Sick Bed
by @zahrabmrs02
in celebration of my 100 followers ga free chapter
thank you all for the support
Falmata kuwa tana zaune ne a ɗaya daga cikin kujerun da ke wajen, tasbaha na yawo a tsakanin yatsunta, amma hannunta har rawa yake yi saboda tashin hankali. Kalmomin istigfari da salati ne kawai suke fita daga bakinta.
Sadiya ma ta rasa yadda za ta yi ta zauna ,ta sake miƙewa ,ta sake zama. tayi tafiya kaɗan, ta dawo. wani irin rashin nutsuwa ya bayyana a tattare da ita, duk da ƙoƙarin da take yi na ɓoye shi Amma cikin su duka…Khalifa ne yafi zama abun tausayi.
Tun daga lokacin da aka shigar da Daddy cikin ɗakin gaggawa bai sake furta ko kalma ɗaya ba. Ya jingina da bangon corridor, kansa a sunkuye, idanunsa na kallon tiles ɗin ƙasa amma ba ya ganin komai.
Tunani guda ɗaya ne kawai yake yi.
Maganar da suka yi a balcony.
Murmushin nan mai ciwo.
Da kuma kalmar nan guda ɗaya…
“Na makara…”
Wani irin ƙunci ce ta tokare masa ƙirji ya runtse idanunsa da ƙarfi.
A dai-dai lokacin ne ƙofar Emergency Room ta buɗe ,dr da ya jagoranci duba Daddy ya fito yana cire safar hannunsa kafin ya gama taku biyu gaba ɗaya suka yi kansa.
“Doctor!”
Dr. Mariya ce ta fara isa gabansa.
“How is he? Ya yake yanzu?”
Likitan ya ɗaga hannu cikin natsuwa.
“Please… calm down.”
Duk suka yi shiru.
Sai ya ci gaba.
“He’s stable.”
Kusan a tare gaba ɗayansu suka sauke wani irin numfashi mai nauyi.
Alhamdulillah.
Kalmar ce kawai ta fara fita daga bakunan su Dr Ya gyara glass ɗinsa kafin ya ci gaba da magana.
“Blood pressure ɗinsa ya yi matuƙar tashi. Gajiyar jiki, rashin isasshen bacci, da kuma matsananciyar damuwa sun taru lokaci guda. Wannan ne ya jawo ya collapse.”
“Subhanallah…”
Falmata ta faɗa tana dafe ƙirji.
Likitan ya gyada kai.
“Alhamdulillah mun samu damar daidaita komai cikin lokaci. Yanzu yana bacci ne saboda magungunan da aka ba shi ,ya ɗan dakata Amma akwai abin da yake son faɗa.
Duk suka sake zuba masa ido.
“He needs complete rest.”
Ya yi magana cikin tsanaki.
abin da ya fi muhimmanci…”
Ya kalli fuskokinsu ɗaya bayan ɗaya.
“Whatever is stressing him this much…”
Ya ɗan girgiza kai.
“…has to stop.”
Shiru ya sake sauka a corridor ɗin.
Shiru mai nauyi.
Domin babu wanda ya iya cewa ga abin da yake damun Kamal,akwai mutum ɗaya da zuciyarsa ta fara haɗa komai.
Khalifa kenan shiyasa me yayi cousing colapas din daddy kuusan mintuna talatin bayan haka zaheera ta iso asibitin tun kafin ta sauko daga mota ana iya ganin tashin hankalin da ke fuskarta. Ta shigo corridor ɗin cikin sauri tana kallon kowa.
“Meya same shi?”
Kafin wani ya amsa mata, Dr. Mariya ta ƙaraso “Yana lafiya yanzu.”
“Alhamdulillah…”
Zaheera ta rufe idanunta tana gode wa Allah kafin ta sake tambaya,
“Me ya faru?”
Dr. Mariya ta taƙaita mata abin da likita ya faɗa sai dai yayin da take sauraro Idanun Zaheera suka sauka kan Khalifa Har yanzu yana tsaye shi kaɗai a gefe.
Nan take ta nufi inda yake.
“Khalifa…”
Ya ɗago kai.
“Ina yini Anty.”
Ta girgiza kai.
“Ba lokacin gaisuwa ba ne.”
Ta kama hannunsa a hankali.
“Zo mu yi magana.”
Ba tare da ya yi musu ba ya biyo ta.
Suka nufi wani lungu na corridor ɗin da babu mutane , Zaheera ta juya ta fuskance shi.
“Khalifa…”
“Na’am?”
Muryarta ta yi laushi sosai.
“Na san Daddy ɗinka ya gaya maka komai.”
Ya ɗan ɗaga gira.
“Komai?”
“Ni twin sister ɗinsa ce.”
Ta yi murmushi mai ciwo “Khalifa… tun muna yara Kamal bai taɓa iya ɓoye min abin da yake damunsa ba ta dafa kafaɗarsa “Na san kasan komai game da shi da Tadala .
“Me ya faru?”
“Khalifa. ya sauke numfashi.
“Mami ce…”
“Meye ta yi?”
“Dazu a dinner…”
Muryarsa ta fara rawa.
“Ta yi announcing engagement ɗin Tadala da Mansoor.”
Zaheera ta tsaya cak.
Ta zaro ido.
“Me kake nufi?”
“Ta ce an ba Mansoor aurenta.”
Ya ci gaba da magana cikin kasala haka yayi briefing dinta
Zaheera ta ji wani irin ciwo ya ratsa zuciyarta gefe ta juya tana goge hawayen da suka taru a idanunta.
A dai-dai lokacin…
Dr. Mariya ta fito daga gaban ɗakin da daddy yake kwance Tun daga nesa ta hangi Khalifa da Zaheera suna tsaye kusa da juna suna magana cikin sirri ,ta tsaya ta ɗan tsuke fuska a hankali ta ƙaraso gare su ,Ta zuba musu ido ɗaya bayan ɗaya.
“Meye kuke kullawa haka ?”
Khalifa ya yi saurin kallon Zaheera.
Zaheera ma ta mayar masa da kallo.
Dr. Mariya ta sake matsowa kusa.
“Khalifa…”
ta maida kallonta kan Zaheera.
“Anty Zaheera…”
Ta ɗan yi murmushin da bai kai zuciyarta ba.
“Ko akwai wani abu game da Kamal…”
Ta ɗan dakata.
“…da ni ban sani ba?”
Zaheera ta zuba wa Dr. Mariya ido na wasu daƙiƙu kafin wani ƙaramin murmushi ya suɓuce mata, murmushin da bai fito daga farin ciki ba, sai dai daga ƙoƙarin ɓoye irin tashin hankalin da take ciki.
ni da nephew ɗina idan za mu yi sirri, dole sai kin sani Mariya?” ta faɗa cikin sanyin murya, tana ƙoƙarin sauya yanayin maganar Dr. Mariya ta ɗan kwar da fuska haba Anty… ni fa tambaya kawai na yi.”
Zaheera ta sauke wata doguwar ajiyar zuciya. Kafin ta ba da amsa, idanunta suka koma kan ƙofar ɗakin da aka kwantar da Kamal. Ta daɗe tana kallon ƙofar kamar tana fatan a wannan lokacin za ta buɗe ya fito yana yi musu dariyarsa irin ta Kamal, ya ce musu babu komai.
Amma ƙofar ta ci gaba da kasancewa a rufe a hankali ta sake maido da kallonta kan Dr. Mariya “Please Mariya…”
Muryarta ta yi ƙasa sosai.
“Ki bar ni na ji da rashin lafiyar twin ɗina ta ɗan dakata, sannan ta ƙara da wata murya mai cike da roƙo.
“Dan Allah.”
Shiru ya ratsa tsakaninsu.
Dr. Mariya ta ci gaba da kallonta ba tare da ta ce komai ba.
A karon farko tun bayan zuwan Zaheera asibitin, ta lura cewa idanunta sun yi jajur saboda hawayen da take taƙurewa. Duk da murmushin da take ƙoƙarin yi lokaci zuwa lokaci, damuwarta ta fi ƙarfin ɓoyuwa.
Nan take zuciyar Dr. Mariya ta tausaya mata.
Ta sauke numfashi.
“Okay…”
Ta matsa kusa da ita ta dafa kafaɗarta cikin tausayawa.
“I’m sorry.”
Zaheera ta ɗan gyada kai.
“Nagode.”
Dr. Mariya ta juya ta kalli Khalifa, wanda har yanzu yake tsaye a gefe, kansa a sunkuye kamar nauyin duniya ya sauka a kafaɗunsa.
Ta ƙarasa gare shi.
A hankali ta shafa kansa.
“Kada ku damu.”
Ta faɗa cikin muryar uwa.
“In Sha Allah zai tashi lafiya.”
Khalifa ya ɗago kai kaɗan.
“Amin.”
Ba a jin komai sai ƙarar na’urorin asibitin da ke tashi lokaci zuwa lokaci, da kuma sautin takun ma’aikatan jinya masu wucewa daga nesa.
Zaheera ta jingina bayanta da bango.
Ta rufe idanunta.
Hotunan rayuwarsu suka fara shawagi a gabanta Kamal ɗin yarinta ,Twin ɗinta abokin wasanta ,mutumin da tun suna ƙanana yake tsayawa ya kare ta idan wani ya ɓata mata rai, kullum shike ɗaukar damuwar kowa a kansa, amma bai taɓa nuna tasa ba Ko ranar da mahaifinsu ya rasu shine ne ya tsaya ya ƙarfafa kowa ranar da ita kanta ta shiga wani hali shi ne ya fara share mata hawaye.
ba shiri hawaye suka cika mata idanu ba a hankali ta ɗaga hannu ta goge su kafin su zubo.khalifa ne ya cigaba da rarrashinta
A hankali , idanunta suka fara yawo cikin ɗakin cikin nutsuwa. Komai ya yi shiru, sai ƙaramar ƙarar monitor ɗin da ke gefen gado yana nuna bugun zuciyar mara lafiyar da ke kwance a kansa. Wannan ƙaramin sautin kaɗai ya wadatar ya sa ƙafafunta suka yi nauyi, saboda kafin ma idanunta su sauka kan gadon zuciyarta ta riga ta san abin da za ta gani.