MATAR ALIYU (The Upside Of Down)
Chapter 1
by @aishaangel
💨 *MATAR ALIYU...* 💨
The Upside Of Down
By Aysher Angel
Page 1
Free page
*Where Romance Meets Chaos....*
*Alhamdullilah I'm Back....✍️✍️✍️✍️*
*Matar Aliyu, The Upside Of Down paid book ne, zaku samu complete ɗinsa akan naira dari shidda 600, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, evidence of payment via WhatsApp *** or MTN card/VTU/MTN transfer to ****
Murmushi ne kwance akan fuskarta yayinda jirgin helicopter yake yawo dasu a saman ruwan mai kyawun kallo, hasken rana wanda ya haske ta cikin ruwan ya ƙara bashi yanayi mai kyau, hannunsa rike da hannunta, babu zato babu tsammani taji ya saki hannunta ya wurgar da ita waje ta kofar jirgin dake a bude, tayi ihu amma sautin engine ya danne muryarta ihunta banza, idanunta a waje na matuƙar mamaki a yayinda komai yake dawo mata a kai tiryan-tiryan, tana witnessing abun da zata kira da lokacinta na karshe a rayuwa.
Wannan shi ake kira makashinka yana tare da kai, tana mashi kallon marar wayo ashe wasa yake da ita? Shin tare da wa ya kulla wannan mugun shirin na ganin bayanta? Tun yaushe ne take mashi kallon biri yake mata kallon ayaba? Shin akwai saka hannun danginta a ciki? Ko kuma shine kadai ya kulla ya aiwatar. Wadannan sune tambayoyi da suke fal a ranta yayinda take tunkarar abun da zata kira da lokacinta na karshe a rayuwa, hawaye suna fita daga idanunta.
Ta faɗa a cikin ruwan mai matuƙar sanyi, tayi iyakar ƙoƙarinta ta hanyar amfani da dukkanin karfinta domin ta cimma saman ruwan amma jikinta yayi mata nauyi, tana nutsewa a ruwan tana kokowa da lumfashinta tana hango jirgin helicopter din da ya juya yana mai nisa wa ganinta har ya ɓace mata, ta lumshe idanu tana nutsewa zuwa kasan ruwan.
*****
Karim Lamido, Jihar Taraba.
Aliyu jiya ya dawo daga aikin hidimar kasa da yayi a jihar katsina, yayi kewar kogin garinsu ya fito da safe yana tafiya a gefen ruwan yana jinsa a matuƙar nishadi na kallon ruwan da yadda igiyar ruwan take kaiwa da komowa, yana tunawa da abubuwa da yawa da suka faru a lokacin yarinta.
Abu ya hango daga nesa kwance a gaɓar kogin, mace ce kwance, da sassarfa ya ƙarasa ya kamata yana girgizata, bata lumfashi ya danna hannunsa akan cikinta domin fitar da ruwan da ta sha, tari tayi ta feso da ruwa, ta bude idanunta a hankali ta ɗaura a kansa, "Aliyu," ta kira sunansa.
Aliyu ya shiga matuƙar rudani, bai santa ba, bai taɓa ganinta ba, amma ya aka yi tasan sunansa har ta kirashi dashi, ganin yana ɓata lokaci kuma tana da buƙatar taimakon gaggawa, ya dauketa ya kama hanyar gida yana tafiya yana sauri-sauri gudu-gudu, ya kwantar da ita a daya daga cikin bukkokin dake a gidan.
Nene ta biyoshi da sauri tana tambayarsa abun da ya faru. "Na ganta ne kwance a gaɓar kogi tana da sauran lumfashi amma tana buƙatar taimakon gaggawa domin ceto rayuwarta."
Ya juya ya fita tsakar gida, ya bata waje domin ta bata taimakon gaggawa da ya dace, bayan mintina biyar ta fi ta sanar dashi cewa ta samu barci.
Ta koma ya bi bayanta suka zauna jigum-jigum suna jiran farkawarta, Nene ta saka masu aiki su girka abinci kafin ta farka, Aliyu tunani ne sosai a ransa, ta kira sunansa bayan da ta ɗaura idanunta a kansa, shin a ina ta sanshi? Domin da gaskiyarta ta kira sunansa yaga hakan a idanunta, zai ƙaryata idan aka ce chanka tayi daidai.
A hankali ta bude idanunta ta ɗaura a kansa, kamar mai raɗa tace, "Aliyu." Muryarta tana fita a hankali.
Aliyu ya ware idanu yana kallonta, yayinda Nene ta fita kawo mata abinci bayan da tayi mata sannu da jiki, da mamaki yake tambayarta a inda tasan sunansa. "A ina kika san sunana?"
Ta faɗaɗa fuskarta da murmushi tana mai shafar fuskarsa, ta kama hannunsa ta sumbata tace, "Of course nasan sunanka my Halal."
Aliyu ya maimaita abun da tace, "Your Halal? Ni?".
"Yeah, I love you my Halal zan cigaba da baka farin har karshen rayuwata."
Aliyu ya rasa bakin magana, ya rasa mamaki zai shiga ko kuma rudani, mi take nufi da kiransa da her Halal, gani yayi ta fara fizge-fizge yayi saurin riketa, tayi luu sai kuma ta bude idanu ta mike zaune, "Aliyu a ina nike?" Ta tambaya.
Wannan rudanin yafi karfin kansa, ɗazu ta kirashi her Halal, yanzu kuma tana wani abun kamar ba ita.
"Miye sunanki?" Ya tambaya.
"FatimaZahra." Ta bashi amsa.
"Daga wani gari kike?".
Tayi jim sai kuma ta ware hannu alamar bata tuna ba. A karo na biyu yace, "Miye sunanki?".
"FatimaZahra... Angel," ta bashi amsa.
"Miye sunana?".
"Aliyu."
"How did you know my name?".
"Ban iya turanci ba."
Aliyu ya zaro idanu ɗazu ta gama turanci kamar baturiyar amurka amma yanzu tana faɗa mashi bata iya turanci ba, ya lumfasa, "Ya aka yi kika san sunana?" Ta ware hannuwa, "Ban sani ba kawai naji na kiraka da sunan ne."
Wanda yayi daidai da shigowar Nene tana dauke da kwano wanda yake dauke da Doya da miya wadda taji kifi.
Ta ajiye mata, "Ki ci."
FatimaZahra kamar jira take ta wawuro kwanon tana loma hannu baka hannu kworya kamar wadda bata taɓa ganin abinci ba, Nene da Aliyu suka zuba mata idanu fuskokinsu dauke da mamaki.
Nene tace, "Ta faɗa maka daga inda take?" Aliyu ya girgiza kai, "Sunanta kawai ta tuna, FatimaZahra, Angel." Wanda yayi daidai da dafe kanta da tayi tana mai sakin ƙaramin ihu, ta kallesu ta kalli kwanon doya da miyar kifi dake a gabanta ta kalli hannunta wanda ya tabbatar mata da itace ta ci abincin, ta fasa ihu tayi ball da kwanon, sauran abincin da ta rage ya tarwatse a kasa.
"What the hell is this? Baku san aikinku bane, waye ya ciyar dani doya, yana sone inyi adding weight in zama laughing stock, and who got karfin halin da zai ciyar dani kifi bayan kun san bana so, kun manta inda timetable na abincina yake ne, ko kuma wani mugun ne a gidan nan ya sakaku, dama nasan gidan nan cike yake da makiyana wadanda basu son ganina a doron kasa."
Ta dafe cikinta tana ihu, "Fuck, zan ƙara kiba in koma abun dariya," tana kakaro amai.
Aliyu ya kamata, "Calm down."
Wurga daya tayi mashi ta kai mashi naushi a fuska saida ya hango taurari, ya koma gefe yana maida lumfashi yana mamakin mugun karfi da take dashi, kamar wacce take cin tuwon kasa, yayi faɗa da maza masu karfi amma bai taɓa amsar naushi da ya kai wannan karfi ba, daga nan bai ƙara gigin nufar inda take ba.
Nene tuni ta rakume a bango tana rawar sanyi, idan tayi mata wannan naushi saidai suyi mata wanka a sadata da makwancinta na gaskiya domin bata tunanin zata rayu.
*Matar Aliyu, The Upside Of Down paid book ne, zaku samu complete ɗinsa akan naira dari shidda 600, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, evidence of payment via WhatsApp *** or MTN card/VTU/MTN transfer to ****
Taku Har Kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)