MIJIN ƘANWATA(ƘADDARATA).

15

by @jamilaumarjanafty

*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty❤️*


M.A JUMARE FOOD AND SPICES
Pure and Natural hygienic tasty.

Muna da garin Ɗanwake da yaji mai kyau dakan hannu, akwai kuka, tsamiya, garin tamba, kuɓewa da daddawa.
Muna aikawa da kayanmu a ko'ina
Anguwan Ma'aji new millennium city kaduna
Phone number ***


*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*

*Sanyi flusher!* 
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. 
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*

*Tightening set na hade mace ta  dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.

*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*

*Muna da gimbiyar zabuwa  da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.

*Page 15*


Kiran sallar farko na asuba ya Tasheta Daman ko min barcinta wannan Kiran Sallar ko da bataji ba Asuba nayi take tashi Saboda ta Riga ta Saba.
Tayi mamakin yanayin Data samesu Daga ita har Sulaiman,Gabadaya ya Kanannadeta itama Tana kan Jikinsa ne Barci ya sa ta saki Jiki bata sani ba.


Kunya ya kamata da Sauri tayi kokarin kwatan kanta Saboda Har Hulan Dake kanta ta Sabule Gashin kanta ya bayyana Har ya bazu saman Fuskar Sulaiman wanda gabadaya kansa ke saman Kafadanta zuwa wuyanta.
Hannu ta saka tana Kokarin Cire sa Daga Zagaye Kugunta da yayi,Sai dai Hakan bai samu ba Saboda shima alokacin ya Farka Daga Barcin daya Daukesa Mai natsuwa da kwanciyar Hankali wanda ya Dade bai yi kamarsa ba.


Fes kuwa ya Bude Kyawawan Fararan Idanuwansa akanta Lokacin Datake kokarin Raba Hannayensa da Jikinta Ganin haka yasa da Sauri ta Kauda kanta Daga kallonsa Cikin Sanyin Murya tace'Asuba tayi..Ka tashi ka koma Chan kada laila ta Fahimci baka nan..!
Lumshe ido yayi kafin ya Bude Cikin Shakewar murya yace"Ina so zan yi sallah..!
Yafada yana kokarin Danne abunda yake ji Data ambaci sunan Laila,Da Sauri ta kwace Jikinta ta Mike tana Daukan Hulanta Dake saman gadon Lokaci Daya tace"Zaka yi wanka ne..?


Kai ya gyadamata Kafin yace"Eh..Ina so naje masallaci..!
Bata Tsaya ba ta nufi Jikin Wardrope din Dake Dakin Tana Fadin"Zaka iya zuwa..!
Daga haka ta Dauko Jakar Ruwwn mganinan tazo ta Tsiyayamai ta bashi yayi Bismillah kamar yadda ta Umaecesa Haka yayi yasha Sannan yayi Hamdala Kamar afarko,Kansa ya Dafe yana jin wani natsuwa yana Shigansa Kallonsa tayi acikin Ranta Tana addu"an AllaH ya yanke mai Wahala maida komai tayi muhallinsa tace ya fara shiga wanka shi ya Farayi yana Fitowa ya maida Jallabiyansa ya Kalli Sunaima Data Zurma Hijabi kamar Zatayi Sallah yace"Zan tafi masallaci..!
Mikewa tayi tana Fadin"in kaje kayi ma kanka Addu"a don Allah..!


Ido ya sakarmata Cikin wani yanayi kafin yace"Nagode.!
Kai ta Kada batace komai ba Har yakai Kofar Fita ya Juyo yana Kallomta Kafin yace"Yau ba inda zaki je..?
Kai ta gyadamai kafin tace"Sai Monday..Zan koma Dutyn  Safe..!
Kai ya gyada kafin yace"Zan rika zuwa ina shan mganina..I need my Self Soon SUNAIMA...!!!
Yadda ya Fadi sunan nata ne sai da taji Ko"ina ma Jikinta ya amsa yana kallon Cikin Idanuwanta ya Fice Daga Dakin Allah yasa ba wanda ya gansa Daman wani Lokacin Allah na Taimakon bawansa kan al"amarin Da ya sanya Duka yakini akansa.
Megadi yayi mamakin ganin Yallabai ya Fito Sallah yau bai ce komai ba Illah yabi bayansa zuwa masallaci


Ba Shakka ya samu Tarin natsuwar Daya Dade bai samu ba sakamakon sallar Cikin Jam"i,Ya zauna Shuru acikin Ransa ya rasa wata addu"a zai yi sai kawai acikin zuciyansa yake addu"an Duk abunda ya Nannade Rayuwarsa Allah ya warware masa ya Bashi Lafiya sai wajen karfe bakwai ya Dawo Gidan ya Haura sama Har Lokacin Shashashen Lailan bata Farka Daga Barcin asaran ba Gefenta ya samu kwanta ya kurama waje Daya ido Fuskar Sunaima ke Giftamai alokacin Duk ko yadda Laila ta Zama Duniyarsa ayanzu.


Kamar yadda Sulaiman yayi alkawarin zuwa wajen Sunaima Duk Dare Allah yana bashi Sa"a da Laila ta Fara Barcinta kamar Allah na kara Doramata Nauyin barcin ne sai ya Lallaba ya Fice zuwa Dakin Sunaima Ita kuma ko tayi barci zata barmai Kofa abude Daya shigo sai ya Tada ita ta bashi mganin yasha ya koma ya kwanta ita kuma bata barci sai dai ta Cigaba da Salla arana ta Uku ne tace mai shima yazo suyi sallar abunda ta Lura ko Ibadarsa an Raunanata sosai,da sun Fara sai yace mata ya gaji nan gefenta zai kwanta ya Fara Barci ita kuma bata barci sai Gabanin Asuba Ta rasa meyasa ta Damu da Halin da Sulaiman yake ciki Addu"an Duka Salolinta shine aciki Bata son ganinsa ahaka Tana Fatan Sulaiman ya Dawo wanda ta sani Mijin kanwarta.


Kullum da asuba yake Ficewa masallaci Daganan ne yake komawa Wajen Laila kuma bata taba Ganewa ba Ballatana Hadimanta ko sau Daya ba wanda ya Taba ganin Sulaiman ballatana akai mata Labari ba ma wanda zai yi Tunanin haka na Faruwa.


Saifullahi ya Kirata ya sanar da ita yaje Zaria wajen Babansa Sama"ila sunyi mgana Shima dai addu"an yace adage dashi,Shima Daganan barayin zai Dake da addu"a Insha Allahu komai Zai zama Tarihi jin haka yasa Sunaima ta Dake bata barci kwana Take Ssllah tana Rokon ma Sulaiman Waraka Daga wajen Allah
Rana ta Hudu ranar bai Samu Fitowa da Wuri ba Har nannayan barci ya Sace Sunaima Data gaji da Jiransa Shi kuma sai chan Dare yazo ganin ta Fara barci yasa ya Fara jan yatsun kafarta Kamar yana mata Tausa.
Cikin barci taji kamar ana Janta Ta Farka agigice Tana neman ta yanka Ihu Saboda ta Rage hasken Dakin akwai Duhu Daya Fahimci Zatayimai Ihu ne yasa yayi Saurin Riketa ya sa Hannu ya Toshe mata baki ita a Tunaninta Bai bata Sulaiman bane Saboda Barcin nata ya Dauketa ne Bagatatan batare data shirya ba.


Sai ta gantsara mai Cizo a Tafin Hannunsa Daya Rike mata Da Sauri ya Saketa Cikin Jin zafin cizon nata yasa yace"Ochhhhh....!
Yafada yana yarfa Hannu kokarin Tashi take yi Saboda akwai Hijabi ajkinta Datayi sallah dashi ganin bata Cikin natsuwarta yasa batare da wani Tunani ba ya kamata ya Rumgume kam kan kafin ya Dago kanta Batare da wani Tunani ba kamar ana Jansa antsaida Duka Tunaninsa akanta ne yasa ya Dora lebensa saman bakinta ya Fara Controling dinsa Cikin Kwarewa kamar wanda Wani abu ke jansa
Kamar amafarki taji ya Rumgumeta Kamshin Turaran Dake Jikinsa taji ta Gane shine,sai kuma taji Tattausan abu samanta bakinta kafin ta Dawo cikin Hayyacinta taji ya Fara yawo da Lebensa saman lebenta Cikin kwarewa tana Kokarin Bude baki taji Ruf ya Zura Harshensa cikin Bakinta ya Fara bata wani irin Sumba mai karfi da Fitan Hayyaci Lokaci Daya yana Rike da ita Tun Sunaima na ganin abun kamar almara har ta Fara gasgastawa cewa wannan al'amarin acikin Duniyarta yake Faruwa yau gata ajikin Mijin kanwatta yana Sumbatarta kamar Allah ya aikosa cikin Fitan Hayyaci abunda wani bai Taba yimata ba Tunda Take shiyasa Kamta ya Fara Juyawa Jikinta ya Fara rawa Jin yadda yake shafa mata Baya Cikin Tattaussaun Hannayensa.
Kamar yadda ta Fita Daga Hayyacinta Shima haka ya Fita Ya Dade bai ji baki mai kamshi da Taushi irin na Sunaima da Farko yaso ya sata ta natsu ne ammh Daga baya sai ya Fita Shima daga Tunaninsa sumbar da tun akan Sunaira bai jin ya kara yima wata mace ko Laila baya yadda yana Hada baki da ita sai dai ita ta Hada dashi da karfi da yaji Kwata kwata ai kamar Tilas ne ammh bawai don yana jin Dadin yin komai da ita ba.


Dalilim Haka yasa ya Dauki Tsawon Lokaci yana Sumbatartar Sunaima Daman Sulaiman Mayen Kiss ne ita kuma alokacin Sunaira bata Tsawon wannan wanan kamar yadda Sulaiman yake iya kai wani Lokaci yana Romancing din mace bai gaji ba Kamar yadda Sunaima gangar Jikinta ya Tallafi Bukatar Sulaiman hannu Biyu bata Dawo Cikin Hayyacinta ba Sai da taji ya Rabata da Hijabin Jikinta Hannunsa saman Kirjinta yasa taji wani Yam..! Daga saman kanta da Sauri ta kwace bakinta Daman Jikinsa ya Saki sai ya koma ya Lafe saman gado ita kuma ta Rarrafawa tayi ta Sauka kan gadon ta Durkushe Tana maida Numfashi kunyar Duniya Duk ya gama Saukan mata meta aikata..?meke Damunta ne..?
Bata iya Hada ido dashi ba Har ta bashi Ruwan yasha Yau dai ya Tsaya sunyi Sallah sosai sai Wajen 4 na Dare Sunaima taji barci ya sake kamata ta Kalli Sulaiman Dake gefenta ya Daga hannu yana addu"a ammh bakinsa baya Motsi sai ya ayyana acikin Ransa baya iya Bude baki ya Fadi wani abu kirjinsa yayi masa Nauyi sosai.


Abun na bata mamaki bai Taba Tambayan ina su Wasim ba alhalin baya ganinsu yasa tana ganin ya shafa addu"ar ta Kallesa tana Fadin",Baka Tambayi su Wasim ba..!?
Kallonta yayu sai alokacin suka Fadomai arai shifa yana Tunanin ko Harda Ciwon mantuwa ya kamasa Banda Laila Sunaima ce kadai bai Taba mantawa da ita ba.
Cikin Wani yanayi yace"Suna ina..?
Kanta na kasa tace"Suna wajen Inna...!


Shuru yayi bai kara mgana ba illah Mikewa da yayi yaje ya Hau gado ya kwanta ya Nannade waje Daya kamar wani maraya tana kallonsa idanuwanta suka ciko da kwallah da Sauri ta kauda kai Bataso ta hau gadon ya Riketa kamar yadda ya Zamemai Jiki sai ta Sulale nan samAn Darduma ta kwanta ai da Asuba ajikin Sulaiman ta jita Shima ya Dawo saman Darduman ya matsu da ita kamar wani yaron Dake neman Nono bai samu ba.
Sati Dayan nan kaf sun Cinyeta Tare Ruwan addu"an ma ya kusa kwarewa kuma ba Laifi Sunaima tana ganin Sauyi Sosai sai dai yana yawan barci in yasha mganin sai kuma yawan Shuru da Shiga Tunani,Sai dai yanzu Ta Saba Dashi Saboda Tare suke kwana sai Da Asuba yake tafiya Tun tana Hanasa Tabata tana jin kunya har tazo ta Saba Allah ya Taimaketa wannan Watan bata da aikin Dare sai wata mai kamawa Shiyasa ta samu Cikakken Lokaci Suna waya da Inna ta Fadamata mganin ya kusa kwarewa Tace Zata Kira kawu Jafarun kila Ahmad Zata Tura ya karbo wani.


Har kuma zuwa Lokacin kuma Laila bata Taba Lura da komai ba Ballatana su Samira sai dai magajiya ta taba ganin Sualaiman sau Daya zai shiga Dakin Sunaima ta kuma Taba ganinsa zai Fito da asuba ammh bata taba Fadama kowa ba ita kanta Fata Take da Addu"an Allah ya Kwato Saraki Daga Hannun Muguwa mace irin Laila.


******

*Abuja...*
9:30am


Gabadayansu suna saman Dining din Dake babban Falon su inda suke Haduwa suna cin abinci Lokaci Bayan Lokaci,Jiya Hajiya Falmata ta Dawo Daga maiduguri,ita da Alhaji Aliyu kakarta wacce ta Haifi mahaifiyarta ce ta rasu Hajiya zabba"u taje gaisuwan ita da yara sun kwama Daya suka dawo ita kuma Hajiya karama tana chan Sai da akayi bakwai Abba yaje suka taho da ita.
Dukkansu suna bada Hankalinsu wajen cin abincin Harda yaran Hajiya Zabba"u Cokali ke hannunta tana wasa dashi ta kasa cin abinci yana lura da ita,ganin gabadaya kamar Hankalinta baya wajen ta shiga wani Tunani,Yasa ya Ijiye Cokalin hannunsa yana kallonta kafin yace"Zabba"u...!!
Bata jisa ba Tayi nisa Cikin Tunaninta Gabadaya Hankalinsu sai ya koma kanta Sadiya ce ke kusa da ita ta Dafa Kafadarta Tana Fadin"Hajiya..Hajiya..!
Kamar daga sama taji Kira Firgigir ta Dawo Cikin Hayyacinta Tana kallon Sadiya ita kuma Cikin yar Damuwa tace"Abba ke mgana fa..!


Sai alokacin ta Dago tana kallonsa kafib tace"Abbansu me kake cewa ne..?
Tafada tana Dafe kanta Hajiya Karama ta kalleta kafin ta kalli Abba ta kasa mgana itama Tun jiya Da suka Dawo Taga Hajiyar kamar tana Cikin Damuwa saninta macece mai kazar kazar da Tsayawa kan kafafunta Abu ne mai Wahala ke sata tayi Rauni.

Cikin Damuwa ya kalleta kafin yace"Meke Damunki Zabba"u..?
Ajiyar zuciya ta Sauke kafin tace"Me ka gani..?
Da sauri yace"Abubuwa dayawa..Ina Lura Dake Cikin kwanakin nan kamar bakya Cikin Hayyacinki..Wani abu na Damumki.yawan Tunani sannan Duk kin zama wata so Cool dake... ana mgana sai ki yi Lose bkya Tare damu kwatakwata..!
Hajiya karama ta kada kai kafin tace"Koni na lura kamar wani abu na Damunta Tun jiya da muka Dawo..!
Sadiya ma tace"Abba ita kadai fa adaki Hajiya kayi ta mgana bata jika ba..!


Saddiqa tace"Ta rage Hira da Fara"a kamar ba Hajiyarmu ba..!
Sadiq ya ijiye mug din Tea dake hannunsa yana Fadin"Jiya ma Danaje Gidan Anty Safiya sai da ta Tambayeni Hajiya...Tace tana Kiranta bata Dauka..Sannan ranar ta Dauka Duk taji ta wani iri..Hajiyarmu meke Damunki Allah duk kin Sauya..,!
Hajiya karama tace"Su Raliya ma haka sukayi ta fada a maiduguri sun ce Hajiya ta zama so Cool..!
Itadai Duk tana jinsu batace komai ba Kanta na kasa Abba ya kalleta kafin yace"Kin ji mganar yar"uwanki da ya"yanki..Ni kaina ai ba yau na Sanki ba zabba'u tabbas wani abu na Damunki..ba abu kadan ke saka Zabba"un Fulani tayi Laushi ba..!
Hajiya ta Dago Daga Dafe kan Datayi kafin tace"Yaushe Rabon da kayi mgana da Saraki?
Gabadaya Tsam yayi yana kallonta haka yaran suma kowa yana Jin abun aransa Daman mgana ne bai samu ba.
Abba yace"Bamu yi waya dashi ba kwana biyu..!


Da Sauri tace"Tun Da kuka Rabu a kargi baku kara mgana ba ko..?
Shuru yayi kafin yace"Eh..Me ya faru..?Shine Damuwar ai shuru lafiyace sannan ga aiki ga kuma Amarya Kila bai gama cin amarcin bane..!
Yafada Cikin Zolaya yana so ya kauda mganar ammh Shi kanshi ya Fara Tunanin wani abu Tunda yake da Saraki bai taba Kwana Biyu bai kira wayarsa sun gaisa ba ammh kimanin Sati Hudu ba wayarsa ba Sakonsa Sai dai sukan yi mgana da Saifullahi da Farko yayi Tunanin Auran da yayi yanzu Da aka kwarari Lokacin nan Jikinsa ya basa wani abu na Faruwa ammh Wannan Halin bana Saraki bane
Duk ko wani Karshen wata yana Hanyar Abuja yazo ya gaishesu waya kuwa Koda yaushe cikin Kiransu yake yi.


Hajiya karama Dake gefe ta kada kai Tace"Ni kaina Hajiya ina so nayi mgana..Wai Saraki Lafiya kuwa..?ni kaina Tun Rabuwar mu daga Kargi bamu kara mgana ba yaron da Bayan kwana Daya sai ya Kirani mun gaisa..Ni Ranar ma na kirasa bai Dauka ba..Ko Rasuwar nan Abbansu ban jiman ya Jita da Har Maiduguri na Tabbata sai Saraki ya Taka..!
Da Sauri Sadiya tace"Wlh Hajiya baya Daukan wayarmu..ni da Saddiqa kan mganar Chanzamana Mota mun Kirasa har mun gaji ba"a Daga ba..!
Sadiq ma yace ya kirasa baisan adadi bai Daga Kiran ba.
Hajiya Zabba"u taji kamar ta Dora Hannu akai ta Kurma Ihu ita kanta ai bata Samunsa a waya ko ta Kira Baya Dauka,ko Ranar da akayi Rasuwarsa ta Kirasa bai Dauka ba ta Kira Saifullahi yace yana Meeting ne ya Samu Zillema Kiran nata.
Saraki ba Haka yake ba Lafiya Lafiya bazatajisa Shuru haka ba Ta kira Samira ko zataji wata mgana bataji komai ba Ta Kira Laila sai ta Rika ce mata baya nan yana wajen aiki in ta Kirata da Daddare bata Dauka Sai da Safe ta Kirata tana Fadin bata ga Kiran ba.


Abun ya Fara Damunta Har ta Fadama Hajiya Salame sai ita ma ta ce mata ita kanta sai tayi Sati batayi waya da Laila ba, ta Dan Kwantar mata da Hankalin cewa su godema Allah Laila da Sulaiman sun hada kansu alokacin Hankalinta ya kwanta ammh yanzu Taji bai kwanta ba Ko Sulaimam baya kusa ta Kirasa in yazo yaga Kiranta zai Biyo ba ita kuwa batasan adadin Kira nawa tayi mai ba bai Nemeta ba.
Ko jiya da sukayi waya da su Fulani suna ta Jajensa suna mai Tsiyan Tunda yayi amarya suka Daina Jinsa bata Tsinke da ba Lafiya ba sai da Sukayi waya da maimartaba da kansa yake Tambayanta Ina Saraki..?yayi Amarya ya manta dashi Daganan tasan ba Lafiya Domin ta Tabbata Rashin Lafiya me ko Ciwo mai Tsanani zai saka Saraki ya manta dasu iyayensa da mainartaba.
Abba ne Dayake ta Nazarinta yace"Bakina waya da ita yar wajen Salamatun ba..?
Kai ta gyada kafin tace"Eh in na Kirata sai tace min yana wajen aiki..!


Bayaso ya Nuna mata ya Damu shima Shiyasa yace mata"Lafiya ke sa Shuru zabba"u kada ki Damu Saraki yana Lafiya da yardan Allah..kawai in kinji Zuciyarki bata natsu ba Juz kiyimai addu"a..!
Kamar zatayi kuka tace"Kasan Kira nawa nayimai bai Dauka ba..?Abbansu Saraki bai taba kwana ya Wuni Cikin Lafiya ba bai Kirani ba. kodai baida lafiya ne..?
Tafada sai ga Hawaye Hajiya karama Tace"Koni da ban Haifesa ba bai Taba kwana Ya wuni bai kirani ba..Mganar Hajiya abar Dubawa ce..!
Abba yace"Kada ku damu yana Lafiya ko Jiya mun yi mgana da Saifullahi..kuma da akwai wani abu Daya Fadamin..!
Hajiya Zabba"u ta Girgiza kanta Tana Fadin"Ni ban yarda ba..Ni uwace naji ajikina ba Lafiya Nidai gobe zan Shirya naje chan Kadunan nagani..!
Abba ya kalleta Kafin yace"A"a bazaki jeba..Ai baki Fimu son Sarakin ba..Ki bari dai mu gani in mukaji Shurin nan da Sati mai zuwa ko Hajiya karama da Sadiya sai suje su gani..!


Bata da yadda zatayi ta kara Cewa wani abu Domin kuka  ne zatayi Sai kawai ta tashi ta Fice tana Sharan Kwallah Hajiya karama tace"Abbansu kayi wani abu..Nima inajin ba Lafiya..!
Abba yayi ajiyar zuciya kafin yace"Kuyimai addu"a..!
Daga haka shima bai kara cewa komai ba ammh iya Tunaninsa yasan shima wani abu na Faruwa sai dai bayaso ya karya musu zuciya zai Binciki SaifullHi yaji ko lafiya ya Tabbata Koma akwai wani abu to yana da masaniya.
Haka Cin abincin ya tashi ran kowa ba Dadi Harta yaran Kowanne Jiki a sanyaye 
Hajiya Zabba"u Daki ta koma sai kuka Saraki shine mafi soyuwa cikin ya"yanta Batason wani abu ya Faru dashi ita Ranta ya gama bata ko Hatsari yayi ake boyemusu koma ya Rasu ne..?Tunanin haka ya kusa wa Tayi Hauka Zuciyarta ta Buga.
Tana cikin wannan Halin Safiya ta Kirata ta waya Sai da ta yanke ta kara Kira Kana ta Dauka Daga yanayin Muryan Hajiya tasan tasan ba Lafiya Cikin Damuwa tace"Hajiyarmu Lafiya..?
Jin haka yasa Hajiya ta Fashe da kuka Safiya Hankalinta ya tashi ta Fara Fadin"Hajiyarmu lafiya Abba ne wani abu ya Faru dashi..?ko Hajiya karama..!
Hajiya na kuka ta cigaba da Fadama Safiya Damuwarta ta Kare da cewa"Safiya Wlh na Fara Mugayen mafarkai kan Saraki yana cikin wani Duhu mai Tsanani yana Kiran sunana yana Mikomin hannu..Bantaba irin wannan mafarkin ba Safiya jikina yana bani Saraki ba Lafiyansa ba..!


Safiya tace"Nima Kiran dana  nayi miki kenan..Abbnsu Hidiya yaje Kaduna Jiya Hajiya har Office din ya Saraki yaje Sakariyarsa tace bayanan yama zata ya Fita ne yace zai Zauna ya Jirasa sai take gayamai yafi Sati Uku bai zo aiki ba..!
Ido Hajiya ta Zaro kafin ta Dafe Kirji Tana Fadin"Innalillahi Wa"inna ilaihirraju"un..!
Safiya tace"Wlh Hajiya..Daman ya Biya su gaisa shima Workshop suka je yi na kwana Biyu jiya suka gama shine yaje su gaisa.yacemin yaga Saifullahi sai dai shima sai kame kame yake yimai Daga gani wani abu na Faruwa..!
Hajiya Zabba"u ta mike Tana Fadin"Yama Faruwa Safiya..bazan zauna ba ko Abbanku ya yarda ko bai yarda ba..Ni zan je kaduna yau naga Halin da ake ciki..!
Da Sauri Safiya tace"A"a Hajiya baza"ayi haka ba..Ki barmin komai a Hannuna zan matsama Abban Hidaya ya kaini kadunan zan je Har Gidan naga Abunda ke Faruwa nayi miki wannan alkawarin..!
Hajiya tace"ki kokarta Safiya..Ina Cikin Tashin hankali..!
Safiya ta tabbatar mata Zataje taga ko Lafiya da haka suka yanke kiran.
Hajiya Zabba"u tana kuka Tana fatan kada wani mummunan abu ya Samu Danta.


Taso ta Kira Hajiya Salame ta Fadamata tace ko zatazo su je su gani ne sai ta Kirata bata Dauka ba Daganan sai bata kara Kiranta ba da Hajiya salamen tazo ta kirata daga baya kuma sai taji kuma ta kasa gayamata wannan wani abu ne Daya Shafi abunda ta Haifa ita Lailar ana Jinta Saraki ne kamar batan Dabo aka Daina Jinsa Da ganinsa.



Littafin Mijin Ƙanwata Free book ne yanzu nake reposting, amma ina siyar da document ga waɗanda ba za su iya jira ba 
1k ne ta wannan acct ɗin 5040273639 Moniepoint Jamila Umar
KO tuntuɓa ta wannan lambar ***.




*Janafty*