SANADIN HIJIRA

Chapter 23_24

by @ummufadeela01

SANADIN HIJIRA

     

         Na

Ummu Fadeela


23/24







Zuge gaba daya ruwan allurar cikin syringe Dr Shettima ya yi kana ya kama hannun Ummie gami da saita daidai jijiyar jininta ya danna kan allurar akai, bai cire ba sai da ya dura duk ruwan allurar ya fara bin jininta sannan ya zare gami da cusa syringe din cikin bag na kayan aikinsa. "Zazzabine mai zafi ya kamata, amma babu wani damuwa mun mata allurar paracetamol  zuwa anjima zafin jikin zai sauka, idan kuma bai sauka ba sai a nemeni, but in sha Allah ma zai sauka din".

Cewar dr yana daukar bag nashi ya yi hanyar waje, bin bayansa Abeey da Umma sukayi suna mishi godiya ya tafi...

Bai wani yi nisa da fita ba wayarsa ta fara burari, murmushin gefen baki ya yi ya gangara gefen kwalta yana gyara parking ya yi picking na call din.
"Dr ban gane ba wai an yi gabas da kare, ba allurar poison mai saka mutuwa nan take  mukayi da kai zaka mata ba? amma na ji kamar kana maganar paracetamol for God sake".... Murmushi Dr ya yi ya ce, "Calm down mana, a halin da take dinnan nan na tabbata ba sai mun mata waccar allurar ba tana gab da zama tarihi, so ayi hakuri kawai komai a sannu ake binsa yanzu haka allurar da muka dinga mata a baya ya fara circulating a jininta, no need for waccar din ta kusa gangarawa"....."Are you sure dr?".


"Yes i assure you, but a sannu fa ake bin duniyar nan komai a sannu sannu ake binsa" "what Dr? A sannu fah, ina ba wannan maganar Duniya gudu take yi dan haka nima dole in zabga da gudu domin in bita dan cimma burina, Kiit aka yanke wayar. daga bangarensa shima ya aje tashi yana ta hada lissafi yana warwarewa shi kadai.
Abeey tun da ya bar dakin Ummie samansa ya koma, tunanin mutumin da ya gani dazu ya dawo mishi sabo fil, zagaye kawai yake ko abincin da Umma ta gabatar mishi ya kasa ci, "Me hakan ke nufi? wannan Alburhan ne ko dai mai kama dashine?" Ya yiwa kanshi tambayar, "Ko dai gizo yake minne kamar yadda Hosni ya ce, amma har murmushi da dago min hannu yake yi. 

Ko kuma dai nima na fara haukacewa ne?" haka Abeey yake ta sambatu shi kadai ba tare da ya samo bakin zaren ba bare ya fara warwara. Yana cikin wannan hali har aka kira magrib, bathroom na shi ya shiga ya dauro alwala kana ya fito ya zura jallabiya milk kala da hula irin mai tsayawa a tsakiyar kan nan ya wuce masallaci, sai da ya gabatar da har sallar isha sannan ya dawo gida.


"Anya yallabai yau kalau kake kuwa, bakaci abincin rana ba, dinner ma gashi a zaune, ga fruits na yanka maka shima baka sha ba,band now karfe tara ta wuce banga kana kallon News ba, which is very hard kai ko da baka da lafiya ne News na karfe tara baya wuceka, me ke damunka ne? Idan ma halin da Safeenatu da dan Albarka suke ciki kake tunani komai zai zama daidai da izinin Allah, addu'a suke bukata ba sanya damuwa a rai ba har kazo wani ciwon ya kamaka in shiga uku" Umma ta fada tana shafa farin gemunshi da ya sha gyara.

Ba dan yaso ba ya biyemata a kokarinta na mantar dashi halin da yake ciki, sai dai bata sani ba wannan wani gagarumin al'amarine da ya girmi shekaru da tunaninta.
Lokacin da dare ya raba Abeey yana kwance a dakinsa yana Baccii, from no where wata irin iska mai karfin gaske ta fara kadawa har labulen windows suna daguwa da bugar junansu, tashi Abeey yayi dauke da mamaki dan iska ake kamar ana tsakiyar damuna har da wani karan hadari rugugugugu haka kamar irin hadarin tsakiyar september mai tafe da tsawa dinnan, mamakine sosai akan fuskarshi wannan wane irin iska ne alhali muna tsakiyar lokacin zafi, laluben gefenshi ya fara sai dai wayam babu Umma babu alamarta. Kafafunsa ya sauke daga saman gadon ya nufi windown dan ganin meke faruwa, tarin mamakine ya kuma yi mishi rubdugu ganin glass na windown a wangale alhali kuma baya barin window a bude dan a kalla Ac biyune a dakinsa. "Haba no wonder mana iska take kadawa haka, may be Fanta ce ta bude windown nan," Abeey ya fada yana sanya kai da kamo handle na tagar zai rufe,Dammmm gabanshi ya fadi a lokaci guda kuma yana kai hannu kan idanunshi ya mutsutsuke su wai ko idanunshi ne basu gwada mishi daidai ba,still shi ya gani tsakar gidan daga can kasa kwanyar da hasken security light tamkar rana, yana tsaye ya jingina da lamp post hannayenshi a harde bisa kirjinsa yana kallon saitin windown Abeey dake hawa na biyu.

Idanu suka hada dashi ya dago mishi hannu yana wannan murmushin dai da ya kasa banbance na mecece.
A wani irin birkice Abeey ya saki tagar ya juyo dakarfi yana sauke wani irin numfashi kamar yayi wasan polo. Dulum yaga dakin ya yi duhu bakikkirin an dauke wuta, "Innalillahi wa'inna ilaihiraji'una" Abeey ya furta lokacin da wutar dakin ta fara wal wal wal tana kawowa ta dauke, nan fa jikinsa ya fara makyarkyata zufa yana yanko masa kamar ya hadiyi kunama, Alburhan! Ya fada cikin kidima..a cikin duhu ya fara jiyo kujerar zamanshi dake can gefe irin kwantaccen kujerar nan tana rawa da girgiza ita kadai kafun ya fara jiyo ana rera waka da wani irin sauti mara dadin ji da sauraro cikin harshen larabci.
Uhibbuka ya akhie Fadlallah.
Ana Uhibbukha hubban shadidan ya Akhie Fadlallah. 
Daaallll wutar dakin ta dawo ta tsaya.rumtse idanu Abeey ya yi da karfin gaske fitsari yana zurarowa daga cikin wandonshi kana zufa yana wankeshi sakamakon abun da ya yi arba dashi. Alburhan ne kishingide bisa kujerar hannayenshi a harde da juna yayinda kujerar take kwanciya tana tashi dashi.idanunshi duka biyu suna zubar da jini kamar hawaye,gefen kanshi a rabe har yana iya hango kwakwalwarshi jini yana zuba da gangarawa ta gefen wuyarshi hakoranshi sun fito zako zako kamar na kwarangwal haka faratan hannunshi da na kafarshi is totally different da na mutane...
"Alburhan dama kana raye?" Wannan ce tambayar da Abeey ke son fitarwa amma yaji tamkar an sanya salatif an kulle mashi baki.
Hhhhhhhhh, wata irin dariya mara dadin ji ta gauraye dakin kafun bisa mamakin Abeey a kace,  "Ina raye akhie Fadlallah,amma matacciyar rayuwa,gangar jikina ta dade da zama kasa amma RUHIII na tana zagayawa a bayan kasa da muradin daukan FANSAAA, ya fada yana jan maganar wanda ya kara hautsina cikin Abeey ya ji kamar zai saki gudawa.
Baya baya ya fara da nufin dira ta bayan taga, sai dai yana isa jikin tagar wanda aka kira da Alburhan dake zaune a can nesa ya miko hannunshi sai ga hannun tana mikewa kamar ana warware igiya ta iso har wajen Abeey ta baya baya Abeey ya yi yana zare ido hannun na cigaba da biyoshi...

**********
FANNE
Su Uwa suna ta kuka har kamar zasu mutu suma, amma abun mamaki ni ko digon hawaye na kasa fitarwa a idanuna, gaba daya garinmu ya kacame da kuka manya da yara mata da maza sai dai na wasu yafi na wasu, bakyajin komai a gidanmu sai sautin kururuwa da ambaton kalmar mun shiga uku mun lalace, mazan gidanmu duka sun kare waye zai jibanci lamuranmu....Zuwa lokacin idan da za'a tare hawayen da jama'a suke zubarwa tabbas zai iya haddasa ambaliya amma ni ko digo daya ya kasa sauka daga kwarmin idanuna, har yanzu ganin abun nake kamar a tatsuniyoyi ko kuma irin labaran nan na kunne ya girmi kaka, har yanzu ban yadda cewa Babana da kuma Ya Almuhajir dina sun rasu ba, gani nake kamar zan farka daga wannan mummunar mafarkin, maganganunsa ne suke ta dawo min cikin kwanyata kamar yanzu yake furta minsu..
A hankali maganganun Baba na dazu suma suka fara dawo min daya bayan daya, shin dama Baba yasan zai rasu ne yasa yake bamu hakuri da yimini nasiha? Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un. Sai yanzu na ji zuciyata ta motsa jikina ya dauki rawa, kwakwalwata ta fara caji, idanuna suka sauka kan akwatin da Baba Da Yaya suka sani shiryawa ne akan suna dawowa masallaci zamu bar garin nan ashe duniyar gaba daya Za su Bari

Kuka ne ya tahomin mai karfin gaske wanda sai yanzu ya zo, tunda nake a rayuwata ban taba yin kuka irin wannan ba kuka nake yi tun karfina har  na fara rasa garkuwar jikina kuma babu mai lallashi, Maahh ma kukan take amma hawayene kawai ke kwaranya dake nuna kukan zuci take.


Misalin karfe biyar aka gama aikin ceton sai dai babu wanda aka ceto da rai, sama da mutum dari biyu da suke a wajen sun rigamu gidan gaskiya, Allah ya karbi shahadarsu!...A waje guda aka hadasu aka sallacesu sannan akaje aka binne, shi ke nan kuma, su baba Da ya Muhajir kam Allah ya takaita musu wahalasun tafi abun su.
Kamar jira ake a gama binnesu muka fara jiyo ruwan bind*gu ta ko ina a lokacin ana gab da kiran sallar magriba, Ratatatatatata,tusshhhh,Bouum,tauuu,shine kawai karan dake tashi, mutum yana iya hango yadda bull*t ke shawagi a sararin samaniya jajawur kamar garwashin wuta, a yayin da ihun jama'a ya karu karar kuma sai karuwa yake yana dada kusanto tsakiyar gari, ridididididdi haka karar kafafun mutane suna ta gudun ceton rai kowa yana mikar gabas dan shiga jeji, yakura da Iya matan Baba Bamaina da iyalanshi suka mike, goya kananan yara sukayi a baya sannan manya suka yi gaba. "Uwani zama bai ganmu ba anan, da irin wannan suka koromu daga garinmu, muka yi gudun ceton rai sai gashi sun biyomu har nan su kashe mana mazajenmu yanzu kuma mu zasu kashe su kwashi yaranmu su wuce dasu. Lallai dole mu tafi neman mafaka, dolece wannan" cewar Iya, zabura Uwa ta yi tana dafa bango ta mike jikinta yana rawa, "Iya ai muma bamu ga ta zama ba Innalillahi wannan wacce irin masifa ce Allah na tuba ka yafeni, daga wannan sai wannan, Yaganah dauko mana jakar dazu, Yaganah da cikinta ya gama durar ruwa ta mike ta na janyo akwatin da suka hada, muna zaune daki da Maahh dan na kasa fita in barta, duk abun da yake faruwa inaji kuma ina jiyo maganganun su Uwa jin kamar suna sauka yasa na sauko da gudu ina haki, a tsakar gida na same su kowa rike da guzurinsa na iya abun da zai iya dauka abun mamaki kuma kowa ya fito daga sassansu wasu ma har sun fara tafiya. "Uwa ina zaki tafi ki barmu a halin da Maahh take ciki, dan Allah ki taimakamin kada ki tafi ki barmu a nan bamu da kowa a  yanzu daga Allah sai ke".


Dakatawa daga tafiyar da take Uwa ta yi kafin ta juyo tayi sakato, "Kan bantan uban can, ni kika sani munafuka marar kunya, a ina kika sanni, me na hada dake, tun wuri ki nemi mai taimaka miki ba dai Uwa ba, a wannan hali da ake ciki ai kowa ta kansa yake, kije ki ciccibi Uwartaki ki goyata kuma ku kama gabanku, "Ratatatatatatatata shaaaaaaaaa" wani karan harbi mai rikita yan hanji suka kara dakar dodon kunnenmu a gefe guda kuma kamar ana watsa kasa a kan roofing shaaaaaa haka zaka ji, wani wawan tsalle Uwa ta yi ta makale jikin Bango tana kamo duk wata addu'ar da tazo bakinta amma ta kasa karisawa.


Wani irin sufa na yi na kamo kafarta ina kaiwa duke, "Dan Allah Uwa ki min rai ki kamamin Maahh, ciki gareta kuma bata iya taka kafarta jikinta ya kumbura bazan iya goyata ba ki taimaka mana Uwaaa. Kafarta ta sanya ta take hannuna da ke rike da bakin zaninta da iya karfinta, tsabar azabar da naji bansan sadda na kurma ihu ba 

"Wayyoooo Babaaaaa kazo ka taimakeniii"na fada da karfi, ba tare da Uwa ta dubi halin da muke ciki ba, batare da ta dubi girman Allahn da na hadata dashi ba, ba tare da ta dubi irin girma da fadin gidanmu da kuma tashin hankalin da muke ciki ba haka ta sa kai ta fice bayan ta murtsuke min hannu da takalmanta ko waigowa bata yi ba, ina durkushe a wajen hannuna duka biyu dafe da kasa kaina a tsugunne fuskata na zubar da hawaye nake kallon kofar da kowa ya bi ya fita daga gidan...


SAURA PAGES BIYU MU GAMA BOOK 1,IN SHAA ALLAH