BABI NA BAKWAI
by @maidambu41
KARFE DUKKA ƘARFE NE...!!!
{Zanen ƙaddarar Falilah }
Wannan shafin naku ne, bakidayanku masoyan LillyBobby
BABI NA BAKWAI
Har kwanan gobe ban daina kukan rashin Ahmad ba, ba wai don ban samu yadda nake so ba ne, na samu fiyye da yadda ban zata ba. Sai dai Ahmad wani duniya ne na musamman domin na samu abin da na rasa a dawowarsa rayuwata.... Eternal Love
Ban sani ba, ko Ya Nafi'u ya gaya musu muna hanya yasa baki daya Yayuna suka cika gidan, hatta Aunty Shatu da take aure a Kaduna tazo, dakin Hajja Mama Ya Man ya wuce da ni. "Ku bata abinci" "tow amma ai kunu take sha" Aunty Zahra'u ta fada tana mika min kofin kunu, girgiza kai nayi ina jin kuka yana kara zuwa min, kawai gani nake kamar maraici sosai ne ya kama ni.
In sha Allah, sai na dawo miki da jin dadin ki da farin cikin da kika rasa, sai na sanya miki dariyar da kika rasa ya dawo eternal.
"Ahmad ba shi nake bukata ba, kai nake bukata, Ahmad ya dawo min da kome bayan na rasa shi, ni shi nake so ba kome ba." Riko hannuna Ya Man yayi yana kallon yadda nake kuka. "Ni ma haka ya gaya min, yana ji kamar akwai abin da ya dawo da shi gare ki, yana jin kamar ya dawo ne domin ya gyara wani abin da ya kasa dakatarwa tun baya, Nana A'ishah! Ahmad ya roke ni ya zauna na tsawon kwanaki yana bin manyan mutane da almajirai domin na yafe muku. Na yafe maku Falilah na yafe muku, Allah ya shiga lamarin ki." Me yafi haka dad'i mutum ya samu yardan Allah da na mijin shi tare da na iyayen shi. Haka na cigaba da kuka domin duk abin da aka min sabo ne, bai min yadda nake so ba, domin na rasa wanda idan yayi min zan yi dariya.
Dakin Hajja na wuce tana kan abin sallah, na koma gefenta na daura kaina a kafad'arta. "Shin ba na gaya Miki wata rana zaki dawo gida ba?" Dake kwantar da kaina a kafad'arta hawaye na zuba min, "Alhamdulillahi" a hankali ta shiga min nasiha da nuna min sakamakon yarda da kaddara, haka har na daina zubda kwalla. Sai dai Ahmad ba mutum ne da zan manta da shi cikin sauki ba, domin ya shammaci rayuwata ainun.
Zuwa yamma Yayuna mata da suke cikin gari sun koma, daga ni sai Aunty Shatu. Ina kwance a gadon Hajja Mama ita kuma tana yanka min fruit domin na sha. "Falilah"
"Na'am" na amsa mata, "kiyi hakuri kin ji" murmushi na mata, sannan na ce mata. "Ba kome, ai ba ku min kome ba." Gyara zama tayi ta miko min robon fruit din ta ce min. "Sadiyah ta sani na roke ki" juyar da kai na nayi, ina me shan fruit din. Bawai dan bani da abin cewa sai dai bana son magana ne. Ganin haka yasa taja bakinta tayi shiru.
Haka kwanaki suka ci gaba da tafiya, zuciyata cike da kewar shi, sati na uku sai ga Alhaji Salisu ya zo min ta'aziyar Ahmad, dauke da kayan arzikn kamar me, kawai kallon shi nayi sau daya na dauke kai,.domin ya kara tsufa kamar ba shi ba, haka ya tafi ban ba shi fuskar magana da ni ba, bayan ta'aziyar da ya min. Kwana biyu a tsakanin su, sai ga Eng. Abin dariya koda yake yazo min da Hanif zai kwana biyu a wurina. Kaina na kasa ya gama min nasiha kamar na Allah ya tafi, koda yake shi Ubangiji ya bamu damar amsar gaskiya koda a hannun shedan ne, bayan tafiyarsa na kalli Hanif sai kace bako. "Dama baka zuwa wurin su Hajja ne?" Idanun shi ne ya cika da kwalla, ya saka hannun shi a bakin shi ya gyada min kai. Kallon shi nayi na wasu lokuta kafin na ce mishi. "Tow meye na kuka?" Na mika mishi hannu, da sauri ya matso jikina yana sauke ajiyar zuciya. Wani irin tausayin shi ne ya kama ni, "Allah ka tsinewa Asad albarka da duk abin da zai ajiye a matsayin zuri'arsa" "kul" Hajja Mama ta ce min, fashewa nayi da kuka, ina kara rungume Hanif kamar raina zai fita. "Hajja" "kar na kuma jin haka, ke fa Uwa ce! Kar ki kara tsinewa dan wani domin laifin shi a gare ki, bar shi da Allah zai saka miki" rungume mu tayi ni da Hanif din. "Allah ya shiga lamarin ku, Ubangiji ya albarkaci zuri'arki ya basu ikon miki biyayya kamar yadda kika yi mana"
Haka na cigaba da samun kulawa a wurin Iyayena da Yayuna, duk sati Ya Nafi'u yana turo min da kudi, ga wanda Ya Man yake bani, haka kawai ina zaune za a kawo min Kilishi, daga Sokoto ake kawowa Ya Man, wani lokacin fura da nono haka za a kawo domin ni, cikina shima lafiyar shi lau, kasancewar Aunty Zahra'u aikinta ne midwife har gida take zuwa min awo, Hajja Mama bata da burin da ya wuce taji Yayuna suna saka ni farin ciki.
Satin Hanif biyu, Eng da kanshi ya zo daukar shi. Ganin yadda ban damu ba yasa shi samun Ya Man da zancen ko zai bar min Hanif ne kafin na haihu, shiru Ya Man yayi kafin ya ce mishi. "Tow Mahmoud zan same ta naji ko tana da ra'ayin haka" haka kuwa ya tafi da Yaron bayan sallah ishe Ya Man ya shigo ina shan fura me sanyi. "Ina wuni Ya Man?" "Lafiya lau, ya jiki jikin ya zaman Ibada " ya tambaye ni.
"Alhamdulillahi." Na fada ina mai da hankali na gare shi. "Ɗazun da Eng Mahmoud yazo daukar Mustapha yake tambaya ko zai bar miki Yaron ne,.shi ne nace ya dakance ni na tambaye ki" murmushi nayi, sannan na ce mishi. "Ya Man duk abin da kuka ce daya ne." "A'a ke muke bukatar jin ta bakin ki" "Ya Man ba ni da zabi yanzu ko ra'ayi sai naku " "Shi kenan Allah ya duba al'amarin ki" "Amin Ya Allah" na furta a hankali, ban san me yasa baki daya nake jina kamar wata sabuwar halitta ba, shiru nayi kaina a kasa domin wani lokacin sai nayi ta jin kamar bani da sauran farinciki Ahmad ya tafi da shi baki daya. Hawaye ne ya zubo min na ajiye kofin furar na share da bayan hannuna. "kiyi hakuri kin ji" d'ago kai nayi, na kalle shi kafin na gyada kai, ina jin wani irin kuka yana zuwa min. "Kiyi hakuri Humairah!" Gyada kai a nayi. "Ya MN na saba da shi ne, Ya Man da za a bani zabi rayuwa ta ko tashi da xan zabi tashi ya rayu ni na taf..." "Ki godewa Allah, domin yasan adadin darasin rayuwar da kika gani, ya kuma san dalilin da yasa ya var ki a raye." Daukar kofin furar yayi ya tofa min Addu'a. Sannan ya mika min kofin, shigowar Hajja Mama ya sashi mikewa. "Falmata zan kwanta, Muhmoud ya ce min zai dawo mata da Mustapha ne shi ne nace bari na tuntube ta naji ra'ayinta.' shiru tayi sannan ta ce mishi. "Yo nafi son ma da humaidah aka dawo mata da ita, domin ita ce mace zata fi son zama da ita." "Kina ganin Salisu zai bata Humaidah a dadin rai ne? Tayi hakuri ta cigaba da addu'a, amma yadda yazo nan yayi gaisuwar nan bana tunanin zai kawo mata Yarta, tunda ba lissafi ne da shi ba." Ya fada yana barin dakin. Kallon Hajja Mama nayi, ina son jin karin bayani. Domin dai nasan tunda Ya Man yayi watsi da lamarina, bana jin ya san kome a kaina.
"Humaidah tana fuskarta matsala ne?" Dauke kai tai, tana faɗin. "Ba wani Babban matsala ba ne, kwanaki Hamza ya tafi unguwar daurin aure ne, ya ga Hajiya Raliyah tasa a kamata har cikin gidan ana dukanta, wai tayi sata. Rikici har hukumar shara'ar musulunci" wani irin abu naji me nauyi kamar an daura min dundumen dutse a kirjina, "humaidah da sata?" "Ke sharri ne fa!" Ta fada cikin sigar lallashi, kasa barci nayi a daren na mike ina gayawa Allah kukuna akan Yarana. Bani da madadinsu a duniya, bani da na biyun su idan narasa su nice nayi asara, zaman azabar da nayi a hannun Hajiya Raliyah, ko makiyina bana fatan yayi, balle kuma yar da na haifa. Wani abu da nayi Imani da shi, matukar na saka abu a raina, tow bana jin shamaki ga Ubangijina, haka kawai nake jin kwarin gwiwa a kansa, duk da ciwon kan da nake fama da shi, da yawan damuwar rashin Ahmad dina, haka bai hana ni, mika lamarin Yarana a wurin Ubangijina ba. Ranar da na cika wata daya dawowa a ranar da sassafe sai ga Alhaji Salisu, tare da Humaidah. Rike da ƙunshin kayanta, "Maamah" ta kira ni, wani irin bude mata hannu nayi, zubda kayan tayi ta fada jikina. Tana kuka tana faɗin, "Maamah kar ki kuma tafiya ki bar ni, Ma'amah please don't let anyone take me away " kara rungumarta nayi ina shinshina kanta, ina matukar Kaunarta irin soyayyar uwa da D'a, wani irin soyayyar ce me dauke da kauna. D'ago kai tayi ta ce min. "Maamah, kiyi hakuri kin ji Hajiya tace min wai ke witchers ne kin cinye Uncle Ahmad" "Ya rasu ne!" Ya fada in more sorrow. "Maamah ayya, sorry Maama!" Muryan Alhaji Salisu yana faɗin. "Ya Malam ga Humaidah nan, na dawo da ita na barwa Mahaifiyarta, ba wai ba zan iya riketa ba ne. A'a kawai zata fi samun kwanciyar hankali da nutsuwa idan aka ce a gaban Mahaifiyarta take zaune, Ya Malam gidana ya fi karfina tun kafin zuwan Falilah, bayan zuwanta kuma na samu gidan sai dan yanzu gidan sai ta Allah, kafin na dauki hakkin da ba zan iya saukewa ba, na dawo da ita. Zan yi kome amma ta zauna anan don Allah kar ku ga gazawata. "Allah ya taya mu riko" Ya Man ya faɗa,kafin ya tafi ya kira Humaidah, tashi tayi ta fita tana amsawa da Na'am Baba, fita suka yi can dai gata ta dawo dauke da manyan leduna, duk kayanta ne da kudi ya bata. Zama tayi a kusa da ni. "Maamah" "na'am" "inji Baba ya ce ki yafe mishi." "Allah ya yafe mana baki daya ." Shiru nayi can nace mata. "Humaidah! Ba kya wanka ne?" Shiru tayi tana kallon kasa, "ko how about school!" Rau-rau tayi da idanu. "Maamah, rabona da school tun kafin ki maida ni gidan mu, Hajiya tace ba zaa yi asarar kudi a yar karuwa ba." Abin tashin hankalin humaidah tana niman shekara sha biyu fa, amma baki daya yarinya fara jajjur ta koma bakakirin. Kalmar Yar karuwa ya tab'a min karma ɗina. "Maamah na tambayi Malamin islamiyya mene ne karuwa." Ba iya ni da nake ba, hatta Hajja Mama da Hajja Jume da zasu shigo birki suka ci. Gabana ne ya fara faduwa, ban san dalilin da nake tsoron maganar da yake shirin fitowa bakinta ba. Sai ji nayi ta ce min. "Maamah ya ce min, mutanen banza ne, Allah yana fushi dasu. Da har nace idan na girma nima karuwa zan...." Rufe bakinta nayi, tare da mikewa jikina yana rawa. Yadda jikina yake rawa yasa naji kamar ana jijjiga ni, a hankali jiri ya kwashe ni. "Innalillahi wa'inna illahi raju'un. Ke riketa" da sauti suka shigo dakin, salatin su yasa Hajja warisah shigowa, suka kama ni, ita kan Humaidah wani irin tsoro ne ya kamata, "Maamah don Allah kar ki tafi don Allah ba zan kuma ba, ba zan kuma cewa zan zama karuwa ba." Ta fada tana hada hannunta. Babu wanda ya bi ta kanta, suka fito da ni aka nufi asibiti da ni. Wato akan rayuwata na fahimci sha'anin Ubangiji, da idan ya wanzar da ikonsa babu me iya canzawa ko sauyawa. Haka yake akan cikin jikina, domin babu wanda be kawo cewa idan muka je asibiti ko kafin mu isa ya fita ba, domin jijjiga sosai nake yi. Bayan tafiyar mu Hajja ta koma wurin Humaidah ita daya. "Hajja Maamah zata dawo?" Rike hannunta tayi, suka zauna. "zata dawo in sha Allah, amma kar ki kuma gaya mata irin wannan maganar kinji, ko kina son ta mutu ne?" Fadawa jikin Hajja tayi tana kuka, "don Allah ki ce kar ta mutu, wallahi ba zan kuma fada ba, in sha Allah zan zama mutanen kirki " shafa kanta Hajja Maamah tayi tana faɗin. "in sha Allah, Falilah sai tayi alfahari daku, in sha Allah."
A can asibitin maternity aka wuce dani, a lokacin Aunty Zahra ta iso da Aunty Sadiya, domin dukkan su Nurse ne. Baki daya mu yaran Ya Man mata, School of nursing muke, amma ni kai tsaye a samu Degree a bangaren nurse din a Maiduguri. Karatun da na kammala shi da kyar. Ruwa aka yi ta daura min da magani, kafin na daina jijjigar sannan cikin jikina yana nan daram. Dole Ya Man da Matansa suka dawo gida, hanya Hajja Jume take gaya musu abin da ya faru. "Har ga Allah Ya Man maka kyauta ba, wallahi gashi kayi abin da baki daya zuri'ar Falilah zata lalace." Inji Hajja Jume. Kamar zai fashe da kuka ya ce musu. "Tow ya zanyi?" Baki daya ya koma kamar mutumin da bai tab'a zaman gaban Malam ba. "Ya kuwa zaka yi? Sai dai mu cigaba da mata Addu'oin, Ubangiji ya kare mata zuri'arta amma har ga Allah ka cutar da Falilah, ita bata ji dadin aure ba, ita bata ji dadin 'Yayanta ba, gaskiya da sakyal;" haka suka iso gidan, suna ta mishi mita, sun zo sun samu Hajja Mama ta kama Humaidah tana mata tsifa, sai satar kallonta Ya Man yake, domin baki daya idan ka cire masifar da su Hajja Jume suka masa ba zata, zai ji tashin hankali ba. Sai da ya ga yanayin fuskarta yadda take tsifar kawai karfin hali ne, gashi yadda take motsa bakinta zaka fahimci tasbihi take, "Falmata!" Ya kira sunanta. Murmusawa tayi ta amsa mishi. "Na'am Ya Man!" "Na zata fushi kike dani?" "Akan me?" "Akan Falilah!" Ya bata, "Ban gane ba?" Ta tambaye shi hankalinta yana kan tsifar. "Kin gane mana Falmata" "ikon Allah, tow Ni dai bangane kome ba." Ganin da gaske bata son maganar yasa shi juyawa yayi ficewarsa. Tasan babu me sauya kaddarar Falilah akan me zata cigaba da jin haushinsa? Ko daya bata jin zafinsa.
Falilah
Kusan wuni nayi a kwance, sai dare Allah ya nufa na farka. Karewa dakin kallo nayi, a hankali na gyara ƙwanciyata. "Zaki iya tashi?" Muryan Aunty Sadiya, "hmm" na ce mata, zuwa tayi ta cire min ruwan, sannan ta taimaka min na tashi zaune. Rike hannuna tai na sauke a sannu sannu, tana min sannun. Har ban daki ta raka ni. "Zaki iya wanka ko na taimaka Miki?" "A'a zan iya" na fada ina gyara zama na. Fitowa tayi ta cigaba da gyara dakin, tana hada min abin da zanci. Har na gama na fito, ajiye min doguwar riga tayi, na dauka tare da komawa ban daki na saka, sannan na dawo dakin. "Zaki ci abinci ne ko sai jin yi sallah." "Sallah zan yi" na fada a takaice, sannan fara kokarin shimfida abin sallah, karba tayi ta shimfida min. Wayar ta ce tayi kara, ta leka tana faɗin. "Huh Ya Nafi'u!" Kwalla ne suka cika min idanu, na d'ago kai na kafe da idanu. "Ok gata nan" mika min wayar tayi, na amsa da sauri. "Dady!" Na furta sai ga hawaye sharrr. "Mene ne?" "Dady Humaidah!" "Zan zo next week in sha Allah, ki bar kukan nan haka zan zo kin ji, da kyakyawar labari " "Allah ya kawo ka" na furta a hankali, sannan na mika mata wayar, sallah na gabatar tun raga azhr har isha, ina zaune a wurin, Addu'a nake akan Ƴaranta biyu nan, Humaidah da Hanif, Addu'a nake Allah ya tsare min Imaninsu, a hankali na fashe da kuka, domin Allah ya gani ban shirya ganin wani heartbreaking ba, wanda na gani ya ishe ni, wanda na samu kaina ya wadatar da ni, idan wani abu ya same su, kai karata zasu yi wurin Allah domin ban cancanci zana Uwata ta gari ba, "Lilly kukan ya isa haka, kodan lafiyar ki" "bar ni nayi kuka, bar ni nayi kuka, na cancanci haka ne, domin laifina yana shirin taɓa min Yarana." "Allah zai kare miki su, jininki ya haura sosai, idan kika shiga damuwa dan cikin ki mutuwa zai yi don Allah kiyi hakuri ki haife shi shima kamar sauran, Allah zai taya ki riko." Da rarrashi ta hanani kuka, Ya Kabiru da Ya Hamza, suka shigo da matan su. "Ke dai an yi yar bakin ciki, so kike ki hana mu cin naman suna!" Inji Aunty Jidda matar Ya Kabir, sai shihudah matar Ya Hamza. "sannu Falilah ya jikin naki?" Murmushi nayi nace musu. "Da sauki sosai fa!" Aunty Sadiya ta mika min mug na tea. A hankali na amsa ina kurba. "Assalamu alaikum" muryan Hajja Mama da Ya Bana, sai matar shi Ubaidah. "Sannu Lilly ya jikinki?" "Da sauki In-law" "Mamana ya jikinki?" " Da sauki Hajja ai da baki zo, ina ga ko zuwa gobe zasu iya sallamata." "Ai Yayanki ya kira yana tambayata wai da fatan kina lafiya, jikinsa ya bashi baki da lafiya" murmushi nayi nace mata, "Eh ya kira Aunty Sadiya mun yi magana da shi." A hankali hira yake tashi a cikin dakin, kafin can aka turo kofar, abokan aikina ne!" "Liman ya jikinki!" Murmushin gefen baki nayi nace musu. "Da sauki fa" "Ɗazun Ruth Joshua take gaya mana ta ga familyn Liman a asibitin nan bata san waye ba, ashe ke ce. Kiyi hakuri muna taso zuwa miki ta'aziya Allah bai nufa ba." "Kai Zuhrah sai kace bashi, baga shi kun zo ba. Ya aikin ki?" Dauke kai nayi daga kallon da Nurse Barak yake min, tare da kallon sauran abokan aikina da muka yi zaman mutunci. "Amma Dr Mu'awiyah bai sani ba ko?" "Sister Zuhrah" "Bro ai dole mu gaya mishi bata da lafiya." "Allah ya baki lafiya shi kuma wanda ya rasu Allah ya kyautata makwancinsa," ya fada yana kallona. "Amin Ya Allah!" Dauke kaina nayi ina dariya yaron nan, shi a yanzu sai ya ce zai dawo min da hannu agogo baya, ina bana fatan haka, yaje shima Allah ya haɗa da wacce zata kaunace shi. Duk Mazan da suka yi shiga rayuwata babu irin Ahmad, kuma ba zan tab'a samun irinsa ba. "Ki rage tunani, wanda ya mutu ya mutu, kina da sauran damar farinciki, idan wani abu ya same ki, akwai waɗanda zasu cutu sama da yadda zaki cutu!" D'ago kai nayi tare da bata rai. Shima b'ata rai yayi yana faɗin. "Muje!" Suna fita ya watsar da hannunsa. "sister Zuhrah! Mene ne mace take bukata a gare ni?" Sake baki tai tana kallon shi. "Ina da Muhalli, ina daukar albashi me kyau ne! Infact ina da mota, kudina saving dinsu nake domin matar da nake su but why falilah take jana a kasa?" Kallonshi sauran abokan aikinsu suke, "Malam Falilah ba zata aure ba, koda yake bana ce don kana junior ɗinta ba ne, a'a kowacce mace da irin nata tsarin, sannan duk Mazan da ta aura ba kananun mutane ba ne, so please ka barta ta ji da matsalarta." "Ina sonta ban damu ba" "Allah ya baka sa'a!" Barinsa suka yi a wurin. Sai wurin goma yan gidan mu suka bar asibiti, Washi gari da sassafe Zuhrah ta kawo min abin karyawa, anan take gaya min abin da ya faru, sai dariya take masa. "Idan kin fita ki kira min shi " na fada babu wasa a maganata. "Me zaki masa?" "Kawai kice ina kiransa" "Ok Ma!" Murmushi na mata, turo kofar da aka yi hade da sallama, yasa na d'ago kai. "Dr Mu'awiya ne!" "Good morning Dr" Zuhrah ta gaishe sa."Morning Zuhrah ashe kuma Falilah bata ji dadi ba " ya shigo yana kafaffa, kamar dai yadda yake can baya. "Sannu Queen ya jikinki?"
"Da sauki" "Allah ya baki lafiya, sai naji ashe Mijinki ya rasu!" "Eh" "Allah ya mishi rahama" "Amin Ya Allah" daga haka ya fita, yana kwambo da kwalisa. Nice na auri wannan me kama da ruwan surki, wai ma kusan mazawa na aura.
Salisu
Muhmoud
Dr Mu'awiya
Ayuba
Sani
Nasiru
Ahmad dunkule hannuna nayi, kamar na nutse a kasa, duk mazan nan babu wnada zan karar da labarin jin dadinsa sai Ahmadi, ya Allah na tuba. Bari na bude littafina wanda na binne shi domin boye abubuwa masu yawan gaske. Ban sani ba ko zaku tsinci inda nayi laifi ku gaya min na gyara domin Rayuwar Yarana, ko Allah zai tsiratar min da mutuncin Humaidah.
***
Rayuwata
Aishatou Falilah Mustapha Liman.....
#Mai_Dambu.