MAƘOFTAKA DA ALJANU

Chapter 4

by @deejasmah

MAƘOFTAKA DA ALJANU 

Khadeejah Bint Ismail (Deejasmah) & Ameenah Abubakar Ƴandoma 

CHAPTER 4

…Daurewa ta yi tare da kirkiro murmushin da ita kanta ta san bai kai zuci ba. "Sannu ku" ta fada tana karewa matan guda biyu masu zubin larabawa kallo. Murmushi suka yi mata tare da yi mata wani irin murmushi da ya karasa firgitata. Ita dai a tsawon rayuwarta zata iya cewa bata taɓa ganin mutane masu haske fari sol tamkar ka taba jini ya fito ba irin matan nan ba. "Ba ki gane mu ba ko? Baki ne mu wancan gidan na kusa dake masu shi ne suka dawo, munga ke ce makwafciyarmu shi ne muka zo ki taimaka mana zamu debi ruwa a cikin rijiyarki da kuma aron tsintsiyar kwakwa" Muryar daya daga cikin matan ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula. Sake watse haƙora ta yi a karo na ba adadi. "Kai ma sha Allah! Ku shigo daga ciki, wallahi na jin dadin dawowar nan taku" ta karasa maganar tana mai basu hanya. Manya mata sa'anninta bi biyu sai kuma karamar yarinya. Ita dai Nana ta kasa gane wacece mai gidan ko kuma duka matan gidan ne da diyarsu daya? "Yawwa dan Ara mana bokitinki mana" Muryar daya daga cikinsu ta fada. "Ku kam ku shigo daga ciki kusha ruwa ku dan huta mana, daga zuwanku sai ku hau jan ruwa?" Murmushi suka yi a tare jin abin da Nana ta fada. "Ke kam ba sai mun shiga daga ciki ba, kamata ma yayi mu yi saurin dibar ruwan nan kinsan aikin da ke gabanmu yawa ne da shi. Sai dai har yanzu ba ki fada mana sunanki ba?" 

Murmushi ta sake yi tana susar wuyanta a hankali. "Suna na Nana fiddausi" ta karasa maganar ta na mai mikawa matar da ke saman rijiyar bokiti. Shuru ta gifta ta dan lokaci kafin mai jan ruwan ta kalli Nana. "Amma dai rijiyar ki akwai dadin jan ruwa ki ji yadda nake ja ji nake kamar in ta Jan ruwan nan har yammaci yayi"
Rass! Gaban Nana ya fadi, sai kuma ta yi tunanin ko ita ce kunnuwanta basu ji daidai ba. Bokiti biyu suka cika da ruwa har bakin get Nana ta rakasu zuciyarta cike da farin ciki.
Kulle gidan ta yi tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya. "Allah na gode maka! Ashe karshen matsalata ya zo, ko ba komai a yanzu zan iya zuwa makwafta in zauna kafin Khaleed ya dawo. Kilama rashin jin motsin wani a kusa da Ni ne ya saka nake firgita kaina da kaina" ta karasa maganar zucin tana mai shigewa kitchen. Karamin gas dinta ta kunnu ganin lokacin tasowar Khaleed daga makaranta ya kusa. Don haka abu mai sauri ta hau shirin dafawa, shinkafa jalof da kifi. 
Karamar gireta dinta ta dauko ta zuba kayan miya . Bayan ta gama kifi ta wanke ta zuba mai ta ɗan bashi tsoro sama-sama ta kwashe ta juye kayan miyar. Ruwa ta tsaida kasancewar shinkafar ta Hausa ce adadin wadda zasu ci ta zuba, tunawa da tayi sunyi baki ya saka ta kara gwangwani biyu. Bayan ta zuba kayan kamshinta har ruwa ya tafasa, shinkafarta ta zuba ta fara bare magi ta daka a karamin turminta. Kifi da magi da albasa a tare da juye su. Lokaci daya gida ya hade da kamshi.
Sake bude tukunyar tayi jin kamar ruwanta ya yi kasa, sai dai abin da ya bata mamaki shi ne. Kan kifin data tura can kasan shinkafar me ya maidoshi sama, bayan ta san ita da hannunta ta danna shi can kasa. Tunanin da take ne ya kawo karshe ganin kifin ya kafe ta da daka-dakan idanunta tare da banka mata harara. "Muguwa! Shi ne hada turani can kasan tukunyar saboda ba ke kike dahuwa ba" ya karasa maganar cikin mummunar murya mai amsa kuwwa. Jefar da ledden hannunta tayi ta fice a guje.

Ta na kawowa bakin kofa ta ji karar mashin din Khaleed. Bata bata lokaci ba wurin ficewa ba tare da mayafi ko hijabi ba. Salati da sallallami khaleed ke yi ya kashe mashin dinsa. “Nana! Lafiyar ki kuwa, kina matsayin matar aure amma kika fito haka tsirara ko mayafi babu?” Ta kasa magana sai nuna masa gidan take yi a rikice. Ganin Nana ta kasa magana ya tabbatae da abin da ke cikin gidan ba karami bane. Hannunta ya kama suka shiga sai dai har yanzu a tsorace take. Kamshin da ya ji ya dakar masa hanci ne ya saka shi washe haƙora. "haba Fiddausi! Ki riƙa addu'a in ba haka ba za ki riƙa tsorata kanki da kanki ne har kije ki jima kanki ciwo wata rana. Yanzu abin da za ayi je kisha ruwa nutsuwarki ta dawo, nima wata takarda ce na zo dauka yanzu zan kai ta In dawo domin lokacin tashinmu ya kusanto" da ido Nana ta bishi domin ta kasa magana sai faman kada kai take ga magana a bakinta amma ta kasa furta ta. A gabanta ya fice da takardar tana jiyo karar tayar da mashin dinsa. Ajiyar zuciya ta sauke ta rufe gidan ta shiga kitchen. A yanzu kam bata ga kan kifin ba komai normal ba wata matsala. Kashe gas din tayi saboda ta san a duk wata sau daya yake yi masu reafelling shi ya sa suke hadawa da gawayi. Babbar kular da take zuba masu abinci ta dauko, na Khaleed ta zuba sai ta zuba na makoftanta ita kam ta kasa ci musamman kifin gani take kamar magana zai sake yi mata. Tsoron dake faman dawainiya da ita ya hanata ta je ta watsa ruwa. Sai dai tsoro take Khaleed ya dawo cikin gidan ya taras da ita bata yi wanka ba, ta san dole ya yi fada saboda mutum ne dan gayu. 

Addu’a ta yi ta shige kewayen tsakar gida, sai dai jininta kan akaifa bata wanke fuskarta ba sai da ta gama wankan kaf! Ta fito tsakar gida sannan.
Sallar ta tayar har ta gama Khaleed bai dawo ba. Mai ta shafa ta murza powder tare da lipstick, wata guntuwar riga iyakarta gwuiwa ta saka tare da dauko doguwar hijabinta da ake kira Jalbab ta saka. Kai tsaye kitchen ta nufa, kular da ta zuba masu abinci ta dauka sai da ta tabbar ta kulle gidan.
Sallama take rafkawa amma shuru babu wanda ya amsa. Can sai ga daya daga cikin matan ta fito daga daki tana washe mata baki. "Nana ce? Sannu da zuwa ai bamu san za ki zo ba. Wai aiki muka gama sai muka dan shiga daki mu huta, kinsan jiki da jini."
Murmushi Nana ta yi. "Haka ne kam. Amma dai koma me ye ya kamata ku ajiye abinci ne na kawo masu. Cike da farin ciki matar ta amsa “mun gode Allah ya saka da alkhairi, gaskiya munji dadi sosai. Ki shigo ciki ki ga gyara mana” cewar matar tana ba Nana hanya. “Aa sai dai idan na dawo yanzu sauri nake yanzu mai gidan zai dawo”
“To shi kenan! Mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi” da amin Nana ta amsa. fitowar da tayi sai da gabanta ya yanke ya fadi, Sakamakon gidanta data hango a bude gashi ba machine din Khaleed ba bare ta saka ran ko shi ne ya dawo. Jikinta na ciri ta fada gidan. Tsaye yake ya sha mur, uwar hararar daya daka mata ita ta yi sanadin faduwar makullan dake hannunta. "Daga gidan uban wa kike? Da na ce kada ki sake ki fita da ya ke ban isa ba haka kika saka kafa kika fita ko?" Ya karasa maganar tamkar ya shaƙo wuyanta. Kwatanta tashin hankalin da take ciki ya wuce misali, yau ita ce Khaleed ke zagi abin da bai taba yi ba a tsawon rayuwarsu. "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" karasa maganar ta yi daidai da ƙarar mashin ɗin Khaleed da ta ji a kofar gida, kallon tsoro ta hau yi ma Khaleed din dake tsaye a gabanta ta na mai ja da baya har ta hade da kofar gida. Juyawar da zata yi suka yi ido hudu da Khaleed dake saukowa daga saman mashin, shi ma ma ita yake kallon. A firgice ta ke nuna shi da hannu dayan hannun kuma tana nuna cikin gidan. Ganin halin da Nana ke ciki shi ya firgita Khaleed a hanzarce ya yi kanta, sai dai kash!  kafin ya karaso Nana ta yi baya luuu..............