BURIN ZUCIYA Chapter 15
*BURIN ZUCIYA♥️* *Arewapen@ayshadansabo*
©️ _Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻_
*Last Free Pages*
*Chapter 15*
Ba wani kwalliya ne mai yawa Surayyah tayi ba,sabida yadda duk take jin jikinta a sanyaye.Daga powder sai nut lipstick da ta murza ma lips ɗinta,girarta ta gyara da brush mai wadatar gashi baki siɗik,sai tayi lining ɗin manyan eye's ɗinta farare tas. Miƙewa tayi ta ciro doguwar rigar straight gown,na atamfa pich colour wanda akai wa adon manyan flawers da cream and blue colour.Sosai kayan Yai mata kyau tare da zama a jikinta,ɗaurin ɗankwali na zamani tayi wanda ya sake haska shigarta.Siraran ɗankunni da sarƙa ta saka silver masu shegen kyau,tana cikin fesa turare Wayarta ta shiga ringing.Nan da nan bugun zuciyarta ya ƙaru,hannunta har rawa yake ta ɗauki wayar tare da tsurawa numbers ɗin da ke yawo bisa screeen ɗin wayan idanu kamar mai son haddacesu.Dab da kiran zai tsinke ta ɗaga,wani irin murya mai sanyi ne ya bugi kunnuwrta.
"Gamu a Unguwar Dosa,ina ne gidan?"
Shine abinda Abdallah ya furta a lokacin da ya fuskanci ta ɗaga wayar.Muryarta mai cike da sanyi da shagwaɓa tayi magana tana sanar dashi address ɗin gidan,ba tare da ta ji mai zai faɗi ba ta kashe wayar tana jingina da jikin mirror ɗin.Ajiyar zuciya ta sauke,tana jinjina yadda muryarsa ta ratsata.Faɗi take a cikin zuciyarta cewa,"Wato dai yadda yake mai kyau,haka muryarsa take mai sanyi da daɗin amo."Idanunta ke hasko mata pic ɗinsa tamkar a lokacin Humaida ke nuna mata.
A ɓangaren Abdallah kuwa ajiyar zuciya ya sauke,sakamakon jin muryarta da yayi.Wani irin abu yake ji na ratsa ilahirin jinin jikinsa,Ya sauke wayar a hankali yana sanar da Rayyan address ɗin da ta faɗi musu.
Basu wani sha wahala ba domin gidan akan hanya yake,koda suka iso a wajen gate ɗin gidan suka faka motar.Daidai lokacin da motar Uncle B ke shigowa cikin layin ya iso gate ɗin gidan,Rayyan ne yayi saurin fita yana masa magana,tare da sanar da Shi cewa sun zo wajen Surayyah ne.
Shigewa da motarsa Ya yi bayan ya basu umurnin su shiga daga ciki.Tunda ya ɗaura ido akan Abdallah yake faman ƙare masa kallo,gayen ya haɗu ta kowani fuska. Musabaha sukai da Uncle B ɗin bayan Rayyan ya sanar masa cewa,Abdallah shine yazo domin ganawa da Surryn.
Jagora Yai musu zuwa sitting room ɗin dake kusa da part ɗin Hajiya Kaka, Yana sanar musu cewa bari ya shiga ya turo musu Surryn.
Da sallama ya shiga sashin Hajiya Kaka,wacce take zaune a falo hannunta riƙe da carbi tana lazumi,sai TV dake kunne yana ta aiki.Zama yayi yana faɗin,
"Granny lazumi ake tayi ne,ina Surry ne? Tayi baki gasu can a sitting room suna jiranta,Surry!"
Ya ƙare maganar yana ƙwalawa Surayyah kira,hakan yasa ta yafa ƙaramin veil a saman kanta ta fito falon.Jikinta gaba ɗaya a sanyaye yake,haka take taku cike da mutuwar jiki.Tunda ta fito Uncle B ya kafeta da ido wani abu na taso masa,yana bin jikinsa.Lips ɗinta da ƙirjinta yake kallo wanda suka tafi da zuciyarsa,kafin ya sauke ganinsa akan ƙugunta yana kallon yadda rigar ya zauna a jikinta shape ɗinta ya fita sosai.Bai san lokacin da ya haɗiye wani miyau mai kauri ba,ya cigaba da zuba mata idanunsa yana faɗin,
"Surry kin bar baƙi a waje,nasa su shiga sitting room,oya maza jeki kada suyi ta jira."
Yadda taji muryarsa ya ɗan canza yasa ta dubansa,sai dai bata iya cewa komi ba tai gaba abinta ta fice daga ɗakin.A hankali take takawa har zuwa ƙofar sitting room ɗin,ta jima a tsaye kamar mai nazarin ta shiga ko ta juya.Kafin daga ƙarshe tayi shahadar ɗaga labulen ɗakin,tana doka sallama da muryarta mai sanyi da daɗin amo.Wanda ya dira a kunnuwar Abdallah da Rayyan dake zaune daga ciki,Abdallah waya yake lokacin da Yayarsa Hafsat.Hakan yasa Rayyan ya amsa sallamar Surayyah,ta shiga tare da samun waje ta zauna tana duban Rayyan ɗin.Wanda tunda ta shigo yake kanbama halittar Allah a wajennan,gaidashi tayi ya amsa da fara'a yana faɗin,
"Barka da isowa sarauniyar mata."
Sai Surayyah tayi ƙasa da kanta tana satan kallon gefenta,inda Abdallah ya lafe a cikin seater Yana waya.Ko kaɗan bata ga alamun ya dubi ma inda take zaune ba,sanye yake cikin milk colour shadda Gezner ɗan gaske.Yayi masifar yin kyau,kansa babu hula sai gashinsa da Ya sha gyara yana ƙyalli.Kallo ɗaya za kai masa kasan cewa ya iya shiga,ga baiwae kyau da Allah Yayi masa.Tunda ta zauna wani daddaɗan ƙamshinsa ke addaban hancinta,sai ta ɗauke ido daga dubansa ta mayar kan wayarta dake riƙe a hannunta.Ɗakin sai ya ɗauki shuru,illah muryar Abdallah dake tashi a hankali ba tare da ana jin me yake faɗi a cikin wayar ba.Sabida yadda Yai ƙasa da muryarsa sosai,koda ya kammala yin wayar kujerar da Rayyan yake ya duba.Wanda Shima Abdallah ya zurawa ido,harara ya sakar masa yana taɓe baki tare da maida dubansa kan wayansa tamkar ma bai san da zaman wata halitta a wajen ba.Duk yadda zuciyarsa ke azalzalarsa da Ya dubi sashin da take sai yaƙi bin umurnin zuciyar nasa,ganin hakan yasa Rayyan tashi yana faɗin,
"Sorry Amaryarmu,bari in baku waje,zan amsa call daga waje."
Yayi gaba yana duban Abdallah tare da yi masa wani sign da ido yana sakin murmushi. Tsaki Abdallah ya ja ƙasa-ƙasa Ya ɗauke ido akan Rayyan ɗin.
Kusan sakan uku da fitan Rayyan,Surayyah ta tuna bata gaida gogan ba.Hakan yasa ta ciri murya tana faɗin,"Ina yini."
Muryarta mai sanyi da daɗi ne ya tilasta masa ɗaga manyan idanunsa,ya sauke akan fuskarta wanda hakan yasa Shi jin wani abu ya tsarga masa har ƙwaƙwalwa.Tabbas Pretty dinsa ce yau zaune a gabansa suna fuskarta juna."Wata iriyar rana ce wannan mai ɗinbin nasara a gareshi?" Ya tambayi kansa yana saurin ɗauke kansa,ganin tana shirin ɗago kai ta dubeshi jin bashi da alamun zai amsa gaisuwarta.
Kamar daga sama ta jiyo husky voice ɗinsa yana faɗin,"Lafiya lau ƴan mata,ya mutanan gidan? Ya jarumta kuma? "
Jin kalamansa na ƙarshe yasa Surayyah dubansa,cikin sa a Shima idanunsa na kanta domin ganin reaction ɗinta.Hakan yasa idanunsu suka sarƙe da juna,Surayyah tayi saurin janye nata tana nanata kalmar.
"Jarumta! "
"Yes,Jarumta.Dole a kiraki jaruma tunda kika iya sanar da Hajiyata cewa ni kike so ta zaɓa miki na zama abokin rayuwarki,tamkar kin san duk duniya babu abinda za ta zaɓa min in kasa amsarsa."Abdallah Ya ƙare kalamansa Yana sake zuba mata idanunsa masu cike da kwarjini,yayin da maganganunsa ke sake rikita Surayyah suna jefata cikin ruɗu da fargaba."Me yake nufi da maganganunsa? Ita ce tace Hajiyarsa ta zaɓa mata Shi,to da yaushe sukai hakan da Hajiyar tasa?" Waɗannan sune tambayoyin dake hautsina kwanyarta.Sosai yake cigaba da morewa kallon halittar da ya kwashi tsayin watanni yana addu'a akan Allah ya sake haɗasu,sai gashi Allah ya amsa addu'arsa ya sake haɗasu ta hanyar da bai yi zato ko tsammanin hakan ba.Sarai ya karanci cewa kalamansa sun jefata cikin ruɗu,amma sai ya dake yana cigaba da faɗin.
"Malama Surayya kinyi shiru,ko miye BURIN ZUCIYARKI akan Abdallah da kika zaɓi biyowa ta hannun Mahaifiyata domin ki mallakeni a matsayin miji?"
Wannan karon Surayyah ta kasa daurewa,ɗagowa tayi gaba ɗaya ta watsa masa manyan fararen idanunta.
"Ya salam! "
Abdallah ya furta a cikin zuciyarsa, Yana jin tasirin wannan kallon har cikin zuciyarsa.Kafin ya jiyo muryarta mai cike da shagwaɓa da rauni tana faɗin,
"Please waɗannan wasu irin kalamai ne ka ke faɗi haka? Ni bani ce nasa Mahaifiyarka ta turo ka zuwa gareni ba,illah nima biyayya nayi na fitowa a yanzu domin in girmama buƙatar Mahaifiyarka da nawa kamar yadda suka buƙata.Ko kaɗan bani ce nace ta zaɓeni domin in shiga cikin rayuwarka ba,please ka daina jefa zuciyata a cikin ruɗu da kalamanka don Allah."
Surayyah ta ƙare maganar muryarta na rawa,alamun dab take da fashewa da kuka idan ya cigaba da ruɗata da kalamansa. Tunda ta fara magana ya tsinci kansa a cikin wani yanayi,yana sake jin ƙaunarta da soyayyarta na bin jininsa.Wace iriyar Yarinya ce wannan mai shagwaɓa da iya narke murya cikin salon sace zuciya? Tabbas dole tayi ta fisgo zuciyar maza har su kasa danne kwaɗayinsu a kanta.Fuskewa Yayi ya ɗauke kansa,cike da taɓe baki yake faɗin,
"Okey tunda kin roƙa na daina,amma fa kisani,Abdallah zai amsheki ne amatsayin zaɓin mahaifiyarsa,ba domin kiyin daidai da irin tsarin macen da yake so ya mallaka ba.Sai domin bana tsallake Umurnin Mahaifiyata akan duk abinda ta nuna tana so.Don haka kisa a ranki cewa Abdallah na da BURIN ZUCIYARsa,wacce yake nema ruwa a jallo.Da zarar ya sake haɗuwa da Yarinyar da ta zama itace ruhinsa,wacce duk wani fitar numfashi nasa da sonta yake fita,to zan aurota in haɗaku ku zama ku biyu.Don haka ko kin mallaki Abdallah a matsayin miji,kada ki saki jiki ki ɗauka cewa naki ne ke kaɗai.Akwai wata da zuciyata ke muradi,wacce ta zama min BURIN ZUCIYATA! Kin kuma san a kullum babu abinda ɗan adam ke so irin ya cika BURIN ZUCIYARSA akan abinda yake so."
Tunda ya cigaba da magana Surayyah ke share hawayen dake gudu a fuskarta,"Me yasa rayuwa tazo mata a haka ne? Me yasa ita ba za ta taɓa samun cikar BURIN ZUCIYARTA na son tayi auren soyayya,tana so ana tsananin sonta ba? Wasu irin kalamai masu ɗaci Abdallah ke jifanta dasu haka?" Ta jerawa kanta tarin tambayoyin tana kai bakin gyalenta ta ɗauke hawayen dake zuba mata.Koda wasa bata sake gigin kallon sashin da yake ba,shi ko Abdallah yana duban duk wani motsinta.Komi yana yinsa ne cikin jarumta matuƙa,domin ji yake tamkar ya janyota jikinsa ya lashe hawayen dake zuba a idanunta.So yake ya sanar da ita cewa,ita ce BURIN ZUCIYAR nasa,amma bazai yi hakan ba domin wani dalili nashi.Bazai taɓa nuna mata,ko Hajiya cewa ita ce BURINsa kuma mafarkinsa ba,har zuwa lokacin da za ta zama mallakinsa ta koyawa zuciyarta sonshi da kanta.Hakan yasa ya basar da ita bai sake cewa uffan ba,illah ma wayarsa da Ya ɗauka yana danne-danne.Ɗakin ya ɗauki shuru tamkar babu wasu halittu a cikinsa,sai musayar shaƙar ƙamshin juna da suke.Cikin sanyin jiki dana zuciya Surayyah ta miƙe ta fara takawa domin barin ɗakin.
"Ina zuwa?"
Shine kawai abinda ta furta ta fice cikin sauri.Sai lokacin Abdallah ya ɗaga kai yabi bayanta da kallo,yana jin zuciyarsa fes cike da wani irin nishaɗi mara misaltuwa.Sai ya koma ya ginjina bayansa da jikin kushin ɗin yana mai lumshe idanu,surarta da yanayin takunta ke gilmawa a cikin idanunsa,yana ma Allah godia da Ya amsa addu'arsa zai cika masa BURIN ZUCIYARsa ta hanyar mallakan Pretty ɗinsa.
Rayyan dai can cikin motar Abdallah ya koma ya lafe yana waya da Zeenat Yarinyar da zai aura,nan da watanni biyu masu zuwa.Tsayin mintuna biyar Surayyah ta ɗauka kafin ta sake yin sallama,hannunwanta ɗauke da tray da ta ɗauro lemu da abubuwan da tai musu. Gabansa ta aje tray ɗin tana mai tsugunawa domin zuba masa lemun pineapple ɗin da Yai mugun daɗi ya kuma ɗauki sanyi,hakan yasa kusancinsu ƙaruwa ta yadda daddaɗan ƙamshinta ya fitini hancinsa.Har hakan ya tilasta mishi zuba mata manyan idanunsa,yana kallon yadda hannunta ke rawa wajen zuba lemun,alamun taji a jikinta idanunsa na kanta kenan.Murmushi ne ya suɓuce masa,amma sai yayi saurin tamke face a lokacin da ta ɗago tana miƙa masa cup ɗin tana faɗin,
"Bismillah,ga lemu
Shi ɗayan har yanzu bai sake shigowa ba,ko za a miƙa masa waje an barshi ba ko ruwa."
Tayi maganar cike da sanyin murya,hakan yasa Abdallah karɓan cup ɗin ya aje a gefensa ba tare da Ya sha ba.Idanunsa da suke mata nauyi ya zuba mata yana faɗin,
"No! Karki damu da Rayyan,nima yanzu za mu wuce,tunda na zo na ga jarumar da ta dage sai ta mallaki Abdallah.Wacce tayi nasarar yima BURIN ZUCIYATA shigar sauri,any way na yaba da zaɓin Uwa ta gari.Dama ni nasan ba za ta taɓa zaɓa mini abu mara kyau ba,ko mara nagarta ba."
Ya ƙare kalamansa yana miƙa hannu ya ɗauki cup ɗin lemun ya kai baki.Kurɓa biyu yai masa ya aje cup ɗin yana miƙewa tsaye,har lokacin kan Surayyah na ƙasa bata sake gigin kallonsa ba.Taku ɗaya biyu Yayi ya tsaya a gabanta,hannuwansa zube a aljihun wandonsa,kafin ya zaro hannunsa ya aje mata bandir ɗin ƴan 100 naira sabbi kar yana faɗin,
"Gashinan babu yawa,kyautar talaka.Ko kati kya saka,ko Ƴan mata."
Bai jira jin komi ba yayi gaba yana sakin murmushi mai ƙayatarwa.Shi kaɗai yasan yadda yake ji a cikin zuciya da gangar jikinsa,dab da zai fita ya jiyo cool voice ɗinta tana faɗin.
"Allah tsare,Ya kaiku gida lafiya.A gaida Hajiya, Na gode Allah ƙara buɗi."
Bai san sanda ya waiwayo yana sake dubanta ba,cikin sa a itama ta ɗago face ɗinta,sai suka ƙurawa juna ido kafin tayi saurin janye nata idanun.Tana jin wani abu na keta zuciyarta zuwa gangar jikinta,muryarsa ta jiyo yana faɗin,
"Bye,sai gani na biyu,a lokacin ne zanji wace ce Surayyah ko?"
Ya ƙare maganar cikin wani irin stone da Ya tilasta Surryn saurin sake dubansa,idonsa ya juya mata cikin wani irin salo da baima san yayi ba.Sai tayi saurin kauda kanta bugun zuciyarta na ƙaruwa sosai.
"Tunda kin kasa cewa komi please ki gaida Hajiya,sai na sake dawowa za mu gaisa yanzu sauri nake kinji ƴan mata."
Cewar Abdallah yana yin gaba abinsa.Har ya fita zuwa gate din gidan mamakin kansa da kansa yake,na yadda yake zaro magana a gabanta.Wani murmushi ne ya suɓuce masa,amma sai yayi saurin haɗe face yana isa ga motarsa inda Rayyan ke zaman jiran fitowarsa,Yai masa tsiya.... ✍🏻
*Anan kawo ƙarshen free pages ɗin,ko ban faɗi ba kunsan cewa ba a ce komi ba game da labari mai ɗinbin faɗakarwa da kuma ƙayatarwa.Don haka kuyi hanzari ku zo ayi wannan tafiyar tare da ku,akwai tarin cakwakiya a gaba.*