ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

10

by @gureenjoh

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO


✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN 

(GUREENJOH)


@Gureenjo on Arewapen

@Gureenjih6763 on Wattpad 


ADABI WRITERS ASSOCIATION


TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. 


GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.



*SHAFI NA GOMA*


Daren ranar da abin ya faru ko sau ɗaya bai runtsa ba gabaɗaya bacci ya kauracewa idanunsa, duk tsarinsa na dare ya gama har Adu'a yayi ya kwanta amma da ya rufe idanu sautin sauƙar hannunsa kan fuskarta ke dawo mishi.


Bai taɓa yin abin da yake jin damuwa a kanshi ba sai wannan bayan ya natsu sossai da alqur'ani sai ya fahimci bai kyauta ba dukda laifinta ne amma yana ganin bai kamata ta haka ya ɗauki mataki ba, despite his anger he was raised to respect women don ko ɗaga murya wa iyayensu mata basu taɓa ji mazan na yi ba wannan tarbiyar gidan ne, sannan beside that addini ma bai yarda da duka a fuska ba saboda irin darajar da Allah yayi wa fuskar dan adam. That guilt eats him alive.


Tsam ya bar gadon ya fita balcony ya tsaya hannunayensa duk biyu zube a aljihun kayan baccin jikinsa idanunsa a lumshe yana shakar iskar da ke kadawa kaɗan kaɗan, lips ɗinshi kuma na ambaton Astagfirullah! Har sai da ya ji sassauci kan ya dawo ko da ya duba time biyu har yayi kawai ya je yayi alwala ya zo ya fara nafila sai da yayi ra'aka shidda ya zauna ya buɗe alqur'ani ya shiga karatu, yana yi ɗin amma har lokacin chan ƙasan ranshi guiltness ɗin na nan, hoton jinin lips ɗinta da kuma idanunta na dawo mishi ya san dole ne suka sake crossing path ya bata haƙuri ba wai don ya ramawa Malam Bala mari ba sai don ya san ya ketare iyakar ubangiji a kanta.


Sai da ya ja Sallar asuba kan ya cewa dalibanshi yau babu karatun safe, gida ya dawo ya ɗan kwanta bacci saboda headache da ya matsa masa.


Ƙarfe tara ma ya farka saboda rashin sabo da baccin safe ya sake wanka ya sauƙo ya karya da abincin Maamah, yana so ya shiga cikin gidan ya gaishe su amma sai wayanshi ya shiga ringing, ko da ya duba Malaminsa ne daga chan saudia.


Murmushi ya saki mai sanyi da ya ƙarawa fuskarsa kyau yayi sliding tare da makalata kunne nan larabci ya tashi, sun kusa awa guda suna larabcewa kan suka yi sallama, sai ya ɗan leƙa media don ganin abin da ke faruwa, karo ya ci da trending topic da aka kwana tattaunawa a platforms, shi ne tsaye dab Wanchan 'yar dabar kaman yadda sunanta yake a wurinshi, daga fuskarta har fuskarshi side view ake gani, ba dankwali kanta kuma sun yi dab kowa ya gani ya san magana yake yi mata.


Kan Caption ɗin ya kai idanunsa 

"Your Sheikh is not what you think he is!"

Ya jima yana kallon Caption ɗin kan ya sa yatsarsa ɗaya ya danna comment section anan storm ɗin ya ke, wasu na cewa kila wa'azi yake mata daga gani kaman ba musulma ba ce, a haka ɗin wasu na dragging ɗinshi inda wasu ke kare shi.


Idanunsa ya lumshe ya sake buɗewa yayi ƙasa ba zai yi scrolling biyu uku bai ga picture ɗin ba different Captions, babu abin da ya tsana irin fake scandals ɗin nan a kanshi, kowani motsi yayi sai an yada duniya kaman da gayya abin amma bai wani damu ba, ya miƙe sanye yake da farar Thob sai jar Ghutra, kafafunshi wasu takalma ne masu taushi baƙake ya fita daga sashen don ya tabbatar samun albarkar iyayensa da ganin murmushinsu ne kaɗai zai sanyaya ransa a lokacin.


Sashen Ammiey ya fara nufa, da sallama ya tura kofar ya shiga.

Mufida ce da rukayya sai wasu friends ɗinsu zaune a parlorn suna hira, ganinshi ya sa duk suka natsu kan suka amsa sallamar suka shiga gaishe shi. 

Amsawa yayi cikin kulawa don yana da wannan dabi'ar na mayar da hankali akan 'yan uwansa, ba wai ya saki fuska ba ne kuma ba dogon surutu ya tsaya yi ba ya wuce ɗakin Ammiey.


"Wayyyoooo Mufy yau na taki sa'a...! Ruwa zan zuba ƙasa na shaaaa wayyoo Allahnaa yau na ga Sheikh har na ji magananshi a zahiri"

Wata kawarsu Farida ta daka tsalle cikin wani irin murna take faɗa.


Ta sha zuwa gidan ba ita ba dayawa cikin kawayensu har da na su Sumayya su kan zo gidan musamman don ganin Shehi wasu su dace wasu kuma har su gama wahalar ko ganinshi ba sa samu su yi.

Hafsy ta lumshe ido ta buɗ

"Yaaaa Allahu! Wai kun ji wani sassanyar kamshinsa da ya cika parlorn nan!"


Farida ta ce 

"ke ta kamshi kike wai kin ga skin ɗinshi? Kafafunsa tsabar fari da taushi a ido kawai za ki kalla ki rantse da Allah ba ya taka kasa ga wani irin tafiya da yake cikin natsuwa kar ki kai ga idanunsa da ba ya wani kallon kurilla wa kowa....Wayyyoooo Allah"

Haka suka ta santi suna wasssafa sa, shi kam tuni ya tsufa gaban Mahaifiyarsa, bayan sun gaisa take ce mishi.


"Na ga kuma abin da ake ta yaɗawa, na san halinka farin sani shiyasa ma daga ni har mahaifinka muka zubar da zancen don samun natsuwar zuciyarka, ina so in ce maka ka ƙara haƙuri komai zai wuce watarana wannan jayayyar da ake yi wa duk wani motsinka zai zama tarihi"


Ba kowa ne zai gane abin da ke ransa ba amma dayake ita uwa ce ta san ya fi kowa tsanar abin da ke faruwa da shi, wannan media ɗin na zama sanadiyar traumatizing mutane dayawa, fake rumors da scandals ɗin idan suka yi yawa suna farautar natsuwar mutum, amma da yake shi ɗin ya riƙe Allah sai ya kan samu sassauci ta wani ɓangaren, so ake a ga ya tozarta ba ya kuma Fatan Allah ya kawo wannan rana.


"Allah ya sa Ammiey jazakillahu khairan"

Ta Yi murmushi.


"Sai batu na gaba!"

Ya ɗaga kai ya ɗan kalleta daga fuskarta ya san abin da zata yi magana a kai, kanshi ya mayar ƙasa aiko dai sai ji yayi tana cewa.


"Akwai Na'ima ɗiyar Hajiya Hadiza kawata mahaifinta Ustaz Abdallah na san ka san shi"

Kai ya gyaɗ

"To ita Na'imar na yaba da hankalinta, yarinya ce marar hayaniya, kyakyawa kuma mahaddaciyar alqur'ani ce da littatafai idan ka samu lokaci ina so ka je ku gaisa, zamanka haka ɗin nan yana damun gabaɗaya zuri'ar nan"


Bashi da halin musu! Ammiey ce ke ba da umurni don haka cikin kwantar da kai ya ce mata 

"In shaa Allahu zan samu lokaci in je"

"yauwa Allah ya yi muku albarka, Allah ya haɗe kanku ya cigaba da kare mana kai"

Murmushi mai kyau ya saki don adu'ar nan ta fi masa duk wani kyauta na duniya.


"Ameen ya rabbi"

Ya amsata kan ya miƙe.

"Na bar ki lafiya Ammiey"

Daga haka ya fice, wurin Maamah ya je itama sun yi hira kaɗan ta mishi nasiha da ƙara ban haƙuri akan rayuwa don wani faɗar Allah da annabi ma da zaka yi haushi kake ba sa.

Daga nan ya isa wurin Daddah suka gaisa tayi ta mishi Adu'o'i yana amsawa ya ce mata akwai tukwicin adu'arta zai turo mata, tayi murmushi tare da Binshi da ido har ya fita.


Ta rasa dalili amma a ranta duk cikin jikokinta babu wanda take yi wa ƙaunar da take yi wa Irshad, tana kuma jin tsantsar tausayinsa shi ne mai gudun duniya amma shi duniya take bi dama haka rayuwa ta gada.


"Daddah kina ƙaunar yaron nan, shiyasa kika ƙi matsa masa batun aure ga mata nan iri iri daga nan har Gembu kowa na miki tayi a yi haɗi yadda aka saba kin ƙi"


Ta kalli ɗiyarta kuma goggon su Irshad ta ce 

"Hindatu shi Shehi ba irin mazan da za'a musu dole a abu ba ne darajarshi ta wuce nan, baki ganin kyautar da Allah yayi mana a kanshi? Muna nan zaune Shehi zai kawo macen da za ta bamu mamaki don na tabbatar ba lallai a matan Fulani ko hausa a samu mai irin ilimi da kuma hange da yake so ba sai dai kila Labarawa"


"yanzu sai ki barshi ya auro balarabiyar ya kawo?"


"Meyasa zan hana? Ba musulmai ba ne?"


Ita dai Hindatu bata ce komai ba amma a kufule take ta rasa Meyasa Daddah da mijinta tun kan su rasu ma suka zama cikin Fulani masu ilimin addini da kuma hange su sam ba sa kyamar wani yare kaman yadda cikakkun Fulani suke yi, har ga Allah ko iyayen su Irshad da Ammar an auro sun ne kawai amma dangi na Gembu da ma su Goggo Hindatu duk ba so suke ba amma Alhj Hardo ya fi su iko dole suka haƙura gashi yanzu Daddah tana so ta musu bukulun wanda suke harin ma ya dawo cikinsu ya ɗauki mata.


Tashi ta yi ta bar parlorn ta koma daki wurin 'yar uwarta suka dasa mita akan lamarin Irshad ɗin, gani suke kowa tsoronshi yake shiyasa ake kaffa kaffa da shi, ko ɗaga mishi murya ba'a yi sai dai lallami da maganar hankali to yaushe ma yayi abin da za'a daga Muryar banda abin su?


Ko da ya isa ɓangarensa shiri yayi don daga an yi azahar akwai wani lecture mai muhimmanci da zai bayar, tsaff ya fita a babban Malaminsa, mai hasken kamala, yana saukowa sai ga Imamu ya tattare gadgets ɗinsa suka yi masallaci, bayan gabatar da Sallar azahar ya zauna kujerar wa'azi, bayan godiya ga Allah da kuma cikakken sallama wa al'ummar musulmi ya kalli camera ɗin ya fara magana...


"Karatun mu na yau sunanshi Riga-ka-fi, kaman yadda duk muka san yanzu zaɓe na gab da ƙaratuwa zan yi magana ne a kanmu mu 'yan arewa... Yan arewa ya kamata a ce zuwa yanzu duk mun farka, lokaci ne ya yi da za mu haɗa kai wurin gina kawunanmu da kanmu, al'umma su ke da alhakin zaɓar duk wani shugaba da zai wakilcesu, amma mene? Tarin bayin Allah za su fita dubbani, kwansu da kwarkwatarsu su sha rana, su yini a layi wurin ganin sun ka da kuri'unsu suna gama wannan wahalar daga zarar buƙata ta biya wannan amana da aka bashi na zaɓarshi zai yasar, wannan wakili ko shugaba zai tafi yana amfani da iyaka tunaninsa da kwakwalwarsa babu abin da ya shafe shi da me waennan bayin Allah da suka zaɓeni suke buƙata? Me suke so ko nema wurin gina tasu rayuwar? 

Saboda haka 'yan arewacin Nigeria akwai babban aiki a kanku na tirjiya da cewa baku yarda ba sai dai ku zaɓi wanda kuke so ya wakilceku kar ku bari a zaɓa muku ko a yi wasa da tunaninku, abin takaici tsabar an mayar da al'umma marasa tunani ɗan siyasa ne zai wakilta wani ya bi Layin zaɓe yana miƙa ɗari biyar ko ɗari biyu yana saye kuri'unku kuna dangwala masa alhali kun san future ɗinku da na 'ya'yanku kuke rushewa na iya shekarun da zai yi da karbar wannan dari biyar din, wani yunwa da wahala zai sayawa kansa tun daga barin gaban wannan Akwatin zaɓe har wasu shekaru huɗun masu zuwa idan ba sa'a ba yunwar ce zata yi ajalinsa. Idan har baku gyara ba har abada za ku zama cikin tankade da rairayar ra'ayoyi da ake yi ba ku da mutanen da za su je su fitar da naku ra'ayin. Ku tsayawa kawunanku da kanku ya ku al'umma kuma ku dage wurin roƙon zaɓin Allah a komai na rayuwa, ku kasance masu duba zuciya ba kalaman baki ba."


Ya ɗan dakata tare da ɗaukar ruwa da ke gefensa ya ɗan kurɓa ya ajiye....