mota da niyyar fita Sai ya fasa 

Gashi  Ramadan ya shigo no more club  Sai dai abin mamaki…Duk lokacin da ya yi shiru, sai ya tuna murmushinta 

Tuno Kalamanta yayi Murmushi yana maka kyau sosai… kamar na ɗauki picture 

ƙaramin murmushi ya Saki yana girgiza kai 

Nadira ta lura mijinta ya fi zama a gida a kwanakin nan , ta gane cewa barazana ko Hauka bazai taba canza Nawaf ba ,dan Bayan zagin da ta masa a waya sai da tayi kwana 4 bata gansa ba yaki dawowa gidan .

sai da tayi  blackmailing dinsa da Ayla kana ya dawo 

Sai gashi idan tayi girki yana ci ,har amsa hirar ta yake time to time ,kawai ta fara samun wani sabon fata ko  dai…Mijinta ya dawo  gare ta?ganin  haka ita ma ta sake dagewa, ta Kara  kula da shi ,ta fara magana cikin natsuwa

Bayan an sha ruwa ta  same shi a balcony Ta miƙa masa cup na coffee ,Na yi maka ba sugar sosai Na san haka kake so 

Ya ɗaga kai Ya kalle ta  ya karɓa ,Thank you nadira ,Kalmar ta yi mata daɗi fiye da yadda ya zata Saboda shekarun nan…Har “thank you” ɗin ma ya yi mata wuya ta ji daga gare shi

Bayan kwana biyu…Nadira ta same shi ɗakinsa yana ta aiki a laptop ,ta zauna kusa dashi ,Uhmm Zauji na biya mana  Umrah 

Oh nice Allah ya kaiku lafiya ,ta dan yi jim  kadan kana tace ba fa iya ni da Ayla ba ne harda Kai ,Allah kaimu Sannu da kokari 

Nadira ta zaro ido  Da gaske?zaka ?Wani irin farin ciki ya mamaye zuciyarta,kiss ta manna masa ta goshi ,nawaf ya runtsa ido 

Bari na fara hada mana kaya ta fice zuwa dakin ta cikin murna,Tana fita ya dauki waya ya mata transfer din kudin umrar data kashe  


Shiru ya ratsa tsakaninsu Khalifa ya kalli wayar da ke hannun mahaifinsa Sannan ya sake kallon fuskarsa Everything okay, Dad?Eh. Komai lafiya ya fada yana dan kawar da fuskar sa gefe ,Khalifa ya jinjina kai 

Amma bai motsa daga inda yake ba 

Daddy  ya lura da wani Kallo da khalifa ke masa ,ya dan daure fuska me ya kawo ka nan?khalifa  ya ɗan yi murmushi ,na fito ne Shan iska sai na tarar kana waya 

Daddy ya zuba masa ido ya kasa magana 

Tadala ce ko?muryar Kalifa ta katse shirun 

Wani abu ya motsa a fuskar Daddy yayi sauri ya danne shi 

Eh Ita ce

Khalifa ya jinjina kai Ta ce tana Jin tsoro ne ?

Daddy bai ce komai ba  A lokacin ne ya tabbatar Yaron nan Ya ji komai 

Daddy Gidanmu yana da girma sosai Ni ma da farko ina tsoron zama ni kaɗai a ciki ,Poor girl  har yanzu dady be tanka ba to me zai ce ?

Dad…

Na’am?Kana kula da Tadala sosai

Sabida Baƙuwarmu ce  khalifa shiyasa 

Is that all?  Daddy ya zuba masa ido Kamar mai son karanta Abu a fuskar dan nasa 

Khalifa ya ɗaga hannuwansa kaɗan

Okay… okay na dame ka questions mu koma ciki 

suka fara tafiya jikin dady a sanyaye daf da zasu shiga khalifa ya koma juyo wa by  the way…I don’t think she’s an outsider yar gida ce itama  ya shige Cikin restaurant din 

Alhaji Kamal ya tsaya a wurin Idanunsa suna kan bayan ɗansa A karon farko Ya ji kamar wani ya kama shi da wani sirri da bai ma san yana ƙoƙarin ɓoyewa ba


Ramadan ya yi nisa Yanzu sun kai kusan azumi ashirin da ɗaya Gaba ɗaya  mansion din Gidadon Katsina ya canza Hayaniyar gidan ta ragu, kowa ya dukufa da  ibada

A ɓangaren Tadala kuwa, rayuwa ta ɗan yi mata sauƙi. Makaranta ta tsaya saboda hutun semester, kuma tana samun damar yin karatu da ibada cikin natsuwa

A wannan ranar, tana zaune a ɗakinta tana karanta Al-Qur’ani wayarta ta yi ƙara 

Anty Zaheera ce ,cikin zumudi ta daga Assalamu alaikum, Anty ina yini,

Wa alaikumus salam folawar mu  Mi kike yi ne?ba komai fa Ina zaune ne kawai 

To, ki shirya Yau a gidana zakiyi  buɗa-baki 

Na Kira sadiya na fada mata ,Wayyo Antyna Nagode can’t wait to see you 

Bayan ta kashe wayar, wani irin farin ciki ya mamaye zuciyarta Ta dade ba ta fita ko’ina ba tana shirin tafiya Sadiya ta shigo ɗakin 

Kin shirya ne? Eh Mami Sadiya ta jinjina kai.

To, ki gaishe ta.

daddy ma ya fadawa matan sa,zaheera ta gayyace shi bude baki dama duk shekara tana gayyatar dady ,shiyasa ma da suka ga tadala ma tafi basu kawo komai ba 

 

Tana isa gidan ganin falon ba kowa kai tsaye ta nufi sama main bedroom din zaheera ,zaheeran ta rungume tadala 

“na yi missing ɗinki fulawar mu ,Tadala ta yi dariya  Ni ma haka Antyna 

By the way, Kamal ma zai zo buɗa-baki nan 

Tadala ta ɗago kai da sauri  Daddy?”

Eh mana gani nayi kuna bukatar zantawa 

Daga nan dakin mardiya ta Nufa Wajan azahar Kitchen suka shiga gaba dayansu inda aka shirya Kayan Shan ruwa 

Suna gamawa  duk suka shige daki dan Watsa ruwa Sabida saukin gajiya 

Horn sukaji ,Zaheera ta yi murmushi Ga twin brother ɗina nan gandoki bazai Bari ma magrib tayi ba 

Ba da jimawa ba ya shigo Sanye yake da farar shadda,hularsa a hannunsa 

Ya fara gaishe da Zaheera idanunsa suka sauka kan Tadala Tsaye  Sanye da  abaya mai launin ruwan kasa 

Mi…dahlia ba magana ?

Ta yi murmushi  ina yini Daddy?Lafiya Lou babyna ya ibada ?Zaheera ta bi su da kallo 

Na ware muku waje  Ni zan kawo muku abin buɗa-baki da kaina kuma gaskiya alhaji kamal ka rage tsaurin ido a gaban nawa ?

Daddy ya dafe kai ,Kina da matsala twin 

Ba wata matsala nida ja fulawar ka ku wuce guest parlor Kafin yara su shigo 


Guest palour …

Shiru ne ya ɗan mamaye falon kasan carpet Tadala ta zauna  Azumi nawa kika sha?ta jiyo Muryarsa a gefenta ,ban sha ko daya ba ta amsa cikin kunya ,Uhmm ban yarda ba mi dahlia ,yanzu that aside ya naga kin rame ?

Azumi ne Dama kam dan ramewa amma Bayan sallah Zan dan ciko zaiyi magana kenan aka Kira sallah ,dabino ya Mika mata ta dauki daya tare da Adduar bude baki Shima yayi daga nan ya nufi main falo dan tafiya masjid dasu junior ,itama daki ta nufa tayi alwala ,mardiya na kwance Wai period dinta yazo cikin ta na ciwo ,brush tadala tayi ta koma guest falon ,har ya dawo ya fara zuba abinci ,a plate daya serving dinsu A wannan lokacin…baya tuna komai  daga shi sai mi dahliar sa daf da zaa Kira isha ya miƙe To, zan tafi mi dahlia zaheera tace kwana  zakiyi Muje ki raka ni  suka jera suna tafiya Chan kuma ya juyo 

 Mi dahlia …

Na’am?

Za ki iya haɗa ni da iyayenki?

Ta zaro ido Papa da Uma?

Eh su 

Gabanta ya faɗi Lalle…Da gaske yake Ba wasa yake yi ba suka karasa harabar gidan 

Hannu na rawa Tadala ta Kira Moussa Bayan Sun gaisa da Yaren su ta fadawa moussa zasu gaisa da mijin Anty sadiya …Ta ba Daddy wayar 

Assalamu alaikum Moussa ya amsa da sauri jin dawa yake waya Daga nan aka haɗa shi da papa  da uma  Daddy ya yi musu barka da shan ruwa Ya yi musu gaisuwa cikin girmamawa suka dinga  mamakin rashin girman kan sa 

Kafin su rabu, ya ce  

Moussa Zan amsa number yanzu ,ka turo mini account number ɗinka   A saya wa autanmu  lemo  

Autanmu ? Kalmar ta bugi zuciyar Tadala  ,har zata raka shi parking lot yace ta koma 

Tana shiga falon taga zaheera ta baje kaya ,zo nan fulawar mu 

Ga sako daga twin Wai Kayan sallar kine 

Anty?

Zaheera ta yi murmushi bude su mana 

Lace uku , Super uku  Bazin uku,Designer shoes Matching veils ,Anty…Duk nawa ne ?

Buɗe ƙaramin box ɗin ki gani mana 

Tana buɗewa taga Gold set  Yan kunne da Sarka 

Ta buɗe baki ta kasa magana Nan take…Maganar Farida ta dawo mata 

An ce a Gidadon Katsina, kullum cikin sayen wa matansa gold yake…

Ta sake kallon kallon Kayan A’a, Anty Kayan sun yi yawa Wallahi sun yi yawa Ina Zan kaisu ?Ta ɗauki ɗaya daga cikin laces ɗin 

Wannan kaɗai ma ya isa 

Mi Dahlia, ai ba ki ga komai ba Indai kamal ne Tadala ta zaro ido Ban ga komai ba?a hakan ? Gobe ma za a kai miki dinki zaheera ta canza hirar dan ta Lura har yanzu Tadala bata San waye gidadon katsina a dukiya ba 

Tadala ta zuba mata ido kamar wacce aka yi wa  sabon harshe 

Anty…Dan Allah a rage Kinga ….Zaheera ta katse ta ,ki bar maganar nace  

Jiki a sanyaye Tadala ta jinjina kai  To Anty

Ki gode wa Allah kawai  

Tadala ta sauke numfashi.

Toh Anty Allah ya karawa daddy budi 

Ameen ya Allah ,tatttara ki kai daki haka ta fara tattara Kayan Ta kasa yarda cewa duk wannan nata ne.

Ta shiga guest room ɗin da ta saba sauka idan ta zo gidan ,ta  zauna a bakin gado, wayarta ta yi ƙara Moussa.

Yaya Moussa

Tadala!

Na’am.

Ke, kin san nawa mijin Sadiya ya turo min?

Ta ɗan yi shiru A’a.”

Million biyu fa 

Tadala ta miƙe zaune

Me?

Million biyu fa! Wallahi, million biyu cif!

Moussa ya ci gaba da magana cikin farin ciki ,Wallahi wannan mutumi ɗan aljanna ne! Yanzu zan kira Sadiya na yi mata godiya 

Da sauri Tadala ta ce,A’a! Yaya, don Allah kar ka kira ta Moussa ya yi shiru Kar na kira ta?Eh Saboda me?Bata san da ya bayar ba.”

Kamar ya ?Don Allah kawai, kar ku mata maganar.

Ashe Wayar  a speaker take  Can ta ji muryar Uma  Moussa, bani wayar 

Tadala?Na’am, Uma.”

An ina kuka haɗu da Alhaji Kamal har ya ce ki haɗa shi da mu?

Uhmm…”Dama ….Na je gidan yar uwarsa ne… Anty Zaheera, wacce nake baki labarinta Shi ma ya zo ,a nan muka haɗu

To, idan haka ne, me ya sa kika ce kar a yi wa Sadiya godiya?

Da sauri Tadala ta ce,A’a Uma… ai Mami ba ta son Alhaji yana yawan kyauta ne Shi ya sa yake yi a boye Ta faɗi cikin rawar murya.

Ba ta san dalilin da ya sa ta yi ƙaryar ba.

Sai dai…Ta ji ba za ta iya bayyana musu gaskiyar lamarin ba Can Uma ta sauke numfashi Allah ya saka masa da alheri.”

Moussa, ka Ka ba Fiza wani abu daga cikin kuɗin nan Tunda mijinta har yanzu ba wani ci gaba ya samu a rayuwa ba 

To Uma Kuma ku yi wa Alhaji Kamal addu’a. Allah Ya ƙara masa arziki da lafiya.

Tadala ta lumshe Idonta 

Amin.

Bayan ta kashe wayar Ta zauna shiru.

Idanunta suka sauka kan ledodin kayan da ke gaban ta  

ta tuna kalmar da Daddy ya faɗa dazu saya wa autanmu  lemo 

Ta dafe ƙirjinta a hankali A karon farko…

Ta fara jin tsoron yadda wannan mutumin yake kula da ita. 💔


A can waje…Daddy ya fito zai shiga mota  kawai ya yi karo da mutum 

khalifa ne Tsaye Hannayensa cikin aljihun wando Yana kallonsa 

 Gaban Daddy ya faɗi 

Khalifa? Me ka zo yi nan? Khalifa ya yi shiru na ɗan lokaci Na zo ne in ƙara tabbatar da abin da nake zargi.

Daddy ya ɗan tsuke fuska me kake nufi?Khalifa ya kalli gidan Sannan ya sake kallon mahaifinsa.

Daddy… did You really love her this much.”

Ko motsi Daddy bai yi ba 

Khalifa ya ci gaba 

Na ga fuskarka yau ,Na ga yadda ka ke kallonta ,Na ga yadda ka ke farin ciki idan tana magana Wallahi, Dad… ban taɓa ganin ka haka ba ,Lokaci ya yi kamar ya tsaya 

Alhaji Kamal ya zuba wa ɗansa ido 

Domin a karon farko…Wani ya furta abin da shi kansa yake tsoron furta wa