JODAH

10

by @sadisakhna


 

______👑 *JODA* 👑_____ 

 

              

 

 

 

Na  

 

*Sadi-sakhna* 

 

Ƴar mutan Jama'are 

 

 

 

 

 

THE TRIO OF TALES  

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)  

 

 

@sadisakhna on Arewapen 

@SAKHNA03 On Wattpad 

*** on Whatsapp 

 

 

LITTAFI NA 1 

 

 

 

 

*HarÆ™a ta (10)*👑 

 

 

 

 

***** 

 

 

 

*Joda* 

 

Kayan jikina na kallah, doguwar rigace buba anyi mata maÉ—auri ta baya kalar BaÆ™i sai É—an kwali fari dana É—aura kalar uniform na su Masu aikin goge goge da shara na makarantar. Ko kaÉ—an hakan bai dameni ba,domin ni baÆ™aramin daÉ—in kayan naji ba,gashi sabon saqi ne kuma a wanke,ba kaman kayan dasuke jikina ba sai wari sukeyi,nima kaina sun dameni inaga kuma wanda yake kusada ni. Fitowa nayi ina tafiya zanje É—akin bincike na jinyar raina fari tass ga cikin ya cika,Ummu hajar ta bani abinci Waina naci naÆ™oshi. 

 

Muryar wata mata na tsinkayo tana Æ™irana. 

 

"Kee keee zo ina zakije bakya gani ana aikine?" 

 

Wata matace lukuta gajeriya,idonta tana muzurai abin tsoro,irin kayan jikinane a sanye da ita,da sauri na Æ™arisa inda take hanunta riÆ™eda wani kwando da akayishi da Gwangwala,É—aya hannun kuma tana riÆ™eda tsintsiya ta tankar dabino. Har na Æ™arisa inda take bata daina hararata ba kaman taga É—an tsiyaki. 

 

"Ina zakije da kina gani ana aiki anan,hala ke baÆ™uwace ko? To mu a nan babu ruwanmu da wata baÆ™uwa,tsoho ko tsohuwa,yaro ko yarinya dolene yayi aiki. Dan haka ga can wancan buhun ki É—auka kina É—iban sharar nan kina kaiwa jujin dayake baya harki gama tass,maza yuda jiki ki kama aiki ba kuÉ—in banza aka saka aka siyoki ba" 

 

Kallon uwar sharar da take gabanta nayi,kuma na tabbatar aikinta ne dataganni tace ni zanyi. Nasan kafin ace na gama wannan aikin to lokaci yaÆ™ure na zuwa ganin baba mahdi,ga kayana suma zasu baci kuma yau na sakasu. HaÉ—iye abinda ya tasomin nayi da sauri na kama aikin,domin lokaci É—aya na tuna ni wacece nafarka daga mafarkin dayake shirin sakawa na bance rayuwar zahiri. 

 

Buhun na jawo kiiiii nazo zan wuce ta gefen wani majalisi da tun daga nesa na hango yarane kamanni amma yau wani balarabene yake koyar dasu,domin naganshi da farar fata irin ta larabawa. Bazan iya É—aukar buhun ba yayimin nauyi fa girma,shiyasa nake jansa a Æ™asa abuna,kuma duk inda na wuce sai kowa yakalleni,nima a raina banso na jawo hankalin kowa kainaba to amma yazanyi.  

 

Kamar a sama na tsinkayo muryar wani namiji bazai wuce saanni dani ba yana min magana. 

 

"Mai Æ™oÆ™ari kice yau harkin fara aiki kenan?" 

 

ÆŠaga kai nayi na kalleshi,da sauri na ajiye buhun tareda durÆ™usawa ina gaisheshi. Murmushi yayi saida fararen haÆ™oransa suka fito ganin abinda nayi,nima wayancewa nayi ina É—an murmushin tareda kaÉ—e hannuna wanda duk Æ™asar jikin buhun ta batamin. 

 

"Waye yakoyamiki karatu haka,gaskiya kin burgeni jiya sosai,gashi badake ake karatun ba kina can gefe amma kika fimu fahimta muda muke gefe" 

 

"Babu wanda ya koyamin,kawai dai inason karatune,shiyasa duk inda najishi nakan maida hankali wajen ganin na haddaceshi,tunda ba koyaushe ne zan samu damar jinba saboda matsayina" 

 

"Nikuma kinga ina samun damar yin katari dashi a kodayaushe amma kuma banason tsayawa na fahimta" 

 

"Aikuwa gwara kamaida hankali sosai,domin ilimi yanada matuÆ™ar amfani,bazaka san hakan ba sai ance bakada damar samunsa tukunna." 

 

"Hakane gaskiya kinada hangen nesan dayafi na shekarunki,zan iya sanin sunanki?" 

 

"Sunana Joda amma zaka iya Æ™irana da baiwa kawai,domin hakan shine sunan da ake Æ™irana dashi" 

 

ÆŠan jimm yayi da alama baiji daÉ—in furucinnawa ba,to amma yazanyi dole na dunga maimaitawa kaina matsayina saboda gudun matsala. 

 

"Na tsaidaki kina aiki ki cigaba kada kiyi laifi amma idan babu damuwa ki faÉ—amin inda kike zan kawo miki ziyara,sunana Hamad ina sonki da Æ™awance idan zaki yadda,tunda nazo Daular nan gabaÉ—aya cikin kaÉ—aici nake,kece mutum ta farko danaji ya kwantamin arai,kuma nasan tarayyata dake zan Æ™aru sosai" 

 

Tun lokacin daya furta kalmar Abota hankali na ya tafi yawocikin jikina,kunnuwana suka fara tantamar anya kuwa najishi dakyau,abota nida Æ´an gidan masu mulki,a yanda tun tashina naga ra'ayul aini na matsayina da irin rayuwar da wanina sukeyi a ciki? Inaa wannan batu bamai yiwuwa bane,hakan yasa batareda na sake jin wani abu dazai É—agamin hankali ba nayi saurin jan buhuna kiiiii nabar wajen. 

 

Bani na gama wannan aikin ba sai azahar,na haÉ—a gumi shirkif ga cikina yana Æ™iran ciroma(yunwa). Cikin halin gajiya na isa sashen inda bayin suke,babu wanda yakalleni kowa harkar gabansa yakeyi. Wajen Addah Nusaiba naÆ™arisa wacce ummu hajar ta mikani wajenta. Babu yabo babu fallasa ta kalleni,kafin ta É—auko wani akwashi ta miÆ™amin. Kunu ne aciki amma yanada kauri da wasu Æ´aÆ´a a ciki,ban tsaya tantance É—anÉ—anonsa na daÉ—ine kokuma na Akasin sa ba,kawai aikashi na farayi cikina,ina godewa Allah dayasa na sameshi har nake sha ma. 

 

Bayan nagama sha sallahr azahar nayi,inaso na tambayi wata a gefena inda zanyi wanka amma ina tsoro,haka dole na daure na tambaye ta 

 

"Dan Allah idan baxaki damu ba ina so nasan inda ake wankane?" 

 

Duk da cikin ladabi nayi mata maganar saboda kada tace nayi mata rashin kunya,amma sai nakega kaman bazata bani amsaba. Ga mamakina ta kalleni fuskarta da fara'ah tace. 

 

"Sannu yarinya hala ke baÆ™uwace jiya naga ummu hajar takawoki nan sansaninmu,sannu kinji kaff cikin bayin dake makarantar nan babu wanda yakaiki Æ™anÆ™antar shekaru. Muje zan nunamik rafin da muke wanka da wanki,nima canne zanje na wanke kayan É—aliban dasuke masauÆ™in gabas,anan nake aiki" 

 

Fara'arta ta sauÆ™in kanta ya burgeni sosai,hakan yasa cikin zumuÉ—i na bi bayanta tareda karbar kayan hannunnata domin na riÆ™e mata,a É—an tazarar take tsakanin wajen da inda muke zaune har tabani labari mai yawa daga abinda ke wakana a gurin,hakan ba Æ™aramin daÉ—i yayimin ba domin nasan zai taimakamin sosai a rayuwar da zata zomin nan gaba a zaman dazanyi a wajen. 

 

Tun kafin mu Æ™arisa wajen yafara Æ™ayatar dani daga nesa,saboda bishiyoyin dasuke gurin,ruwa da kuma tsuntsaye kyawawa,tunda nake ban taba ganin waje mai ban sha'awa kamarsa. Bakina a bude har muka Æ™arisa inda ruwan yake gudana daga jikin wani dutse dashi ma abun kallone. Lokaci guda naji duk wata damuwa ta yaye daga cikin kaina,shauÆ™i da muradin ganin abun É—ebe kewa ya cikata. 

 

Tattare rigata nayi shiga ciki inata wasa da dariya, Yau É—aya nasake sashen jikina na yarinta yayi abinda yakeso.  

 

Wanka mukayi na tayata ta gama wankinta tsaf,nima ta wankemin nawa danazo dasu najikina,a yanda take mu'amala dani na kula tanayimin kallon Æ™anwarta ne,ko tana da ita sun rabu ko kuma tana sha'war ace tanada itan. 

 

"Ƴar uwa munata magana amma bansan da wanne suna zan Æ™iraki,gashi kina tayimin abinda yaya takewa Æ™anwarta ko Æ´ar uwarta" 

 

Murmushi tayi da yayiwa fuskarta kyau,domin babu Æ™arya duk da tanada duhun fata amma kuma ba mummuna bace. 

 

"Hmmm kinada manyance Joda duk da bakida yawan shekaru,nikaina idan kina wata maganar shuru kawai nake ina kallonki,inama Ƙanwata tana raye ko ya girmanta zai kasance. Suna na Rahilah amma zaki iya Æ™irana da Æ´ar uwa,sannan idan kina bukatar wani abu to ki sanar dani,idan baifi karfina ba zanyi miki kinji." 

 

ÆŠaga kai nayi cikin farinciki nagode Allah daya haÉ—ani da ita a lokacin danake bukatar wani bango na jingina. 

 

Sai bayan la'asar muka dawo daga rafin,domin saida muka tsaya kayan suka É—am bushe lafin muka É—ebesu,madadin lokacin da suke bushewar sai mukaje É—iban mangwaro a wani lambu dayake kusada wajen. HaÆ™iÆ™a zuwan namu wajen ba Æ™aramin nishaÉ—i yabani,naji daÉ—in sanin wajen sosai,koba komai zai kasancemin wajen yin tunani dakuma warware matsala idan ina cikin mawuyacin hali,kokuma nayi kewar mahaifana. 

 

Da ummu hajar mukaci karo a bakin kewayennamu tana tsaye tana Æ™are mana kallo daga nesa,hannunta rikeda wani kwando da ganyayyaki a ciki,da alama itama daga cikin jejin ta dawo. 

 

"Keda yakamata ace kinje aiki yau ya akayi naganki kin fito tanan,sannan na tambayi masu aiki a sashen wajen magani sunce bakije aiki ba meyasa......" 

 

Zubewa nayi akan gwuwoyina tareda saurin cewa. 

 

"Kiyi haÆ™uri ya shugabata,haÆ™iÆ™a nayi Æ™oÆ™arin zuwa aiki,amma sai aka samu akasi wata mata sanye da kaya irinna daga cikin masu shara a wajen da majalisu suke ta hangeni, nayi Æ™okarin faÉ—amata aiki zanje amma bata bani damar hakan ba,saitace na tayasu aikin dasukeyi. To kuma aikin yanada yawa bamu gama ba har bayan azahar. Sannan nadawone bayan naci abinci ganin lokaci yaÆ™ure shiyasa banje ba muka tafi rafi yin wanka" 

 

Dukkansu zubamin ido sukayi har na gama zayyano bayanin. 

 

"Naji to amma nan gaba ki kiyaye batawa iyayen gidanki akan bawa É—an uwanki,ko wanne hukunci zai miki dolene ki fara cika umarni wanda sukeda iko akanki kafin ki cika nasa umarni. Bawai ina goyon bayan dakiyi rashin kunya bane amma idan har kin yarda da wayonki to ina fatan kin gane mai nake nufi. Muje ki tayani aikin gyara maganinnan,zan sauyamiki kaya zuwa irinnawa gudun kar hakan taÆ™ara faruwa,daga yanzu zakina rakani É—iban magani idan kin iya ke zaki dungayi. Domin jikina yafara gajiya da wannan aiki,gashi har yanxu Hakeem bai dawo ba. " 

 

Mikawa Rahilah kwandon kayanta nayi tareda mata sallama kafin nabi bayan ummi hajar. 

 

Aiki da dama mukayi,wani tayi da kanta ina gani wani kuma tasakani nayi. Bayan mun gama gyara maganin kuma na riÆ™e mata wani kwando shima da wasu magunguna a cikin,wasu an sakasu a kwalba saboda na ruwane,wasu kuma na garine.   

 

Alama tayimin dana biyota,babu musu kuwa nabi bayanta zuwa wata Æ™ofa dake cikin wajen,tana buÉ—ewa na kallah ashe É—akine mai girma sosai,dukkan wajen gadajene da akayisu da kara,matane a wajen manya da yara da tsoffi sun kai wajen talatin kowa na kwance a nasa gadon,wasu ma a gadajen babu kowa a kai. 

 

Cikeda mamaki nake kallon wajen ina rarraba ido,ban taba sanin bayan inda muka baroba akwai waje mai girma kaman haka ba. 

 

ÆŠago ido tayi ta kalleni ganin gabaÉ—aya idona ya shagala ta kallon majinyatana,É—an murmushi tayi kafin tace. 

 

"Shin kina mamakine haka da kallon mutane a wajen" 

 

"Ahah ranki yadade nayi mamaki ne domin ban taba tunanin a bayan Æ™ofar akwai waje mai girma kaman haka ba." 

 

"Wannan wajen akwai irin su guda uku a nan bangaren,wannan na mata ne,akwai na maza daga bayan Æ™ofar da take kallon wannan,sannan akwai wasu Æ™anana kaman guda goma domin ajiye manyan mutane da suke buÆ™atar sirri,kokuma ajiye mai cutar da takeda hatsari ko kuma kama wani idan sukayi tarayya,dan haka kada wannan yabaki mamaki". 

 

Bayine kaman su goma mata suna ta kai kawo a wajen,sanye da kaya mai kalar na Ummu hajar Kore,amma kuma anyi musu É—inki irinna bayi. Wasu na goge goge wasu na rarraba ruwa ko kuma mikawa wani idan yanada bukatar wani abun. Kusan kowanne gado akwai mai zaman jinya a kalla mutum É—aya. Wasu kuma basuda shi su kadaine.  

 

A abinda na kuladashi shine dukka mutanen dake wajen babu bawa ko kuma talaka liÆ™is a wajen,kowanne masu gata ne a wajen ahalinsu basuda lafiya aka kawosu neman magani,kenan shi bawa da marar kuÉ—i babu wanda zai damu dashi idan bashida lafiya kenan. Naso nayi mata wannan tambayar amma ina tsoron wuce gona da iri. Na Æ™udure a raina dole sainayi bincike akan hakan,sannan inaji a raina inama zan taka wani babban matsayi a duniya,da nayi amfani dashi wajen gyara wannan gurbatacciyar al'ummar tamu wacce take cikeda zalunci. 

 

"Wannan tana fama da ciwon cikine,tanayin amai akai akai kuma kashinta yayi ruwa sosai,wanda yakai bata iya tashi ta tsaya batareda an riketa ba. Abinda yake jawoshi yawancin cin gurbataccen abince ne,kokuma shan ruwa marar kyau. Mukanyi garin foda na gawayi a basu kullum da safe cikin ruwa mai É—umi da danÉ—anon gishiri rabin bawon kwakwa guda É—aya, yana taimakawa wajen Æ™arawa jiki karfi dakuma dawo da abinda jiki ya rasa." 

 

Wani yaro na kallah a gefena shikuma numfashinsa yana sama sama,lura da kallon danake masa tayi,hakan yasa ta isa gareshi tana duddubashi,mahaifiyarsa na rikeda shi cikin halina na tausayawa. 

 

"Yana fama ne da ciwon Æ™irji,ta inda ake gane haka shine idan mutum yana yawan Æ™orafi da ciwon kirji,numfashinsa yana sama sama,tari da kuma kasala na jiki. To sai mu tafasa tafarnuwa ayi masa sirace dashi safe da yamma. Sannan akan yi amfani da mai na tafarnuwar dakuma kitsen ayu a dunga shafa masa a kirjin na tsawon wani lokaci. Kokuma ruma a ruwan É—umi kullum da safe idan ya tashi dakuma dare idan zai kwanta." 

 

Dukkan bayanin datake faÉ—a babu wanda na bari ya subuce batareda yashiga cikin kunnena ba. 

 

Cigaba dayi da bayanin matsalar yaron dayake gaba. Shikuma jikinsa duk Æ™uraje abun tausayi,sai ihu yake yana sose sose. 

 

Tsugunnawa tayi a gaban gadonsa tana kallon yanayin jikinnasa kafin tafara cewa. 

 

"Wannan kuma akan ganeshine idan kikaga idon yaro yayi ja ,zazzabi yana yawan rufeshi sannan baya samun ishashshen bacci da nutsuwa saboda Æ™aiÆ™ayi. Kazuwa kenan maganin ta shine. Akan shafa É—anyen manja mai kyau wanda ba'a haÉ—ashi da komai ba bayan anyi masa wanka da ruwan dumi da gishiri. Kokuma man zaitun shima yana taimakawa sosai" 

 

"Ranki ya daÉ—e kizo kigani Jininta ya dawo yau kam yafina kullum domin har zuba yakeyi wayyo Allah" 

 

Wata matace take faÉ—in hakan cikin razani da fargaba,wanda hakan yasa ummu hajar isa gareta cikin sauri,nima nabi bayanta hannuna rikeda kwandon maganin. 

 

 

A zaune take akan gadon mai yin maganar tariketa a zaune,sai layi takeyi kana gani kasan faÉ—uwa zatayi idan tasaketa. Tsummokaran dasuke Æ™asanta wanda ta zauna akai duk sunyi jagab da jini har É—iga yakeyi a Æ™asa. Wajen duk ya gauraye da Æ™arni. Wasu daga gefe har kauda kai sukeyi. Kallon wajen na sakeyi kuma na kulada yanda wani mai cutar yakan damun wani mai cutar,sannan wani a nasa lalurin yana buÆ™atar sirri kaman wannan sunason gyarata amma yawan idanun dayake kansu yasa basujin dadin zaman. 

 

"Wannan tana fama da matsalar zubar jini sosai,Satinta huÉ—u da haihuwa tayi doguwar nakuÉ—a har takai É—an baizo da raiba,tun a lokacin take zubar jini. Muna bata abinci mai gina jiki kaman Farfesun hanta dana wake. Saikuma kunu na Æ´aÆ´an kuka. Sannan akan fada ganyen kukar yazama ruwan shanta" 

 

Tsugunnawa nayi na kalli cikinta,ya kumbura sosai kaman akwai wani É—an aciki. ÆŠaga kai nayi na kalleta kafin nace. 

 

"Ance kin haihu to amma menene a cikinki daya kumbura haka?" 

 

Itama saukar dakai tayi ta kalli cikin tareda dannawa,da alama taurine a ciki.  

 

"Bansan menene ba wani abune mai tauri,tun kafin na haihu nake jinsa,har na haihu amma bajeba yana nan" 

 

Kallon ummu hajar nayi cikin girmamawa kafin nace. 

 

"Tun tashina a yanda na kulada rayuwar nan,wani abu kawai baya kasancewa face Allah yasaka wani abu daya kasance yasaka faruwar wannan abun. Inaga kaman zaifi ta kwanta ki duba menene a cikinta,wataÆ™ila shine yakesaka zubar jinin. Maganin abinda yake saka zubar jinin shine yafi akan bata abincin dazai saka jikinta ya jure zubar jinin." 

 

Daga masu zaman jinyar har ita kanta ummu hajar kallona suke da mamaki,amma ummu hajar bata Fasih ba saita umarci marar lafiyar data kwanta,kwantar da ita matar tayi duk na Æ™ura ido ina kallon mai yake faruwa.  

 

Hannunta É—aya tasaka a saman cikinta,É—ayan kuma tana tattaba gefe da gefe,tsakiyan ta dawo daga tsakiya tana daddannawa,wanda haka yasa marar lafiyar yamutsa fuska alamar taji zafi. 

 

"Ina jin wani abu mai tauri a saman mararta kaɗan,lokacin dasuka zo na duba mahaifarta babu abinda yasameta tana matsayarta amma ban kulada kumburin baya bajewa ba saboda a lokacin bata dade da haihuwa ba daidaine a samu cikinta da kumburi kafin mahaifarta ta motse zuwa girmanta na ainihi. Tabbas Bana Almahdi ya kalli wani abu a tattare dake dayace na dunga zagaya marasa lafiya tareda ke,kuma nadunga ƙoƙari wajen yi miki bayani karna duba ƙanƙantarki,ke ɗin ta Fasihmman ce. Nagode da wannan gyaran dakikamin. Duk ɗaliban dana tabayi babu wanda yake maida hankali haka a karon farko har ya gano wata matsala irin wannan. Kici gaba da kallon marar lafiya da zuciyarki bawai da ƙwayar idonki ba,idan kikayi hakan zaki taka wani mataki mai muhimmanci a harkar ilimi na lafiya"