Chapter 18
Qarfe goma na safiya driver Momma ya yi parking a compound ɗi gidan Safiyyah.
Tun qarfe takwas na safe ta shirya amma tunanin Ko HAYDAR ya na gida ya sa ta ɗan jinkirta, ga shi ta kira wayar Safiyyah ta tambaye ta amma wayar ba ta shiga.
A parlour ta haɗu da Barira me aikin safiyyah,tsugunnawa Barira ta yi ta ce barka da zuwa Hajiya ina kwana,lafiya qlau Barira ALIYU yana gidan? Ta tambaya.
A'a Hajiya ya koma wurin aiki.
Tana jin haka ta wuce ɗakin Safiyyah direct.
A ɗaki ta same ta a zaune tana ta tunani, ba ma taji shigowar ta ba sai da ta dan taɓa ta sannan ta juyo a ɗan tsorace.
Ganin Momma ce ya sa ta yi ajiyar zuciya ta ce sannu da zuwa Momma yawwa Safiyyah.
Ina kwana, lafiya qlau.
Gefen gadon ta zauna ta na kallon ta, sai da ta gama studying ɗin ta for some minutes sannan ta ce me kike son faɗa man Safiyyah?.
Shiru ta yi ta kasa magana sai kuma tace,kafin na faɗa maki abinda nake son faɗa ina roqon ki ki yafe man Momma.
Shiru tayi tana tunani sai kuma ta ce kar ki ji komai Safiyyah baki da wanda ya dace ya san matsalar ki sama da ni.
Kuma na yafe maki,mu ke yi wa Allah laifi ya yafe mana,meyasa bazan yafe maki ba ? Abin farin cikin ma kin yi nadama.
Murmushin qarfin hali ta yi ta ce nagode sosai Momma,sannan ta fara magana.
Wata rana bayan mun fito daga lecture, ina ta jiran Hamma Khaleel ya zo ya dauke ni amma bai zo ba.
Hakan ya sa na zauna a bakin department din mu ina jiran shi.
Na dade a zaune sai ga wata course mate ɗina shema'u.
Zama tayi a gefe na ta ce man sannu, ɗagowa na yi daga danna wayar da na ke yi na ce mata yawwa.
Murmushi ta yi ta ce ina yawan ganin ki a class amma bamu taɓa magana ba.
Murmushin nima na yi na ce eh.
Muna zaune sai ga wata mota ta tsaya a dan gaba da inda muka zauna kaɗan.
Matasan samari ne su biyu suka fito daga cikin motar.
Har sun wuce mu sai suka dawo,ɗaya daga cikin su ne ya ce sannun ku muka ce yawwa.
Wanda ya fara yi mana magana ne ya qara cewa don Allah office din H.O.D muke nema ba mu gane kwatancen da aka yi mana ba.
Tunda suka zo ido na ya sauka akan wanda bai ko kalli inda muke ba,ban taba jin ina son wata halitta a rayuwa ta ba kaman yadda naji ina son shi a lokacin ba.
Amma sai dai kash, ko arziqin kallo ban samu daga gare shi ba,shema'u da ta fuskanci hankali na baya wurin sai tayi musa kwatance.
A cikin zuciyar ta kuma ta ce Alhamdulillah ga dama ta samu.
Bayan ta gama yace ya gode sannan suka bar wurin, bayan sun tafi ta ce qawata na ga hankalin ki gaba ɗaya baya nan da alama kin kamu ta faɗa ta na dariya.
Murmushi na yi na ce a'a kawai ina tunanin wani abu ne,kallo na ta yi ta ce haba Safiyyah ai hausawa suka ce labarin zuciya a tambayi fuska.
Kar ki ji komai ai ba haramun ba ne,kiyi mashi magana sai ki ga an dace kin san fa hausawa sun ce a rashin tayi akan bar arha.
Maganar da ta fada ne yasa naji na samu qwarin gwiwa.
Muna zaune a inda muke suka fito zasu tafi sai na tashi na je inda suke na ce har za ku tafi?
Wanda ya yi mana magana da farko shi ne dai ya qara cewa eh,murmushi nayi nace toh masha Allah amma don Allah idan ba damuwa zan iya yin magana da kai ?
Nayi magana ina kallon wanda yaqi cewa komai, wanda suke tare da ya fahimci magana nake son mu yi sai ya koma cikin mota ya zauna.
Gaida shi nayi amma bai amsa ba ya ce malama ki fadi abinda zaki fada sauri na ke yi.
Hakan da ya fadi yasa naji duk jiki na ya yi sanyi, sai na ce ka yi haquri na tsayar da kai, dama ina son na fada maka ne ina sonka kuma idan babu damuwa ina so ka bani dama mu fahimci juna.
Kallo na ya yi irin kallon anya kanki ɗaya kuwa? Sannan ya daure fuska.
Ko me ya tuna oho sai kuma ya sassauta da hade ran da ya yi ya ce ke yarinya ce,maganar soyayya ba ita ya kamata ki maida hankali a kai ba.
Kamata ya yi kiyi focusing akan yadda zaki gina rayuwarki,kinji?.
Yana gama fadin haka ya wuce cikin mota ya bar ni a tsaye a wurin.
Ina kallo motar su ta bar wurin, sai bayan sun tafi na iya ɗaga ƙafafuna na koma inda muke na zauna.
Ina zama ta ce ya kuka yi da shi?
Girgiza mata kai nayi alamun babu nasara.
Kafaɗa na ta dafa ta ce kar ki damu, wannan duk mai sauqi ne idan har zaki bani hadin kai.
Nayi maki alƙawari shi da kanshi zai zo ya neme ki.
Kallon ta na yi da mamaki na ce ta ya ya hakan zai yi wu kina gani fah bai ko saurare ni ba da na yi mashi magana?
Dariya ta yi ta ce kar ki damu, ki bar komai a hannu na.
Ban wani dauki maganar ta na sa a zuciya ba don ban ga ta yadda hakan zai faru.
Lokacin da Hamma Khaleel ya zo dauka ta ta ce na ba ta number na, fada mata nayi sai ta kira ni ta ce nima nayi saving number ta.
Wata rana ina zaune a ɗaya daga cikin gossip chairs na bakin departement ɗin mu,sai ga wata baƙar lexus ta yi parking a ɗan nesa kaɗan da inda na ke a zaune.
Ban ko ɗaga kai ba na cigaba da karatun da nake yi.
Alamun tsayuwar mutum na ji a gefe na hakan ya sa na ɗago na ga waye?
Idanu na firfito da su waje don ban yi tsammanin qara ganin shi ba.
Murmushi ya yi man abinda ya qara dimauta ni kenan,don idan ban yi qarya babu wanda ya kai shi iya murmushi kaf faɗin duniya.
Empty seat ɗin dake gefe na ya nuna ya ce may i?.
Gyada mashi kai na yi da sauri na ce why not.
Zama ya yi sannan ya ce i'm sorry about the last time, ina cikin ɓacin rai ne shiyasa.
Murmushi na yi na ce babu komai.
Kallo na ya qara yi sannan ya ce dama na zo ne na sanar da ke nima abinda na ke ji akan ki.
Tun lokacin da ki ka yi man magana na ji nima na kamu da son ki amma a lokacin raina a ɓace ya ke shiyasa,amma yanxu a shirye na ke na karɓi soyayyarki.
Kuma ina son da kin koma gida ki sanar da su saboda ba na son a dauki lokaci ba tare da na mallake ki ba.
Sunkuyar da kaina na yi alamun naji kunya.
Momma zaki iya tuna wata rana da na dawo gida ina ta farin ciki? Kowa ya rinƙa tambaya ta me yasa nake ta murmushi?.
Jinjina mata kai Momma ta yi alamun ta tuna.
Cigaba ta yi da ba ta labarin ta ce toh ranar ne HAYDAR ya furta ta man kalmar so ya kuma ce na faɗa a gida zai turo iyayen shi a sa mana rana.
Bayan kwana goma da haduwar mu da HAYDAR soyayya ta yi qarfi a tsakanin mu,kullum mu na cikin waya da juna.
A lokacin ne kuma kwatsam wata rana ina kwance sai ga kiran Shema'u,bayan mun gaisa ta ce ƙawata kin samu kan saurayi kin manta da ni ko?.
Dariya na yi na ce haba ya za'a yi na manta da ke.
Toh ai shikenan tunda kin ce haka.
Wani abu na ke son faɗa maki.
Tohm ina jin ki.
Na san dai kin san ba haka kawai aka samo kan saurayin ki ba ko?
Da rashin fahimta na ce ban gane me ki ke nufi ba.
Dariya ta yi ta ce ban san rainin wayo, kin san dai da taimakon boka aka shawo kan shi ko?
Dafe qirji na na yi na ce na shiga uku boka fa ki ka ce Shema'u me ya haɗa mu da boka kuma?.
Don Allah ki ce man da wasa ki ke?
Ganin ina raina mata hankali yasa ta ce kin ga idan har hakan bai yi miki ba sai na sa boka ya dakatar da aikin da yake yi.
Banyi tunanin komai ba na ce eh gaskiya ki sa shi ya daina ni na san HAYDAR tsakani da Allah ya ke so na ba wani asiri.
Ta na gama jin abinda na ce ta ce toh shikenan kuma kar ki zo kina kuka da ni daga baya.
Ina da yaqinin tsakani da Allah HAYDAR ya ke so na sai ban damu ba.
Ba mu taɓa yin awa biyu ba mu yi waya ba amma ranar na kira wayar HAYDAR ya fi sau goma be ɗaga ba daga baya ya ɗaga ya ke tambaya ta wacece ni?
Babu bayanin da ban yi mashi ba amma yaqi ya fahimce ni ya tabbatar min da be sanni ba.
Da farko na ɗauka wasa yake naga abu har washe gari.
Gashi na yi wani irin shaquwa da shi wanda nake ganin bazan iya rayuwa babu shi ba.
Hankali na ya yi ƙololuwar tashi bani da wata mafita sai ta qara kiran Shema'u.
Da na yi mata kiran farko bata ɗaga ba, na qara yi mata na biyu tana ɗagawa ta fashe da dariya ta ce haba yan mata tun a kwana na biyu?
Qasa da murya na yi na ce don Allah Shema'u ki yi haƙuri ki taimake ni na yadda kiyi duk abinda ki ka san hankalin HAYDAR zai dawo kaina na yadda.
Dariya ta yi tace yaro yaro ne ai dama ta yaro kyau ta ke ba ta ƙarko.
Shikenan tunda kin ce haka nan da minti goma zai kira ki a waya.
Tun bayan da muka kashe waya na ke kallon lokaci amma sai naga kaman ma baya gaba, haka na yi haƙuri na cigaba da jira har minti goma ya cika.
Yana cika sai ga kiran shi yana shigowa cikin waya ta,wani ihu nayi kafin na ɗaga.
Marairaice murya ya yi ya ce kwana biyu ba mu yi waya ba amma ban damu ba.
Bana san duk wani abu da zai tuna min baya hakan yasa na ce ma sa bana da lafiya ne.
Ina faɗin haka ya ce sai ya zo ya duba ni da qyar na lallaɓashi ya haqura.
Haka rayuwa ta cigaba har aka zo aka yi maganar auren mu.
Tun bana iya zuwa wurin bokan da kai na har na fara zuwa.
Bayan mutuwar maman Ayaanah Shema'u ta ce man yanxu lokaci ne da ya kamata nayi amfani da shi wurin azabtar da Ayaanah dan ita ce zata iya kawo man tsaiko cikin rayuwa ta da HAYDAR.
Nayi amfani da shawararta kullum ina cikin azabtar da ita tun tana jaririya.
Kuma ita ce ta hana a bawa Mamy Ayaanah ta riqe ta.
Naje wurin bokan da yake yi mana aiki ne na tarar ya mutu gawar shi babu kyan gani,nayi kuka na yi da na sanin rayuwar da na jefa kaina saboda son zuciya don Allah Momma ki yafe man ki kuma taya ni bawa HAYDAR haƙuri don na san tabbas an zalince shi.
Nayi nadamar duk wani abu da na aikata.
Kuma a shirye nake na karɓi duk wani hukunci da za'a yi man.
Tunda ta fara magana Momma ke kallon ta amma ta rasa abinda zata ce mata.
Wayarta ta dauka ta kira Addah Fatimah da Hamma Khaleel ta ce su same ta a gidan Safiyyah yanxu.