4
by @pherty001
ƙararrawar da nayi qara ke nuna lokacin tashi breakfast yayi sautin ta ko ina kake jin sa, wanda hakan ya sanya ɗalibai suka soma surutu cikin murna da saba wa juna yayin da kowa ya kama shirin fita waje domin shan iska ko siyen abin da zasu ci, cikin lokaci qanqani ɗaliban ajin suka fice ɗaya bayan ɗaya har ajin ya rage qalilan mutane ne kawai aciki, banda Nurayyah dake zaune a kan kujerarta ba bu inda zata je kuma babu alamar ma zata fita cos gyara littafin ta tayi tana cigaba da karatu tana ƙoƙarin nutsar da tunaninta gaba ɗaya a cikin karatun domin ta manta da yunwar dake ƙalubalantar cikinta a daidai wannan lokacin kuma ta sani yunwa tana damun tane saboda qamshin abincin wasu da take jiyowa shiyasa sau da dama take ficewa daga class taje wani guri daban inda ba kowa ta zauna har sanda zaa gama breakfast a dawo aji.
Bayan wani lokaci mai tsawo da aka ɗauka ana hidimar break, sai ga su Waleeda sun dawo ajin tare da ƙawayenta suna takunsu na nuna isa da jin wasu shegu ne, hannunsu maƙare da kayan abincin da suka siyo da suka haɗa da snack boxes, meat pies, da manyan gwangwanin drinks da chilled water, Waleeda ta tsaya a tsakiyar ajin tana kallon Nurayyah da har yanzu take duƙe kan littafi, ta gatsine fuska tare da watsa mata wani kallo na tsantsar raini da ƙasƙanci kafin ta juya ta dubi Amira ƙawarta ta ce da babbar murya "I am highly surprised yadda wasu mutanen suke jure biyan wannan expensive school fees na makarantar nan amma kuma abincin da mutum zai ci, ordinary lunch money a rasa kashin da za a ba shi ya siya", Amira da sauran ƙawayen Waleeda suka kwashe da wata shegiyar dariya suna taya ta maganganu masu zafi da cin mutunci waɗanda suka soki zuciyar duk mai sauraro, Nurayyah ta nuna juriya ta musamman domin ko kallon sashen da suke ba ta yi ba, ba ta kuma ɗaga kanta daga kan littafin ba koda kuwa na sakan guda ne duk da yadda maganganun suke dukan ƙirjinta babu ma wanda zai yi tunanin da ita suke sai wanda ya san dama akwai ƴar tsama a tsakanin ta da Walida.
Ana haka sai ga fadila ta shigo ajin ɗauke da nata kayan abincin da ta siyo masu yawa, ta nufi teburin Nurayyah kai tsaye ba tare da ta bi ta kan su Waleeda ba, ta zauna a kan kujerar dake gaban desk ɗin Nurayyah sannan ta soma cirewa Nurayyah nata abincin daban ta ajiye mata a gabanta kafin ta cire nata ita ma ta shirya shi, Nurayyah ta ɗago kai a hankali ta dubi fadila a lokacin da idanunta suka yi rau-rau sun cika da ƙwalla tamkar za ta fashe da kuka saboda tsantsar cin mutuncin da su Waleeda suka gama yi mata a yanzun nan. Fadila ta lura da yanayin fuskar aminiyar tata, ta tsura mata idanu cike da damuwa tana faɗin "Me ya faru kuma my dear? naga idanun ki sun yi jawur lfy", Nurayyah ta girgiza kanta da sauri ta goge fuskarta tace "Ba komai kawai ƙura ce ta shiga idona", fadila ba ta gamsu ba amma sai ta soma rarrashinta ta hanyar tura mata abincin gaba tace "Just eat your food kafin mu fara wani darasin", Nurayyah ta girgiza kanta cikin wani raunin murmushi na yaƙe tace "A'a nagode sosai fadila", jin haka ya sanya fadila ɓata rai lokaci guda tana kallon ta da wani irin yanayi na bacin rai kafin tace "Meyasa kike min haka kowane lokaci? Kin gode kamar yaya?"
A sanyaye Nurayyah ta saukar da kanta ƙasa tace "Kuɗin abincin naki ne fadila, bai kamata kina kashe kuɗinki kina siya min abinci a kowace rana ba, you are always modernizing everything kina ɗorawa kanki nauyina wanda sam ba na jin daɗin hakan", fadila ta sake ɓata rai ta harzuka tana mata wani kallo mai cike da tuhuma kafin tace "Au ashe ma ba kya jin daɗin hakan ban sani ba, I thought ni da ke aminan juna ne, I thought yadda na ɗauke ki a zuciya ta haka kema kika ɗauke ni, ko ni na gaya miki kuɗin da ake ba ni a gida baya isana ne or what? Kin ga malama don't ruin my mood today, maza ɗauki kayanki kici, idan har kinsan ina da matsayi a zuciyar ki kada ki sake kallon abuna a matsayin ba naki ba, just consider everything I have as yours tunda muna tare", Nurayyah ta ji daɗin kalaman fadila sosai, ta jinjina kanta cike da godiya kafin ta ɗauki snacks ɗin ta soma ci a hankali tana jin wani sanyi dake ratsa ranta saboda dama can yunwa take ji a cikinta.
Suna cikin haka, sai suka ji daga bayan su an soma tafi da wata irin shewa ta keta ana faɗin "Haba dai, even the food sai an siya mata sannan take samu ta ci, wataƙila kuɗin makarantar ma bara iyayenta suke yi a gari kafin su haɗa a biya mata, ko kuma taimako ake nema mata a social media gurin masu kuɗi", Waleeda da ƙawayenta suka sake fashewa da dariya suna kallon sashen su Nurayyah cikin alamun gori da baƙar magana. Fadila ta matso kusa da Nurayyah ta ce da ita cikin ƙasa-ƙasa da murya "Please don't pay attention to them, kada ki sake ki kula su koda da kallo ne, karatu aka turo ki kiyi a makarantar nan kuma shi kika zo yi ba neman faɗa ko jure gori ba, and everything will soon come to an end tunda mun kusa kammala karatunmu gaba ɗaya watarana sai labari, Allah kaɗai ya san waye zai ci moriyar karatun nan a nan gaba", Nurayyah ta jinjina kanta da sauri ba tare da ta ce uffan ba kodayake har cikin ƙasan zuciyarta tana jin zafi da raɗaɗin abinda Waleeda da friends ɗinta suke mata a gaban daukacin ɗalibai.
Babu jimawa bayan ɗalibai sun gama dawowa ajin jiran malamin darasi na gaba, sai ga Principal ya shigo cikin ajin nasu da wani irin taku na natsuwa, ajin suka miƙe tsaye suka gaishe shi cikin girmamawa da nuna ladabi na ɗalibai da jiran umarni domin su zauna. Bayan ya ba su umarnin zama, ya gyara tsaiwarsa a gaban allon gaba ya fara magana cikin harshen turanci mai nuna kwarewa yace "Good afternoon class, as usual every year we select two top students who have the highest scores in their final examinations to process a full scholarship for them to study abroad for higher education, and this year we are going to look into the performance and pick another two qualified students", Jin abinda ya faɗa ya sanya ajin aka ɗauki tafi na farin ciki da sowa. Ya ci gaba da ba su shawarwari masu amfani akan su dage su yi karatu da kyau su fuskanci jarrabawa mai zuwa, sanda ya gama jawabi zai tafi ɗaliban su ka masa godiya ya fice daga ajin.
Bayan fitar Principal ɗin, sai ajin ya ɗauki wata irin hayaniya da sowa ta farin ciki, domin kusan class ɗin an riga an san mutum biyu ne kawai suka fi dacewa da kuma samun wannan dama ta scholarship ɗin, wato Faith da kuma Nurayyah, waɗanda sune suka fi kowa ƙoƙari da fasaha a ajin gaba ɗaya. Nan take abokan karatunta da dama a ajin waɗanda suke ƙaunarta kuma suke son ta sami wannan tallafi na karatu suka soma tururuwa zuwa gaban desk ɗinta suna taya ta murna da faɗin "Congrats Nurayyah, you really deserve it" tun kafin ma lokacin ya cika, saboda a lissafinsu har sun gama ganin ta riga ta samu scholarship ɗin ma, yayin da a ɓangare ɗaya Waleeda da ƙawayenta dake zaune a can baya suka haɗe rai fuskokinsu babu ko digon murna, suna kallon yadda ƴan aji suke nuna farin ciki ga Nurayyah cikin takaici da baƙin ciki.