HAULA HABEEB

BABI NA UKU

by @amdeeytejjdunique587

💎🌹 HAULA HABEEB 🌹💎




                     By




Amdeey Tejj d'Unique ✍️







BIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.






BABI NA UKU

Habeeb

Yana fita ya hau mota, bai zarce ko'ina ba sai gidan gona. A can ya zauna ya ƙarasa aikin da yake yi. Bayan ya gama, ya fita ya soma zaga gari. Yawo kawai yake yi ba tare da ya san inda zai je ba, duk don kada ya koma gida ya buɗe Salim. Shi ba wasu wurare yake zuwa ba, don ba ya son hayaniya sam. Abokai kuma sai dai kai idan ka gaji ka neme shi, za dai a gaisa a chat, da yake kuma yawancin abokan nasa ba ’yan Nigeria ba ne, wasu kuma ba a gari ɗaya suke ba. Abokan nasa na nan ba su da yawa. Salim mamaki yake yadda yake da tarin abokai a irin wannan hali nasa. Aboki kuma babban amininsa kenan Salim, don zai iya cewa da shi kaɗai ya yarda a ƙaf duniya. Yana da zurfin ciki sosai, amma ba ya iya ɓoyewa Salim duk wani abu da ya shafe shi, ba sirrinsa da Salim bai sani ba. Sai da ya gaji kafin ya tsaya a wani café ya sha coffee, sannan ya ɗau hanyar gida.

Yana shiga ya yi parking a space ɗin da shi kaɗai yake paka motocinsa a wajen. Ya fito kai tsaye ya nufi ɓangaren nasa. Yamma ta riga ta yi, don kiraye-kiraye sallar magariba ake yi. Ya sa key ya buɗe ƙofar, yana shiga babban parlour na side ɗin, da ya gaji da haɗuwa ya fara raba ido yana neman inda zai hango shi, amma wayam. Kai tsaye ya wuce ɗayan parlour ɗin da shi ma ya ƙayatu sosai, nan ma dai babu shi. Bai jira ba ya shige bedroom ɗinsa inda ya bar shi, nan ya same shi kwance a kan sofa, har yanzu yana barci, sai dai kana gani ka san ba a son ransa yake baccin ba.

Ya ɗan yi murmushi shi kaɗai, ya san ya yi laifi. Ƙaunar ɗan'uwan nasa, da shi kaɗai ya fahimce shi ciki da waje na sake shiga ransa. Ya sunkuya daidai kansa ya kalle shi, a hankali ya kai hannu ya shafa suman kansa. Murya can ciki, kamar an tilasta masa yin maganar, ya ce, “Buddy get up, now it’s time to pray.”

A can cikin baccin Salim ya ji muryarsa. A hankali ya buɗe idonsa da har zafi suke masa don barci, saboda wannan ne round-three, idan ya tashi ya ga bai dawo ba sai ya koma. Azahar kawai ya yi, bai ma san an yi la’asar ba. Ya ware idanunsa a kan nasa, kafin ya mayar da dubansa a kan agogo. Lumshe ido ya yi, kafin ya miƙe zaune yana salati. Ƙala bai ce masa ba, ya miƙe. Har ya doshi ƙofa, sai kuma ya dawo ya tsaya ya ce, “Zan iya samun wayata ko har yanzu...”

Bai ƙarashe maganar ba, ya miƙe ya zira hannunsa a aljihunsa ya ciro waya da keys ɗinsa, ya ɗora masa a kan tafin hannunsa. Bai ce komai ba, ya karɓa ya fice daga side ɗin ma baki ɗaya. Shi kuwa bathroom ya shiga, ya ɗauro alwala, ya nufi masallaci da sauri-sauri jin an tada da sallah.

Haula

“To, amma lallai ma Gwaggo, ni da zan auri mai kuɗi me ya haɗa ni da girki? Ai sai dai na zauna a dafa a kawo mini, in wanke goma in tsoma biyar. Ke Gwaggo ba ki ga mutanen gidan nan ba ne? Ai matar mai kuɗi ba ta shan wahala a wajen girki. Ni ma in na auri mai kuɗi za ki daina wannan aikin, sai dai ke ma ki huta, a dafa a kawo miki, ki ci ki kwanta.” Cewar Haula kenan da ke zaune gefe guda a cikin kitchen ɗin tana ta zuba kamar kurma. Gwaggo jin surutan nata sun ishe ta, ta ce, “Ki tashi ki zo ki dinga ganin yadda nake aiki kin ƙi, amma kin zauna sai surutan banza da hofi kike yi min. Ke ban san yadda za ki yi ba idan kin yi aure.” Shi ne ta hau rattabo mata bayanai.

“Za ki yi min shiru da wannan soki-burutsin naki mara kai ki zo ki yi abin da nake magana a kai ko kuwa?” Gwaggo ta faɗi cikin ɗaga murya.

“To, ni kam Gwaggo, Allah ba zan iya wahalar girkin nan ba. Kuma ke da kuɗinki ni da miki aiki, zan dai taya ki yanka kayan lambu, amma ni ba zan iya girki ba. To ni kuwa me zai haɗa da kitchen? Ai sai dai in shigo in duba ’yan aikina.”

Cewar Haula kenan, kuma tunaninta kenan ba tare da ta san abin da ƙaddara ta shirya mata ba gaba kaɗan. Ba ta san cewa kwanaki kaɗan masu zuwa wannan maganar za ta nanata kanta a cikin kanta ba. Aka ce makaho ba ya ganin gari, don da ta san abin da ƙaddara ta shirya mata, da ba ta yi wannan kalami ba. Idan ma ta yi, to za ta janye.

“To ma haka, kawai in ƙone, a zo idan mai kuɗin ya zo ya ce ba zai auri ƙonanniya ba.” Ta miƙe ta je za ta ɗauki robar kayan lambun. Gwaggo za ta yi magana, Salim ya shigo.

“Sannu da aiki Gwaggo,” ya faɗi yana mai ƙarasowa ciki.

“Yauwa babban mutum, sannu. Ka dawo kenan, ya aikin?” Ta tambaya bayan ta amsa gaisuwar.

“Aiki Alhamdulillahi. ” Ya ƙarasa jikin fridge ya buɗe ya ɗauki drink, ya mayar ya rufe.

Muryar Haula ya ji tana faɗin, “Ya Salim, ka ce za mu yi karatu yau, in zo kenan?”

Ɗan murmusawa ya yi, kafin ya ce, “Ba yau ba ai,” yana mai nufar hanyar waje.

“Ayya Yaya Salim, ni dai gani kawai mu je yanzu.” Ba ta jira wani abu ba, ta rufa masa baya tana faɗin, “Gwaggo, zan yanka in kawo miki.” Gwaggo ba ta iya cewa komai ba, sai kallon takaici da bita da shi. Ita kuwa ba ta ma san tana yi ba, abin da ta sa kanta za ta yi kawai shi ne a gabanta.

Shi kuwa Salim bai san ma ta biyo shi ba, sai da ta ga zai shige ɓangarensa ta ce, “Ya Salim, karatun fa?”

Ya juyo, “Haula, ba na ce miki ba yau ba, ina da aiki yanzu.”

Ta turo baki gaba, kafin ta ce, “To, ga yanka kayan lambun Gwaggo, sai ka taya ni, tunda na karɓo kuma na ce zan yi don ta bar ni in zo. Kuma ni tsoron kar na yanka hannuna nake ji, kuma ban iya ba, ka ɗan taya ni mana.” Ta karyar da wuya kamar abar tausayi.

Duk da yanayinsa ba ya jin daɗi, amma sai da ya murmusa don wautarta ta ba shi mamaki. To in ba haka ba, ya za ta ce wai ya taya ta yanka kayan lambu? Ga ta a haka, kai ka ce mai hankali ce, sai ta tafka shirme za ka gane. Wasu lokuta kuma ta yi abin masu hankali. “To ai ni ban iya ba, wannan aikin mata ne ai,” ya faɗi yana murmushi.

“Zan nuna maka yadda ake yi. Ka ga kai ma idan ka yi aure sai ka dinga yankawa matarka. Ai malamin su Mardiyya ta makarantarmu ya ce wai Annabi yana taya matansa aiki a gida. Kuma wai ma meye, sauran dai, na manta. To, kai ma ka ga sai ka koya.”

Murmushi ya yi, ya ce, “Haulat ’yar makaranta. To, amma ke me ya kai ki ajinsu lokacin karatu?”

“Yauwa ai ban ba ka labari ba. Zo ka zauna ka taya ni, sai ka ji.” Ta nemi wuri a ƙasan carpet ta zauna.

Shi ma girgiza kai kawai ya yi, ya nemi wuri ya zauna a ƙasa. “Ina jinki,” ya faɗa yana kai hannunsa cikin kwandon, ya ɗauki ice ball lotus yana ɓarewa daga ledar da aka yi wrapping ɗinsa.

“Ka ga ita wannan Mardiyyar ƙawa ta ce fa, amma ta girme ni, kuma ajinsu ajin manya ne. Ranar ne wani malaminmu, wai subject ɗinsa suka fi so, don haka kar mu dinga magana, ga shi sai wani Turanci yake yi. Ni kuma ina so na karɓi biro a wurin wata yarinya, kuma ni ba maganar kurame na iya ba, kawai sai na yi magana na ce ta ba ni biro. Shi kuma sai ya kore ni aji. Ai ko, na ce ba zan sake zama in yi karatunsa ba, tunda shi ba shi da mutunci. Kuma dama ni ba fahimtar Turancinsa nake ba.”

A wannan karon ma murmushi ya sake yi, kafin ya ce, “To, ai shi ma malamin shi ne ya zo, kuma Turancinsa ai a hankali za ki iya.”

“Hmmm, ba ka san shi ba ne. Shi fa Turancinsa da ban da na sauran malaman, sai ya dinga wani iyayi.” Ta yi maganar tana yatsine fuska, sai kuma ta sake cewa, “Shi ya sa na je ajin su Mardiyya. Yauwa Yaya, in tambaye ka mana.”

“Ina jinki Haula,” Ya yi maganar yana murmushi, hannunsa riƙe da wuƙa ya dage wai shi yana yanka kabeji, sai farɗe shi yake kamar za a ba raguna. Zuciyarsa cike take da nishaɗi, don tun jiya ransa a ɓace yake a kan abin da Habeeb ya yi masa. Yau ma ya ƙi su haɗu, amma a cikin ’yan mintuna da ya zauna da Haula, kaso mafi yawa na ɓacin ransa ya shuɗe.

“Wai dama a makaranta ma ana koya yadda ake yin wanka ne?”

“Wanka kuma?” Ya mayar mata da tambaya cikin tambaya, don shi bai fahimci inda gundarin labarin nata ya dosa ba.

“Eh mana. Ranar na je ajin su Mardiyya ina maƙale a waje, ba wanda ya gan ni. Sai na ji malamin nasu yana cewa tunda ya koya musu yadda ake alwala, yanzu sai wanka. Na ce, kai dama ba su iya wanka ba ne? Kuma ina ce Maman mutum take koya masa ba a makaranta ba? Ko ni, ba Gwaggo ce ke yi mini ba, ni nake kayana. Ai kuwa in gaya maka, na gudu. Na ce ni ba ruwana da ganin yadda ake cire kaya tunda duk manya ne.”

Duk yadda Salim ya so ya riƙe dariyarsa, kasawa ya yi, har yana riƙe da ciki, duk da kuwa yadda ya so yin hakan.

Ita kuwa, oganniyar ba ta jira ba ta ci gaba, “Hmmm, Yaya, kai ma dai abin dariya ya ba ka kenan. Ni kam tsoro ya ba ni.” Ta yi maganar ita ma tana murmushi.

“Kanta abu kazan uba! Salim!” Haula ta ji an furta daga bayanta. Da sauri ta juya, Mami ta gani tsaye tana bin ta da mugun kallo.

“Yanzu Salim, kai ne da yankan kabejin? Abin har ya kai haka? Ke kuma don uwarki kina ’yar aiki, sai ki ba wa ɗan gida aiki?” A fusace Mami ta yi maganar, dama akwai haushinta da take na zaginta da ta yi.

Da sauri Salim ya tashi ya rungume ta, har yanzu dariya ba ta gama barin shi ba. Da hannu ya yi wa Haula alamar ta kwashe kayan ta tafi. Shi kuma ya ja Mami tana fisgewa ya yi side ɗinsa da ita.

Ita kuma ta tattare kayan aikin ta nufi kitchen da su. Bakin nan kamar ya taɓo bango. Tana isa ta tarar da Gwaggo ta gama abinci tana zubawa a warmers. Ajiye kwandon ta yi, ba ta ce komai ba za ta fice. Gwaggo ta ce, “Ina kayan lambun da kika yanka?” Juyawa ta yi ta nuna mata su.

Cike da haushin ganin yadda ta ɓata kayan, ba ta yi wani abin arziki ba, ta ce, “Yanzu don tsabar iskanci, haka kika ga ina yankawa? Ki duba ki ga yadda kika ɓata abubuwan nan.”

“To, ai ba ni na ɓata ba, Yaya Salim ne, da na ce ya taya ni, shi kuma ya yanka haka.”

Tsabar takaici Gwaggo ba ta iya cewa komai ba, sai juyawa da ta yi ta ci gaba da abin da ke gabanta. Dama ta sani ai, Haula ce fa, shi ya sa ba ta jirata ba ta yanka wasu, don ta san in dai Haula ce, hmmm. 'Allah ya shirya,' ta faɗa a zuciyarta. Sai da ta haɗa komai ta juya ta ce, “Ki zo ki fara rage min kayan nan ki kai, ni ma gani nan a bayanki.”

Miƙewa ta yi, fuskar nan kicin-kicin, sai wani tauna flagyl take, ita a dole an ɓata mata rai. Ɗaukar farantin ta yi ta fice. Ita ma Gwaggo ba ta ɓata lokaci ba ta bi bayanta.

Habeeb

A hankali ya sake ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin a karo na kusan uku, bayan kiran wayarsa da ya yi ko sau ɗaya bai ɗauka ba. Don a tsarinsa ba ya kiran mutum fiye da sau ɗaya, don shi ma ba ya so a kira shi more than once. In har ka kira shi fiye da sau ɗaya, to ba zai kira ka ba ko ya ga missed call ɗin. A cewarsa, tunda ka kira sau ɗaya, in har ya shiga ai za a ga missed call, tunda ba a ɗaga ba, ba ka san uzurin da mutum ke yi ba. Knocking kuma ba ya yi, don ba zuwa ɗakin kowa yake ba sai dai shi a zo nashi. Ɗakin Daddy ne kawai yake zuwa, shi ma sai dai idan ya neme shi. Idan ya je kuwa a waya yake kiransa shi kuma ya ba shi izinin shiga. Idan ya koma office kuwa, ai sai dai shi a yi masa knocking ya ba da izinin shiga, sai dai ya kira ka ka zo ko ya aika maka, ba dai shi ya je ba.

Yana juyawa zai bar ƙofar kenan, aka buɗe daga ciki. Salim ya fito, bai ko kalli inda yake ba, ya ratsa gefensa ya wuce kamar bai gan shi ba, ya gangara downstairs.

Ransa ya so ɓaci don ganin wulaƙancin da Salim ɗin ya yi mishi, amma dai ya share. Ya san Salim na fushi ne da shi, amma shi bai ga abin da zai yi fushi da shi ba. Shi kawai yana yi masa gudun raini ne a wajen waccan mara kunyar yarinyar, don ya ga ya sake mata da yawa. Shi fa, ta ya shi riƙe girmansa yake kawai.

Ɗage kafaɗa ya ɗan yi, ya zira hannunsa a aljihunsa, shi ma ya gangaro downstairs ɗin. A nan ya samu kowa a dining, ba shi da niyyar zuwa wajen, hakan ya sa ya fice daga side ɗin gaba ɗaya ba tare da ya bari wani ya gan shi ba. Sai Salim ne ya hango fitarsa, shi ma kau da kai ya yi kamar bai gan shi ba, don haushin abin da ya yi masa yake ji har yanzu.

Yana fita side ɗinsa ya wuce. A nan ya tarar da dinner ɗinsa, bai bi takansu ba, ya wuce kitchen ɗinsa. Coffee ya haɗo, ya zo ya zauna yana sha a hankali yana danna wayarsa, har ya gama. Ya ɗau lokaci yana zaune a wajen yana danna waya, message ne ya shigo wayar, ba suna a lambar. A notification ya fara karanta saƙon, bai gama ba ya fahimci mai saƙon. Ransa ya ɓaci, kashe wayar kawai ya yi ya ajiye a parlour, shi kuma ya shige ciki. Bathroom ya wuce kai tsaye. 

******

HAZ Mansion, Family Meeting Hall

“To, ya kuke ganin za a yi? Don ba zuba masa ido za mu yi ba. Ita waccan ta tafi, Allah ya jiƙanta, ba sai na tsaya dawo da bara-bara ba. Kowa da ke nan ya san komai, ya san dalilin auren nan, don haka ba ɓata lokaci za mu yi ba. Kuma idan an samo wacce za a haɗa su, shi kansa auren ba ɗaukan lokaci za a yi ba.” Cewar Daddy kenan, wato Alhaji Salahu, daga cikin ɗakin tattaunawar ahalin gidan.

Abba, wato Alhaji Sammani, ya ce, “Wannan gaskiya ne. Muna da abubuwa da yawa nan gaba, wannan kamar buɗe ƙofa ne, don ma shi ɗin ba shi da ra’ayin ’yammata ne, da sai dai wani zancen ba wannan ba. To, kafin a yi mana shigar sauri, ya kamata mu yi abin da ya dace cikin sauri, kafin a samu matsala.”

“Ni ma dai wannan ne tunanina, ban yi magana ba ne kawai don kada ku ce na yi sauri.” Cewar Uncle Bulama kenan.

Hajiya Hashi, wato Mommy, matar Alhaji Salahu, ta ce, “To, me muke jira? Ya kamata a yi abin da ya kamata, ba wai wannan maimaicin zance ba, tunda ga mu mun zauna.”

Uncle Sammani ya ce, “To, shikenan. Yanzu ya kuke ganin za a yi? Wa za mu samo, da wa za a haɗa su?” Ya yi maganar yana raba idonsa a kan ’yan uwan nasa, yana jiran me za su ce.

“Ni a ganina, gida bai ƙoshi ba, ba a kai nama dawa ba. Kuma komai yana da buƙatar sirri da rufin asiri, ko don shi kan kansa yaron. A halin yanzu, Nabila ba ta kai wacce za a ce za a yi mata aure ba, sauran yaran kuma yanzu suke tasowa. Farida ce kawai a yanzu za a iya aura masa. Kun ga ba wani abin sai an tsaya ana yin tunane-tunane ko wani dogon nazari a kai ba ne.” Cewar Hajiya Safina, wacce ake kira Umma, matar Alhaji Bulama.

Daddy ne ya ce, “Wannan maganar taki haka take Safina, amma ya kika ce ke Uwar yaro?” Ya yi maganar yana kai dubansa ga Mommy.

“A gaskiyar magana ita ce, tsakanin Habeeb da Farida ba a shiri saboda halinta, wanda hatta ita mahaifiyarta ba ta yarda a kan laifin ’yarta idan ya yi mata hukunci ba, sai dai ta yi shiru don ba yadda za ta yi. A wannan karon kuma maslaha ake nema, kuma kowa ya san dalilin yin auren nan, don haka ba za mu yi abin da kafin mu kai ga gaci a zo ana wani maganganu ba. Don haka a yi abin da ya dace kawai.” Ta ƙarashe maganar tana kau da kai gefe.

Hajiya Zaina, wato Mami matar Alhaji Sammani, ta yi wa Mommy wani kallo, a ranta ta ce, “Dama yaushe Hashi za ta so ni da alheri? Amma dai ba damuwa, ta yi iya nata ta gama, lokacinta ne.” Ta yi ƙwafa a ranta kawai, ta ci gaba da saƙar zuci.

Uncle Bulama ya ce, “Tabbas wannan maganar taki gaskiya ce, sannan mafitar mu muke nema, ba abin da za a zo ana kace-nace ba.”

Abba ya ce, “To, yanzu ya za a yi? Ya kamata mu fitar da matsaya don sanin tudun dafawa.”

Mommy ta gyara zama, sannan ta haɗe rai don gudun raini ko musu a kan abin da za ta ce a wajen kowa, kafin ta ce, “Akwai Hibba, ’yar wajen Umminmu. Na ga ta su ta zo ɗaya da shi sosai, don akwai sabo a tsakaninsu. Don haka nake ganin ko ba komai, ta wajenta ma za mu fi samun sauƙin komai tunda akwai sabo a tsakaninsu.” Ta yi shiru tana duba reaction ɗin kowa da ke cikin meeting hall ɗin, lokaci guda tana jiran jin amsar kowa.

Ɗan murmushi Daddy ya yi. Abba na shirin magana, ya katse shi da faɗin, “Wannan maganar taki tana kan hanya, don ko ba komai ana buƙatar wacce ta saba da shi don rage sauƙin tafiyar. Amma kina ganin ita Hibbar za ta amince?”

“Haba Alhaji, mu ne fa iyayenta, ba ita ba ce ta haife mu ba. Sannan santalelen saurayi irin ɗana, wace mace ce ba za ta so kasancewa da shi ba? A’a, babu wallahi.” Ta ƙarashe maganar da ’yar dariya, jin ta samu abin da take so, don ta san tunda Daddy ya amince, ba wani mai sauran musu, kuma an kashe case ɗin kenan.

Da haka suka tsaya matsaya kan gobe za a ji ta bakin yarinyar. Idan ta amince, ba ɓata lokaci ba za a sa rana. Daga haka kowa ya watse bayan sun sake tattauna wasu abubuwa. Haka kowa ya tafi uzurinsa, duk da akwai waɗanda ba haka ransu ya so ba, amma ba yadda za su yi. Amma akwai waɗanda suka yi nasu shirin, a ɓoye suka tsara abin da za su yi a bayan fage, bayan tsarin da yanzu suka tsara tare.

Waɗanda nasu tsarin kawai suke yi, ba tare da sun san abin da Shi wanda ikon komai da kowa ke hannunSa ba. Suna nasu ne, Shi ma yana naShi. Abin da ba su sani ba shi ne, ƙaf tsarin da suka yi a yanzu, ɗaya ne zai tabbata, sauran kuma zai juye ya zo yadda ba su yi zato ko tsammani ba. Lamarin zai jawo abubuwa da yawa, ya kuma zama sanadin abubuwa da yawa.



#amdeeytejjdunique
#haulahabeeb.