BIYU A ƊAYA

Chapter 4

by @barista

BIYU A ƊAYA 


***
  YOTA 13 
Team of FIVE INK legends 

Dedicated to you my Apple 🍎 Na'ima SARAUTA 👸🏻

Page 4


          GHANA 

Ta iso gida cikin tashin hankali, da ƙyar ta kawo kanta gida, shiru farfajiyar gidan nasu babu kowa, duk suna cikin ɗakunansu ta wuce ɓangarensu ta turo ƙofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama, ta ajiye jakarta a madaidaicin palourn su da babu komai a ciki sai shimfiɗaɗɗiyar leda carpet, ta zauna tana sauke numfashi tare da jinginawa jikin garu, ta runtse idanunta, tana sake tunawa da abin da Alaja ta faɗa mata a restaurant da kuma abin da yake ƙoƙarin faruwa da ita...

"Kin dawo"

Ta ɗago da idanunta da suka sauya kala ta kalli mahaifiyarta dake tsaye ta ce

"Eh Mama"

"Ya kika dawo da wuri? Ina Majada da Jummai da kuma Alaja?"

"Mama na gaji ba zan sake zuwa restaurant ba, na daina wannan aikin"

Samun wajen zama Mamanta tayi, cike da mamaki take duban Bilqees ta ce

"Bisa wane dalili?"

"Mama kawai bana son aiki"

"Bilkisu kenan, yanzu har kin yi girman da za ki zaɓa wa kan ki rayuwa? har kin kai lokacin da za ki dinga jayayya da mahaifiyarki? To ki sani wannan aikin shine rayuwar mu, in ki ka bari to kin kuwa kashe mu"

"Zan nemi wani aikin Mama wannan aikin na Alaja bai dace damu ba, da kuma rayuwar mu"

"Bilkisu!"

Mamarta ta daka mata tsawa tare da kiran sunanta, duk da bata jin daɗin jikinta amma ta sami ƙarfin halin yin magana cikin ɗaga murya 

"Alaja da kike gani ita ce silar da kike takama dashi, ita ce ta tsaya tsayin daka ta baki rayuwa me kyau, au yanzu shine za ki ja da ita, lallai Bilkisu wuyar ki ta isa yanka"

"Mama tun dana taso nake yiwa Alaja biyayya, nasan tana ƙoƙari sosai akan inganta rayuwata, to me yasa zata tura ni hotel wajen namiji"

Ras gaban Mamanta ya bada, tasan wannan ba ƙaramin aikin Alaja bane, to ta manta alkawarin da ta ɗaukar mata ne? ko kuma akan maganar da su kayi ne yasa take ƙoƙarin yin hakan? Amma mamarta ta dake tare da cewa 

"Kul kada na sake jin wannan maganar a bakin ki, kuma aiki yanzu kika fara"

Miƙewa Bilqees tayi ta ɗauro alwala saboda gabatar da sallah la'asar, tana alwala tana tunanin zuci, wai shin me yasa Mama take tsoron Alaja ne? Shin wacce iriyar alaƙa ne dake sakanin Mama da Alaja? Ya aka yi ma mamanta ta damƙa amanarta a hannun Alaja....

"Omoo see fine girl"

Taji murya daga gefenta kuma ta shaida muryar.
Ko kallonsa bata yi ba, ta san daga ɗakin da ya fito don haka tana idar da alwala ta shigo ta gabatar da sallah, Mamanta ma ta fito ta ɗaura alwala ta shigo ta idar da sallah, ta ce Bilqees ta ɗaura tukunyar dare. 

Bilqees ta mik'e ta hura wuta, ta ɗaura abinci nan da nan ta kammala har dare Mama bata sake mata fuska ba, don haka ita ma bata sake cewa komai ba har suka ci abinci, sun kwanta kenan Alaja suka shigo gida saboda hayaniyar da suke yi, daga baya kuma su kayi shiru. Bacci ya ɗauke Bilqees ganin haka yasa Mama ta lallaɓa ta shiga ɗakin Alaja ta tadda ta zaune tana shan kankana Mama ta zauna tare da cewa 

"Sannu Alaja"

Alaja sai da ta haɗiye sauran kankanan dake bakinta ta amsa da 

"Yauwa Maman Bilqees"

Sauke numfashi Maman Bilqees tayi sannan ta ce

"Alaja yau ko tsayawa ba ki yi mun gaisa ba? ai ko ɗan sannu da dawowan nan nayi miki ai da daɗi"

"Maman Bilqees are you teasing me? You know everything, amma ki ke nunawa ba abin da kika sani"

"Uhm Alaja ban fahimci abin da kike nufi ba, me kuma na sani?"

"Bilqees ta faɗa miki abin da ya faru a restaurant yau, shin so kike na maimaita miki ki ji daga bakina ne?"

"A'a Alaja cire ni cikin wannan abin, ni ai ba zan shiga tsakanin ku ba, kun fi kusa, ke da ƴarki ni na isa, wane yaro"

"Hehehe Maman Bilqees kina da wayo sosai, nayi tunanin kin manta ne, to amma ita Bilqees ta manta wacece ni?"

"Kin san yaro da kuruciya anma ba zata taɓa manta wa dake ba"

"Tayi min rashin kunya, don haka kada ta sake zuwar min restaurant"

"A'a Alaja ki yi hakuri nawa Bilqees take har yanzu dai yarinya take, zan yi mata faɗa ba za ta sake yi ba"

"Ai gani take ta girma wuyanta ya kai yanka..

"Haba Alaja ki yi hakuri mana, Bilqees fah ƴar kice tun da mahaifinta ya rasu kike ɗawainiya da ita, nononki ne kawai bata sha ba"

"To na ji amma ta kiyaye ni ba a min iskanci"

"To zan ja mata kunne, amma Alaja ina neman wata alfarma"

"I don't have money woo"

A tunanin Alaja kuɗi Maman Bilqees take so ta ran ta mata, murmushi Maman Bilqees tayi ganin cikin sauri Alaja ta fassara maganar ta da neman rancen kuɗi, kai Alaja da kuɗi sai a hankali, ta sauke numfashi tare da cewa 

"A'a ba kuɗi zan tambaya ba"

"Ina jinki to"

"Nayi wa Baban  Bilqees alkawari zan kula da Bilqees ko da bayan ransa ne, zan bata tarbiyya kamar yana raye, zan tsare mutuncin ta kamar yana raye, ba zan bari ta zubda ƙwalla ba"

Tayi shiru tana jin ɗaji cikin zuciyarta, ji take dama ace ba a taɓa halittar ta ba, ji take ina ma wannan rayuwar duk mafarki ne...

"Ina sauraron ki Maman Bilqees"

"Alaja ina so ki rufa min asiri ki bari na cika wannan burin na mahaifinta, na sani kin yi mata abin da ko mahaifinta iyakarsa kenan, amma ina so Bilqees takai budurcinta ɗakin mijinta, ina so Bilqees tayi rayuwa cikin daraja da mutunci"

"Any way, za mu yi magana akai amma ba yanzu ba"

"To na gode sosai Alaja"

Ta mik'e tana ƙoƙarin fita, Alaja ta ce

"Maman Bilqees da fatan baki manta yarjejeniyar da mu kayi ba?"

"Eh ban manta ba"

"lokacin yana dab da ƙarasowa"

"Na sani amma akwai Allah"

"Daman akwai shi, kuma shi ya bamu tsawon rai har muka iski shekarar, to ki sani lokacin yana yi ba zan ji tausayinki ba, ba zan saurari magiyar ki ba, zan ɗauki Bilqees na har abada!"

Tana gama faɗin hakan ta shige ciki, Maman Bilqees dake tsaye kamar ta ƙwala ihu haka take ji, ta juyo da ƙyar ta nufo hanyar fitowa...

Bilqees dake maƙale tana sauraron duk abin da suke tattaunawa, tun da taji fitar Mamanta tasan wajen Alaja za ta je, don haka ta lallaɓo ta fito, don tasan a tunanin Mamanta tayi nesa a bacci. Taji duk abin da suka tattauna kuma wannan abin ba sabo bane duk lokacin da Alaja da Mamanta suke tare to shi suke tattaunawa akai, sai dai maganar su ta ƙarshe ce ta ɗaga mata hankali..

"Yarjejeniya?"

Ta furta a hankali, jin alamun motsin fitowar Mamanta ne yasa tayi sauri ta laluɓo ta dawo ɗakinsu ta kwanta....

Maman Bilqees da ƙyar ta kawo kanta ɗakinsu, ta kwanta, cikin tashin hankali, ya za tayi da ranta abin da take tsoro shi yake shirin faruwa, ya za tayi ta hana faruwar abin, ya Allah ya kawo mata ɗauki...

Tana saka da wannan tunani bacci ya ɗauke ta.

Bilqees tun da ta saka kanta a kan pillow bacci ya gagareta, ta rasa dalilin da yasa Mamanta ke lallaɓa Alaja, ko da laifin Alaja ne sai tayi ta bata hakuri, tun tana ƙarama take fuskantar wannan al'amarin. Wai shin ma, menene haɗin su da Alaja? wacce iriyar alaqa ce a sakaninsu da ita? Wacece Alaja a rayuwarsu? To in ba Alaja kenan ba za su rayu ba? saboda yadda take jin Mamanta ke faɗin Alaja ita ce gatansu. Wai shin ma, wacce yarjejeniya ce sakanin Mamanta da Alaja da take cewa lokacin wannan yarjejeniyar ya kusa cika.....

Da wannan zancen zuci bacci ya saci Bilqees ba tare da ta samo amshoshin tambayoyin ta ba...

Washegari 

Kamar yadda Bilqees take yi in ta tashi a bacci haka tayi, ta kammala aikinta sannan ta shigo palour ta zauna, ta ɗauko wayarta da sai tayi kwana biyu bata yi amfani da ita ba, ta hau buga game, shiru Mamanta bata tashi ba, tun da ta idar da sallah. Bilqees ta ci gaba da game har 8:00am taji alamun motsin fitowar Mamanta daga ɗaki ta ɗago tare da gaida ta

"Bonjour Maa"

Ta ce da Mamanta ina kwana da yaren French, Mamanta ta maida mata da yaren.

"Comment ca va?"

Take tambayar ta, how are you? Ya ya take? Ta amsa cikin siririyar muryarta da 

"Ca va Bien?"

I'm good, ta bata amsa da lafiya kalau, ta kalleta a hankali Mama ta ce

"Ya kike zaune, ba za ki je wajen aiki bane?"

"Umm ... Daman... Uhm akan abin da ya faru jiya ne.. na ce..

"Bilqees ki tashi ki shirya ki tafi wajen aiki nayi magana da Alaja a daren jiya, ta ce ba komai, ya wuce"

Sauke numfashi Bilqees tayi, tsam bata son tayi mutsu ko jayayya ta tashi ta fito ta shige toilet ta rage kayan jikinta ta watsa ruwa sannan ta fito ta shirya cikin uniform na wajen aiki, a lokacin Mamanta ta zuba musu abinci a plate suka ci tare sannan ta yi wa Mamanta sai an jima ta fito tsakar gidan babu kowa, tayi saurin fitowa bakin gate ta samu mashin ya kawo ta Alaja special restaurant......


******************************

Nigeria, Maiduguri KIRAWA'S FAMILY 

Horn yayi a ƙofar gida, Baba Musa ya buɗe masa, ya shigo kai tsaye parking space ya wuce yayi parking, ya fito ya nufi ɗakin sa. A gajiye ya dawo ya ajiye side bag nasa da wayarsa a kan tabur sannan ya rage kayan jikinsa ya faɗa toilet ya watsa ruwa, ya fito ya ji jikinsa wasai ya shirya cikin kayan wasan ƙwallon hannu sannan ya fito ya wuce side inda suke motsa jiki....

Da isowarsa ya tadda ƙannensa da suke wasan ƙwallon ƙafa har sun fara, bai bi ta inda suke ba, ya iso inda shi yake buga ƙwallon hannu, a hankali yake motsa jiki yana zaga wajen, ya ɗan tsaya yana sauke numfashi sannan ya fara twisting a hankali yake motsa hannayensa, cen kuma ya fara stretching yana mimmiƙa hannayensa...

"Likita bokan Turai"

Ya dakata tare da yin murmushin gefen laɓɓe, ya ce

"Sa'eed how fah? Sai yanzu?"

Sa'eed ya sosa keyarsa tare da cewa 

"Bacci ne ya sake ni bayan sallah asuba"

"Oh ka kwana chatting ko?"

Dariya yayi yasan me Dr Waahab ke nufi ya ce

"A'a bros nayi baccin dare mah fah sosai"

"Ni ido biyu na kwana a hospital, gashi kuma na dawo gida ban koma bacci ba, har sai na idda motsa jiki kuma nayi breakfast sannan na kwanta na rama bacci"

Ɗauko ƙwallon Sa'eed yayi yana ɗan buga shi da ƙasa yana bouncing ya ce

"Wa zai iya irin rayuwar ka, ni ban taɓa ganin wanda yake ƙin baccin dare irin ka ba"

"Nupe ba ƙi bane fah, wasu abubuwa ne nake yi, balle kuma yanzu da nake senor doctor kaga ni da baccin dare ai mun yi hannun riga"

"Lallai bros matar ka zata sha fama kam, let's play"

Suka soma wasan, sun jima suna yi yau ma Dr Waahab Waseem KIRAWA ne ya kwamushe wasan, suka zauna Sa'eed ya ce ba damuwa shima ko da watarana ne zai yi nasara suna hira suna dariya. Dr Waahab Waseem KIRAWA bai cika hira ko hayaniya sosai ba, in dai hira me tsawo ce to ko yana tare da Sa'eed ko mahaifinsa.....

"Barkan ku da safiya manyan mu"

Cewar ƙannensu da suka iso daga filin wasan buga ƙwallon ƙafa, suna share gumi, Ya Sa'eed ne ya amsa da 

"Barka dai footballers, kuma kun tashi a wasan kenan?"

Sageer Mustapha KIRAWA ne ya amsa da

"Eh fah me ya rage mun yi wining"

"To Abdullahi kai ko ya ka bari hakan ta faru?"

"Ya Sa'eed hariya ce amma ba komai ai ba a gama ba, gobe ma rana ce"

Dariya su kayi suna kallon Abdullahi Umar KIRAWA wanda ya gama kulewa sabar takaici ko kallon ƴan team nasa bayyi ba, yana huci"

"Little bro kada ka damu daman haka wasan ya gada, ko ka kada wani ko a kada ka"

Cewar Dr Waahab Waseem KIRAWA, a lokacin da yake ci gaba da goge gumin dake fuskar sa. Abdullahi Umar KIRAWA ya sauke numfashi tare da cewa 

"Kyale su gobe ma rana ce"

"Kada ka cika baki Abdul kawai ka bada gari ba za ka iya ja dani ba"

"Ba zan bada ba har sai nayi nasara"

Dr Waahab Waseem KIRAWA bai sake tofa baki ba, ya ɗauki ruwan roba ya kwankwaɗa sannan ya ajiye yana jinsu har Abdul yayi zuciya ya bar wajen, sauran ma suka tafi, Ya Sa'eed ya kalli Dr Waahab da ya kurawa gefe guda idanu da alama ya faɗa a kogin tunani, ya matsu ya ɗan ɗaura hannu akan kafaɗar sa tare da cewa 

"Ya dai Likita?"

A hankali ya sauke numfashi ya dubi Ya Sa'eed cikin kulawa yayi magana 

"Jikin Mommie ne yake damuna, har yanzu nake ganin kamar babu sauyi, kuma bana so a fitar da ita outside"

"Ban tari numfashinka ba Likita amma ina ganin a fitar da ita ƙasar wajen kawai shine mafita, kaga an kaita hospital a garin Kano jiki yaƙi sauki haka ma Abuja nan ma gidan jiya, kawai a fitar da ita ko za a dace"

Ya sauke numfashi yayi shiru na wani lokaci sannan yayi magana 

"Na ɗaurata akan wasu magungunan, mu bari zuwa wani lokacin"

"To Allah ya bata lafiya"

"Amin"

Dr Waahab Waseem KIRAWA ya mik'e zuwa ciki ya bar Sa'eed a zaune yana amsa waya. 

A hankali ya tura ƙofar ɗakinsa ya shigo, da mamaki yabi ko'ina da kallo, ganin an gyara komai sai ƙamshi ɗakin ke yi, gashi an ajiye masa basket na breakfast daga gefe. A hankali ya ƙaraso ya tsugunna ya buɗe kulolin yaga farar doya ce sa egg sauce sai kuma kunun gyaɗa dake jug, ya rufe ya tashi ya rage kayan jikinsa ya faɗa toilet.....




Comments and share fisabilillah