Chapter 21_22
SANADIN HIJIRA.
By
Ummu Fadeela
21/22
DOOUUOOMM sautin ya bada na fashewar wani abu. A take kasar garin ta jijjiga na tsawon second biyar da duk wani mahaluki mai rai sai da yajisa, a lokaci daya wani irin hayaki bakikkirin mai tafe da 'kura suka turnuke sararin samaniyar garin gabaki dayansai, wani irin jijjiga ginin masjid din yayi kafun fiye da rabi ya zubo kan mutane da yawancinsu already they've gone, hatta ginin gidajen dake kusa da wajen sun zubo a kasa tsabar karfi da girmar B*mb din da aka dasa kuma ya tashi a lokacin da aka timer...Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, shi ne abun da jama'a keta nanatawa a bayyane da zuciyoyinsu, B*mb,b*mb ya tashi.
Duk in da kake ko me ka ke yi sai kaji wannan karar, ina tsaye rike da buta zan debi ruwan alwala na ji wani irin kara da tunda na zo duniya ban taba jin makamancin sa ba jikina na ji ya fara jijjiga kafin in tsaya cakkk a waje daya. tuni butar hannuna ta subuce zuwa kasa da gudu Yakura ta fito daga daki hannu ta daura aka ta fasa ihu mai karfi.
"Wayyoooo shi ke nan tamu ta kare, nan ma sun biyo mu sun biyo mu nan ma" kafin ta sauke hannu kowa na gidan ya fito tsakar gida salati mukeji a waje ana gudu yara suna fadin "B*mb ya tashi a Jumma'a".
Kofar masallacin cike yake makil da jama'a masu aikin sa kai ana aikin ceto. komai ya zama bakikkirin a wajen dakyar ake zakulo mutane daga karkashi baraguzan ginin da ya rufto, yayin da wasu part parts ake zakulosu dan Bomb din mai karfi ne yayi pieces da jikunnansu. Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un... A gigice mata da kananan yara suka fara fitowa daga gidajen su ana ta gudu kawai zuwa bakin massalaci kowa yana addu'ar Allah yasa abun bai rutsa da danuwanshi ba, jama'ar gidanmu ma ba'a barsu a baya ba Uwa ce ta fara daura hannu aka ta zunduma ihu kafin ta fice a tamanin ko takalma babu a kafarta Yaganah tana biye da ita da gudun itama, daga nan sauran mutane suka rufa musu baya, ban san ya akayi ba sai tsintar kaina na yi cikin masu gudu zuwa bakin masallacin.
Isowar mu ya yi daidai da fitar da shi, kwakwalwa bazata iya fasalta yadda ya zama ba, idanu ba za su jure ganinsa a haka ba, Babane kwance rabi da rabi duk da yadda ya zama hakan bai hanani da sauran yan uwana ganeshi ba, ihu su Uwa ke yi abun mamaki na nemi kuka na rasa a idanuna ko da ko taruwar hawayene, bamu gama shiga tashin hankali ba sai da aka fitar da su Baba Bamai, baba aisami, da sauran wadanda suka tafi tare, kamar wacce aka sanyawa mayen karfe haka naji wani abu yana jana, duk da an sanya wani zare an zagaye wajen dashi haka naji na daga abun amma kamar jikina baya motsi sai ganina na yi durkushe a gabansu su duka, "Baba, Ya Muhajir!"na ji an fada kamar da muryata kamar kuma ba ni nayi maganar ba, ganinsu kawai nake kamar suna min gizo murmushin da ya min dazu ya shiga dawomin fresh, ji nayi fuskata tana nadewa asai murmushi nake yi, "Ka tashi da wasa nake maka na san baka aikata ba, ka tashi ka gani wallahi da wasa nake maka, baba ka tashi kaima Maahh tana gida ita kadai muka bari,".
Na kuma jin an fada kasa kasa still kamar da muryata..!
Wani irin ihu Yaganah ta saki lokacin da aka fitar da Almuhajir, kafin a hankali duhu ya mamaye ganinta ta fadi kasa warwas ita ta yi suman da ni ban yi ba,bgashi nan kwance shidin ne dai da suka kulla kulalliyarsu ita da uwarta akan yau za'a daura musu aure, amma hukumullahi ya sauk'a.
Ina nan zaune a gabansu amma bana duniyar mutane, dan nesa nesa nake hangosu kamar kiyashi, kwakwalwata ta tsaya cak daga aikinta haka bugun zuciyata da fitar numfashina duk bana jinsu, ji nake kamar ina kasa kamar kuma ina sama idanuna kamas babu alamar ko digon hawaye, tabbas wani tashin hankalin yafi gaban suma ko kuka, addu'a nake son yin in roki Allah ya tadani daga wannan mummunar mafarkin, amma harshena ya kasa motsawa..!
Iface ifacen da yai yawa a wajen ne ya sanya masu aikin ceto fara korar mata da yara don su yi aikinsu yadda ya kamata.(A dukkan duniya duk inda aka samu faruwar ya'ki dama mata da kananan yara sune suke tagayyara sune suke shiga uku, mussaman MACE, ta ko ina abun ya shafe ta, inma Babanta, Mijinta, danta ko Dan-uwanta ne aka kashe).
Ban san ya akayi ba na dai jini kamar wacce ake tafiya da ita sama daga haka ban kara sanin abun da ya faru ba sai bude idanu na yi na ganni zaune jikin Maahh da ke cin kuka har fuskarta ya sauya daga kamanninta.
******
Aminullah*
Sun yi sahu a cikin jejin da suke suna gabatar da sallar jumma'a, ko wannensu yana rataye da bindigarsa a kafada, daga nesa da in da suke sosai suka jiyo karar, ko wanda bai sani ba bai taba ji ba yasan wannan fashewar B*mb ne balle su da suka saba mu'amala da ita idan ta kama. ana idar da sallar ko ta kan addu'a babu wanda yabi duk suka mike kowa yana gyara zaman bindigarsa da tsayuwa cikin shirin ko ta kwana.
Abun magana Al'ameen ya dauka jikinshi har rawa yake ya sanya saitin bakinshi, "Capt.A.F Almisry ke magana, hello hello" Wani bakin abu mai kama da waya dake kan teburin MG ya fada, daukarta yayi zuwa saitin bakinshi shima jiki a mace, "Capt. Mun samu labarin wani abun fashewa ya tashi a masjid inda ya hallaka mutanen da har yanzu ba'a gama tantance al'kaluman yawansu ba" MG ya yi maganar ba tare da ya jira Amin ya ce wani abu ba.
A bangaren Al'ameen kuwa dama yasan hakan zata faru, but ba ya kira bane dan a bashi kanun labarai, jami'an tsaron kasata suna da idanu ta ko ina, idan sun so zasu iya dakile komai kafin afkuwarsa jibi yanzu kasa da mintuna biyar da faruwar fashewar amma har sun samu labari a headquarters.
"Sir" Al'ameen ya fada yana kamewa waje daya, zamu tunkaresu yanzun nan a shirye muke tsafff" No capt, kada ka aikata komai tukunna zan kiraka in the next 1 hour."kafin ya ce wani abu kiitt yaji an kashe kiran, sororo ya yi yana bin abun hannunsa da kallo kafin ya durkushe da wani irin karfi ya hada hannu bibbiyu ya buga a kasa.
"Nooooooooooo"
Ya fada cikin wani irin karaji wuyarshi da kirjinshi suna budewa kamar zasu fashe tsabar fad'i, take tsuntsayen dake saman bishiyu a jejin suka tattashi daga wajen zamansu suna shawagi a sararin samaniya tsabar karfin ihun da Al'ameen ya yi, dagowa ya yi yana watsar da ciyayin da ya figo tun daga kasar jijiyansu lokacin da ya kaiwa kasar wajen cafka idanunsa kamar zasu yi aman wuta fuskarsa zuwa kafadunsa suna digar da ruwa kamar an watsa mishi bokitin ruwan zafi. "Nooo dole ne mu fita yau kam, wannan dole ne,me ne amfaninmu idan bazamu iya kare rayukan fararen hula ba, ina alkawarin da mukayi na aikata hakan?" shi kadai yake magana kamar mahaukaci a lokaci guda yana nufar cikin Tent nasu yana warware taswirar jejin da yan bindigar suka yi maboya...
MG.
Yana yan ke wayar ya shiga neman wata lamba sai dai ta yi ringing har ta gaji ba'a daga ba, bai karaya ba ya kuma kira, sai dai nanma har ta gaji da burarinta ba'a dauka ba.Tun da ya ajiye kan wayar ya kifa kansa saman teburin dake gabansa ba shi ya dago ba sai da ya kusa mintuna goma a haka, lokacin da ya dago idanun nan sun yi jajur dasu shima, a dan kwanciyar da yai din nan ya samo mafita kuma zai aiwatar sai dai abun da zai faru ya faru kawai, without thinking twice ya shiga neman Al'ameen,bwayar tana yashe a inda ya yarda ita Musty ne da ya ankara abun tana magana ya dauka da hanzari ya shige Tent da Amin ya shiga yana mika mishi," Capt. Ku wuce yanzun nan, and make sure kun yi clearing komai yadda ya kamata"...."Yes Sir" cewar Al'amin yana sarawa, dama ya gama kudurtawa a ranshi ko da bai ce su je ba lallai zai fita yanzun nan sai dai kome za'ayi daga saman an dade ba'a yi ba...!
Da wani iri gudu ya fito wajen Tent din, "Every body should be ready, zamu fita service yanzun nan" Ya fada da karfi, tuni sauran collegues na shi din suka shiga shirya kayan aiki da warming na motoci masu sulke da na dibar marasa lafiya in case ko za'a samu jin ciwo ko mutuwa ba fata ba, ya yin da irinsu Daniel kuma suke ta shirya mugun nufinsu a zuciya, a gaggauce Al'ameen ya dauko rigarsa bulletproof ya daure a kirjinsa dama already suna cikin uniform complete, hular sojoji mai kama da kwano jikinshi kuma kamar ciyawa ya kifa a kansa baka ganin komai sai idanu da tsinin hanci da kuma bakinsa Wata safa ya sanya a hannu, hakama Musty irin shiga daya suka yi da Al'amin, koda suka fito an gama shirya komai sojojin duka suna cikin shiri exactly irin na Al'amin a gefe daya kuma an gama settings na komai babu bata lokaci suka fara hawa motoci suna barin wajen, wata mota mai kafar kaca Al'ameen ya hau motar ita ke sarrafa kanta daga sama ya tsaya daidai inda wata doguwar bindiga mai jigida take makale. A guje rundunar suka bar wajen kana suka durfafi hanyar garinsu FANNE, wanda kwata kwata bai fi tafiyar awa daya ba daga in da suke aka bar wasu tsirarun sojoji masu gadin filin.......
SPAIN*
Da kyar ya samu Mom ta sake shi daga rungumar da ta yi mishi tana kuka kamar zata shide ganin an fara kiran passengers, "Take good care of your self Son," ta fada tana sumbatar tarin sumar dake saman kan JACK, rungumarta ya yi shima sannan ya dago yana kissing kumatun ta, take care of your self too and my little love Mom" Jack ya fada yana barin wajen da sauri zuwa ciki jirgin da zai tafi dasu Dubai daga can zai canza jirgi zuwa Nigeria.
Ba wannance tafiyarshi ta farko ba, hasalima dan nata yana wahala yayi cikakken wata daya a kasarshi but wannan karon tafiyar tasha bambam da wanda ya sabayi, duk da cewa ita ta matsa yayi tafiyar amma tunda lokacin yayi ta ke jinta wata iri, kamar tace ya fasa, but tafiyace ta inda bai taba zuwa ba kuma neman maganin cutar kanwarshi guda daya tal da Allah ya bashi, goge hawaye idanunta Madam Mareyya ta yi tana daga mishi hannu da fatar samun nasara a kan abun da ya kaishi....!
A hankali ya daga sagaggun kafafunsa time da jirgin ta gama landing afilin tashi da saukan jirage na kasa da kasa dake birnin tarayya. Takowa ya farayi zuwa sauk'a dan tuni an fara fita, a tsakiyar matakalar ya tsaya yana wani irin shaka da fisgar numfashi da karfi jin wani irin iska mai tafe da sanyi sanyi zafi zafi yana busoshi, sanye yake cikin wasu riga da wando Ash colour, kalar idanunsa wandon mai fadine sosai kamar buje sai dai daga can kasa robace dan haka a matse take wajen kaurin, ya janyo kafar dama sama har kusa da guiwarsa sai hakan ya kara taimakawa wajen fitar da fadin wandon na hagun kuma yana nan normal, a saman rigar kuma ya daura wani jacket mai kama da rigar sanyi Red colour mai layi layin fari bisa hannun na kamfanin Givenchy, sai wasu takalma NIKE ash colour da igiyarsu Red dake sanye kafarshi a wuyarshi kuwa wata chain na diamond ne keta walwali kwantaccen gashin kanshi da aka mik'ar dashi sunyi tsilli tsilli a tsakiya iska yana ta kadasu suna kwanciya da tashi a lokaci daya, duk da rigar da ya sanya mai doguwar hannunce,hakan bazai hanaka iya hango zanen TATTOO dake cike daga wuyarshi har tsintsiyar hannunshi ba, idanunsa makale da wata ubansun Shade ba'ka kana bakinshi zuwa hanci rufe da facemask, hakan ya takaita mishi rubibin mutane tun a cikin jirgin ma amma duk da haka wasu sun kureshi da idanu suna doubting kamar shi ne kamar kuma bashi ba, tabbas ya hadu gayu iya gayu, a kallo daya idan ka mishi bazaka iya dauke kan ka ba.
Capt.Jack Smith Edward ya shigo Nigeria, shin zai dace da samun maganin little sis din tashi? tukunna ma wace irin magani ake nema haka da sai a nan Nigeria za'a samu aka tsallake turai? muje dai zuwa.
Shade na fuskarshi ya zare yana makala ta a gaban rigarshi, kana ya sauke facemask nashi kasa, Woww. Cikin kasa da minti daya illahirin jama'ar dake filin jirgin hankalinsu ya dawo kansa har rige rigen tahowa gareshi ake,(kada ku manta Jack Worldbest ne a fannin kwallon kafa dan haka ko a bayan idanunshi yana da Fans balle an ganshi ido da ido, baga ma'aikatan filin ba manya da yaransu baga pasinjas din da suka taho tare ba baga masu shirin tashi yanzu ba, kowa burinsa ya dauki hoto da Jack, yayin da wasu ke ta mikomishi memo dinsu yana karba yayi dan rubutu a kai ya mika musu duk wanda ya samu damar isoshi kuwa tsayawa yake su dauki hoto yana dariya da fara'a yana daga musu hannu, bashi ya samu kansa ba sai da motar Hotel din da yai booking ya iso, kafin ya samu salama nan ma yana tafiya ana binshi yawanci matasa ne da magidanta, kunsan dai maza da harkar BALL 5and6 ne.
Saida ya shige backseat security ya rufe yana zagawa shima ya shiga driverseat, har anfara jan motar amma mutane basu daina binsu ba yasa Jack sauke glass yana daga musu hannu amma fuskar nan tasha mur dan zuwa lokacin sun fara bashi ciwon kai, wadanne irin mutanene su haka?
Hooo my country people.😷.
*******
Abeey yana hakimce a bayan rantsatstsiyar motar shi, tasowarsa daga office ke nan a hanyarshi ta zuwa gida traffic ta tsaida su a daidai wata shataletale, kamilalliyar fuskarshi tana bayyana tsantsar damuwa, wayace guda biyu a hannunshi yana ta gwada layin Al'ameen amma bata shiga, duk wata layi da yasan zai iya samunsa ya gwada amma abu daya ake sanar mishi.
"SWITCHOFF"
Sosai yake cikin damuwa da tashin hankali dan gaba daya jaridu da gidajen tv dana rediyo har ma da yanar gizo gizo sun dau dumi ta ko ina labarin fashewar da ya auku a in da su Al'ameen suke ne Breaking news dan haka duk wani da yasan dan uwansa soja yana can ya shiga damuwa, musamman Abeey da tun fil azal bai son wannan aiki na Aminu taurin kai ne kawai irin nashi, kwafa ya yi yana aje wayar saman babbar rigarshi, kamar an ce ya juya a gab da motarsa ya hangoshi a bayan wata bakar mota yana zaune amma idanunshi suna zube fess kan Abeey, suna hada idanu ya sakar mishi lallausar murmushi gami da daga mishi hannu yana waving nashi, wani wawan zabura Abeey ya yi yana kokarin balle marfin motar ba tare da ya kula a tsakiyar titi suke ba, adai dai lokacin ne kuma traffic ta basu hannu, da wani irin gudu motar ta sa kai ta yi gaba, "Alburhan!" Abeey ya fadi a hankali kafin da sauri ya ce, "Bala maza kabi waccan bakar Corollar kar ka yadda ta bace maka, hanzarta kayi sauri, taka motar da kyau mana!". Ya fada a tsawace wanda bala driver zai iya rantsuwar bai taba jin uban gidan nasa a irin yanayin nan ba.
Gudu yake iya iyawarshi yana bin motar bai fi minti uku da fara bin motar ba suka nemeta ko sama ko kasa suka rasa inda motar tabi, ba karamin girgiza zuciyar Abeey ta yi ba, me hakan ke nufi, "is Alburhan still alive?" ya yiwa kanshi tambayar da babu mai bashi amsa, haka suka gaji da bulayin nema akan manyan titunan Abuja suka koma gida amma damuwa yanan tattare dashi dan har wani sarawa kanshi ke yi kamar hawan jininsa yana son tashi.
Wani tashin hankalin ya tawar a gida domin Badariya ya samu ta hargitsa gidan gaba daya tun da suka kalli labarai da jin abun da ya faru a inda Al'ameen yake ta hargitse bayan gudawan da ya barke mata yau harda ihu take tana buga kanta a bango ita dai sai ta tafi inda yake.
"Ku barni in tafi in diboshi kar su kashe min shi" haka take ta fada, a gefe daya kuma Ummie ce a cikin dakinta ke ta fitar da wani irin gurnani mai bada tsoro da tausayi ga duk mai Imani dan haka gidan duk ya rikice, isowar Abeey ya yi dai dai da isowar Dr Shettima, da kyar suka iya kama Badar aka zurkud'a mata allurar bacci, ba jumawa kuwa baccin ya kwasheta, dakin da Ummie take suka shiga dukkansu, tana kwance zuwa lokacin babu abun da ke iya motsawa a jikinta sai wannan gurnani da take yi mai bada tsoro, hada idanu Dr shettima ya yi da Umma ta yi saurin janye nata idanun, dan haka ya juyo da kallonshi kan Abeey dake kure Ummie da idanu har wasu ruwa sun fara taruwa a cikin kwarmin idansa
"Yallabai baka ganin ya dace a mayar da patient din nan asibiti? ina ganin a can sai tafi samun kulawa dan condition nata yana kara zama worst daga dukkan alama anything can happen a kowanne lokaci".
Wata irin bugun gaba ne ya samu Umma a lokaci daya tana zaro ido, "Asibiti kuma" maganar ya kubuce ba tare da ta shiryawa fitar shi ba, duk kallonsu suka mayar gareta da sauri ta daidaita nutsuwarta tana waskewa kamar batace komai ba. "Dr kaci gaba da dubata a nan, muna shirye shiryen fitar da itane da zarar Aminullahi ya dawo, yanzu dai ka bata taimakon gaggawa, ni tunda ta samu kanta a halin tabin hankali ban taba ganinta a irin wannan yanayin ba" Cewar Abeey muryarshi tana son karyewa amma yana karfafata, wasu allurai dr shettima ya fitar ya fara hadawa, ta gefen idanu ya kalli Ummah yana cigaba da zuqe ruwan allurar cikin babbar syringe.Hannun Ummie ya kamo sannan ya saita jijiyar jininta.....