1
by @pherty001
Sanyin yammacin rana ya ratsa ta cikin gidan, gida ne matsakaici wanda bangon sa ya fara cin kansa saboda tsufa, duk da haka a gyare yake, irin gidan nan ne na talakawa masu rufin asiri average middle-class struggling home. A gefe guda na tsakar gidan, sautin kukan kaji ne ke tashi daga cikin kejin da aka gina da raga, inda kajin ke kai da kawowa suna jiran abinci.
A kan wata tsohuwar kujera mai dauke da tsumman matasai, Jaddi take zaune kishingide. Idanunta a lumshe suke saboda raɗaɗin jikin da take ji, jikinta ya nuna alamun sugar ɗinta ya tashi, numfashinta yana fita da sauri-sauri.
Daga cikin ɗaki, Nurayyah ta fito, yarinya ce mai kwarjini duk da shekarunta sha shidda ne kacal. Sanye take da doguwar rigar atampa wadda ta zauna mata ɗas a jiki, ta yafa babban hijab ɗinta, ko a yanayin talauci, Nurayyah akwai nutsuwa.
"Jaddi, mu tafi lokaci yana tafiya," Nurayyah ta faɗa tana kamo hannun kakar tata cikin kulawa.
Sannu a hankali suka fito har babban titi, inda Nurayyah ta tsaida Adaidaita Sahu. "Malam, Barau Dikko Specialist Hospital zaka kai mu," ta faɗa da wata irin nutsuwa. Sun yi ciniki, sannan suka shiga, suka nufi asibiti,
Motar adaidaita sahun ta tsaya daidai kofar shiga sashen gaggawa da marasa lafiya na waje, wato GOPD (General Out-Patient Department) na asibitin Barau Dikko. Hayaniyar mutane, kukan jarirai, da kuma warin magunguna da sinadaran asibiti suka tarye su tun kafin su kai ga shiga ciki. Nurayyah ta biya ɗan adaidaitan, sannan ta kamo hannun Jaddi wadda kusan rabi ne kawai na nauyin jikinta take iya dauka, sauran duk ya tafi saboda radadin ciwon da yake ratsa kashinta.
Suna shiga ciki, Nurayyah ta ji gabanta ya fadi. Mutane ne birjik a zaune a kan dogayen kujeru na karfe, wasu ma a kasa suke zaune saboda rashin gurbi. Layin katin asibiti ya zama kamar maciji, kowa yana rike da takardarsa yana kallon agogo. Nurayyah ta jawo Jaddi zuwa wani dan lungu, ta samu wata tsohuwar kujera ta zaunar da ita.
"Jaddi, bari na karbo mana kati, dan Allah ki danyi hak'uri kinji," Nurayyah ta fada muryarta na rawa. Jaddi bata iya magana ba, sai kawai ta gyada kai, idanunta sun yi luf-luf, launin fuskarta ya sauya daga launin fata ya koma wani irin kalar toka-toka saboda sugar da jikin da take ji.
Nurayyah ta koma layin katin, Bayan ta karbo ta dawo tana jira layi yazo kansu, nan ne ta fara ganin abin da ya fi ciwon jiki radadi wato rashin adalci. Mutane na ta faman kukan yunwa da jinya, wasu tsofaffi ne sun kusa faduwa amma ba wanda ya damu dasu kowa ta kansa yake. Idanunta suka kalli wani bawan Allah da aka shigo da shi a keken marasa lafiya (wheelchair), kafarsa a nade da bandeji wanda jini ya riga ya bata duk jikinsa, aka ce masa ya jira sai an duba wadanda suka riga shi saboda akwai layi sosai a wurin.
Tana cikin wannan tunanin, sai ga wata nurse sanye da fararen kaya ta shigo, tana taku cikin takama, a bayanta da wata mata sanye da leshi mai tsada, kanta kunshe da mayafi, tana baza qamshin turaren da ya mamaye gurin nan take, batare da tabi layi ba, kuma ba tare da tambayar kowa ko neman izinin su ba, nurse din ta bude dakin likita ta shigar da matar nan.
Nurayyah ta bi su da kallo cikin mamaki kafin ta dubi sauran mutanen dake wurin kowane ransa a matuqar bace, abin ba a nan ya tsaya ba, Nurses din wurin sun mayar da asibitin kaman kasuwa da zarar sun ga wani mai gari ko mai kudi ya zo, sai su kwashe kafa su nufi inda yake, su karbi takardunsa su wuce da shi gaban likita, yayin da talakawa wadanda suka kwana a wurin suke kalle-kalle, waɗannan "Special Patients" din ba su san abin da ake kira layi ba, suna zuwa ne da iko da gadara, ma'aikatan asibitin kuma na yi musu biyayya domin neman abin hannunsu.
A gefe guda kuma, talaka idan ya yi magana, sai nurse ta masa magana "Wai kai baka gani muna aiki ne? ka zauna idan lokacinka ya yi za a kira ka!"
Nurayyah ta koma kusa da Jaddi, ta tsugunna a gabanta tana goge mata gumin da yake ta keto mata, ta dubi kakar tata, wadda yanzu numfashinta ya zama sama sama, ta kalli sauran marasa lafiyar da ke kusa da ita, wata mata ce ke kuka tana rungume da ɗan ta wanda ke fama da zazzabi, amma nurse din ta wucewar ta sai faman hira take da kawarta akan kalar ɗinkin da za su yi na biki.
Akwai wani irin zilla da Nurayyah ta gani a idanun mutanen wurin. Wani irin yanayi na "mun barwa Allah", inda dan adam ke ganin kamar rayuwarsa ba ta da daraja muddin ba shi da kuɗi, Zuciyarta ta cika da wani irin ɗaci da kunci,
Rikicin ya barke ne lokacin da wata nurse ta sake fitowa tana kiran sunan wani mutum da yanzu-yanzu ya shigo. Wani matashi da yake zaune kusa da Nurayyah tun safe, wanda mahaifinsa ke kwance a jikinsa yana nishi sama-sama, ya kasa daurewa, ya mike tsaye da sauri, idanunsa sun yi jawur.
"Haba dai! Me kuka dauke mu? Dabbobi?" Muryarsa ta amsa a fadin corridor din.
Nurses din suka tsaya, daya daga cikinsu ta murtuke fuska, "Lafiya kake ihu kaman ɗan ƙwaya? Baka da kunya ne?"
Matashin ya kara matsawa kusa, "Kunya? Ai ku ne baku da ita! Kuma baku tsoron Allah, tun karfe bakwai na safe muke nan, gashi har karfe biyu ta kusa, kunce mu bi layi, mun bi layi, mun bi doka, amma tun da likitan nan ya zauna, sai mutanen da kuke so kuke shigarwa, waɗanda kuka san su, ko waɗanda suka ba ku kudi, duk waɗanda kuke shiga dasu babu wanda ciwon sa ya kai na waɗanda suke wurin nan suna jira, mahaifina zai iya mutuwa a nan, amma baku damu ba! duba ku gani, ga wani tsoho can acikin ciwo baku damu ba, ga yaron can numfashin sa sai sama sama yake duk hakan bai dame ku ba, Saboda mu talakawa ne bamu da uba a gwamnati, dama komai ya koma SIYASA a yanzu?"
Sauran marasa lafiyar suka fara tofa albarkacin bakinsu. "Gaskiya ne! Wallahi rashin tausayi da adalci ne wannan, haka suke mana ko yaushe, Allah ya isa bamu yafe ba!" Wurin ya hargitse da muryoyin mutanen da suka dade suna haɗiye bacin rai da bakin cikinsu.
Nurse din ta ja tsaki, ta kalli sauran abokan aikinta, "Ku kyale su, idan sun gama haushin sai su zauna, kuma ma, ba za a sake duba kowa ba tunda kun zama marasa kunya." Ta juya zata tafi, tana wani irin yatsine fuska wanda ke nuna ko oho da rayukan mutanen dake gurin.
Nurayyah ta kura wa nurse din idanu, wadanda suka cika da hawayen da suka ki zubowa, ta kalli yadda mutane ke mutsu-mutsu cikin radadi, ta kalli yadda jikin Jaddi ke rawa, ta fahimci wannan duniyar ciwo da jinya ba kawai neman lafiya ba ne, fafituka ce ta kare mutuncin dan adam, a asibiti ma sai an nuna son kai ga wanda ake so, sai an nuna KUƊI DA SIYASA?
Ta sake matse hannun Jaddi, tana jin wani irin kishi da radadi a zuciyarta, ta fada a ranta, wata rana ba zamu zauna a wannan layin na kaskanci ba, a yanzu abin da kawai take bukata shi ne likita ya duba Jaddi kafin lokaci ya kure musu.
Rana ta fara karkata, yammacin ranar ya ratsa ta manyan tagogin asibitin Barau Dikko, yana raba corridor din gida biyu, sashe mai haske da kuma sashe mai duhu. Amma ga marasa lafiyar da ke wurin, babu wani haske a zukatansu.
Hayaniyar safe ta fara lafawa, ta koma wani irin nishi na gajiya, yunwa da kuma dacin rai.
Nurses masu aiki na yamma (Evening Shift) suka fara shigowa, suna kallo sanda suka fara handing over da masu morning shift,
"Ai yau akwai gajiya, mutanen ne sai kace kudan zuma," daya daga cikin nurses din safe ta fada tana gyara bakin mayafinta.
Babu jimawa Likitan dake duba mutane tun safe ya fito, sanye da farar rigarsa ta lab coat rataye a hannunsa. Ya yi mika, ya kalli jama'ar dake zaune a layin kamar bai gansu ba, sannan ya wuce abinsa don tashi daga aiki.
Wani irin nishi na yanke tsammani ya tashi daga cikin jama'ar, mutane da dama suka fara kallo-kallo, wasu sun kwashe kusan sa'o'i bakwai a zaune, wasu ma basu karya ba tun safe domin gudun kada a kira sunansu ba sa nan. Ganin likitan ya tafi ba tare da ya duba ko da rabin mutanen ba, ya jefa kowa cikin duhun damuwa, cos ko kwata ba'a duba acikin su ba sai daga masu zuwa ƴan alfarma.
Mintuna kadan bayan tafiyarsa, wani sabon likita ya iso, Matashi ne, yana tafiya cikin takama da sanyin kunne, Jama'a suka fara gyara zama, kowa yana sa ran yanzu zaa duba shi, Nurayyah ta gyara wa Jaddi zama, tana kokarin karfafa mata gwiwa duk da cewa itama fargabar take ko zaa duba su ko bazaa duba su ba.
Doctor ɗin bai shiga ba sai da yayi magana da nurses akan wadanda ke nan kaɗai zai duba, a sanya katin su a layi,
Amma abin da ya faru ya sa mutane daskarewa, Maimakon ayi yanda yace sai nurse ta fito da katin wadanda ke kan layi ta ajiye a gefe bayan ya shiga office, ta dubi sauran nurses tana faɗin "ina da patients pls da muka zo tare nake so a duba, bari na kira su", ta fita ta kira wacce take waje tana jiran ta, "Hajiya, shigo da ita," ta fada cikin sanyin murya.
Wata mace ta shigo, rike da hannun wata yarinya yar kimanin shekaru bakwai, Suturar jikinsu kawai ta isa ta gaya maka wane mataki suke a rayuwa, Matar na sanye da tsadadden leshi Mai kyau, kanta sanye da babban mayafi na kamfanin Vaisace. Yarinyar kuma tana sanye da rigar sanyi mai kalar ruwan hoda (pink), gashinta ya sha gyara da kyakkyawan ribon, ko a tafiyarsu akwai alamar hutu, basu kalli kowa ba, kamar basu ma san akwai mutane a wurin ba, Nurse din ta bude musu dakin likita kai tsaye, suka shige.
Wata mata dake zaune nesa kaɗan da Nurayyah, wadda take goye da danta mai shekaru uku jikinsa ke karkarwa saboda zazzabi, ta mike da ƙyar, ta nufi teburin nurses din tana kuka, muryarta na rawa.
"Don Allah, don son Annabi, ku dubi ɗan nan nawa, tun safe nake nan, ko ruwa ban sha ba, idan kudi kuke so daban, ku fada min nawa ne? Ko duba nawa ne zan fita na nemo muku, muddin dai za a duba min shi, dan Allah kada ya mutu a hannuna," ta faɗa tana kallon su gwani ban tausayi.
Nurses din ko kallo ba ta isa ba a gurin su, ɗaya daga cikinsu tana danna waya, tana tabe baki, dayan kuma tana rubutu a wani littafi, sauran kuma suna maganar samarin su, da ƙyar ta sami wata ta kula ta,
" ki daina mana surutu a nan kowa ma da tasa matsalar ya zo koma ki zauna, idan kudin ne da ke ai sai ki tafi asibiti mai zaman kansa (private)," daya daga cikinsu ta fada ba tare da ta kalli matar ba.
Ana cikin wannan hatsaniyar, kwatsam sai aka ji wani nishi mai karfi daga inda wannan matashin da yayi faɗa ɗazu yake. Mahaifinsa, wanda ya dade yana fama da numfashi, farat daya sai ya fara wani irin fizge-fizge. Idanunsa suka karkata zuwa sama, kirjinsa ya fara dukan sama-sama.
"Baba! Baba! Me yake faruwa?" Matashin ya shiga ihun kiran mahaifinsa.
Nan take hankalin kowa ya tashi. Nurayyah ta mike tsaye, tana kallon yadda dattijon yake kokawa da numfashi na karshe, mutane suka fara taruwa a kansu, Nurses din da dazu suka nuna halin ko-in-kula, suka ga abin ya zama na gaske, sai suka rugo da gudu da stethoscope a hannunsu,
"A ba shi iska! Matsa ku ba shi wuri!" Nurse din tana kokarin danna ƙirjinsa, tare da ɗora stethoscope ɗin.
Amma ina, rai ya riga ya yi halinsa, nishi na karshe ya fita, sannan jikin dattijon ya yi sanyi qal, ya koma tamkar busasshiyar icce a kan kujerar asibitin.
Wani irin shiru ya biyo baya, shiru mai nauyi da radadi, daga nan kuma sai ɗakin ya ruɗe da kukan matashin nan da kuma zage-zage daga mutanen dake gurin. "Kun kashe shi! Saboda son kudi da rashin adalci kun kashe shi, bamu yafe ba Allah ya isa!" Wani ya fada cikin fushi. Fada ya barke tsakanin ma'aikatan asibitin da kuma samari da ke wurin, kowa yana huci kamar zaki.
Nurayyah tana tsaye, duk jikinta rawa yake yi, idanunta sun kafe akan gawar dattijon nan, itace gawa ta biyu da ta taɓa gani a rayuwarta bayan ta mahaifinta, jikinta ya dauki rawa, wani irin tsoro ya ziyarce ta, tsoron da bai taba dukan zuciyarta ba, ta kalli Jaddi, wadda yanzu hankalinta ya gama tashi, Jaddi tana kallon gawar, tana ambaton Allah, amma idanunta sun nuna tana j
cikin tsoron ko itama nata lokacin ya kusa, kada ta mutu a wurin itama ba'a duba ta ba, musamman yadda numfashinta yake neman gagararta.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un... Nurayyah, mu tafi... mu tafi daga nan," Jaddi ta fada cikin muryar dake nuna cewa ranta ya baci kuma ya firgita.
Nurayyah bata tsaya wata-wata ba, tana ganin yadda mutane ke dambe, wasu na kuka, wasu na kiran jami'an tsaro, ta damki hannun Jaddi da dukkan karfinta, hannun yarinyar mai shekara goma sha shidda yana karkarwa kamar an hura mata iskar sanyi, ta ji kaman idan basu bar asibitin nan ba, itama za ta rasa Jaddi a wannan layin na kaskanci.
Cikin rawar kafa da sauri-sauri, suka ratsa ta cikin taron mutanen, suka fita wajen asibitin. Suna fitowa babban titi, Nurayyah ta ga wani wuri a gefen titi karkashin wata bishiya mai inuwa, inda akwai wasu duwatsu na zama, ta kai Jaddi ta zaunar da ita, sannan itama ta zube a kasa a gaban kakar tata, tana gumi duk da sanyin yammacin da ya karu.
Nurayyah ta kalli hannuwanta dake rike da na Jaddi, ta ga yadda fatar jikin kakar tata ta tsufa, ta ga yadda jijiyoyin jikinta suka fito, ta ɗaga kai ta kalli ginin asibitin Barau Dikko daga nesa, a idanunta, asibitin bata kasance gurin neman lafiya ba, ta koma mata kaman karkashin kasa inda ake binne mafarkin talaka da cin amanar su.