Chapter 19
Bayan tafiyar Tasneem Munarh ta kalli Jay ta ce
" Wai ni Jay har yanxu besty na maiduguri?."
Shiru ta yi bata amsa mata ba, amma har idon ta ya fara haɗa ƙwalla.
Saurin majewa ta yi don kar Munarh ta gani.
Sai kuma ta ce " muje ciki sai na faɗa maki."
Ɗakin Mom ta kai ta sannan ta ce " toh ga Mom nan ki tambaye ta."
Ta fita daga ɗakin baki ɗaya tana goge hawayen da ya fara sakkowa kan kumatunta.
Mom ce ta kalleta ta ce " daughter me ki ka tambayeta?."
Ce mata fa kawai na yi " har yanxu besty na maiduguri?."
Ita ma shiru ta yi da farko sai kuma ta ce " boye miki ba shine maslaha ba, tunda duk tsawon lokaci dole zaki sani."
" Bayan qannen mahaifinki sun zo sun tafi da ke, wata rana na shiga gidan ta ke ce man bata da lafiya."
" Na ce ta je asibiti?."
" Tace man a'a."
Ni ce ma na takura akan dole sai ta je asibiti,sai ta ce shikenan gobe da safe sai taje.
" Washe gari da safe ni da kai na na je na kaita asibiti."
" Anyi duk wani gwaje gwajen da ya kamata amma ba'a gane me ke damunta ba."
" Hakan ya sa suka ce zasu riqe ta na yan wasu kwanaki don su qara bincikawa sosai."
" Washe gari da safe na haɗa breakfast na tafi asibiti."
" Lokacin da na je asibitin ta yi man murmushi ta ce har na zo?."
" Na ce mata eh, ya jikin na ta?"
" Ta ce da sauqi amma yau numfashi ne ke ba ta wahala ."
" Na ce shima zai yi sauqi in shaa Allah."
Hannu na ta riqe ta ce " Maman Jay ina ji a jiki na mutuwa zan yi."
" Don Allah ko wata rana kin ƙara haduwa da Maimunatu,ki faɗa mata ina sonta kuma na so a ce rayuwa ta bani wata damar da zan yi rayuwa tare da ita."
" Nasan ko ban faɗa ba zaki riqe man ita kaman 'yar ki da kika haifa."
Tari ta fara saboda maganar da take yi.
" Kiyi shiru ki dena magana kinga kin fara tari."
Duk da ta yi shiru amma bata daina tarin ba.
Lā ilāha illā Allāh, Muḥammadun Rasūlullāh na ce ta yi ta maimaitawa.
A hankali ina faɗa tana maimaitawa.
Murmushi ta yi qara maimaita Lā ilāha illā Allāh, Muḥammadun Rasūlullāh, " a lokacin ne kuma rai ya yi halin sa."
Tunda Mom ta fara magana Munarh ke hawaye,
Rungume ta Mom ta yi ta ce " ki yi haƙuri kin ji Maimunatu."
" Addu'a za ki yi mata, ba kuka ba, and in shaa Allah ba zan taɓa bari ki yi kukan rashin uwa ba."
Jinjina kai ta yi ta ƙara rungume Mom sannan ta ce " ina da tabbacin za ki yi man fiye da abinda besty zata yi man."
" Allah ya jiƙanta ya yi mata rahama."
" Ameen."
Ɗakin Jay ta koma ta ga sai raɓe raɓe ta ke ba ta san ma haɗa ido da ita.
Ji ta yi tana son ta ɗan fita daga gidan ta sha iska,
Sai ta kalli Jay ta ce
"wai ni a wani garin Mamy ta ke?"
"A nan garin take Jay ta bata amsa"
" Yawwa ki shirya gaskiya muje gidan ta."
Kallon ta ta yi ta ce " yamma fa ya yi,why not ki bari zuwa gobe?"
" Gaskiya ni yau na ke son mu je."
Kallon ta ta yi ta ce " gaskiya Munarh kina da matsala."
Murmushi ta yi ganin har ta ɗan sake da ita.
" Dama har yanxu kina nan da wannan ɗan banzan taurin kan na ki Munarh?."
" Yanxu dai tsaya na shirya tun kafin ki cinye ni ɗanya,ta fadi haka tana dariya."
Munarh ta zauna a gefen gadon tana jiran Jay ta gama shiryawa.
Ganin yamma ya riga ya yi yasa ta ɗakko wata plain doguwar riga na material da vintage scarf ta saka.
Bayan ta gama shiryawa ta ce " Muje."
Ɗakin Mom suka shiga suka faɗa mata inda zasu je,Allah ya kiyaye ta ce musu.
" Mom ina Ayaanah? sai mu tafi da ita."
" Ayaanah tana ɗakin Hajiya."
"Tohm shikenan bari muje sai mu tafi da ita"
Ɗakin Hajiya Mama suka je, tare suka same su da Ayaanah Hajiya Mama na bata labari ita kuma tana aikin dariya.
Tana ganin kowa da shiri ta ce " ku kuma ina zuwa kuna gani dare ya fara ?"
Munarh ce ta yi dariya ta ce " kai Hajiya Mama ko fa qarfe shida bata yi ba kina kiran dare."
" Gidan Mamy zamu je na gaishe da ita."
" Wai Aisha ki ke nufi?.
" Ki ji man tsohowa da muna da wata Mamyn ne ban da ita."
"Ai shikenan sai ku yi ta zuwa."
" Jay ta kallla ta ce dama wani abu ya dade a raina ina son na faɗa amma dai na kama baki na na tsuke."
" Wai ni Aisha ko ta canja hali ne.?"
" A iya sani na duk lokacin da na ɗebo qafa na zo Abuja, zaki ga ta zo gaishe da ni amma wannan karan shiru kake ji kaman an shuka dusa."
" Ko dai sabbin ƙawaye ta yi suka hure mata kunne?."
" Da dai ba haka take ba wallahi."
Girgiza kai Munarh ta yi ta ce " mai hali dai ba zai taɓa canjawa ba."
" Yanxu dai Ayaanah muka zo mu ɗauke maki tare da ita zamu je."
Kallon su ta yi ta ce " A'a babu inda zaku je da ita ku in kun saba da gantali da dare,ita dai babu inda zata je."
" Haka nan ta fita taje ta kwaso mura?."
" Ku dai da ku ka yi niyya sai kun dawo."
Babu yadda suka iya suka ƙyale ta suka tafi.
Suna zuwa Jay ta yi leading ɗin ta har zuwa entrance ɗin gidan.
Taɓa handle ɗin qofar ta yi sai ta ji shi a buɗe sai kawai ta tura qofar ya bude.
Babu kowa a parlourn ƙasa sai kawai suka wuce na sama.
Tun a stairs ɗin qarshe Jay ta fara jin maganar Jiddarh tana ta bawa Mamy labari.
Sallama suka yi bayan sun shigo cikin parlourn.
Mamy da ta basu baya ta juyo don jin muryoyin su a bayan ta.
Su din ne kuwa ba kowa ba.
Jiddarh ce ta taahi da gudu daga inda take zaune ta rungume Jay ta ce " aunty Jay yau ke ce a gidan nan?.
" Lallai za'a yi ruwa da ƙanƙara, ta faɗa tana dariya."
Mamy dake ta kallon Munarh ta ce " ƙaraso Maimunatu na rungume ki."
Qarasawa ta yi wurin Mamy ta rungume ta ta ce " na yi kewar ki sosai Mamy."
"Nima na yi kewar Maimunatu."
Jiddarh ta kalla ta ce " ahhh lallai su Jiddarh an girma."
Dariya ta yi ganin yadda Jiddarh ke kallonta tana ta son ta tuna imda ta san ta.
Ta ce " Kin ga Mamy Jiddarh bata gane ni ba."
Dariya ita ma Mamy ta yi ta ce " Haba dama ya za'a yi ta gane ki, lokacin da ki ka tafi she's just ten."
" Kin ga kuwa ai ba za ta gane ki ba."
Jinjina kanta ta yi alamun gamsuwa ta ce " kuma haka ne."
" Mamy ina yaya HAYDAR da yaya Zannur?."
" suna Lagos,da yake a can suke aiki,ta bata amsa."
" Amma dai sunyi aure ko Mamy? Ta ƙara tambaya."
Dariya ta yi ta ce " Hali dai yana nan ashe har yanxu.
Dariya ta yi ba ta dai ce komai ba .
Jay ta ce " ai sai abinda ya ƙaru Mamy don Mass communication ma ta karanta."
Dariya Mamy ta yi ta ce " ai ga alamu nan sun nuna."
Hira suka yi sosai har sai bayan maghriba sannan suka yi ma Mamy sallama suka tafi.
"Momma, ko ɗume waɗi nde noddu-ɗaa min e suudu Safiyyah?"
( "Momma lafiya ki ka kira mu gidan Safiyyah?.")
Addah Fatima ta faɗa bayan sun shigo parlourn Safiyyah ita da Hamma Khaleel.
"Jam alaa, Fatima."
("Ina kuwa lafiya Fatima")
" Ina cikin tashin hankali."
" Na rasa wani irin tunani zan yi ƙwaƙwalwa ta ta cun ku she, shiyasa na kira ku."
"Ko ɗume waɗi?"
" Momma lafiya me ya faru Hamma Khaleel ya tambaya."
Abin da Safiyyah ta faɗa mata ta faɗa musu baki ɗaya.
"Ɗum wonaa tarbiya ka mbadanaa maa Safiyyah."
(" Wannan ba ita ce tarbiyar da aka yi maki ba Safiyyah.")
"Ɗum wonaa no tarbiya maa waɗi."
("This is not how you were raised.")
"A yewtii tarbiya Mamma."
(" kin ci amanar tarbiyar Momma.")
"Taa haala e makko."
(" Ba faɗa zaku yi mata.")
"Don Allah, njaafoy on. Wallahi, mi nadamii ko mi waɗi. Ko Ceyɗan majjiniyam, Mi yiɗaa waɗde ɗum, amma mi waɗii kusur."
(" Don Allah ku yi haƙuri wallahi nima na yi nadamar abinda na aikata sharrin shaiɗan ne wallhi ba da son raina ba ne, na san na yi kuskure.")
"Nadamde tan waɗi? Tawa a anndi ko waɗi. Allah yo yaafo maa."
("Kina ganin nadama kaɗai ta isa?kin san kuwa abinda ki ka aikata?Allah ya yafe maki.")
Addah Fatima ta faɗa kasancewar ta fi Hamma Khaleel zafi.
Kuka Safiyyah take yi sosai tana ƙara nadamar abinda ta aikata.