Chapter 17
*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty❤️*
M.A JUMARE FOOD AND SPICES
Pure and Natural hygienic tasty.
Muna da garin Ɗanwake da yaji mai kyau dakan hannu, akwai kuka, tsamiya, garin tamba, kuɓewa da daddawa.
Muna aikawa da kayanmu a ko'ina
Anguwan Ma'aji new millennium city kaduna
Phone number ***
*HIJABS CORNER BY JANAFTY*
*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design, muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
****, tuntuɓa ta wannan lambar*
*KADUNA/ZARIA*
*Page 17*
Mikewa Laila tayi daga kan jikin Sulaiman Lokaci daya tana Tattaro kalaman da zatayi amfani dashi Saboda kada safiya ta fahimci wani abu na faruwa in bata manta ba, a koda yaushe sukayi waya da mommy gargadin datake mata kenan kada ta sake ta bari wani daga bangaran Sulaiman yasa ita ke jan Ragamar Rayuwarsa.
Da Mirmishi ta tinkari Safiya ita kuma ba ita take kallo ba Hankalinta na wajen dan"uwanta da taga ya rame kamar ba Saraki ba,Bata damu da Laila ba ta wuceta bata ma sani ba ta karisa gaban Sulaiman cikin karin mamakin ganin ko bai mgana bai mata ba ko bai ganeta bane..?
Haba taya za"ayi ace ya saraki bai ganeta ba sai dai in wani abu ne yake Faruwa..!
Kai tsaye tace"Ya Saraki Hajiya ta Damu da Halin da kake ciki bama Hajiya ba kowa da kowa ashe kai Lafiyarka kalau ayi ta kiranka a waya baka Dauka..!
Tafada Lokaci daya tana kara nazarinsa Dagowa yayi ya zuba mata ido da Rinanun idanuwansa azuciyarsa farimcikin ganinta yake yi yana so yace mata wani abu sai dai bai da wannan ikon Laila na wajen yayi kokarin mikewa idonsa na kallon Laila sai kuma ya koma ya zauna kamar wani Sakarai Gaban Safiya ya Fadi ta kallesa Daga sama har kasa na wani Lokaci Tana nazarinsa kafin ta Juya tana kallon Laila cikin nazarinta wacce ta Kakaro mirmishi lokaci daya tana fadin"Sannu da zuwa Anty Safiya..!
Ko amsa mata batayi ba ta sake maida kallonta kan sulaiman cikin son Cire Shakkunta tace"Ya saraki mgana fa nake yi..?meyasa hajiya ke kiranka baka Dauka..?ai ko baka Saurari kowa ba ita ta chanchanci ka Saurareta..!
Sanda take mganar ji yayi kamar ya tashi ya Rumgumeta ya Fadamata bai sani ba wani bakinciki ya Lullubeshi sai alokacin ya Tuna da Hajiya Hajiya fa itace ta Haifesa har da ita ya manta da ita.
Laila na kokarin mgana kawai kamar an Fizgi bakinsa taji yace"Bansani ba Safiya..bansan Hajiya ta kirani ba ni mantawa nake da kowa da komai komai yana Hannun Lailata harda duka Wayoyina..!
Yafada yana saurin kauda kansa yama ji kamar bashi yayi mganar ba kamar an fizgo mganar daga bakinsa ne Wata uwar Harara Laila ta sakarmai wanda yasa ya marairaice yana Fadin"Don Allah kiyi hakuri Lailata..bansan na fadi haka ba..!
A muryansa kamar zai saki kuka Safiya datayi mutuwar tsaye kanta ya Sara Kirjinta ya bada wani Dam!
Jikintaya fara rawa ta dafe kanta ita ba yarinya bace tsakaninta da Sulaiman shekaru hudu tasan komai a shekarunta yaci ace ta Fahimci wani abu.
Hawaye suka ciko idanuwanta hakoranta suka fara kafkaf kamar wacce zazzabi yakamata Laila kuwa kokarin kare kanta take yi Cikim Muryanta take fadin"Kaji Habibina da wata mgana?saboda kaga Anty Safiya kake bani hakuri..?kinji kyalesa fada fa ya gami mun yanzu shine don ya ganki ya sauya mgana..mganar wayarsa kuma ta Fadi a kasa ne Screen ya Lalace ba"a ganin mai kira tana Hannuna wayar nayi nayi a siya wata yaki yace yafison agyarata to tana wajen gyara mai gyaran wayar ne sakarai ya bar wayar a kunne kuna ta Kira shuru..!
Safiya data gama jin Rainin Hamkalinta cikin wata murya tace"Ke baki da waya ne..?ko ya Saraki ya rasa yadda zai kira iyayensa ne..?sannan nazo gidanan tun Safe bakwanan da kuka dawo na aiko a sanar daku me kikace..?
Bazaku ga kowa ba..Daman haka kuke ma baki in sun zo..?
Laila na shafa girarta tace"Ai bamu san ke bane..na zata!
Bata gama Rufe baki ba Safiya ta kariso gabanta batayi wata wata ba ta Chakumi wuyanta Cikin bacin rai da karaji take fadin"Me kika yi ma Dan"uwana Laila..?Don buraubanki me kika bashi yasha ya koma haka..?
Ayadda take mgana ranta ya gama baci idonta kuma ya rufe Cikin karaji take mgana tana jijjiga Laila Da karfi wacce ta tsorata ta fara rawan murya tana Fadin"Ni...ni..ban yi komai ba..!
Fas..!Fas..!
Safiya ta tsinketa da mari har guda Biyu dama da Hauni da sai da ta nemi ta kife Safiya ta sake Chakumota Cikin Tsawa da karaji take kara fadin"Nace uban me kika basa yasha don Uwarki Salame..?
Sulaiman daya mike da Sauri ya Zaro ido Dashi da Laila wacce ta Fashe da kukan tsoro da makirci tana Fadin"Wayyo Ni me nayi mai..?habibi zata kasheni wuyana..!
Kamar kububuwa haka ya karisa ga Safiya ya rike hannayenta Dake wuyan Laila yana kokarin bambareta safiya da bata gani daman bata Daukan Raini itace sak Hajiya zabba"u a Tsaye take bata daukan Raini ko kadan
Safiya batama tsaya bi ta kansa ba ta kara kwadama Laila mari a wajen kunnenta Daya shigeta Cikin karaji ga Hawayen takaichi sun fara zubo mata ta jijjigata tana Fadin"Zaki fadamin ko sai nayi miki dukan tsiya..?
Laila sai Habo ta baki ta hanci tana Lakato hannunta taga jini sai ta fasa Ihu kamar zai Tsaga gidan tana Fadin"Sulaiman kana gani yar'uwanka zata kasheni ko..?
Kalli ta fitarmin da jini fa na shiga uku..!
Take fada tana kuka da ihu wanda yayi daidai da shigowar Sunaima Falon ta iske su magajiya Tsaye hannu Dafe kan kirji Ita dasu Samira kafin ma ta tambayi ba"asi ta samu amsar tambayanta na jiyo ihu da Hayaniya Daga upstsir Cikin mamaki ta kalli magajiya tana Fadin"Meke faruwa ne..?hayaniyar suwaye nake jiyowa..?
Magajiya tace"Hajiya Safiya ce kanwar Yallabai ta haura sama ba Dadewa sai kuma mukaji ihu da Hayaniya..!
Sunaima tayi jim aranta tace ko sun samu Labari ne..!
Ganin bata da amsa ne yasa taja Jikinta zuwa Dakinta ammh gabadaya Hankalinta na Falo tana son sanin meke Faruwa..?kodai wani abu ne ya samu Sulaiman din..?sai da gabanta ya fadi da tuna da hakan Saboda ayanayin datake ciki bata kaunar wani abu ya samu Sulaiman ko Saboda su wasim.
Sulaiman yayi iya yinsa ya Raba Hannayen Safiya da wuyan Laila ya kasa Cikin bacin rai ya kalleta yana fadin"Sakarta Safiya...!
Ko ta kansa bata bi Laila ta shaka Duk tayi wujiga wujiga,Safiya ta kara kaimata mari sulaiman ya tare yana Fadin"Kada ki karamin dukan min mata Safiya..!
Cikin karaji sai alokacin ta Dago tana kallonsa cikin hawaye tace"Bazan daina Dukanta ba sai ta fadamin me tayi maka..?me ta baka kasha ta mallake ka..?
Ido ya Bude mata yana Fadin"Ni nace miki an mallakeni..?
Safiya na kuka tace"Aini ba yarinya bace nasan komai haka kake..?kalli yadda fa ka koma ya saraki..?
Tafada tana nunasa sai kuma ya koma yana bin kansa da kallo ganin haka yasa tayi kukan kura ta kara danko Laila datayi gefe tana sosa wuyanta Lokaci Daya tana Zare idon Wahala ganin tayo kanta yasa ta fasa ihu da gudu sulaiman ya tare Safiya bai yi wata wata ba ya saka Hannu ya Tsinketa da mari cikin Rashin Hayyaci sai kuma daga baya yazo yana Takaichin kansa yabi hannunsa da kallo.
Safiya tadafe kuncinta cikin kuka tana Binsa da kallo Cikin muryan kuka tace"Saboda wannan abar ka mareni ya saraki.?saboda ina so ta fada da bakinta abunda ta aikata maka..?
Laila daga bayansa ta rikosa tana Fadin"Habibina ka karota..So take ta Kasheni in kuma bazaka iya Koranta ba ni zan tafi in bar maka gidanka..!
Tafada cikin kuka ai jin abunda tace kamar dalma haka yaji da sauri yace"A"a ba inda zaki je sai dai ita ta fita ta barmiki gidanki..Ki kama Hanya,ki Fita tunda ba zaman lafiya ya kawoki ba..!
Safiya sai ta kara Sandarewa hannu Dafe da kunci tana kallon Laila tana kara Tabbatar da zarginta tace"Yanzu Saboda tace ka koreni sai ka koreni ya Saraki..?nice fa yar"uwanka Safiya..!
Kai ya Dauke yana fadin"Umarninta shine nawa..Just go Safiya..Bana so ki fita kina sakawa ina jin kaina kamar bani ba!
Yafada cikin wani yanayi Safiya ta tsaya tana ma laila wani kallo kafin tace"Ki Rubuta ki ijiye Alkadarinki ya karye Laila..Tunda Uwarki taci Amanar zaman Tare da kaunar da ke Tsakaninta da Hajiya to ki sani kema watan tonon asirinku yazo daka ke har Uwarki..!
Daga haka ta Fice tana sharan hawaayenta tana fita Laila ta Bita ta saka ma kofa key ta tadawo Sulaiman na mgana bata sauraresa ta shige Bedroom ta banko kofa duk da taji jiki hannun Safiya bata wannan take ba Wayarta ta Dauko ta fara Neman Hajiya Salame ta fadamata abunda ya Faru sai dai kash ta kasa samunta ta Kira Hajiya Zaliha ita ta sameta cikin Rudewa ta fadamata abunda ya Faru Hajiya zaliha ta dafe kanta tace"Kash meyasa kika bari wani daga ahalin Sulaiman ya Fahimci wani abu..?Saboda sharadin mallam ne..!
Laila na Sharan jinin Dake hancinta tace"Bansan da zuwanta ba..Tana zuwa ta fara dukana tana cewa sai na Fadamata me nayi ma sulaiman..!
Hajiya Zaliha tace"Ina fatan baki fadi komai ba ko..?
Da sauri tace"Eh ban fada ba wlh..nayi ta kiran mommy ban sameta ba..!
Kai ta kada kafin tace"To kada ki kuskura koda wasa kice wani abu..Domin in wani ya sani bayan ni da ke da salame makarin mganim zai karye ne yanzu ni ina ghana Kada ki damu zan kira mamar naki muyi mgana abu daya nake so dake koda wasa kada aji komai abakin ki Sulaiman kuma yana karkashinki ne ayanzu bazai iya yin komai batare da izininki ba..!
Laila ta Sauke ajiyar zuciya tana Fadin"Kina ganin ba mtsala Anty Zaliha..?
Da sauri tace"Kada ki damu bakomai..!
Da haka suka yanke kiran sai lokacin ta samu salama bata so asamu mtsala domin tana jin dadin yadda ta samu mallakan sulaiman acikin sauki.
Toilet ta shige tana kokarin gyara kanta Hanci da baki jini na Zuba Safiya tasan kan mugunta Har kunnenta sai da ya tasa Saboda Zafin hannunta
Safiya kuwa a Zafafe take saukowa saga Stair kamar zata kifa tana saukowa Falon ta samu kujera ta zauna tana Huci cikin Tsawa tace su magajiya su zube agabanta jikinsu na rawa suka Gurfana agabanta suna rawan Jiki ba bata Lokaci tace tana son sanin abunda ke faruwa acikin gidan nan Samira dasu marliya suka yi Tsuru tsuru sun kasa mgana saboda suna tsoron Laila Magajiya ce ta Ssmu dama daman ita take jira ta Fadema Safiya duk abunda ke faruwa tun ranar da Laila ta kwana daya agidan har zuwa yau din nan kafin ta gama Safiya tajike da hawaye harda majina su samira ma ta Daka musu tsawa suma suka yi jawabi abu Daya ya kara Rikita Safiya jin datayi komai na Rayuwar Sulaiman yana Hannun Laila bama ata matarsa wannan Bai damu da ita ba kamar yadda suma Danginsa basu damu da ita ba ya"yansa har dasu Laila ta shafe a kwakwalwar Sulaiman lalle za""ayi Tashin hankali ta inda aka Hau ta nan za"a sauka Dole.
Masaukinta ta koma Tana sharan kwallar Tsausayin dan"uwanta ta rasa wa zata Kira ta fadama Halin da suke Ciki,Tana kuka ta Kira Fadila ta zayyanemata komai itama nan Hankalinta ya tashi cikin Damuwa take Fadin"Yanzu muka gama waya da Hajiya karama Hajiya na kwance ba Lafiya jininta yahau sai da likita yazo ya dubata ya daura mata Drip sai kuka take tana kiran sunan ya Saraki..!
Safiya tace"Kij ji ko..?wlh Bazamu bari akasahemana dan uwa ba..kuma bazamu bari a mallake mana Dan"uwa ba,yanzu irin sakamakon da Inna Salame zatayi ma Hajiyarmu kenan..?ki kalli yadda tayi fadi tashin Taga ya saraki ya auri Laila fa Fadila..?
Fadila tace"Uhm..Dan adam din kenan aikata abunda bakayi tsammani ba..Baiwar Allah nan Marigayiya sunaira muka Dora mata karan Tsana haka take bin mu muna mata wulakanci tazo ta rasu maimartaba ya nema masa yayarta itama muka Dora mata duk da ita bata bimu ba ammh akallah ai basu mallake mana dan"uwan sun raba mua da komai nashi ba..Daman sau tari wani abunda muka so ba Alheri bane kuma na Tabbata hakan daya Faru ishara ne ga Hajiya damu dangin miji masu kin matar dan"uwansu saboda wani Daliki yau ga wacce muke so sanadinta yasa,muna neman rasa Mahaifiyarmu..!
Safiya na Sharan hawaye da jan majina tace"Wlh fadila gaskiya kika Fada sai yanzu nake auna wasu abubuwa..Kai duniya ina zaki Damu?
Fadila tace"Bari kawai..yanzu ta ina zamu fara ko Kargi zaki tafi ki sanarma maimartaba..!?
Safiya tace"A"a ba chan zani ba..Ta inda aka Hau ta nan za"a sauka Gobe tun safe zan koma Abuja yanzu ma saboda Dare yayi ne da wlh ban kara kwana agarin nan ba Hajiya zan je na samu na Fadamata komai itace Tsanin komai so nake taji da kunnenta..!
Fadila tace"Kina ganin ba mtsala..?
Safiya tace"Matsala ai akwaita Fadila kema kin sani ammh gwara mu tari abun da sauri kafin su kara Shiri..!
Fadila tace"Gaskiya ne ina ita Sunaimar ina yaran suke..?
Safiya tace"yaran magajiya tacemin Suna gidansu sunaima chan takai su saboda Zirga zirgan tafiya makaranta ita kuma ni ban ganta ba..Ban kuma Tsaya bi ta kanta ba yanzu mafita muke mema fadila..!
Fadila tace"Shikenan sai goben yadda kukayi da Hajiya ina jiranki..!
Daga haka suka yanke kiran Ranar barci barawwo ne kadai ya Sace Safiya asuban fari ko karyawa batayi ba tayi shirin tafiya dama da kayan kwana Daya tazo bama wanda yasan taafiyanta ta Buga ma megadi tace Direba ya Fito su kama Hanya.
Sunaima itama batayi wani barcin kirki ba domin tun fara shan ruwan adduan nan yau ne rana ta farko da sulaiman yayi fashi bai zo ba ta saba da barci a kirjinsa yau bashi yasa sai dai juye juye sai da ta gaji da Kwanciya tataahi ta Dauro alwala tazo ta kabbarta sallah gabadaya Salolinta da addu"anta kam Allah ya kwato Sulaimam daga hannun Azzaluma irin Laila tayi sauka akan hakan bata san iyaka ba haka Saifullahi duk dare goshinsa akasa yana Rokon Allah ya dawo da Sulaiman yadda yake hakama Abba Tunda ya samu Labari bai kara barci shima Goshinsa na kasa yana kai kukansa ga Allah domin shi kadai ne ke baka yau ya baka gobe bai gaji ba.
Karfe 10am na safe Safiya ta dira agida hajiya karama na shashenta batama san ta shigo ba ko gida bata wuce ba Sadiya ta iske a bedroom din Hajiyar tana gyara shimfidanta tana gaisheta dakyar ta amsa Lokaci Daya tana Kallonta tana Fadin"Ina Hajiyar..?
Sadiya cikin boye mamakin ganinta Tunda hajiyar bata da Lafiya tasama ranta ita tazo gani Cikin Ladabi tace"Yanzu ta shiga Tiolet zatayi wanka..!
Safiya ta karbi gyaran gadon tana Fadin"Barmin na karisa kije zan yi mgana da Hajiya..!
Sadiya batayi gaddama ba ta Fice Dauke da wayarta zuwa Dakinsu ita da Saddiqa yau basu da lecture sadiq ne ke dashi ya tafi tun Safe.
Bata kawo ma ranta komai saboda daman in suzo suna mgana da Hajiya basa zama awajen Saboda Ladabi.
Safiya bata iya karisa gyaran gadon ba, Hajiya ta fito daman tana ciki Tunda taji mganar Safiya ta kasa wanka Cikin natsuwa Safiya na kallon Hajiya duk ta rame ido ya Fada Tsausayinta ya kamata ya zataji in taji Labarin an Mallake mata d'a masu suyowa agareta.
Hajiya zabba"u tabi Safiya da kallo Cikin Dashewar murya tace"Safiya tun da naji muryanki gabana ya Fadi me ya faru ne..?ko yau zaki tafi gidan Sarakin ki gano halin Dayake ciki..!
Safiya ta sauke numfaahi kafin tace"Daga chan nake ma yanzu Hajiya...!
Hajiya ta kwalolo ido Cikin mamaki tace"Bangane ba..!
Hannunta ta kama ta zaunar da ita agefen gado itama ta zauna agefenta tana Fadin"Jiya naje yau kuma da Safe na kamo Hanya ban gayamiki bane nace bari na bari sai na dawo..!
Hajiya Cikin Sauri ta Damke hannun Safiya tana Fadin"Safiya wani hali kika ga Saraki..?nayi mafarkinsa jiya na gansa yana kuka yana kiran sunana Safiya..!
Sai hawaye sharrr..Safiya ta Hadiye miyau kafin tace"Hajiya Allah ne yake nuna miki saboda ke uwace..Da gaske ne Saraki na cikin mayuwacin Hali na neman agaji da taimako..!
Hajiya ta fiddo ido waje tana Fadin"Innalillahi Safiya me ya Faru..?
Safiya tace"Inna salame taci Amanarki Hajiya..ita saka yarta laila ta mallaki Ya Saraki ya manta da kowa da komai Hatta da ku iyayensa da yan'uwansa da ya"yansa Hajiya laila ita ke Da ragamar duka Rayuwar Saraki...!
Hajiya ji tayi kamar mganar tana mata amsa kuwwa cikin Fitar Hayyaci tace"Safiya ban...ban gane ba..!
Nan fa ta shiga warware ma Hajiya komai tunda ga farko kamar yadda taji kuma tagani Kafin ta gama Hajiya ta jike da Hawaye da majina kuka Share Share Kirjinta na Bugawa Fat Fat Cikin Fitan Hayyaci ta Rike hannayen Safiya tana Fadin"Safiya ni Salame zata ma haka..?
Shiyasa ta rage kirana in na kirata ina nata Compain kan rashin samun saraki sai itama tace bata waya da Laila sakamakon da zatamin kenan?
Safiya tace"Wlh Hajiya ya Saraki duk ya susuce baki gani ba nifa har marina yayi akan laila ya koreni abunda tun muna yara ya Saraki bai da Saurin hannu Hajiya...Wlh in bamu mike tsaye ba zamu rasashi gabadaya..!
Hajiya ta fizge hannunta ta mike da Sauri Jiri ya kwasheta sai da Safiya ta Rikota Cikin karaji tace"Lalle Salame ta Tono ma kanta ni zatama haka..?d'an nawa zata saka yarta ta susutashi...?ita na Haifar ma wa..?
Safiya tace"Hajiya taci Amanarki wlh
Daman ance wani abunda muka so ba Alheri bane..!
Hajiya ta wuce wajen wardrope tana Fadin"Nagani Safiya..naga karshen Soyayyah da Amana daga lailar har Salame sai sun gane kuransu zan nuna musu ina nan a zabba"u na ban Chanza ba..Ki tsayamin yanzu zamu juya Kaduna naganin ma idona komai Safiya domin na fahimci ta inda zamu bulloma lamarin..!
Safiya tace"Shikenan Hajiya ammh Abba fa..?ga hajiya karama..!
Hajiya ta Dauki kayanta tana fadin"kada ki damu bazamu sanar dasu ba sai mun je mun dawo..!
Daga Haka ta shige Tiolet ta Sawo kaya doguwar rigar atamfa ta sako Mayafi jakarta Safiya ta rike mata suka fito shashen Hajiya karama suka shiga Safiya ta gaisheta ta amsa Cikin Sakin Fuska ta gaida Hajiya tana kara mata sannu da Hajiya tace zasu fita bata kawo komai ba ta zata wani waje zasu je kuma ita bata da son jin kwakwaf sai bata ce komai ba.
Suna fita Direban Anty Safiya na jira suka fada shi kanshi yaji mamaki da yaji kaduna zasu kara komawa sai dai bai ce komai ba.
Har suka isa Kaduna Hajiya sai Maimaita ni Salame zata ma haka..?ni Salame zataci Amana..?sai hawaye suna isowa Hajiya bata jira komai ba ta Fito daga Motar ta fada gidan so take tayi arba da Saraki ta ganin ma idonta Safiya na bayanta sanda suka shigo Falon da magajiya suka ci karo tana ganinta ta Duka tana gaisheta bata amsata ba illah cewa datayi"Ina Saraki..!?
Magajiya kanta na kasa tace"Yana Sama dakin Laila..!
Mamaki take har Safiya takoma Abuja ta dawo ita batayi tunanin tafiya tayi ba,Tare suka Haura sama kai tsaye zuwa Dakin Laila Hajiya ce agaba Safiya na bin bayanta suka Tura Kofar suka shiga Safiyace tayi sallama Hajiya ji take kamar ta Bude ido ta ganta gaban saraki.
Laila tana zaune afalo kan Daya daga Cikin kujerun da sukayima Falon kwanya Kafa daya kan daya tana waya Tana sanye da riga da wando jean da Shirt da suka kamata sosai Gabanta Center table shake da kayan marmari sai marliya dake gefe tana goge goge su hajiya suka fado falon
Laila ta dauka bata gani daidai ba Domin da safe ta sauka kasa ta tambayi Safiya samira suka tabbatar mata da cewa ta wuce Auwali megadi ke fadamata sai alokacin hankalinta ya kwanta Sulaiman na ciki ta Hanashi Fitowa ita ta zo nan ta zauna Tana waya da kawarta da sukayi makaranta tare.
Hajiya har gaban Laila ta isa Idanuwanta sun yi jajir da Sauri wayar hannun laila ta subuce ta Mike Cikin Rawan jiki tana Fadin"Hajiya...Ha..jiya sannu da zuwa..!
"Ina saraki...?
Hajiya ta fada Lokaci Daya tana Tsareta da ido Laila bakinta na rawa tace"Yana daki...!
Hajiya bata tsayaba ta Fara tafiya tana kwala Kiran"Saraki...SULAIMAN...!
Yana zaune daman kamar akan kaya yake jiya Laila ta kasa ta Tsare bai samu satar hanya ya fita wajen sunaima ba,itace aransa tun safe yake so ya Sulale yaje ya ganta Laila taki barinsa kamar ta Fahimcesa yasa ta mai kaahedin kada ya fito ko falo ne
Kamar daga sama yaji kiran Kamar Muryan Hajiya ita uwa ai dabam ce Haka yaji kamar ana jansa sai gashi a Tsakiyar falon agaban Hajiya yana kallonta.
Hajiya kallonsa take yi daga sama Har kasa cikin Tsausayinsa Cikin karaya tace"Saraki nima an saka ka manta dani..Nice fa Hajiyarka mahaifiyarka..!
Sulaiman na kallonta kwarmin idanuwansa sun cika da kwallah Laila ya kalla dake ta Kifta ido alamun ba ta da gaskiya Cikin marairaicewa yace"Lailata in mata mgana..?kinga fa Hajiya ce!
Hajiya ji tayi kamar Duniyan na yawo da ita Safiya tace"Hajiya kin ji kuma kin ga abunda nake fadamiki ko..?ki shaketa sai ta fadi inda suka Binne asirin nan mun hakosa don ubanta..?
Ai Hajiya kamar kububuwa haka ta Dumfari Laila sai dai ina Sulaiman bai bari ba ya shiga Tsakaninsu Hajiya Cikin zubar kwallah tace"Saraki matsa kabani waje..!
Kai ya girgiza yana fadin"A"a Hajiya bazan bari ki daketa ba..!
Ai batasan sanda ta bangajesa ba Safiya na ganin haka ta tayata Damko Lailan data fasa wani gitattacen Ihu Daya Fiddo da Sunaima Daga cikin Daki.
Hajiya ta rika zagmata maruka Sulaiman na riketa yana Fadin"Hajiya Hajiya..!
Fadi take"Saraki ba kai bane..ba haka kake ba Laila ki Fadamin me kikayima D'ana..?
Laila dataji wuya ranta ya kawo wuya tayi kukun kura ta ture hannun Safiya ta kuma bangaje Hajiya da sai da ta Fadi kasa daman bata da karfin Jiki sulaiman na ganin haka yace"Hajiya..!
Jikinsa na rawa Safiya ta kuta tace"Hajiyar kika kada Laila..?
Laila na kokarin daidaita kanta tace"Ita taja..ai ba uwata bace ke kinzo kin Dakeni kin zageni sai na bari itama tazo ta Dakeni D'anki da kike mgana a mijina ne budemai gaba nake yana Shiga kinga kuwa Dole yamin biyayya ke kina budemai gaba ne ballatana ya Fifitani sama Dake..!?
Hajiya data mike idonta ya Rufe da Cin Zarafin Laila ta Daga Hannu ta wanke ta da mari tana Fadin"Ko ban bude gaba ya shiga ba..Don Uwarki salame da bata baki Tarbiya ba na Bude gabana ya fito ta ciki!
Laila ranta ya baci sai Hawaye Tuni ta manta da Sharadin Mallam ta kalli Hajiya da Safiya da suke Huci da Takaici hannunta Dafe da kunci tace"Eh din an mallake shi din..So kike yadda na gama wahala akansa kafin ya aureni bayan mun yi auran kuma na kara wahala..ko kuma na zauna ina jure cin kashin da kuka saba ma matarsa tun tana da Rai..?baki isa ba Kin Haifi Sulaaimam ammh Dole ki kauda ido akansa Mommy ai tafini saninki tasan bazaki barni naji Dadi agidam Mijina ba Shiyasa ta karbomin mganin mallaka yanzu Sorry to say Hajiya ko Dukanki nace Sulaiman yayi zai yi sai dai bana son Ya Tozarta watarana ammh zan iya sakashi ya Koreki..!
Ta juya bangaran Sulaimam bata ma Lura da yanayinsa ba yadda Idonsa ya juye da kuma yadda ya Dafe kansa Cikin bada Umarni tace"Habibi ka koresu in kuma ba haka ba ni zan Tafi na bar maka gidan..!
Tafada Cikin bada Umarni Hajiya datayi mutuwar Tsaye tana Hawaye Safiya ma ta kasa mgana sai kuka Hajiya ta kalli Laila kawai sai tayi Dariyan kuka ta kara Daga hannu ta Zagmata mari tana Fadin"Ba Korata zaki sa yayi ba marin ki zaki saka ya rama miki Mara tarbiya..!
Laila tayi kuta tana Fadin"Habibi kana gani ko..?
Sulaiman na Dafe da kansa Dake juyamai Cikin fitan Hayyacinsa yana jinsa kamar abubuwan da suka Faru acikin mafarki ne.
Ganin ya tsaya yaki motsi yasa ta Daga hannunta da niyyar marin Hajiya tana Fadin"In bai rama min ba zan rama da..!
Bata gama Rufe baki ba Taji an Damke hannunta Lokaci Daya an yarfamata mari Tare da wani Hambarin da sai da ta wuntsila kanta ya Daki kujera sai da ya fashe cikin Fitan Hayyaci ta Dago wadanda tagani suna kallonta Cikin bacin rai da tsana da wani Fushi yasa ta Firgita ta fara ja da baya
SUNAIMA DA SULAIMAN ne cikin Wani irin yanayi sun kare gaban Hajiya dukkansu suna Fitar da Hucin Yadda zuciyarsu ke azalzala.
Littafin Mijin Ƙanwata Free book ne yanzu nake reposting, amma ina siyar da document ga waɗanda ba za su iya jira ba
1k ne ta wannan acct ɗin 5040273639 Moniepoint Jamila Umar
KO tuntuɓa ta wannan lambar ***.
*Janafty*