Chapter 20
Hello Sooraj."
Bayan ya amsa Saleemarh ta ce " kazo gida na yanzu Umman Kazaure na son ganin ka yanzu."
Ya yi mamaki sosai jin Ummah na neman shi.
" Toh yaushe ma ta zo garin ni ban sani ba.?" Ya tambayi kanshi.
Ganin bai da me ba shi amsa ya sa ya ɗauki key ɗin motar shi ya ɗauki hanyar zuwa gidan Saleemarh.
Tafiyar minti talatin ce ta kawo shi gidan Saleemarh.
A bakin gate ya yi parking motar shi sannan ya sakko ya yi knocking.
Bayan ya jira an buɗe mashi ya shiga ciki.
Ƙofar parlour ya gani a buɗe sai kawai ya tura ya shiga ɗauke da sallama a bakin shi.
Shaheedarh da fitowar ta daga kitchen kenan riqe da jug ta amsa mashi sallamar da yayi.
" Yaya sannu da zuwa." ta faɗa bayan ya zauna.
" Yawwa Shaheedarh ina Saleemarh da Ummah?"
" Suna ɗaki yaya, bari na kira su."
Ɗakin da su Saleemarh ke ciki ta shiga ta aje jug ɗin a gefen Ummah sannan ta ce " Ummah ga yaya can a parlour ya zo."
Jinjina kai ta yi sannan ta ce " maza jeki ki gyara fuskar ki sai ki je ki kai mashi ruwa."
" Kai Ummah har sai na wani gyara fuska ta? Yaya ne fah."
Daƙuwa ta yi mata ta ce " ki ji man yarinya ina ce maki ga yadda zaki yi kina ce man yaya ne? Yayo."
Dariya ta yi tq ce " kai Ummah,kuma yanzu ya ganni sai ya ga na yi kwalliya ai sai ma ya yi tunanin wani abu."
" Toh ya yi ta tunanin mana,za ki tashi ko sai na bige ki."
Tashi ta yi ta ta fi gaban madubi tana turo baki.
Dariya Ummah ta yi ta ce " Iya turo bakin ne ai."
Saleemarh ce ta dungure ta ta ce " banza ana nema maki mutunci kina yi wa mutane iskanci."
Ita dai Shaheedarh bata fahimci me suke nufi ba ta cigaba da gyara fuskarta.
Bayan ta gama ta ƙara gyara daurin dankwalinta sannan ta biyo bayan su ta fito parlour.
Kitchen ta wuce ta dakko tray ta ɗora ruwa da lemu da kuma glass cup a kai sannan ta fito.
Inda ya yake a zaune ta ƙarasa ta janyo center table ta dora tray ɗin a kai ta ce " yaya ko na zuba maka?"
Gyada mata kai ya yi ya ce " ɗan zuba man ruwan Shaheedarh."
Robar ruwan ta buɗe sannan ta zuba mashi a cikin glass cup din ta miqa masa.
Zata zauna a ɗaya daga kujerun parlourn Ummah ta ce " Shaheedarh ɗan bamu wuri zan yi magana da yayan ki."
" Idan na gama zan kira ki ina son zanyi magana da ku duka."
Miqewa ta yi ta ce " toh Ummah."
Ɗakin da ta fito ta koma ta zauna ta na danne danne a wayarta.
" Yanzu Momma me ki ke ganin zamuyi?"
" Mafita ɗaya ce muje muyi magana da iyayen ALIYU, don ni wannan auren ma ban san wani irin aure zan kira shi ba."
Juyawa ta yi ta kalli Safiyyah ta ce " yanzu shi ALIYUN ya na gari ko yana wurin aiki?."
Waya ta ɗauka ta fara neman number Mamy.
Dialling number ta yi bayan an ɗaga suka gaisa, Momma ta ɗan yi shiru saboda sosai ta ji tana jin kunyar abinda Safiyyah ta aikata.
Mamy da ta ji shirun ya yi yawa ta ce " Hajiya ko ba kya ji na ne?"
Ɗan gyaran murya ta yi ta ce " don Allah so nake ki kira ALIYU ki ce masa idan yana da lokaci ya zo gobe akwai muhimmiyar maganar da nake so za muyi da ku gaba ɗaya."
Shiru Mamy ta yi ta na jin abinda Momma ke cewa, bayan ta gama ji ta ce " Allah dai yasa lafiya?."
Shiru Momma ta yi sai kuma ta ce " Idan ya zo ɗin dai sai muyi magana."
" Toh shikenan zan faɗa mashi kuma ko yana da wani abu ai zai iya ɗagawa."
" Allah ya nuna mana goben."
Bayan sun gama waya da Momma ta ɗauki waya ta kira HAYDAR.
Bayan ya ɗaga sun gaisa ta ce " ALIYU surukar ka ta kira ni ta ce wai tana son muyi magana gobe mu duka."
" Ina fatan ba wata matsala kuka samu da matarka ba?."
Shiru ya yi yana tunani sai kuma ya ce " mata kuma Mamy?"
"Kin manta matata ta rasu shekaru shida baya?."
" Kaga bana son iskanci ALIYU, Safiyyah nake nufi matarka."
Baya son su yi jayayya sai kawai ya ce " toh shikenan goben in shaa Allah zan zo."
Har za ta kashe wayar sai kuma ta ce " kuma idan za ka zo ka taho tare da ɗan uwanka."
Bayan sun gama waya Mamy ta yi ta juya wayar a hannunta tana ta tunanin maganar da suka yi da HAYDAR.
Ita kuma Momma bayan sun gama waya ta ce " ke kuma tashi mu tafi banga amfanin cigaba da zaman ki a gidan ba."
Addah Fatima dake ta aika mata da harara ta ce " Albasa dai bata yi halin ruwa."
" I'm highly disappointed in you Safiyyah."
" Da wani ne ya faɗa man wannan maganar zan yi tsalle na dire na ce ƙarya ake yi miki."
Hamma Khaleel da ya ke ta sauraren su ya ce
" haba Fatima ya isa haka mana."
" Laifi ta riga ta aikata sai dai fatan Allah ya shirya ta."
" Hmmmm ta ce sannan ta ɗauki wayarta ta ce Momma mu je naga kaman bata shirya tafiya ba."
" Tashi ki ɗakko hijabinki."Hamma Khaleel ya faɗa.
Ɗaki ta shiga ta sako hijabin sannan ta dawo parlour.
Motocin su duk suka shiga ita kuma Safiyyah ta shiga gaban motar Momma.
Bayan tafiyar Shaheedarh Ummah ta kalli Sooraj ta ce " Sooraj ban taɓa shiga shirgin gidan ka ba."
" Amma kuma ba haka ne zai sa nayi shiru ba idan naga wani abu da zai cutar da kai ba."
" Saleemarh ta kira ni a waya ta faɗa man irin rayuwar da kake yi kai da matarka."
" Babu ruwa na da bincikar hukuncin da kake yi wa matarka idan irin hakan ta faru."
" Abinda nake son ka sani shine kai ne a sama da ita, ba ita ce a sama da kai ba.
" Ya kamata ace matar ka tana girmama ka, sannan ta girmama ' yan uwanka."
Tunda Ummah ta fara magana yake hararar Saleemarh don yasan ita ce duk ta faɗa wa Ummah komai da komai.
Taɓe baki Saleemarh ta yi ta ce " iya hararar ce dai, mutum ba iya duka na zai yi ba."
Ummah bata biye musu ba ta cigaba da magana.
" Yanzu abinda nake so da kai aure zaka ƙara."
Da mugun saurin ya ɗago ya kalleta yana son gaskata abinda kunnen shi ya ji.
"Aure kuma Ummah?"
" Amma ni Ummah ai ban ce ina son ƙara aure ba."
" Ba shawara nake baka ba umarni ne."
" Kuma na zaɓar maka wacce zaka aura."
" Saboda da farko na ɗauka kana da hankalin da zaka zaɓar wa 'ya 'yan ka uwa ta gari."
" Amma sai na ga ba haka ba."
" Don haka a wannan karon na zaɓar maka wacce zaka aura kuma ba kowa bace sai Shaheedarh."
Tsabar shock bai ma san ya miqe tsaye ba sai da Ummah ta ce " ko ban isa bane?"
" A'a Ummah kin isa."
" Toh koma ka zauna."
" Amma Ummah ban ƙi maganar ki ba amma Shaheedarh yarinya ce ƙarama."
" yarinya me shekara goma sha bakwai ita ce yarinya ƙarama Sooraj a maganar aure?."
" Lallai toh mu lokacin duk da aka aurar da mu ba mu yi ko shekara sha huɗu ba."
" Ke kuma Saleemarh kira man Shaheedarh."
Kamar dama abinda take jira kenan ta miqe ta shiga ɗakin da Shaheedarh ta shiga ta ce ta zo Ummah na kiran ta.
Bayan ta fito ta ce " Ummah gani."
" Yawwa toh zauna."
Bayan ta zauna ta ce " alfarma nake nema a wurin ki Shaheedarh kuma na san ba za ki taɓa bani kunya ba."
" Shiyasa ma na zaɓe ki."
" Ki faɗi ko ma menene Ummah In Shaa Allah ba zan taɓa baki kunya ba."
" Yawwa ɗiyar albarka dama nasan ba zan samu matsala daga wurin ki ba."
" Ba wani ya baki labarin abinda kuka gani a gidan Sooraj ba,ku da kan ku kuka ga irin rayuwar da yake yi."
" Ina son ki temake ni ki auri Sooraj,saboda ke kaɗai na yadda ba za ki cutar da shi ba."
" Nasan tarbiyar da aka yi miki,kuma ina da yaƙinin zaki zama matar rufin asiri a wajen shi."
Sunkuyar da kanta ta yi ƙasa don bata taɓa tunanin abinda Ummah zata nema a wurinta kenan ba.
Gashi baza ta iya cewa Ummah a'a ba.
Saleemarh ce ta ce " kinga ba ma son munafurci idan za kiyi magana ki yi, kin wani yi shiru."
Ummah ce ta ce " haba Saleemarh ya za'a yi ta saka baki ana maganar aurenta ai shirun da ta yi ya tabbatar da amincewarta."
" Allah ya yi muku albarka gaba ɗayan ku."
Ta kalli Sooraj ta ce " kaje gida ka faɗawa matarka cewa zaka ƙara aure kuma nan kusa ba da dadewa ba."