Zumar Hamada 🍯 🏜️

Wrapped In Blessings

by @zahrabmrs

Zumar Hamada 
Page 21
Private jet ɗin Alhaji Kamal ya ya tashi daga Abuja zuwa katsina ,Cikin jet ɗin kuwa kowa ya samu mazauninsa 
A gaba akwai Daddy tare da matansa ,suna ta magana kan yadda za su ƙarasa shirin Sallah idan sun isa Katsina
Anty Zaheera na tare da Ibrahim da Kamal Junior  ,mijin anty Zaheera dan katsina ne shiyasa suke sallah a Chan this time around gidansu zata sauka cos maman Mijin nata na umrah 
 Ameerah kuwa Tana  Kaduna a can za ta yi Sallah tare da dangin mijinta 
ameenatu ma Tana abuja tare da mijinta ba yadda batayi ba ya barta taje katsina sallah  ba ,yace Shima yana bukatar iyalinsa a kusa …Safa da Marwa suna gefe ɗaya suna kallon wani film a tablet Tadala da Mardiyyah kuwa…Tun tashin jirgin ba su yi shiru ba Sai hira  suke yi, Lokaci zuwa lokaci Mardiyyah tana sa Tadala dariya , amal na kwance a gefe ba lafiya ,A gefe guda kuma…Kuna ta ware kanta EarPods na kunne, ba  waƙar  take ji ba  Fuskarta ɗauke da rashin walwala Tun bayan faɗan Anty Zaheera…Ta kasa sakewa ,har yanzu tana jin kunyar bulalar da aka yi mata alkawari a gaban kowa
Khalifa ya tashi daga inda yake Ya karaso  a hankali ya zo ya zauna kusa da Tadala 
Ya haɗe hannayensa Sirrin me ake yi ne haka?
Mardiyyah masa hararar wasa ,Akwai abubuwan da ba a gaya wa maza Ta matsa kusa da Tadala girls talks ne
Tadala ta yi dariya  Khalifa ya girgiza Ka yace Anty Tadala fada min mana…tunda mardis taki  mardiyyah ta kalli Khalifa Ta sake kallon Tadala..Wait ..Duk suka kalleta  Anty kuma?Kai da Tadala age mates ne fa Wani sabon salo ne wanna ?Wallah, Mardiyyah, for almost two weeks kenan Khalifa ya fara ce min Anty
Sai wani girmama ni yake yi Na yi, na yi, ya ƙi Ko me ya sa… oho?  maybe yana tunanin kina da kanwa mace  shine yake kamun kafa tun yanzu ,gabadaya suka kwashe da dariya ,Banda Khalifa Wanda Idanunsa suna kan Tadala yace  Kin fi ni sanin dalilin dayasa nake ce miki anty ay 
dariyar da ke fuskar Tadala Ta ɗauke Gabanta ya faɗi Ta zuba masa ido Shi ma ita yake kallo Kallon nan…Da ya fara yi mata a kwanakin nan Kamar yana son ya faɗi wani abu , Ta yi saurin kau da kai Kin fi ni sanin dalili ,Wane dalili?Shin yana nufin…?A’a Ba zai yiwu ba Ta haɗiye yawu A karo na farko tun da suka shiga jirgin…Ta rasa abin cewa Gashi kuma…Su Daddy suna can gaba Ba ya kusa Ballantana ta ɗaga ido ta nemi amsa daga fuskarsa 
Shiru tayi yayinda mardiyya da khalifa suka cigaba da hirarsu 
Bayan jirgin ya sauka duk suka nufi  gidan Hajiya Katon mansion ne mai cike da nutsuwa da ƙamshin alfarma irin  gidajen Katsina. A tsakar gidan akwai bishiyoyi da furanni kala-kala, yayin da masu aiki suke kai da kawowa cikin ladabi Tun daga bakin ƙofa zaka  fara jin wani irin annashuwa Mun iso gida Ahmad ya fada cikin murna  Gaba ɗaya suka nufi babban falon hajia .
Tana zaune kan wata babbar kujera, sanye cikin atamfa mai launin ja  da farin gyale a kanta ,Duk da ta kusa shekara saba’in da biyar, fuskarta cike take da kamala da annuri Wani irin kwarjini ne na uwa da face dinta Tana ganin su murmushi ya bayyana a fuskarta Alhamdulillah…barka ku da zuwa 
Cikin nitsuwa, ɗaya bayan ɗaya aka fara gaishe ta 
Kowa yana durƙusawa ko zama cikin ladabi, tana amsawa cikin mutunci, tana tambayar lafiyar kowa.
Khalifa, ya kasar sanyi ?
Alhamdulillah, Hajiya.
Yan biyu , ya makaranta?
Lafiya lau, Hajiya 
Daya Bayan daya hajia take kiran su tana  tambayar su yanda suke 
Har aka zo kan Tadala Cikin sanyin jiki ta ƙaraso Ta ɗan durƙusa Assalamu alaikum, Hajiya Idanun Hajiya suka sauka kanta  Wa alaikumus salam ,Hajia ta gyara zaman ta 
Ina yini hajiya? Matso kusa yar nan ,Yau Allah Ya yi na ga yar ɗakin Zaheera wacce kullum sai an ba ni labarinta tadala ta sadda kanta kasa 
 Ya sunanki,yanmata?Sunana Tadala 
Tadala? Eh Hajia 
Baki da wani suna ne? Tadala ta jinjina kai 
Ina da shi  ,Hajia tace Ina jinki ?
Papa ya ce ni sunan mamansa  ne… ba a faɗa Amma dai FATMA Zahra ne, tadala ta fada cikin tsoro Kamar tayi laifi (ta tuna yadda papa baya son a kira sunan ko da wasa tsabar son  da yake wa mamansa Kafin ta rasu ,Fatima Zahra Sunan mahafiyata kenan masha Allah cewar hajia 
Hajiya ta kamo hannunta Ta kalleta da kyau  ta ce cikin taushin murya ni daga yau Fadimatu zan dinga kiranki 
tadala ta maimaita a ranta Fadimatu Amma sunan ya yi mata daɗi sosai To,  hajia.
Allah Ya albarkace ki Fadimatu 
ameen ya Allah hajia
 kuma ki saki jikin ki kinji ?kema yar gidace 
Bayan an gama gaisawa da Hajiya, masu aiki suka fara ɗaukar akwatuna zuwa ɗakuna.
Tadala ta bi Mardiyyah, Safa, Marwa  Amal ,da Kuna zuwa ɗakin da aka tanadar masu  Babban ɗaki ne sosai Akwai gadaje huɗu masu girma, kowanne an yi masa shimfiɗa A gefe kuma akwai dressing area da babban balcony da yake kallon lambun gidan 
Welcome to our Eid room  mardiyyah ta kalli tadala Tana cire mayafi 
Marwa ta jefa jakarta kan wani gado 
Ni da Safa nan muke  Safa ta gyada kai yeah sis Always 
Mardiyyah kuma ta nuna wani gado 
Ni da Tadala a nan  Ta juyo tana murmushi 
Right, roomie?Tadala ta yi dariya 
Right
cikin sanyin jiki amal ta zauna a dayan gadon gaba daya suka fara  mata ya jiki 
Kuna kuwa Tun da suka shigo, ta zauna kan gadonta ita kaɗai EarPods na kunne
Wayarta a hannu  Kamar ba ta tare da su.
Mardiyyah ta taɓe baki Drama queen
Kuna ta ɗan harare ta

Bayan ɗan lokaci suka gama shirya kayansu A lokacin yaran uncle Bashir kanin dady Wanda suka dawo gidan hajia da  zama suka shigo ,Nana da Nasiba ,very friendly girls cikin lokaci kadan suka ware da tadala suna ta hira 

A ɗaya ɗakin kuma Zahra da Yusra ne a ciki 
Bayan an sha ruwa Babban falon Hajiya ya cika da jamaa  yaya da jikoki,  A tsakiyar falon kuwa Alhaji Kamal ne zaune a gefen Hajiya ,Sai maƙale  mata  yake kamar wani ƙaramin yaro ,Hajiya ta kalle shi Ta girgiza kai Kai yanzu, da girman ka a gaban jikokina  ka zo ka wani maƙale min sai ka ce wani yaro? dariya ta kaure a falon Khalifa ya ce Dad, caught in 4KH
Hajia ta kalli shi Duk wata sai ka zo Katsina ,Ballantana ka ce kewata kake Daddy ya ɗan matsa kusa da ita Hajiya, ganinki sau daya a wata baya isata Ki dawo Abuja mana, yadda zan riƙa ganinki kullum 
kullum fa kace ?eh mana hajjaju 
Ni dai bani barin katsina mahaifata 
Hajiya dramar  ku bata kare wa ke da yaronki, Wata mata ce ta shigo Tana da fara’a sosai zata kai kusan shekara 56,
Tare take da yaranta mata 4 namiji 1  daga gani suma suna ciki  wadatar rayuwa shar dasu,dan daddy kaf yan uwansa ba wanda be dangwali arzikin saba  Bayan an gama  gaisuwa 
Hajiya ta yi murmushi Ga Aishatu Ta kalli Tadala Wannan ita ce Aishatu, yayar Kamal da Zaheera Ita ce babba a cikinsu Kece bakuwa shiyasa nake gabatar dake ga sauran yan uwan  Cikin ladabi Tadala ta gaishe da Aishatun itama ta amsa Tana tambayar ta mutan gidan 
Kamal, har yanzu ba ka girma ba? Gskia Ka tashi daga gefen hajia kar Ka balla mana uwa  Daddy ya yi dariya Kada ki fara Anty ,ke da kuke gari daya Kuna tare ko Yaushe ,kiri kiri kun hanata dawowa abuja Captain Bashir ne ya shigo Shiru da natsuwa  ne a tattare da shi shi ke binsu Zaheera ,yaransa 4 biyu yan mata suna tare da hajia a nan gidan …
Asiya  da hauwa Suma suka karaso 
Dukkansu sun yi aure kuma suna zaune a Katsina ,Nan da nan falon ya ƙara cika da hayaniya da raha.
Chan sai ga Abubakar wato autan hajia Dr ne a katsina specialist hospital Shima Bayan Babbar sallah zaayi bikin sa .
masha Allah duk an hallara ga ,fadimatu yar uwar sadiya ,itama da zama yar gida hajiya ta kara gabbatar da tadala ,kaf yaran hajiya ba Wanda yayi Tadala kallon banza sun jiku da tarbiya taga alama 

Tun kafin asubah, Gidan Hajiya ya fara motsawa ƙamshin turare da na girki suna gauraye  gidan Kowa ya tashi cikin annashuwar Eid A 
ɗakin ’yan mata kuwa mardiyya ce ta fara  shiryawa chan sai ga tadala  sanye da emerald green lace  An yi mata dinkin daya dace da jikinta ,set din gold dinta ta kasa Tana fitowa daga toilet inda ta shiga saka Kayan suka hada ido da mardiyyah tadalaaaa oh my God kin ganki kuwa ?you look so beautiful kamar wata princess 
twins da Kuna duk suka maida attention dinsu kan tadala ,wani irin bakin ciki ne ya turnike su ,most especially Kuna ,ji take kamar ta bankawa tadala wuta ita da kayan su kone 
mstwwww wallahi ya mardiyya ban San Yaushe kika zama low class ba ,gold din ne biki taba gani ba ko lace din ?mardiyya ta kalli Kuna ,don’t spoil my mood its eid morning and watch your mouth 
twins dai basu ce uffan ma sai fushe fushe suke dan da suka ga Kayan tadala ji suke gaba daya tayi outshining dinsu 
muyi pics tadala you look stunning Amal ta matso suka fara pics da mardiyya da tadala 
falon hajia suka nufa dan gaishe ta daga nan a wuce eid ,matan gidadon katsina ansha golds ko wacce tayi kyau daidai gwargwado gaban sadiya ne ya fadi da taga kyaun da tadala tayi ,Allah ka rufa min asiri kasa kar yarinyar nan ta sami wanda yakai hubbi kudi ta aura wanan kyau haka ta ayyana a ranta
kai masha Allah buzuwa haka kikayi kyau cewar umma cikin murmshin yake itama dai sadiya yake  take tayi  irin lace din da zata sa gobe zaheera ta siyawa tadala kaicho falmata kuwa ko Kallo tadala bata ishe taba 

Bayan an dawo daga Sallar Eid…Gidan ya sake cika da hayaniya Matan gidan gaba ɗaya suka nufi kitchen domin kammala abinci Domin Hajiya ba ta yarda a bar komai a hannun masu aiki ba Dole matan  gidan su dan yi wani abu da kansu dik ba wani Abu suke da wuce supervising ba 
Tadala kuwa…chan gefen wata bishiya ta koma Wayarta ta yi ƙara Farida ce Da murmushi ta  daga tace farida gayuuu farida tace tadala buzuwa duk sukayi dariya  sun dade suna hira har farida ta hada tadala da mamanta da sauran yan gidansu Farida tana ba ta labarin yadda ta yi Sallah a Yobe ita kuma tana ba ta labarin Katsina inda sukayi zasu hadu next week Monday a school 
daga nan tadala ta  kira Moussa Bai jima ba ya haɗa ta da Uma Assalamu alaikum, Uma  Wa alaikumus salam  Yaya Sallah uma ?Uma ta yi dariya Wannan Sallar shar damu Har abinci na aika wa maƙota muna ta shagali har kayan sallah munyi 
Aghali ya karɓi wayar a Wajan Uma  tadala Kin san me muka saya? A’a sai ka fada 
Kaji biyar muka soya ,Iyye lalle shar daku Aghali har Kaji biyar ?
Eh fa Harda naman kasuwa jiya na kaiwa Anty fiza nata cefe nan sallah ,Wani irin farin ciki ya cika Zuciyarta  Alhamdulillah Ka samu kayan sallah ko Aghali ?eh mana a Shagon Mansoor dinki na saya yadi har ya rage min farashin kudin ,kwallah ta cika mata ido Jin Murnar da Aghali yake Akan Kayan sallah sallar data wuce harda Koke Koken sa bashi da kayan sallah 
Uma ta sake karɓar wayar tace tadala Kuma Alhaji Kamal ya kira mu da  wayar Moussa ya yi mana barka da sallah  Tadala ta yi shiru wani irin girma Daddy ya ƙaru a idonta kuma taji dadin hakan haka kawai Mansoor bai taɓa kiran Uma ko Moussa ya yi musu barka da Sallah ba sai ta sa shi gaba ,daga nan ta kira fiza suka sha hira idan fiza ke tambayar ko sadiya ta canza hali ,tadala tace lafiya lou suke zaune duk dan ta kwantar masu da hankali hafsat ta amsa waya tana ta cewa tadala tazo ta tafi da ita tayi missing dinta Bayan ta gama waya da Hafsat
har yanzu murmushi ne fuskar Tadala  kiran daddy ke shigowa wani ɗan murmushi ya suɓuce mata Assalamu alaikum daddy Ina kwana 
Wa alaikumus salam… Barka da Sallah, amaryar Kamal  ,kunya ya rufe ta Kamar tana ganinsa a gabanta
Daddyyyy…Ta faɗa cikin shagwaɓa 
Dariyarsa ta fito daga ɗayan ɓangaren.
You look so beautiful, baby… kamar ranar aurenmu Tadala ta dafe goshinta.
Daddy pls  Ta sake faɗa cike da kunya A hankali ta tambaya A ina ka ganni? Ni fa ban ganka ba Daddy ya yi murmushi Yanzu haka ma ina hangonki Tadala ta zaro ido  ta juya ,Ta duba gefenta Babu kowa ,Ta sake duba balcony Babu shi  baki ta ɗan turo baki gaba To me na yi yanzu idan kana ganina? murmushi Daddy ya yi Baki kika turo 
Nan take Ta sa hannu rufe bakin  gskia ka mun wayo ni ban ga kwaliyar  Sallar kaba… ina ta nemanka 
Daddy ya yi shiru na wasu daƙiƙu Wani irin daɗi ya mamaye zuciyarsa 
Da gaske Mi Dahlia? Kina nema na? baki ta buɗe bata San sanda maganar  ta subuce mata na Uhmm…
Ya yi dariya Kar ki damu Gobe za ki ganni Zamu yi hawan sallah 
Dama nasan zakiyi ay gidadon katsina guda 
Gidadon Katsina? A ina kika ji sunan nan?
Ta yi dariya I have my ways
Ya yi murmushi ,you Little detective 
Suna ne fa da duniya ta sanka dashi ya zaayi kayi mamakin dan na sani 
Mardiyyah ta fito kenan ta hango tadala ga waya a kunne sai murmushi take 
ashe waya kk tun dazu ?nasan dai bazai wuce da mansoor bane 
Kafin Tadala ta yi magana… khalifa yayi gyara murya Da alama ya ji tambayar  Ya juyaYa kalli Tadala sai kuma ya ce a taƙaiceBa shi take waya ba.
Mardiyyah ta zaro ido Huh? Khalifa bai ƙara cewa komai ba Ya ci gaba da tafiyarsa Ya bar su a tsaye 
Ta kalli bayan Khalifa ta kalli wayarta ta sake kallon inda ya wuce Tambaya ta sake dawowa zuciyarta
Wai… me Khalifa yake nufi da ita ne?Kuma…Ta yaya ya san ba da Mansoor take waya ba ?