RIGAR ARO

2

by @pherty001

*RIGAR ARO*




©️Fertymerh Xarah💞




2





Duk da iskar dake kadawa a qarqashin icce da suke zaune hakan bai hana zufar Jaddi dake fita a goshinta tsayawa ba, tana zaune a kan dutse, idanunta sun yi luf-luf, zuciyarta kuma tana dukan sauri saboda firgicin mutuwar da ta gani a gabanta. Ta kalli Nurayyah, wadda take tsugunne a gabanta tana hawaye, sannan ta yi wani irin nishi mai nauyi.

​"Nurayyah..." Jaddi ta kira sunanta cikin muryar da ba ta fita da kyau. "Mu koma gida kawai, ba zan iya zama a asibitin nan ba idan mutuwa ce, na gwammace na mutu a dakina cikin mutunci, maimakon na mutu a kan wannan layin na wulakanci."

​Nurayyah ta girgiza kanta da sauri, hawaye na zuba a kuncinta. "A'a Jaddi! Ba za mu koma gida ba, ba ki da lafiya, jikinki zafi yake yi, numfashinki kuma bai daidaita ba, dole ne likita ya duba ki zan koma ciki na sake rokonsu, ko ma na nemo wani likitan daban..."

​"A'a Nurayyah," Jaddi ta katse ta, tana rike hannun jikanyar tata. "Kin ga abin da ya faru da wannan bawan Allah, kuma ga wata matar ma da ɗan ta ne a kusa da mu, amma nurses din nan suka kyale wancan tsohon ya mutu kaman dabba ni ma haka kike so ki gani? Mu koma gida Addu'arku ta fi mini maganin da ba a ba ni da tausayi da rashin adalci."

​Sun dauki lokaci mai tsawo suna wannan saqa da warwaran. Nurayyah tana tsoron rasa Jaddi  idan suka koma gida ba tare da an yi mata komai ba, ita kuma Jaddi tana tsoron wulakancin asibitin ya kashe ta kafin ciwon ya yi kisa daga karshe, ganin yadda Jaddi ta dage, Nurayyah ta yarda cikin damuwa.

Nurayyah ta mike ta goge fuskarta. Ta bar Jaddi a zaune, ta nufi bakin titi inda ta tari wani Adaidaita Sahu (Napep), ta fada masa unguwar da zai kaisu bayan sun yi ciniki, Nurayyah ta taimaka wa Jaddi ta mike da kyar, suka shiga napep, tafiyar duk a shiru aka yi ta, Nurayyah na kallon titunan Kaduna amma zuciyarta tana can gida, tana tunanin yadda za su yi da ciwon nan.

​Suna isa kofar gidansu, mai Napep din ya ajiye su Nurayyah ta taimaka wa Jaddi ta fito tana dingishi, daidai lokacin ne Malam Musa, makwabcinsu wanda kowa ya san mutumin kirkine da son mutane, kamar ma shine matsayin uba a gareta yanzu, tunda duk abinda take so na makaranta idan Jaddi bata da kuɗi wurin sa take zuwa, yana kokarin fitowa daga gidan sa.

​Malam Musa ya tsaya turus ganin yadda Jaddi take tafiya kaman wadda za ta fadi, ga Nurayyah fuskarta duk ta kumbura saboda kuka.

​"Subhanallahi! Jaddi, me yake faruwa? Nurayyah, lafiya daga ina kuke haka?" Malam Musa ya tambaya cikin kulawa da tashin hankali.

​Nurayyah ta kasa boye damuwarta. Nan take ta shiga ba shi labarin komai tun daga layin da suka bi, yadda aka rika shigar da masu kudi, har zuwa yadda wannan dattijon ya rasu a gaban kowa ba tare da an taimaka masa ba. Tana maganar tana kuka, muryarta na rawa. "Baba Musa, asibitin ynxu babu adalci babu tausayi sai son zuciya, saura kaɗan Jaddi ta rasa rayuwarta a wurin saboda rashin adalcin su."

​Malam Musa ya jinjina kai, ransa ya baci kwarai. "Wannan gaskiya ne Nurayyah, rashin tausayi ya yi yawa a yanzu, ku kwantar da hankalinku, shigo da ita ciki ta kwanta ta huta kada ku sanya damuwa a ranku."

​Ya kalli Nurayyah ya ce, "Karki damu, yanzu zan aiko Lawali mai Chemist, Lawali ya san aiki, kuma zai zo har gida ya duba ta, ya ga abin da ya kamata a ba ta kafin gobe mu ga abin yi."

​Cikin kankanin lokaci, suna shiga gida, Jaddi ta kishingida a kan katifarta, ba a dade ba, sai ga Lawali ya shigo, sanye da wata yar riga mai aljihuna da yawa, rike da wata karamar jaka ta magunguna, shima mutum ne mai barkwanci da tausayi.

​Ya gaishe da Jaddi, sannan ya fito da na'urar auna suga da ta hawan jini, ya debi jinin Jaddi ya auna.

​"Jaddi, kin ga dai yadda kuke wasa da jiki ko?" Lawali ya fada yana murmushi don ya kwantar musu da hankali. "Sugarki ne ya dan yi sama, sannan kuma ga tashin hankali da kika sa wa kanki jinin ya hau kaɗan, karki damu, zan ba ki wani magani yanzu da zai saukar da shi, sannan na baki wasu allurai da za a rika miki na kwanaki biyu."

​Ya fito da wasu magunguna ya mika wa Nurayyah, ya yi mata bayanin yadda za ta ba Jaddi ya kuma tabbatar mata cewa nan da sa'o'i kadan Jaddi za ta ji sauki idan ta samu barci, bayan ya kammala, ya fita yana yi musu fatan alheri.

​Nurayyah ta sauke ajiyar zuciya. Koda yake har yanzu akwai damuwa a ranta, amma taji wani sanyi ganin cewa a cikin unguwar su, akwai mutanen da har yanzu suke daraja talaka kuma suke taimakawa ba tare da nuna bambanci ba, ta zauna a gefen Jaddi, tana shafa kafarta, tana kallon kakar tata har barci ya ɗauke ta.


Nurayyah tana zaune a gefen katifar Jaddi, idanunta kyam a kan fuskar kakar tata wadda barci ya kwashe ta bayan Lawali ya gama yi mata allura, dakin ya yi shiru, sai karar numfashin Jaddi da kuma sautin agogon bango da yake bugawa a hankali, bugun agogon yana dukan zuciyar Nurayyah, yana tunatar da ita yadda lokaci yake gudu da kuma yadda rayuwa take juyawa.

​Iskar daren dake shigowa ta tagar dakin tana da sanyi, amma Nurayyah ba sanyin take ji ba, wani irin daci take ji a makogwaronta, tana da shekaru goma sha shidda kacal a duniya, shekarun da ya kamata ace tunaninta ya tsaya ne a kan littafan makaranta da kuma mafarkin gobe mai kyau, abin da ta gani a asibiti yau yadda bawan Allah ya rasu a gaban kowa saboda rashin adalci da rashin kishi na ma'aikata ya fasa mata zuciya ta fahimci yanzu rayuwar idan baka da kudi, numfashinka ba shi da daraja a idon mutane, taji yanda mutane a wurin suke zagin gwamnati suke debewa gwamnati albarka tare da adduar Allah ya kawo masu sauyi mafi alheri daga wannan gwamnati, me hakan ke nufi kuskure daga gwamnati ne ko me?.

Ta soma tuna mahaifinta, bata san Maman ta ba, tana haihuwar ta ta rasu, ranar da komai ya fara rugujewa Mahaifinta ya shiga wata yarjejeniya ta filaye da wani abokin kasuwancinsa, wanda suke ganin kamar dan uwa ne, abokin sane sosai kuma ɗan siyasa ne, sai abokin ya juya wa mahaifinta baya, Filaye da gidajen da Alhaji Abdullah ya zuba dukkan jarinsa a kai, mutumin nan ya ce nasa ne, kuma kuɗin jarin mahaifin ta ya ninka na abokin sa sau uku.

​Abin da ya fi ci mata tuwo a ƙwarya shi ne lokacin da aka je kotu, ta ga yadda aka murkushe gaskiya aka mayar da ita karya domin abokin sa ya fi mahaifinta a gwamnati da fada a ji a lokacin saboda yana cikin siyasa, alkalan suka karkata shari'a. A ranar da aka ba da hukunci cewa Alhaji Abdullah ba shi da gaskiya, Nurayyah taga yadda mahaifinta ya koma lokaci ɗaya, taga yanda baqin ciki da rashin adalci ke kashe xuciyar cikakken namiji irin mahaifinta, ya dawo gida kafafunsa na rawa, idanunsa sun rine sun yi jawur saboda baqin ciki.

​Karayar arziki da ya samu bai tsaya a nan ba biyan bashi da kokarin farfadowa ya cinye ragowar abin da suke da shi damuwa ta yi wa Alhaji Abdullah yawa, har ta kai ga wata rana da daddare, zuciyarsa ta buga Nurayyah ba za ta taba mantawa da yadda ta ga mahaifinta yana nishi yana rike da kirji ba, har numfashinsa ya yanke a kan idonta ita da Jaddi.

Don ganin Nurayyah ta ci gaba da karatu, Jaddi ta rungumi kiwon kaji da siyar da ƙwai da zomaye a bayan gida.

 Nurayyah ta kalli hannun Jaddi wadanda suka fashe saboda aiki tana tuna yadda kakar tata take tashi tun asuba tana share dakin kaji, tana ba su abinci, tana duba lafiyarsu idan kaza daya ta mutu, Jaddi takan yi bakin ciki ba don komai ba sai don kudin makarantar Nurayyah da zai ragu.

​"Nurayyah," Jaddi takan ce mata idan tana karatu da daddare ko kuma kowane lokaci idan ta ganta da littafi a hannunta, "kar ki damu da halin da muke ciki yau. Ilimi shi ne kadai gatanki. Mahaifinki bai bar miki komai na dukiya mai yawa ba amma ya bar miki tarbiyya, da gida ɗaya kacal a duniya, zan tsaya akan ki zan zame maki gata a duniyar nan ko da zan rasa komai nawa."

Nurayyah ta sauke numfashi, hawaye ya wanke mata fuska ta kalli hannun kakar tata da yake rawa a hankali cikin barci tana tsoron rasa Jaddi, Idan Jaddi ta tafi, wa ya rage mata? A wannan rayuwar da ta gani a yau, inda talaka yake matsayin dabba a idon masu mulki da masu kudi, ta yaya yarinya kamarta za ta rayu ita kaɗai babu uwa babu uba babu kuma Jaddi?

​Ta tuna yadda aka wulakanta su a asibiti, tana jin wani irin kiyayya ga rashin adalci yana dasuwa a zuciyarta ta lura daga gwamnati ne da gaske saboda bata bincike akan aikin da ma'aikatan da ta ɗauka take biyan su domin su mata aiki akan abinda suke aikatawa a asibiti da gaske suna buqatar canji suna buqatar sa uwar gwamnati ba irin wannan da ta shekara 3 akan mulki babu cigaba ba, kuma a hakan take so ta qara zarce wa.

​Yanzu tana da shekaru 16, tana jin nauyin komai, nauyin kula da Jaddi  a kafadarta, dame zata kula da Jaddi dole sai tayi karatu sosai dole sai ta jajirce na ganin ta cimma burin ta na zama likita, yadda jajircewar Jaddi yake ba ta kwarin gwiwa a rayuwa shi yake saka ta jin tabbas zata cika wannan burin na zama cikakkiyar likita, kuma dole ta zama jaruma domin ta kare kanta da kuma tsohuwar da ta sadaukar da komai domin ta, ta tallabe habarta da hannuwanta biyu, idanunta kyam a kan fuskar kakar tata, a wannan lokacin, wani irin kallo take yi wa Jaddi kallon da ya hadiye kauna, tausayi, da kuma wani babban kudiri wanda yake neman fasa zuciyarta ya fito.

​"Zan zama likita irin wacce kike so, zan yi qoqarin ganin nayi karatu sosai domin cimma burin ki, karatu mai zurfi da zan riqa duba lfyr ki ba sai mun je asibiti an wulaqanta ki ba kina dani Jaddi," ta fada a hankali a cikin ranta, muryarta na rawa da wani irin karsashi. "Zan zama likitar da bazata taba tambayar talaka kudi ba kafin ta duba halin da yake ciki. Zan zama garkuwar wadanda ba su da murya nayi masu adalci ko da gwamnati bazata duba hakan ba."

​Wani irin haske na daban ya fara ruruwa a kwayar idon Nurayyah yayin da take hango kanta a nan gaba, ta kudiri aniya a ranta cewa, idan har Allah ya nuna mata ranar da za ta sanya farar riga, to ranar karshen wahalar duk wani mara lafiya da ya zo karkashin kulawarta ne, ta tuna yadda aka yi wa bawan Allahn nan aka kyale shi ya mutu a wulaqance a reception na asibiti, ta tuna yadda nurses din nan suke magana da isa da nuna fifiko batare da sun tausaya wa halin da marassa lfy yake ciki ba.

​"Babu wani marar lafiya da zai sake kuka a gabana," ta rantse. "Babu wani da zan bari a tauye wa hakkinsa don kawai ba shi da kuɗi, ko don ba shi da wani a siyasa, zan sanya kowa ya ji cewa shi ma dan Adam ne mai daraja mai kuma ƴanci a ƙasar sa."

Tana gama tunani, ganin Jaddi ta sami barci ta tashi ta soma gyara gidan duk da ba wani datti yayi ba.