BABI NA BIYU
💎🌹 HAULA HABEEB 🌹💎
By
Amdeey Tejj d'Unique ✍️
BIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
BABI NA BIYU
HAULA
“Wayyo Gwaggo! Ni kam yunwa nake ji, ga shi yau kaina ya yi zafi, wallahi. Ni duk na gaji ma.” Ta yi maganar tana narkewa tare da zubewa a kan kafet.
“To ai dama haka shi karatu ya gada, sai an yi haƙuri da juriya zai wuce kamar ba a yi ba. Ki tashi ki cire uniform ɗin tunda Allah Ya sa yau ba ki yi datti da su ba kamar yadda kika saba.” Cewar Gwaggo.
“Wai Gwaggo kin san wani abu kuwa? Wani malami aka kawo mana mai shegen iyayi, ya wani dage sai wani Turanci yake mana ya ƙi yin Hausa. Ga shi ya dage sai kiran mamanmu da babanmu yake yi.”
“Ƙila karatun ne ya zo da haka. Tashi ki je ki sauya kaya ki ci abinci.” Cewar Gwaggo don yanke maganar, tun da ta san in dai ta fara wannan shirmen nata, to ƙarshe ba za a gama lafiya ba.
Maimakon ta tashi ta je ta yi abin da aka saka ta, tunda ta ce yunwa take ji, ina sai ta sake gyara zama.
“Wai kin san me Gwaggo, su kuma sauran yaran har da wani ‘yes’ suke cewa. Ni kam shiru na yi mai, na ƙi amsawa. To iyayena sun mutu, ya dage sai kiran su yake yi, yana ta wani ‘father’, ‘mother’. Na ce ni kam ba zan amsa zagi ba, har rubutun shi ma na ƙi yi tunda ya zage ni.” Ta yi maganar tana yatsine fuska.
Gwaggo ta zage ta, ta samu saitin bayanta da ma kusa da ita take, ta ɗuma mata wani uban dundu da ya sa ta gantsarewa. Ba shiri ta miƙe tana tsalle tana wayyo, tana cewa Gwaggo ta karya mata baya.
Cikin ɓacin rai ta ce, “Yanzu tsabar iskanci a yi muku karatu ki ƙi amsawa ki ƙi rubutawa, wai ke wace irin mutum ce?”
Cikin kuka ta ce, “To Gwaggo, ba ranar ba ne aka ce mana ‘father’ shi ne baba, ‘mother’ kuma mama?”
Yunƙurawa Gwaggo ta yi, a fusace ta yi waje. Gwaggo na kiranta, amma ina ta yi gaba. Kai kawai ta girgiza tana yi mata addu’ar shiriya a ranta. Ta fito ta zauna a hanyar garden tana sharar hawaye, don abin da Gwaggo ta yi mata yau ya yi mata ciwo.
Farida ce ta fito daga garden hannunta riƙe da waya tana dannawa. Kallonta ta yi, kamar za ta wuce, sai kuma ta dawo ta tsaya a kanta kafin ta ce, “Ke! Kukan uban me kike yi mana a gida kina cika mana kunne?” Ta yi maganar cikin izgilanci.
Ba ta ko kalleta ba balle ta sa ran za ta ba ta amsa. Duk da zagin da ta mata ya sosa mata rai, to amma tana gudun kada ta yi magana ta sake laifi a wajen Gwaggo, tunda ta ga kamar ba ta kishin iyayen nata ne. Idan ba haka ba, ta yaya za a zage su ba ta ma rama ba, amma a ga laifinta.
“Ke don ubanki ina magana kin yi min banza ko? Shegiya ’yar masu aiki, dama ɗan talaka akwai faɗin rai.” Jin Farida tana magana cikin hargagi shi ya katse mata tunani.
Ai kuwa ta kaita bango, don ko Gwaggo za ta kashe ta ne, wallahi ba za ta jure a ci mutuncin iyayenta ba. Don haka ta miƙe tsaye ta kai duba ga Farida cike da fitsara, ita ma ta ce, “Uban matambayi ya sani kukan. Kuma ai masu aiki mun yi muku rana, tunda muna yi muku aikin da kuɗin naku bai isa ya yi muku ba. Idan kin isa ki je ki zuba kuɗin a kicin ki ce ya dafa abinci ya kawo miki. Talauci kuma, Allahn da ya ba ku dukiya shi ya ba mu talauci, ba don ba ya son mu ba. Ba kuma don bai san hanyar da zai ba mu arzikin ba, sai don haka Ya ke son ganinmu mtsw!” Ta ƙarasa maganar da tsaki.
Cikin hargowa Farida ta ce, “Don ubanki, ni kike faɗa wa haka?”
“To, ai baki, in ya san abin da zai faɗa, bai san abin da za a mayar masa ba.” Ta yi maganar tana murguɗa baki har da wani fari da ido.
Ai kuwa Farida ta yi kanta, a guje ta kwasa ita ma. Ba ta ankara ba ta ji ta ci karo da mutum, shirin ƙwacewa take ta gudu, ta ji an riƙe ta sosai. Gabanta ne ya faɗi, ko dai hannun wancan azzalumin ne ta faɗa. Innalillahi, to yau dai da alama ba ta da sa’a.
Kici-kicin ƙwatar kanta za ta fara, ta ji muryar Farida na faɗin, “Yauwa Yaya! Wallahi yau sai na karya yarinyar nan, tunda ba ta da kunya.”
Jin an ce “Yaya” ya sa cikinta ɗurar ruwa, kenan a jikin mugun nan take. Innalillahi! Yau ita kam ai sai gawarta.
Muryar wanda ta ji ne a lokacin da Farida ta yi yunƙurin dukanta, ya sa ta saki wata ajiyar zuciya yana faɗin, “Ke! Me ta yi miki za ki doke ta?”
Wata sabuwar ajiyar zuciya ta sauke da ba ta san ta riƙe ba. Da wata ƙwarin gwiwa ta taso.
Farida ta ce, “Yaya Salim, zagin Mami da Abba ta yi fa, wai masu kuɗin...”
“Yi min shiru. Me kika yi mata ta zage ki? Haka kawai ai ba za ta zage ki ba, ko mahaukaciya ce ke?” Ya yi magana da zafi a muryarsa.
Za ta yi magana ya dakatar da ita da faɗin, “Za ki ɓace min daga gani ko kuwa?”
Bubbuga ƙafa ta hau yi, a guje ta shige cikin gida. Ya kai dubansa ga Haula, suna haɗa ido, kunya ta rufe ta tuni, sai ka ce da gaske ta yi zagin.
Kai a ƙasa ta ce, “Ba laifina ba ne Yaya, wallahi ita ta fara. Gwaggo ce kuma ta doke ni, na fito ina kuka, sai ta kama zagina, wai na cika mata kunne, shi ne shi ne...”
Salim ɗin da sauri yake saboda wani record ya zo ɗauka a ɗakin Habeeb, a ƙagauce ya ce, “Bar maganar nan Haula, idan na dawo sai mu yi sauri nake, yanzu mu je wajen Gwaggo na ba ta haƙuri.”
Bai jira amsarta ba, ya damƙi hannunta ya nufi part ɗin su da ita. Suna shiga suka tarar da Gwaggo za ta fito. Bai ɓata lokaci ba saboda saurin da yake yi, bayan ya gaishe ta cikin girmamawa kamar yadda ya saba, ya ba ta haƙuri sannan ya ce, “ Haula ta je ki cire uniform ɗin ki sa kayan gida.” Daga haka ya fice.
Duk da Gwaggo ba ta ji daɗin yadda ya riƙo hannunta ba, amma ta ɓoye hakan. Duk da cewa Salim ɗin ba shi da mugun hali, amma Shaiɗan fa ai bai bar kowa ba. Don Haula ta wuce lokacin da kowane namiji zai dinga taɓa ta kawai sai muharraminta, wanda a yanzu kuma ba ta da shi. Ita ba ƙaramar yarinya ba ce, girman ƙauye ne ya sa shiriritarta ta yi yawa. Duk da dai asalinta gaɓuwa ce, shekarunta sha biyar, amma yanzu take ƙirgar dangi. Har yanzu jira take ta ji ta ce mata ta girma, amma shiru, tana tsoron ta tambaye ta kuma ta shiga uku a wajen Haula. Don idan ta dinga shan tambayoyi, ko a kotu iyaka kenan. Idan ma ba ta canja mata ba, ta ɗauko wani sabon salo irin na ɗirkaniyarta.
Motsin Haula da ke raƙuɓe a bango ne ya dawo da ita zahiri. Kallonta ta yi, suka haɗa ido, sum-sum ta wuce ɗaki kamar munafuka. Ta so ta ba ta dariya, kuma ta ba ta tausayi, amma ba ta nuna ba don Haula zuma ce sai da wuta. Ta yi murmushi, ta wuce kicin.
Salim
Yana fitowa daga ɓangaren Habeeb da ke gefe guda na gidan, wanda shi ne asalin side ɗinsa bayan wanda yake da shi a can cikin gandun gidan, ya hango Mami da Farida za su nufi BQ da sauri. Ya fasa shiga motar da ya yi niyya, ya nufi inda suke don ya san abin da zai kai su.
“Mami, ina za ki?” ya tambaya kamar bai san inda za su je ba, bayan ya isa inda suke.
“Wannan mara kunyar yarinyar Gambon, za ni je in ladaftar da ita, tsabar samun waje har tana da bakin zagina da Abbanku.” Mami ta faɗa cikin fushi, don dama ba ta da haƙuri.
Ya kalli Farida, ta sunkuyar da kai, kafin ya kai dubansa ga Mami, sannan ya ce, “Mami, wannan munafukar ce ta zo ta gaya miki ƙarya da gaskiya ko? To wallahi ba haka ba ne, don ni na ji su, ita ta fara zaginta, kuma Haula ba ta rama ba, na zo wajen. Kin kuma san ba za ta zage ku a gabana ba.” Ya yi maganar cikin kare Haula.
Farida za ta yi magana, ya ce, “In kika yi min wata magana sai ji miki ciwo.”
Mami ta ce, “Kai ai dama ba ka ganin laifin wannan aljanar yarinyar, komai ta yi daidai ne. To, yau sai ta bar gidan nan tunda ba ta da mutunci.”
Za ta wuce, ya riƙo hannunta cikin ƙanƙantar da kai, da tausasa murya ya ce, “Haba Mami, kin san duk son da zan yi wa Haula ai bai kai ki ba, kuma kin san ba yadda za a yi ta zage ki in barta ko? Please ki yi haƙuri.” Ya yi maganar, hannunta cikin nashi, ya karyar da murya, “Haba Mamina, Babanki ne fa.”
Ajiyar zuciya ta yi, kafin ta juya ba tare da ta ce komai ba. Dole ta sa Farida ita ma ta bi bayan Mamin, rai a ɓace don ba haka ta so ba. Tana juyawa, Salim ya zabga mata ranƙwashi a kai, ta saki ƙara, Mami ta juyo, “Me ka yi mata? Ka daina taɓa mini yarinya fa, tam.”
“Sorry Mami,” ya yi maganar yana dariya, daga haka ya shige motarsa, ya fice...
******
“Wannan hanyar ta rushe, sai dai mu samo wata hanyar, amma ni ina zargin wani abu.”
“Eh, ni ma na yi wannan zargin, tunda kin san ba mu kaɗai ke yaƙin ba, dole akwai wanda ya yi mana zagon ƙasa. Amma ko waye shi, in har na gano shi, hmmm.” Ta yanke maganar ba tare da ta ƙarasa ba, tana jijjiga ƙafa, alamar dai Allah ne kawai ya san abin da za ta iya yi.
“Wannan haka ne, ya kamata mu nuna masa mu a tafe muka kwana, mu nuna masa banbancin baccin makaho da mai ido.”
“Wannan faɗa ma ai ɓatawa ne.”
“Amma yanzu me kike gani ya kamata next? Don kin san ba zuba ido za mu yi ba, ya kamata mu motsa.”
“Har yanzu ba a sake zama a kan maganar ba, amma na san za a yi, idan aka yi sai mu san abin yi. Ni zan wuce, lokaci ya tafi, kuma ina da wajen zuwa.” Daga nan ta miƙe, ta mayar da sun-glasses ɗin da ke fuskarta, ta sanya face mask, kamar dai yadda ta shigo ɗazu.
“Zan wuce, na riga na yi payment ɗin komai, sai anjima.” Daga haka ta fice daga VIP ɗin eatery ɗin da suka kama.
“A sauka lafiya, sai na jiki.”
Ba ta amsa ba balle ta juyo, ta yi ficewarta. Sai da ta tsaya ta karɓi ATM ɗinta a wajen cashier ɗin da ta ba shi tun shigowarta, kafin ta yi waje.
******
HAZ Mansion
Haula
Cikin dariya ya ce, “Haba Haula, ke wa ya ce miki zaginki yake yi?” Ya tambaya, dariyar ba ta sake shi ba.
“To ai na gaya maka, su suka ce mana ‘mother’ ita ce mama, ‘father’ kuma shi ne baba.” Ta faɗi da dukkan gaskiyarta.
Wata dariyar ce ta sake kama shi, ya ce, “Please Haula ki bar ni haka, amma wani subject yake koya muku?”
“Wai Social!!! Menene ma, oho, ni dai ma na manta. Yauwa ban faɗa maka ba, har da wai ‘and their children’ kuma ranar wannan malamin ya ce ‘children’ yara kenan fa. To, ni dai wannan makaranta ba zan sake zuwa ba, tunda mu da iyayenmu suke zagi. Su dai waɗancan su yi ta zuwa, dama yarane ba su da wayo. Ni ce dai mai hankali a ajin, sauran yarane kaf, don duk na girme su.”
Salim dariya kawai yake, da ƙyar ya samu ta sassauta, kafin ya ce wani abu ta sake tare shi da wata maganar.
“Yauwa ka san me? Da na faɗa mata sai ta hauni da faɗa, har tana dukana. Haka ranar wai zan tayar wa mutum hawan jini ya mutu. Kuma ranar malaminmu ya ce mutum ba ya rayuwa sai da jini, tsakani da Allah idan jininka ya hau ba ka gode ba, idan kuma ya yi ƙasa ya ƙare kenan fa, sai ka mutu. To, ni kam Allah ya sa nawa ya dinga hawa kullum kar in je in mutu. Ka san fa ita Gwaggo ba ta yi boko ba, sai karatun allo irin na ƙauyenmu, shi ya sa ba ta sani ba, amma zan dinga koya mata idan na dawo.”
A wannan karon, Salim sai da ya sauka a kan kujerar da yake saboda dariya, yana so ya tsaya ko don ya ganar da ita sosai ta fahimta, amma ina.
Habeeb da ke tsaye jikin tagar ɗakin nasa yana waya, kasancewar a garden suke, daga windon ɗakinsa kuma kana hangen wani ɓangare na lambun, yana ta hangen su tun ɗazu. Shi yaushe rabon da ya ga wannan aljanar yarinyar ma? Tun ranar da ta yi mishi wannan haukan, Daddy ya hana shi ɗaukar mataki, ba su sake haɗuwa ba sai yau da ya gan su da Salim. Tsaki ya ja, a ransa yake faɗin Salim akwai ja wa kai raini. In ba haka ba, meye na wannan dariyar a gaban wannan mara kunyar yarinyar? Ba ka ba ta fuska ba ma ta rainaka, balle kana mata dariya irin haka. Ya sake jan tsaki, shi Salim ɗin ma ya fi ba shi haushi. Ba jin me suke cewa yake yi ba, amma ya san bai wuce haukar da ta saba ba, shi kuma ya dage sai dariya yake kamar gaula. An ce zama da maɗaukin kanwa ke kawo farin kai, to ko dai shi ma ya fara tafiya ne?
Tsaki ya ja, kafin ya bar jikin tagar ya koma cikin ɗakin. Ɗayar wayarsa ya ɗauko da ke kan sofa, ya shiga recent calls, lambar Salim ɗin shi ne last call ɗinsa jiya, hakan ya sa yana shiga bai sha wahalar nema ba ya danna mai kira. Sai da ta kusa yankewa kafin ya ɗaga.
Salim, da bayan dariyar da yake ta lafa, yana shirin fara wa Haula magana kenan, ya ji wayarsa na ruri. Ya ciro daga aljihun wandonsa, ganin mai kiran ne ya sa sai da ya sake saita kansa kafin ya ɗaga, tana daf da tsinkewa ya ɗora a kunnensa. “Ka zo ina part ɗina,” abin da aka furta kenan bayan an yi sallamar da ko amsawa ba a bar shi ya yi ba, aka katse wayar. Ya murmusa kawai, sannan ya miƙe ya ce, “Haula, bari in je, ana kirana, amma za mu ƙarasa, kin ji.” Duk da yana so ya fahimtar da ita abubuwan sosai yadda za ta fahimta, don a bayananta ya gano tana da fahimta da kuma riƙe abu idan aka faɗa mata, sai dai wauta da yake damunta da kuma ƙauyanci.
“Ina za ka je? In zo in raka ka?” ta tambaya.
“Wajen mutuminki zan je, za ki je?”
“Toooo, wa zai je wajen wannan da ba ya dariya? Ai sai kai. Sai ka dawo, na san yanzun nan kila ma Gwaggo tana nemana.” Ta miƙe ba ta jira amsarsa ba ta fice.
Ya bi ta yana murmushi, shi ma ya fice daga lambun, ya nufi sashen Habeeb. Yana zuwa ya sa key ya buɗe ƙofar, kasancewar yana da makullin ɓangaren. Bai tarar da shi a parlour ba, sai ya nufi bedroom ɗinsa. Zaune ya same shi a kan sofa yana danna computer.
Bai zauna ba, ya ce, “Gani bro, ya aka yi?”
“Zauna,” kawai ya ce, ya ci gaba da aikinsa. Kusan awa ɗaya yana zaune, bai ce masa komai ba, kamar ma ya manta da shi ne. Ganin hakan ya sa ya magantu.
“Bro, wai ya ake yi? Almost one hour ina zaune ba ka ce mini komai ba.”
“Eh, na sani, ban manta da kai ba.” Ya yi maganar bai ko kalli inda yake ba.
Zaman ya ci gaba har kusan minti 30, zuwa yanzu ya fara gundura da zaman, ga shi kuma ba hira ake yi da shi ba, sai dai ku yi ta zama uwa kurame.
“Bro, ko in je in dawo ne?”
“A’a.”
“To, wai me zan maka ne? Ka faɗa mini sai in je, kai kuma ka ci gaba da aikinka.” Ya yi maganar cike da gundura da zaman.
Rufe laptop ɗin gabansa ya yi, ya kalle shi kafin ya ce, “So kake in barka ka je ka zauna kana shashanci da kai da waccan mahaukaciyar ko? Wai kai Salim, ko kai ma ka fara zama irinta ne? Da alama kai ma kan nan naka da motsi, if not ta ya za ka zauna kana dariya hahaha a gaban yarinya, neman ta rainaka ko? Wannan yarinyar da ba ta ga fuska ba ma, ya aka ƙare da ita? Ba inda za ka je, ka zauna a wurin.” Daga haka ya ci gaba da aikinsa.
‘Na shiga uku,’ Salim ya faɗa a ransa. “Yanzu tsakani da Allah, ni yaro ne za ka ce za ka min kulle? Ga shi kai ba hira ake yi da kai ba, sai dai mutum ya zauna har bakinsa ya yi tsami.” Shi abin ma dariya yake son ba shi. Wai shi ne za a kulle kar ya fita? To, ai ko Farida idan ba babban laifi ta yi ba, ba ya tunanin za a yi mata haka balle shi.
Ƙala bai ce masa ba, ya ci gaba da aikin gabansa.
“Bro, in dai Haula ce ma ka bar ni don ta tafi, kuma akwai inda zan je.” Nan ma bai kula shi ba.
“To, shikenan sai mu yi hira to, tunda ka ƙi ka bar ni.” Nan ya fara ɗauko masa zantuka kala-kala, ya ɗauko hirar office, ya ɗauko na duniya.
“Wallahi Salim, idan ba ka min shiru ba sai na sa tape da super glue na liƙe maka baki. Kai ba ka gajiya da surutu ne? Mutum ya yi ta magana ba gajiya, mtsw.” Ya ƙarashe maganar da tsaki, don shi kansa har ya fara gajiya da surutan Salim.
“To, sai ka bar ni in tafi, don ba zan iya zama kamar kurma ba.”
“Okay, to tashi ka fita.” Ya yi maganar cikin gatse.
Tashi Salim ɗin ya yi kamar bai fahimci da gatse ya yi ba.
“Wallahi idan ka fita sai na ɓata maka. Ka zauna kuma ka min shiru.” Daga haka ya juya bai sake magana ba.
Yau ina ganin ikon Allah ni kam, ƙiri da muzu, wai ni ake wa kulle sai ka ce mace. Ya san tunda ya rantse, to ba da wasa yake ba, hakan ya sa ya koma ya zauna ba da son ransa ba. A ransa kuma yana mamakin yadda ya tsani haɗa shirgi da Haula, ita ma kuma a ɓangaren ta haka. Wayarsa ya ciro ya tura wa Mommy saƙo, don ya san ita kaɗai za ta fanshe shi. Ba a ɗauki lokaci ba kuwa ta kira shi, ya ɗaga da gangan ya sa wayar a hands-free.
“Hello Mommy, barka da rana.”
“Yauwa Salim, na ce saƙon nan da na ba ka ka kawo mini, masu shi sun zo karɓa.” Mommy ta furta daga cikin wayar.
“Okay Mommy, amma ki tambayi Bro don ya sani aiki."
"Okay, ba shi wayar.”
Karɓa ya yi, kafin ta ce wani abu ya ce, “Okay Mommy, zai kawo.” Ba ta ce komai ba ta yanke kiran. Maimakon ya ba shi wayar, sai ya sa a aljihunsa ya miƙe, don ya san ƙarar ta isa wajenta. Keys ɗin da ke kan centre table da Salim ɗin ya ajiye bayan ya shigo, ya sa hannu ya ɗauka, shi ma ya zira aljihunsa.
Da kallo kawai Salim ke bin sa, mamaki ya hana shi magana. Muryarsa ya ji yana faɗin, “Bari in je in kai mata da kaina.” Daga haka ya fice ba tare da ya jira me zai ce ba, ya fice daga side ɗin baki ɗaya, ya kulle ta waje.
Bai motsa daga inda yake ba, don ya san kullewa zai yi. Haushi kam iya haushi ya shaƙa, don yau Bro ɗin nashi ya kai shi bango, kuma sai ya san ya yi masa haka. Gyara zama ya yi kawai ya kwanta a kan sofa don haushi, ko inda TV yake bai nema ba. Haka ya yi ta juyi a kan sofa har barci ya yi awan gaba da shi don dole.
#amdeey_tejj_dunique
#haulahabeeb.