Aaminat (Bazawara)
by @auntyindo
*AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka.
Ayeesha Abdulkareem
*AUNTY INDO*
Tare da
Salma Abdulkareem
Free page
PAGE 2
Yau da daddare Aaminat ta na zaune ta na Azkhar Umaima ta shigo ta na dariya "Abba ya ce ki zo" ta faɗa ta na ɗan tsoshe bakinta sabi da dariyar da take yi.
"To ki ce ina zuwa" ta faɗa ta na ƙoƙarin tashi, ba ta ɓata lokaci ba ta nufi ɗakin Abban bayan ta ƙara gaisheshi a karo na biyu ya ce "Maza ki shirya ki fita Allah ya kawo Manemin Aurenki, kuma kar in ji kar in gani, in kika sake ki ka koreshi za ki gamu da ɓacin raina, ko bakya so ki haƙura haka nan don zaman banzan nan naki ba shi da amfani." "To Abba" ta faɗa kanta a ƙasa. Mama ta yi wani ɗan murmushi gami da cewa "Kamar gaske" ba ta kalli inda ta ke ba ma bare ta tanka mata. Ɗakinsu ta koma ta shirya har ƙasan ranta daɗi take ji gami da Addu'ar Allah ya sa mutumin kirki ne ya ce zai Aureta ta huta da tsangwamar Al'umma, Fati ce ta matso kusa da ita ta tsaya ta na ƙare mata kallo kafin ta tuntsire da dariya, "Gaskiya sai kin yi Jagira" Aaminart ta ce "Ke ni ba zan yi ba" Fati ta ja tsaki kafin ta ce "Ƙazamar Mace." Aameenat ta murmusa dan dai ita ba ta iya sa'insa ba kuma ma Fati ba Abokiyar yinta bace, amma ko Mama Mahaifiyar Fatin ba za ta taɓa kaita tsafta ba.
Cikin sauri ta shirya ta fita, ya na zaune kan kujerun da aka aje ɗaya tashi ɗaya tata, ta ƙarasa da sallama, amsawa ya yi ya na murmushi ya ce "Zauna mana." Ta zauna sannan ta gaishe shi, ta yi shiru, bai ce ba ba ta ce ba su ka shiga zaman kurame, Agogon Wayarsa ya duba ya ga dare ya fara yi gudun kar ya makara ya sa shi cewa "Sunana Salis Bara'u, an bani labarinki ne aka ce in zo mu gana ko zamu daidaita kuma ina fatan hakan." ɗan murmushi ta yi ba tare da ta ce komai ba ''Duk da nasan sunanki amma ina son ƙara ji daga gareki. "Aaminat" ya yi murmushi ya na cewa "Suna me daɗi, an ce min Shekararki ishirin da Bakwai, to amma wace makaranta ki ke zuwa? nasan har yanzu anata neman ilimi ne" ya ƙarasa maganar ya na wani mugun washe baki, in ta fahimta dai ba'a gaya masa gaskiyar cewa ita Bazawara ce ba kenan! jinjina kai ta yi cike da mamakin halin ɓoye-ɓoyen nan na Abba gashi wai a dole sai ya Aurar da ita sai bi yake ya na tallanta. "Yanzu ba karatu nake ba ai Zaman Zawarci na ke yi. "Bab.. ban..gane ba Zawarci kuma? tsokanata ki ke yi?" murmushin takaici ta yi kafin ta ce "Ba Zolaya bace ita ce gaskiyar ni ban iya ɓoye-ɓoye ba gwara kasan wadda ka Aura, in har za ka iya ka so ni don Allah ba don wani abu ba, amma ni Bazawara ce." gyara zama ya yi gami da sauke gwauron numfashi kafin ya kalleta ya ce "Ki na da Ƴaƴa ne??" "Ba ni da ko ɗaya. "To ki sanar min abin da ya sa ku ka rabu ke da Mijin naki. shiru ta yi ta na tunani kafin ta girgiza kai ta ce "Ba zan iya ba." tsaki ya zabga ya gyara zaman Hularsa ya tunkuɗota gaba sannan ya fara magana "Ai in na Aureki na ƙi cin Biri na ci Dila kenan, Matata Ma ta fiki Yarinta don dai kawai Ƙazama ce shi yasa na ke son ƙara Aure, amma da in Auri Bazawara ai gwara in zauna da Ƙazamar Matata har zuwa lokacin da zan samu Budurwa, wa ya san ma irin abin da ki ka yi Wancan ɗin ya sakeki? ai duk wanda ya ɗebarwa kansa Bazawara ya ɗebowa kansa aiki, me za ka samu a Kale in banda takaici, ni ba zan iya Auren sauran wani ba, ki gayawa Abbanki in zai sa ayi tallarki a dinga gayawa Mutane gaskiya, don a zamanin nan ko an zo dole a tafi don ba me yarda da wannan damfarar." ya na kaiwa nan ya miƙe ya kakkaɓe tijararriyar rigarsa ya yi hanyar fita.
Aaminat kuwa tin da ya fara hawaye suka shiga tsere akan fuskarta, tashi ta yi ta shiga Gidan da gudu, a hanya su ka yi tawo mu gama da Umar, ya daka mata tsawa da cewa "Kehh!!!!! menene hakan ko ciwon hauka ya kama ki ne??" Kukan da ya ke cin ƙarfinta ne ya samu damar fitowa, cikin shashshekar kuka ta fara cewa "Kowa sai ya ce ba zai Auri Bazawara ba sai ka ce ita ta tsarawa kanta Ƙaddara?, idan ba su Aure mu ba a haka za mu Mutu cikin fuskantar ƙasƙanci da wulaƙanci kenan??, nima fa ban sani ba Ya Umar ban san Kamal zai yi min haka ba, Ban sani ba wallahi, kowa ya tsaneni har iyayena da ƴan Uwana, wallahi Tallahi ba ni da laifi, don son raina ba zan taɓa zaɓar irin wannan Rayuwar ba, Abba ya kawo min Mutane da yawa amma sai su ce ba za su Auri Bazawara ba."
Kukanta ne ya ƙara ƙarfi ta toshe bakinta da gefen Gyalenta sannan ta kutsa kai cikin gida. "Aamina!!! Aaamina!!!" Ya Umar ya shiga watsa mata kira
Bata tsaya ba taci gaba da tafiya, ta na shiga ta yi gamon katari da su Abba, Umma, Mama, da sauran Yaran curko curko a tsakar gida don kuwa sun ji muryarta lokacin da ta ke yiwa Umar Magana. Mama ta ce "An yi abin da aka iya ko?"
ganin kowa ya tsirata da ido ya sa ta yi saranda ta kasa wucewa, Abba ya ce "Kukan me ki ke wa mutane?"
"Abba shi ma cewa ya yi ba zai Auri Bazawara ba" Abba ya doka tsaki kafin ya ce "Ai tinda ba ƙaunar Auren nan ki ke ba sai ki zauna, ga ki ga gidan nan, kullum aikinki kenan ki ce sun ce ba za su Aureki ba idan kuma na tambayesu sai su ce Ƙarya ki ka yi musu, ai ga gida ga ɗaki sai kita zama" Umma ta ce "Allah i kyauta". daga haka ta bankaɗa labule ta shige ɗaki, Mama ta riƙe haɓa gami da cewa "Lallai Makircin yarinyar nan ya ƙara girma, ga yadda ta shigo da kuka kamar wadda ya sokawa wuƙa a Zuci??" Goge hawayen ta shiga yi cike da ɓacin rai ta ce "Wallahi Abba ba ni da laifi ba gaskiya su ke faɗa maka ba, ni dai ina neman Alfarma don Allah idan za'a ƙara kai Tallata a faɗa musu gaskiyar ni Bazawara ce, idan ba haka ba ko anyi Auren Wallahi dole a rabu don ba a ginashi a tubalin gaskiya ba tin farko." a fusace Abba ya ce "Ɗan Iska ki ke neman maidani?? Kina nufin so nake na yaudaresu?? to tinda ba ƙaunar Zawarawa ake ba ba sai ace ke Budurwar ba ce ai Ƙaryar kare kai Halak, shashasha Mara kan gado." ya na gama faɗe ya yi fuuu ya bi iska su ka yi waje.
Mama ta ce "Ai kin gani, mun yi nasihar har mun gaji, ki ta korar samari Aamina wai ni ko Namijin Aljani gareki ne???"
Umar da ya dafe bango ya riƙe ƙugu ya na saurarensu sai a lokacin ya ce "Ta na fa da gaskiya Mama, fisabilillahi ko wanene ba zai taɓa lamunta ya Auri mace da sunan Budurwa ba bayan kuma Bazawara ce, kuma ko dama ace ni ne ko kuma Anas Ɗan uwana, nasan ku kanku iyayenmu ba za ku taɓa amincewa ba, mu sai mu haƙura amma ku iyayen ku zage sai kun nemawa Ƴaƴanku Ƴanci, maganar gaskiya Ƙaramta ce wai a gayawa Mutum Budurwa ce ya zo ya tarar da wannan Kakar su wanen, kuma Bazawara ma" ya na kaiwa nan ya buga tsaki ya fice, Aaminat ta faɗa ɗaki ta ci gaba da kukanta sample sample.
Mama da su Fati su ka gama tsugun-guninsu su ka tashi.
washegari
Daga Abba Umma Mama ba wanda ta gaisar ya Amsa sabi da fushin da su ke da ita. tin da ta gama Ƴan wanke-wanke da shararta ta shige ɗaki ba ta ƙara ko leƙe ba sai in za ta yi Alwala, sai yamma liƙis ta ji ciwon Jiki duk ya isheta don kuwa zaman guri ɗaya ba abin da ba ya haifar mata har ciwon kai, tashi ta yi ta sola wanka sannan ta fito ta shirya cikin doguwar rigar Atamfa, mafici ta ɗauka ta na kaɗawa.
Siyama ce ta yi sallama a tsakar gida ba tare da ta jira wani ya bata izinin shigowa ba ta danno kai don tasan in ta tasu ce ba za su barta ta ga Ƙawarta ba, Da sallama ta shiga ɗakin kafin ta ce "Aaminat Mutanen ɗaki." Aaminat ta yi dariya kafin ta ce "Na ji daɗin ganinki wallahi dama ni kaɗai nake zaune gashi su Fati ma ba sa nan bare in ji surutansu." Siyama ta ce "To surutan su Fatin har abin daɗi ne?" "Ai motsi ya fi laɓewa Siyam's." Siyama ta jinjina kai kafin ta ce "Ba fa zama zan yi ba, tashi mu je Gidanmu." ba gardama ta miƙe ta zura hijab sannan su ka fice.
Kafin su ƙarasa gidan Aaminat ta ce "Wai don Allah Siyama akwai wani aibu babba ne a tare da Bazawara?" cak ta tsaya gami da cewa "A'ahh!! tsaya kin ji na faɗa ne??" "Ke fa daɗi na dake Saurin rigimewa, bance kin faɗa ba tambayarki na yi ko kin ji labarai a wasu gurin, na ga kowa ƙyamata ya ke, kamar ma zargina ake." Kafin Siyama ta yi magana sai jin Hucin Mota su ka yi ta yo kansu da mugun gudu.
Su ka tsallake da gudu zuwa gefe. Me Motar Ko ya kula ya ci gaba da gudunsa.
Cikin Zafin nama Abdulkareem ya wawuri wani rangwamemen dutse ya wurga akan Glass ɗin Motar ya yi tsawa kwatsa-kwatsa, me Motar ya ja burki Ƙuuuuu, sannan ya fito a fusace, Majalisar tasu ya kalla cike da hargagi ya ce "Uban waye ya jefe min Mota ??? Ba ku da hankali ko?? ba ku san darajar Mota ba ko?? to wallahi ko waye sai an biyani Glass ɗina!!" Abdulkareem ya miƙe ya gyara kafaɗu sannan ya nufi gaban Matashin ya tsaya, a dake ya ce "ni ne na Fasata sai me??"
"Sai Ubanka ya biyani, Mahaukaci ne kai?? ka san darajar Mota kuwa???" "Kai Malam kar ka sake ka zagi Ubana, kuma an fasa banza ba za a biyaka ba in kana da ƙarfi ka ƙwata. Fass Matashin ya kwaɗawa Abdulkareem Mari, shafar fuskarsa ya yi kafin ya murmusa ya ce "Na gode" Cikin Sauri Aaminat da Siyama su ka yo riiiii zuwa gurin domin raba faɗa, Abdulkareem ya yi saurin cire Takalminsa ya wurga gabansu, cikin Ɗaga Murya ya ce "YaYa Aaminat kar ki tsallake layin da Takalmin nan yake." Aaminat ta zazzaro ido ta na kallonsa, shi kuwa ya yi kamar ba shi ya yi maganar ba, haka kawai sai ta tsinci kanta da komawa baya a memakon ta ƙarasa.
Matashin ya ce "Godiya nace kai min?? ina ne gidan Ubanka??, kai Yaran nan ina ne gidan Uban wannan Yaron??" ya faɗa ya na Kallon su Haisam Cokali, sai ya ga sun sa masa ido kawai kowa ya ƙi magana, maida hankali ya yi akan Abdul ya na tambayarshi gidansu, duk Tambaya ɗaya Mari Ɗaya shi kuwa Abdulkareem aikinsa ya ce Ba zai faɗa ba, a ƙalla ya yi masa mari ya kai Shida kafin Abdulkareem ya ɗaga masa hannu gami da cewa "Kar ka Ƙara dukana". "Idan na ƙara za ka rama ne??" "Ka dai ji maganata, kar ka bari ka gani" "Ai dama ance Talakawa baƙin ciki garesu, shi yasa za ka fasa min Mota, To idan na bar unguwar nan ba tare da an biyani ba Allah ya Tsine min." Abdulkareem ya yi dariya kafin ya ce "Ai ka mari kuɗinka kuma, Fuskata fara ce kyakkyawa a ƙalla duk Mari ɗaya Dubu Biyar ka ga ka Mari Dubu Talatin kenan, don haka Sai ka Zareta, ina nufin ka Zari ƙafarka in dena ganinta anan, Sakarai Mara wayo, a ganinka Namiji kamar ni zai zauna ka mareshi ne har haka sabi da na fito daga gidan Mahaukata? nasan Shekaru kawai za ka ban amma ba uwar da za ka nuna min, Na bari ka mareni ne sabi da wadda ka so kashewa Darajarta ta fi Ƙarfin Kuɗi ya Siya shi yasa na Sa jikina Fansa, idan kuma ba ka haƙura ba duk da haka ka kira POLICE wannan Katangar itace ta gidanmu, anan in ka yi gaba akwai Gata A baya ma Akwai Gate, ta ko ina in ka je za ka iya shiga ka sa a zo a kamani Ni kuma Zan sa a Ɗaureka!!!"