CHAPTER 5
by @deejasmah
Ikon Allah ne ya kai shi gabanta kafin ta kai ga zamewa ƙasa amma ta riga da ta some idanun ta sun ƙafe, jijjiga ta ya soma yi yana kiran sunan ta amma ina tayi nisa. Kinkimar ta yayi ya buɗe ɗakin ya shiga da ita, a kan kafet ya kwantar da ita har lokacin yana kiran sunanta ''Nana! Nana!! Jannah!!!". Amma ba ta ma san yana yi ba balle ta iya motsawa, kitchen ya fito ya ɗauki ruwa ya koma ciki yana shafa mata amma ko motsi ba ta yi ba. A yanzu kam duk dauriyar Khaleed hankalin shi ya tashi don bai taɓa ganin tashin hankali irin na yau ba, idanun nan sun kaɗa sun yi jawur damuwa ya bayyana kan shi ziryan.
Wayar shi ya ɗaga yana fara neman wanda ya zo kan shi a lokacin don ya san dole sai ya kai ta asibiti amma hakan ba zai yiwu kan mashin ba tunda jikin ta ya riga da ya saki, sai dai number da ya kira ba ma ta shiga ko kaɗan yana dubawa ma ya ga network ɗin wayar ta shi ta ɗauke ɗif duka emergency yake nuna masa. Tagumi yayi ya na kallon ta ya ƙara kai hannu ya shafa mata ruwa yana cewa '' Jannah kar ki tafi ki bar ni don Allah, Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!".
Ganin zaman ba zai fisshe shi ba ne ya sanya shi fita da key a hannun shi, gidan ya datse ya hau mashin ɗin shi ya fita zuwa bakin hanya. Ya daɗe a tsaye kafin ya ga wani mai Napep ya shigo unguwar da tarin kwalaye a ciki, saka masa hannu yayi mutumin ya tsaya yana cewa '' Alhaji ba tafiya zan yi ba, kaya na kawo".
''Na sani ai, shi yasa na tsayar da kai, in ka kai kayan ina zaka je?".
''Babu, nema na fito shi zan cigaba da yi''.
''Toh don Allah taimako nake so in Ka ajiye kayan nan ka taimaka ka kai mu asibiti ni da iyalina ba ta da lafiya''.
''Allah sarki, Allah ya bata lafiya. Mu je bawan Allah nan gidan Alhaji Rabe zan tsaya'' ajiyar zuciya ya sauke tuna gidan Alhajin ne a farkon layin na su, babban gida ne sosai don gidan mata huɗu ne a gidan kuma su kan ɗan taɓa abun arziki da su kasancewar su (Khaleed) ne wainda suka fara tarewa a layin. Taya shi yayi suka kwashe kayan zuwa gidan kafin ya kuma shiga gaba mai keke ya bi shi a baya har zuwa gidan su, buɗewa yayi ya shiga ya fito saɓe da Nana a kafaɗar shi. Kwantar da ita yayi har lokacin dai bata ko motsi kafin ya maida mashin ɗin ta shi ya shiga kuma datse gidan, kana ya fito ya shige keken ya zauna bayan ya ɗaura kan ta bisa cinyar shi yanda kwanciyar zai iya musu daɗi. Gani yayi mai keken ya fito ya saki labulen da bai lura akwai ba ya gyara musu yanda ba za'a gan ta kan hanya ba, sosai Khaleed ya ji daɗi don dama yana ta lissafin hakan a cikin ran shi.
Tafiyar ta su zuwa asibiti ya zama cikin shiru irin mai firgitarwan nan musamman ta Khaleed da bai san me za'a tarar ba, inda Allah ya taimaka asibitin da suke zuwa nan farkon unguwar ne ya sanya ba su yi tafiya mai tsayi ba aka iso. Shi ya shiga ya shaidawa ma'aikata cewa yana da mara lafiya haka suka fito da gadon marasa lafiya aka ɗaura ta a kai, sallamar mai keke yayi ya tafi bayan ya masa addu'ar samun lafiyar ta ya ja keken shi cike da tausayi ya tafi.
Cikin ƙanƙanin lokaci ma'aikatan lafiya suka rufu kan Nana domin ceto rayuwar ta, aka bar Khaleed cikin damuwa sai kaiwa da komowa yake ya gaza zama balle natsuwa ta riske shi. An ɗauki kusan awa biyu kafin babban likitan ya fito daga emergencyn da aka shigar da Nanan ajiyar zuciya Khaleed ɗin ya sauke ganin rahama a fuskar likitan, duban shi yayi da kyau yana cewa '' mu je ko?".
Bin shi yayi a baya zuwa ofishin shi yana jin ƙirjin shi na bugawa, sai da suka zauna kafin ya iya cewa '' Likita lafiya dai ko?".
''Alhamdulillah, lafiyar ta ƙalau firgici ne ya sanya ta suma amma bayan nan babu komai. Sai dai ina taya ka murna matar ka tana ɗauke da cikin wata biyu da sati uku''.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya saki yana jin farin ciki yana mamaye masa zuciya, Nanar shi, Jannahn shi tana ɗauke da ciki na shi a karo na biyu a rayuwar su tare. Sai kuma ya tuno faɗuwar da tayi daren jiya yanda ya zo ya same ta da kuma firgicin ɗazu da safe don haka yace '' amma likita ta faɗi fa jiya, wani abu bai samu cikin ba?".
''Babu abinda ya sami cikin, sai dai yana barazanar shafin cikin nata don mahaifar ta ba wani ƙwari ne da shi ba. Amma za mu yi mata ɗaurin ciki don tabbatar da zaman shi lafiya kuma za mu bata bedrest kar tayi aikin ƙarfi daga nan har san da cikin zai shiga wata na huɗu. Kuma za mu riƙe ta a nan don tabbatar da zaman lafiyar ta kafin mu ga yanayin yanda jikin zai yi, ta farfaɗo amma mun yi mata allurar bacci saboda ƙwaƙwalwar ta ta samu natsuwa. Za ka iya shiga ka gan ta amma ban da hayaniyar da zai iya tada ta''.
Godiya yayi wa likitan ya fita zuciyar sa cike da abu guda uku, cikin Nana, ɗaurin mahaifa, Bedrest. Abubuwa ne da ya taɓa jin su amma na yau sun kuma sanya shi a cikin damuwa musamman in ya tuna baƙin halayen da take nuna masa a zamantakewar su. Shin me yake faruwa ne da ita haka? Sanin bai da amsar tambayar shi ya sanya shi shiga ɗakin da take kwance inda ya gan ta kwance samɓal tayi wani kalar fayau kamar wacce ta shekara tana ciwo, yawu ya haɗiye cike da tausayinta ya zauna gefen ta hannun ta mara cannula ya riƙe cikin na shi yana shafawa a hankali. Sai lokacin ya samu natsuwar kiran gidajen su don ɗazu bai ma hayyacin shi balle ya tuna shaidawa wani halin da ake ciki.................