5
by @pherty001
*RIGAR ARO*
©️Fertymerh Xarah💞
5
Aka buga qararrawar da ke sanar da ɗalibai an tashi daga makaranta gaba ɗaya na wannan ranar, harabar makarantar ta cika da hayaniyar ababan hawa da kuma ɗalibai da suke ta tururuwar fitowa waje, fadila da Nurayyah suka fito tare har zuwa babban gate ɗin makarantar inda qanana da manyan motocin na iyayen yara suke fake suna jiran fitowar yaransu, Nurayyah ta tsaya a gefen titi tana jiran isowar motar gidansu fadila, yayin da fadila take tsaye a gefenta saboda dama hakan suke yi, kullum idan aka tashi daga makaranta sai direban gidan su fadila ya zo ya ɗauke su sannan su fara biyawa ta unguwar su Nurayyah su sauke ta a kofar gida kafin fadila ta wuce gida, wannan karamci da kyakkyawar dabi'a ta fadila tana ɗaya daga cikin abubuwan da suke ƙara dankon soyayya da amana a tsakanin abokanan guda biyu.
Suna tsaye a wurin suka ga fitowar wata Latest Range Rover Sport kalar baƙi mai sildin glass, ko ba'a faɗa ba sun san ta gidan su Waleeda ce kusan kullum da ita ake kawo ta kuma ake xuwa daukarta, motar ta zo daidai inda Nurayyah take tsaye a gefen titi, Waleeda ta danna maɓallin motar ta sauke glass ɗin da yake gaban kujerar da take zaune, ta zuro fuskarta waje ta dubi Nurayyah da wani irin kallo mai cike da tsantsar raini, tsana, da kuma wulaƙanci wanda ya isa ya sa mutum jin zafi a ransa, Waleeda ba ta ce komai ba illa tayi mata wata shu'umar harara mai nuna ƙasƙanci ga rayuwar Nurayyah kafin ta sake danna maɓallin ta mayar da glass ɗin motar sama, driver ya ja motar da wani irin gudu wanda da alama Walida ta bashi umarninyin haka.
Nurayyah ta bi motar da kallo cikin sanyin jiki da rauni, tana jin wani irin ba daɗi da radadi dake ruruwa a tsakar zuciyarta akan yadda Waleeda take yi mata abubuwa na rashin mutunci da cin zarafi a kowane lokaci ba tare da ta yi mata komai ba, koda yaushe tana jurewa tana haɗiyewa domin karatu ne kawai ya kawo ta gurin, fadila da ta lura da yadda aminiyar tata ta kafawa motar ido cikin damuwa, ta juyo ta dube ta da wata irin kulawa tace "Nurayyah, if you keep stressing yourself akan waccan marar mutuncin kuma marar hanksli, you are just hurting your own feelings for nothing, ire-iren su sam ba sa gaban fuskata saboda kowa a makarantar nan ya san zallar bakin ciki da pure jealousy ce kawai suke yi a kanki saboda ƙoƙarinki da daukakar da kike da ita a aji", Nurayyah ta ja wani dogon numfashi na juriya ba tare da ta ce komai ba a daidai lokacin da motar gidan su fadila Mercedes-Benz S-Class ta zo ta faka a gabansu, direban ya fito cikin sauri da ladabi ya buɗe musu kofa suka shiga tare suka zauna a kan lafiyayyun kujerun fatar motar.
Bayan direban ya shafe lissafin nisan dake tsakanin makarantar da unguwar su Nurayyah har ya kawo ta kofar gidansu ya faka motar, Nurayyah ta juyo ta kalli fadila da wani kyakkyawan murmushi dake bayyana irin godiyar dake ranta tace "Thanks ƙawata, I really appreciate everything you do for me", fadila ta gyaɗa kanta cikin nuna jin daɗi tana murmushi tace "You're welcome, take care of yourself", kafin direban ya ja motar suka wuce da gudu. Nurayyah ta juyo ta shiga cikin gidansu da wani irin sabon kwarin gwiwa, natsuwa, da kuma karsashi dake ruruwa a jikinta gaba ɗaya, domin tana jin wani babban farin ciki na son baiwa Jaddi gagarumin labarin scholarship da aka sanar a makaranta yau, ta sami Jaddi ta gama girka abinci tana kwashewa a inda suke ajiye abincin da zai kaisu har dare su ci.
Nurayyah ba ta tsaya wata-wata ba ta ruga da gudu cikin zallar farin ciki ta je ta rungume Jaddi ta baya da dukkan ƙarfinta, tana wata irin dariya ta nuna murna tamkar a ranar ne aka yi mata albishir da cewa ita ce ta sami wannan gurbin karatu na zuwa ƙasar waje, ta matse kakar tata sosai a jikinta tana jin kuncin da take sha a hannun su Waleeda duk ya kau sanadiyar jin ta a jikin kakarta. Jaddi ta ɗan firgita da rungumar ta ba-zata, ta juyo da ƙyar tana kallonta dafe da ƙirjinta, ta dube ta cikin rauni da tana faɗin "Nurayyah, kinsan fa ba lafiya ce da ni ba a kwanakin nan, kada ki kada ni ki kashe min kashin baya da babu sauran ƙwari a jikin nawa yanzu, wannan wane irin farinciki kike yi haka mai cike da hauka, me ya faru ne dake yau a makaranta kika fado min a jiki?"
Nurayyah ta saki murmushi cike da kaunar Jaddi ta soma taya Jaddi ɗaukar abinci zuwa ɗaki saboda ta rage mata aiki, bayan ta gama kwashe abinci ta gyara wurin da Jaddi tayi girki, ta cire kayan makarantar kafin ta sanya na gida mash sauƙi, ta dawo kusa da Jaddi inda ta zauna a ƙasa a ƙafafunta, ta soma ba ta labarin sanarwar da Principal ya yi a makaranta game da scholarship akan zuwa ƙasar waje wanda acan zata yi karatun likitanci ta cika burin su, idanun Jaddi suka cika da wani irin haske na farin ciki wanda ya zarta na matashiya, ta zaro idanu tana kallon jikarta da take gani tamkar wata tauraruwa mai haske a cikin rayuwarta, ta sanya hannayenta tana shafa kan Nurayyah tana addu'a Allah ya ba ta sa'a ta samu wannan kujerar, cos a wurinta wannan ita ce mafi girman nasara da zai iya samun ɗiyar talakawa mai burin zama ƙwararriyar likita da zata canza rayuwar talakawa a wannan ƙasa, Jaddi ta soma yin ƙwalla masu zafi, ba ƙwallar baƙin ciki ba, amma ƙwallar tunanin cewa gaba kaɗan zata yi matuƙar kewar Nurayyah, tana tunanin yadda zata zauna ita kadai a gidan ta kwana ita kaɗai babu Nurayyah a tare da ita dole zata shiga damuwa sosai ta sani, Nurayyah kaɗai take gani taji sanyi a ranta, itace dangin ta da take dasu acikin Kaduna sauran duk suna qauye.
Nurayyah ta lura da yadda idanun Jaddi suke zub da ƙwalla, nan take farin cikinta ya gauraye da wani irin damuwa, jikinta ya yi sanyi tamkar an watsa masa kankara, ta matsa kusa da ita tana tambayar ta cikin murya mai rauni da tausayi "Jaddi lafiya kike hawaye? Jikin ne ya tashi ko kuma wani abin ne yake damunki mu tafi asibiti yanzu nan?" Jaddi ta girgiza kanta a hankali, ta share hawayen da suke gangarowa kan kuncinta, ta kamo hannun Nurayyah tana faɗin "Zan yi kewar ki sosai Nurayyah, kece sanyin idaniya ta, ke kaɗai ce jinin da nake gani a kullum nake jin farinciki a raina, idan kika tafi wacece zata kula da ni? waye zan gani na ji sanyi a raina a wannan gida da nake jin kamar zai cinye ni da shiru idan babu ke?"
Jin wannan maganar ya sanya gwiwowin Nurayyah yin sanyi suka sage, duk wani farin ciki da take ji na nasarar scholarship ɗin ya gushe a lokaci ɗaya, ta ji tamkar duniya ta tsaya cak, ta kalli kakar tata da idanuwa masu cike da ƙwalla tana cewa "Jaddi wallahi na fasa zuwa idan har zaki shiga damuwar rashina, ina so kullum mu kasance tare, zan shiga makarantar a nan ƙasar na yi karatuna anan ba sai naje ba ki bar kukan ki bar damuwa dan zan tafi na fasa tafiya kinji, ba sai na yi nesa da ke ba, ba zan iya jure ganin kina kuka ko kina jin kaɗaici cos ke ce rayuwata, ba tare da ke ba, ba kowa bace ni a duniyar", Jaddi ta matse hannun Nurayyah sosai, ta ƙago wani murmushin yaƙe domin ta ƙarfafa mata gwiwa ta ce "Duk yanda nake son kaina, na fi son cigaban ki fiye da yadda zaki iya tunani, abu ɗaya nake so ki yi min a rayuwa idan kin je wannan ƙasar, kada ki manta da tarbiyar da na ba ki, please kada ki gurbata rayuwarki akan tarbiyar da na ba ki, idan kika tsare kanki da mutuncin ki, tabbas zan fi kowa farin ciki da nasararki, ina miki fatan alheri, zan yi alfahari da ke ko a ina kika kasance".
Nurayyah ta ja numfashi mai nauyi, ta riƙe hannun Jaddi sosai tana kallon zurfin idanunta tana faɗin "Nayi miki alƙawari, ba abinda zai canza daga tarbiyar da kika ba ni, kuma zan yi karatu na cika miki burinki na zama irin likitar da kike son ganina, Jaddi ba za a ƙara wulaƙanta min ke a asibiti ba, ba za ki sake bin wannan layin da ake cutar da talakawa ana nuna ba su da daraja ba, ba za ki sake zubar da hawayen ƙunci saboda zaluncin nurses ko likitocin da ba su da tausayi ba, bama ke kaɗai ba, duk wani talaka zan tsaya a kansa matuƙar ni ce wacce zata duba lafiyar su, zan zama likitar da zata mayar da kowa ɗaya, zan zama muryar waɗanda ba su da murya a asibitoci", Jaddi ta ɗan murmusa cikin farin ciki, ta shafa kan jikar tata tana sanya mata albarka wanda ke shiga zuciyar Nurayyah kamar wani ruwan sanyi, kafin Nurayyah ta tashi ta debi abinci don su ci tare, suna tattauna yadda rayuwarsu zata kasance a nan gaba da yadda zasu yi kewar juna, cike da fatan scholarship ɗin zai zama babban matakin da zai fitar da su daga cikin kuncin rayuwa zuwa ga yalwa da daraja.