7. Sirri ne
Maryama ce zaune kan kujera dake wakeken living room ɗinsu tana kallon TV.
Wayarta dake kan side stool ya fara ringing. Hannu tasa ta lalumo wayar ba tare data waigo ta kalli screen ɗin wayar ba. Ta ɗauka tasa daf da kunnenta.
"Maryama bestyyy…!”
Maryama ta ɗaga gira cikin murna da jin Hauwa ce.
"Oh, Hauwee, ya kike? Kwana biyu kin share ni."
Daga dayan layin Hauwa tace,
"Maryama bana son sharri. Nine na share ki? Wai mema kikeyi dana kira kamar bakisan ni bace."
"kiyi haƙuri dan Allah ban ma duba screen ɗin wayar bane shiyasa. Kallo nake yi.”
“Okay. To ya kike? Da fatan kowa lafiya.”
“Kowa lafiya ƙalau. Ya Kaduna? Da fatan you are having fun. Naga kwana biyu bana ganin ki online sosai. Nayi miki messages amma shiru."
"Komai lafiya lau. Kawai dai sometimes mutum zaiji ya gaji da komai na social media ɗinnan.
Naga kin turomin pictures na birthday ɗin Hasina. Kunyi kyau sosai."
Maryama taso ta gane akwai damuwa tattare da Hauwa. Yanda take magana a sanyaye ba kamar yadda tasaba ba. Taso taji ko akwai wani abu amma sai ta share kada ta zama mai shishshigi.
"Aifa munsha fun. Gaskiya kinyi missing. Na faɗa miki har bracelet ɗina wanda na saka rannan na yar ban lura ba.”
“Kash…! Maryama wannan priceless inheritance ɗin naki? Ah lallai kunyi having fun sosai. Nagani kuwa cikin hotunan kina sanye dashi. Garin yaya kika yar? Ina fatan dai kin samu."
"I am not sure ina na yar fa, kuma ban samu ba har yanzu. Munyi waya da Hasina tace zata tayani nema."
"Aiyya, Allah yasa a samu. Ba daɗi irin haka.”
“Ameen dai. Hauwee akwai wani labari da nake so na faɗa miki, but ba yanzu ba.".
Hauwa tace, "Haba ke kuwa, ki faɗa min mana yanzu naji ko menene."
Maryama tayi dariya. “No."
"Why?"
Cikin muryar tsokana tace,
“Sirri ne."
"Sirri kuma? Dama a tsakanin mu akwai sirri ne? Da Allah ki faɗa min abu bana son jan rai."
"Zan faɗa miki nan bada daɗewa ba amma yanzu is not the right time."
"To wannan wani irin sirri ne haka da har akwai lokacin faɗan sa? Nifa kinsan bana son ɓoye ɓoye.” Hauwa ta ƙarasa maganarta cikin ƙaramin tsuka.
Maryama ta tuntsure da dariya.
"Haba Hauwee, kada kiji haushi. Ina so na tabbatar da wani abu ne kafin na sanar dake. Kinga abin zaifi kawo light."
Hauwa tace, "Umm, to shikenan ai madam light, idan lokacin yayi kya fito ki sanar dani.”
Suka yi dariya.
"Any latest ta wajen ki? Ina labarin guy ɗin da kika faɗamin Uncle ɗinki ya haɗa ku?"
Hauwa ta tambaya, “Najib?"
What a coincidence! Itama Maryama wanda zuciyarta ke mata gizo a kansa sunan shi Najib.
"Eh shi. Da fatan dai komai na tafiya dai dai. Kuma when zaki dawo Abuja? Na fara kewarki fa.”
Kawo wa batun Najib yasa Hauwa tayi shiru na ɗan ƙanƙanin lokaci tana nazari.
Tana ganin alamu Najib baya ji da ita kamar yadda take ji dashi.
Sau tari zata kira wayanshi bazai ɗauka ba, sannan bazai yi calling back ba. Haka a normal text ko online chat. Shuru ne ta wajen shi.
Ta lura kusan kullum dashi take kwana dashi take tashi a ranta. Tana tsoron kada tunanin sa yayi mata yawa ta zama abin tausayi.
Tana cikin damuwa.
"Um... yana nan. But gaskiya munyi kwana biyu bamuyi waya ba. Zancen dawowa kuma, Kar ki damu na kusa. Ba wani daɗewa zanyi sosai ba. Ko muyi video call gobe?”
Maryama tace, "To shikenan. Allah ya kaimu goben."
Da gama wayarsu Maryama taci gaba da kallon TV, tana mai fatan sake haɗuwa da Najib kwana kusa cikin ranta, duk da tasan hakan zai yi wuya tunda dai ba wani sanin juna sukayi ba.
****
Hasina ce ke tafe daga ɗakinta zuwa ɗakin yayan ta. Da isarta kofar tayi knocking sau uku. Dataji shiru sai ta buɗe ƙofar a hankali tare da yin sallama.
Shiru ba amsa.
Ta waiga kallonta daga ƙofar bathroom zuwa kofar closet tana kiran yayanta.
"Ya Najib,"
Shiru ta sake ji alamar dai baya nan.
Tasa kai ta fice daga ɗakin ta sauƙa ƙasa zuwa living room. Mahaifiyarta ta gani zaune kan ɗaya daga cikin royal coushins ɗinda ke jere gefe guda. Ɗauke take da waya daf da kunnen ta tana fadin,
"To shikenan ai babu komai. Kinsan an fa ɗaɗe ba'a haɗu ba gaskiya. Gashi nan bada daɗewa ba Hasina zata wuce Florida karatu. Kinga kuwa idan tazo za’ayi zumunci sosai...
Eh, Allah sarki..,"
Hajiya Bilkisu ta waiga taga ‘yar autan ta ke zuwa inda take. Hasina ta samu gefen kujera ta zauna daf da mahaifiyarta. Hajiya Bilkisu ta mayar da kallonta kan TV taci gaba da magana a waya.
"Yauwwa na gode sosai a gaishe da kowa. Sai mun sake waya."
Hasina ta langaɓe kai kan kafaɗar mahaifiyarta.
“Ummi waye zata zo?"
Hajiya Bilkisu tace, "Jamila ce zata zo kwanan nan.”
"A’a nayi murna sosai. Gaskiya it has been long ban ganta ba.”
“Nima haka nace.”
“Allah ya kawo ta lafiya.”
“Ameen ‘yar autan mama.”
Hasina tayi dariya cikin jin kunya ance mata auta sannan tace,
“Ummi wai ya Najib ya fita ne? Sau biyu ina shiga ɗakinsa amma bana samun shi."
"Ai idan dai baki ganshi ba to ya fice. Tun kafin azahar yabar gida wai zaije gurin abokansa. Wani abu kike so ne?"
"A'a. Dama bracelet ɗin ƙawata ce ya ɓata jiya. To shine tace na tayata searching, shine nace bari na tambaye shi ko maybe he has seen it in the car.”
"In the car kuma? Ya akayi abin ƙawarki ya shiga motar sa?"
"Ummi Maryama ce fa, wanda ya kai ta gida, unguwar Maitama jiya da daddare."
"Au Allah sarki, ‘yar gidan Alhaji Muhammad Sadiq ko? To Allah sa ki samu. Amma ina ganin daya gani da zai miki magana. Ko da bai miki magana ba nasan zai sanar dani har ma ya kawo in assumption cewa naki ne tunda dama kina yawan yar da kayanki anyhow.
Kuma ya shigo ɗakina kafin ya fita amma bai faɗi komai akan wani bracelet ba. But idan ya dawo ki tambaye shi ki tabbatar."
Hasina tace, “To Ummi, idan ya dawo zan tambaye shi."
****
Abokan Najib sunji daɗin sake ganin shi bayan haɗuwar su wajen shagulgulan bikin Habib. Su uku ne sannan Najib na huɗu, suke haɗe a ƙayataccen restaurant ɗinda suka saba haɗuwa.
Sai da sukayi sallan azahar suka ci abinci sannan suka shiga bawa juna labarai na bayan rabuwa. Suna cikin nishaɗi da labarantawa juna Habib ya ɗago kai ya dubi Najib.
“Wai yane abokina? What’s the news between you and my adorable cousin?”
Najib ya ɗago idanu tare da ɗaga gira alamar tambaya.
“Ina so abokantakar mu ta ƙara ƙarfi sosai duk da nasan mun riga mun zama kamar ‘yan uwa. Kuma idan ban manta ba, Hauwa na ɗaya daga cikin irin matan da kake so fa. Dalilin haka yasa tun farko na haɗa ku a waya kafin kuga juna.
She’s pretty and all. Ga addini da sanin ya kamata, ga son karatu da ilimi sannan kuma ‘yar uwata ce, a very close one. Na santa sosai kuma ina tunanin kun dace da juna.
But kamar babu wani progress tsakanin ku. Meke faruwa ne Najib? Ko dai slow burn love kukeyi ban sani ba?”
Dajin tambayar da Habib yayi a ƙarshe, kusan kowa yayi dariya banda Najib.
Maganar da Najib Ke gudu kenan.
Najib ya karkata kallon sa gefe kamar mai tunani a lokacinda ya sanya hannun sa a hankali cikin jeans pocket ɗinsa, yatsunsa suka ci karo da sarƙar data naɗe kanta.
Murmusawa yayi tare da sauƙe ajiyar zuciyan da hayaniyar gurin ya boye sautin ta.