3
by @pherty001
Washe gari Nurayyah ta tashi da wani irin nauyin idanu da kuma mutuwar jiki saboda bata sami barci sosai ba ta kwana cike da tunanin rayuwa iri iri, ganin har rana ta fito ta ratso ta window ɗaki taji hankalin ta ya tashi domin ta makara.
Ta tashi da sauri, tana gama sallah ta fara da gyaran gidan duk da cewa karami ne, kula da tsaftar da yake samu ya sa ya zama abin sha'awa ta share ko'ina, ta wanke tsakar gida inda zomaye suke zuwa su bata, ta wanke bayi, ta saka turaren wuta mai kamshi Jaddi take adanawa don tasan Nurayyah da barnar turare tana son qamshi sosai, Nurayyah ta kunna kadan, nan take dakin ya dauki wani sanyayyan kamshi wanda yake ratsa zuciya, yana ba da yanayi na nutsuwa.
Bayan ta gama wannan, ta nufi rumbun kaji, sai kuka suke suna ta faman neman abinci, ta zuba musu abinci cikin kwano, tana kallon yadda suke ta faman cin abinci cikin hargits wani murmushin jin dadi ya subuce mata a lokacin da ta hango Jaddi ta fito daga dakinta.
"Jaddi! Kin tashi lafiya? Jikin naki ya yi sauki?" Nurayyah ta fada da sauri, tana karasawa kusa da tsohuwar.
Jaddi ta yi murmushi, fuskarta cike da farinciki da kyakkyawar zuciya. "Alhamdulillahi, Nurayyah na sami sauki sosai Addu'arki ce ta karbu."
Jaddi ta kalli jikarta a ranta, tana jin wani irin daci da kuma alfahari tana kallon Nurayyah a matsayin wata baiwa da Allah ya ba su yarinya kyakkyawa, mai hankali, kuma mai hazaka shi yasa ko bata da komai ko da duk abinda ta mallaka zata siyar sai ta nemawa Nurayyah ilimi,
Bayan Nurayyah ta yi wanka, ta fara shirin makaranta cikin uniform na Queen Amina collage, riga ce fara sol mai laushi, ta sanya siket mai kalar maroon. Duk da cewa uniform ɗin ya ɗan tsufa, yadda take goge shi da kula da tsaftar sa yana sa ta fito daban a cikin ɗalibai, ta sanya fararen safa da takalmanta bakake waɗanda suka sha (polish) har suna kyalli kamar sabbi. Dogon kitson kanta kuwa ta tattara shi ta daure a bayan kanta, ta sanya qaramin hijab, ta ɗauki jakarta mai ɗauke da littattafanta kafin ta fito daga ɗakin.
Jaddi ta shiga daki ta jima kadan sannan ta fito da kuɗi a hannunta ta mika wa Nurayyah naira dari biyar (500) "Ga kudin mota da na abinci Nurayyah kar ki zauna da yunwa a can na san halin ki bakya son cin abinci"
Nurayyah ta kalli kudin zuciyarta ta yi sanyi ta san yadda Jaddi take tashi fadi kafin ta samu wannan kudin, ta san irin sadaukarwar da tsohuwar take yi wajen biyan kudin makarantar da kuma bata na abinci kullum, kuma tasan kuɗin ba zasu isa taje school har taci abinci ta dawo acikin su ba, amma dan kwantar mata da hankali tace", "Jaddi, wannan ya yi yawa..."
"A'a basu yi yawa ba Nurayyah nasani, qilama ba zasu ishe ki ba, kiyi haquri da yanda rayuwa tazo mana watarana sai labari kinji."
Nurayyah ta sunkuya ta sumbaci hannun Jaddi, sannan ta fice tana murmushi.
Tafiyar rabin sa'a ne ya kai ta kofar makarantar, Queen Amina makaranta ce daga cikin tsofaffi kuma fitattun makarantun mata a Arewacin Najeriya, tana da manyan gine ginen azuzuwa masu kyau, da wajen gwaje gwaje na kimiyya da aka tanada domin koyarwa, class ɗin karatu ɗauke da littattafai iri-iri da kuma filayen wasanni da ke ba ɗalibai damar gudanar da harkokinsu cikin walwala. Gine ginen makarantar masu launin madara da koraye, tare da tsarinta mai kayatarwa dake ba wa duk wanda ya shiga harabarta sha'awar kasancewa a cikinta
Nurayyah ta sauka daga mashin ɗin da ya kawo ta ta gyara jakarta a kafada ta shiga cikin harabar makarantar dake cike da natsuwa da sanyin bishiyoyi tana tafiya a hankali ne a kasa ba acikin mota kamar sauran yara da ake wucewa dasu ciki ba, kwarjinin da take da shi ya sa idanun mutane da yawa suka karkata gare ta tana da wani irin "natural elegance" (kyau na fuska da dabi'a) wanda kudi ba zai iya saya ba, halittar tane haka.
"Nurayyah!" Wata murya mai dadi ta kira sunanta.
Nurayyah ta juyo, fuskarta ta washe sanda suka haɗa ido da best friend ɗin ta, tace "fadila!"
fadila 'yar gidan wani babban dan kasuwa ce, babanta mai kuɗi ne sosai, abokai ne sosai tana matuqar son Nurayyah batare da ta duba matsayin su ba, kuma sosai take taimakawa Nurayyah ɗin "Wai yau kin makara kadan? Na riga ki zuwa." cewar fadila tana kallonta,
"Dole ne fadila, na tsaya aikin gida yau cos Jaddi ba lfy," Nurayyah ta amsa cikin sanyin murya.
Suna tafiya tare, suna hira, fadila ita kadai ce ta san sirrin rayuwar Nurayyah a school ɗin, kuma tana girmama yadda Nurayyah take jajircewa duk da halin da take ciki.
Suna shiga cikin class kai tsaye suka nufi wurin zaman su, seat ɗin Nurayyah yana gaba dana fadila,
A can ƙarshen class, zaune take akan kujerarta kamar wata sarauniya Walida kenan, Walida ita ce 'yar gidan wani babban Sanata a ƙasar nan kyanta ba abin kushewa bane amma ya lulluɓe ne da girman kai da kuma kyamar talaka a kusa da ita akwai ƙawayenta guda biyu waɗanda suke biye da ita kamar inuwa duk inda taje ko kuma duk abinda zata yi sune suke goyon bayanta.
Walida ta lura da shigowar Nurayyah ta ji wani irin kishi ya taso mata har makogwaro. Ta kalli yadda uniform din Nurayyah, duk da sun tsufa, amma sun zauna daram a jikinta, ta kalli yadda fatar Nurayyah take sheki Kuma ta tabbata Nurayyah bata shafa irin mayukkan da take shafawa masu tsada a jiki, ko kuma wanda take wanka dasu, irin kyawun fuskar Nurayyah ke saka ta tsananin kishi akan ta.
"Duba ki gani," Walida ta fada, tana kallon kawayenta da babbar murya don Nurayyah ta ji. "Wannan makarantar fa ta fara lalacewa ta yaya za a rika barin mutanen da ba su da ko kudin sayen sabon uniform su rika shiga aji daya da mu? It smells like... poverty around here."
Kawayenta suka kwashe da dariya, Nurayyah ta ji maganar ta soke ta har zuciya ta runtse idanunta, tana kokarin danne hawayen da suke neman zubo mata ta san Walida tana neman ta ne ta yi magana, amma ba za ta ba ta wannan damar ba.
fadila ta ja hannun Nurayyah. "Kyale ta, Nurayyah kishi ne kawai yake damun ta domin kin ninka ta kokari da natsuwa, dan Allah kada ki kula ta."
Nurayyah ta zauna ta bude Jakarta ta ciro littafin ta a duk ajin kowa ya sani idan ana maganar basira, Nurayyah ce kan gaba ko malamai idan sun shigo, girmamawa suke ba ta domin tana da ƙwaƙwalwa sosai akan karatun ta, duk wani activities da zaa yi ko kuma zaa tura student's wata makaranta dole Nurayyah na ciki, wannan ya saka hassada da kishi mai tsanani a zuciyar walida saboda tana ganin ita yar mai kuɗi ce yar sanata amma bata samun kulawar malamai kamar yanda ake bawa Nurayyah a school ɗin.
Walida ta tashi, ta karaso har gaban teburin Nurayyah ta dora hannunta mai zanen lalle a kan littafin Nurayyah. "Ke banza, magana muke miki? Ko ba kya jin hausa ne? Ko kuma kunyar asalin naki ne ya sa kika kasa magana kina ƴar talakawa?"
Nurayyah ta dago kai a hankali. Idanunta suka sarke da na Walida, akwai wani irin haske a idon Nurayyah da ya sa Walida ta ji wani tsoro ya ziyarce ta, amma ta dake.
"Walida," Nurayyah ta fada cikin murya mai natsuwa amma mai nauyi. "Makaranta muke, ba gasar nuna arziki ko talauci ba, idan kina jin haushin kasancewa ta a nan, to ki bar makarantar mana, kije dai dai da irin taku ta ƴaƴan masu kuɗi tunda Kinga talakawa ma suna iya affording wannan, amma as far as muna makaranta ɗaya dake we are the same saboda kuɗin da ake biya miki nima shi ake biyamin ba kyauta nake karatun ba kuma ba bashi ba may be ma ina rigan ki registration duk da talaucin mu."
Ajin yayi shiru ana kallon su, karo na farko Nurayyah ta maidawa walida magana Wanda ya bawa kowa mamaki a class ɗin musamman fadila, Walida ta fusata, fuskarta ta yi ja taji kunya tace "Zaki gani! Yar matsiyata kawai!"
Daidai nan, malamin lissafi (Maths teacher) ya shigo, kowa ya nutsu, a zuciyar Nurayyah, ta san wannan fadan yanzu aka fara shi, tasan halin walida tasan bazata haqura ta kyaleta ba, rayuwarta a Queen Amina ba karamin kalubale bane, ta sani tana da kwarin gwiwar cewa wata rana, hazakarta zata sa Jaddi tayi alfahari da ita, bata damu da yin kuɗi ba, damuwarta kawai talaka ya sami ƴanci aduk inda ya sami kansa.