6
by @pherty001
*RIGAR ARO*
©️Fertymerh Xarah💞
6
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya tamkar walƙiya yayin da kwanaki da makonni suka riƙa shuɗewa kamar ƙiftawar ido, ɗaliban makarantar suka soma shiri suna fuskantar jarrabawar kammalawa ta ƙarshe wadda ita ce zata zama babban mizanin da zai raba tsakuwa da tsabar hura, a wannan lokacin ne Nurayyah ta ƙara duƙufa da dukkan ƙarfinta da hankalinta gaba ɗaya wajen yin karatu dare da rana, ba ta da wani babban buri da ya wuce ta ga ta samar wa kanta wannan gurbin karatu na kyauta zuwa ƙasar waje domin ta canza rayuwar kakar ta, duk dare tana kwana tana sallah tana kuka tana roƙon Allah ya dafe mata ya ba ta nasara mafi girma, duk da a daidai wannan lokacin tana cigaba da fuskantar matsaloli da ƙalubale masu yawa daga ɓangaren Waleeda da ƙawayenta da suka ƙaru fiye da kowane lokaci, ba sa fashi wajen jifa da ita da kalaman soki-burutsu da gori a duk sanda suka ganta tana karatu, suna kiranta da sunan mai kwadayin da ba zai taɓa kaiwa gaci ba, koda yaushe suna ƙoƙarin ruguza mata mood ɗinta na karatu ta hanyar nuna cewa talaucin gidansu ba zai taɓa barinta ta tsallake ƙasar nan ba koda kuwa ta rubuta jarrabawar da jini ne, amma duk da wannan tsanani na zuciya da karayar da suke saka mata bai saka Nurayyah fasa karatun ta ba, ta sanya juriya ta dake ta riƙe addu'a a matsayin babban makaminta na yau da kullum.
Cikin ikon Allah aka soma jarrabawa kuma aka kammala ta cikin nasara gaba ɗaya, bayan an idar da kowane sashe na jarrabawar aka shiga shirin gudanar da bukukuwan kammala karatu na ɗaliban sakandare, wanda al'ada ce ta makarantar gudanar da Graduation Ceremony da Prom Night na inda ɗalibai suke sanya daddalan gajerun riguna da kaya domin murnar party, ana gudanar da dinner da raye-raye gami da raba lambobin yabo na musamman ga waɗanda suka yi fice a fannoni daban-daban na rayuwar makaranta, duk kusan rabin kyautukka Nurayyah ce ta karɓa, wurin ya kasance cike da nishadi da kuma kukan bankwana tsakanin abokan juna waɗanda suka shafe shekaru tare.
Bayan wasu kwanaki da kammalabukukuwa na ban kwana da suka yi, ranar da kowa yake jira ta zo, ranar fitar sakamakon jarrabawa (final results). Nurayyah ta tafi makarantar zuciyarta tana dukan uku-uku cike da fargaba da kuma kyakkyawan zato duk da tana tunanin insha Allah zata ci kyautar zata samu, sai dai kash, a maimakon a nuna cewa Nurayyah ce ta zo ta farko ko ta biyu kamar yadda makarantar suka sani kuma suka zata, sai aka ba ta matsayi na uku gaba ɗaya, ma'ana an ɗauki maki (scores) na ƙoƙarinta an juyawa Waleeda su aka rubuta a sunanta, aka bayyana cewa Waleeda ce ta cancanci wannan gurbin na scholarship ita da Faith, wanda hakan yana nufin sunan Nurayyah baya cikin waɗanda makaranta zata ɗauki nauyinsu zuwa ƙasar waje.
Nan take hankalin Nurayyah ya tashi matuƙa, wani irin jiri mai tsanani ya kwashe ta, numfashinta ya kusa tsayawa cak saboda tsantsar rashin adalci da cutarwa dake bayyane gaba ɗaya, bama ita kaɗai ba amintattun abokan karatunta dake tare da ita a kullum sun shiga cikin damuwa domin sun sani sarai an tafka mummunan zalunci an cutar da ita aka ba Waleeda wadda ba ta taka rawar gani ba a rayuwar karatunta, Nurayyah ta fashe da wani irin matsanancin kuka mai ban tausayi, hawaye masu zafi dake bayyana kuncin zuciyarta suka riƙa zuba ba ƙassaba, fadila ita ma ta fashe da kuka mai raɗaɗi tana taya aminiyar tata kukan baƙin ciki da rashin adalci na rayuwa, suka zauna a wani sako na ajin suna kuka tare tamkar waɗanda aka yi wa mutuwa, cikin rarrashi da muryar kuka fadila ta juyo ta dubi Nurayyah tace "Kada ki bari wannan abin ya kashe miki gwiwa gaba ɗaya my dear, ko za mu je mu tambayi malam Sirajo mu ji meyasa aka yi miki wannan rashin adalcin, a ina ne kika sami matsala a cikin jarrabawar naki da har Waleeda ta fiki maki bayan kowa ya san ƙoƙarinki kuma kowa yasan Walida bata da wannan qoqarin?"
Nurayyah ta ɗago idanuwanta waɗanda suka kumbura suka yi jawur tamkar wuta saboda kuka da ta sha, ta kasa cewa komai saboda yadda makwarwaron muryarta ya toshe da kuka, amma a cikin ranta ta gamsu da shawarar fadila domin tana tunanin ko wani kuskure ne na sunaye aka samu wajen tsara sakamakon jarrabawar, ta tashi a sanyaye jikinta babu kuzari ko kaɗan suka nufi ɓangaren ofisoshin malaman makarantar, fadila ta dake ta share hawayen dake fuskarta sanda suka kusanci ofis ɗin, ta juyo tana kallon Nurayyah cikin tsantsar tausayi tare da sanya gefen mayafinta tana share mata nata hawayen tana ƙarfafa mata gwiwa, ta kama hannunta dake rawa suka tura kofar tare da yin sallama mai rauni a bakinta.
Malam Sirajo yana zaune a kan kujerarsa yana duba wasu ayyuka (assignments) na wasu sauran ɗalibai sanda suka shigo cikin ofis ɗin, yana ɗaga kai ya haɗa ido da Nurayyah da idanuwanta suka yi jawur suka kumbura saboda kuka, sai da zuciyarsa ta girgiza ta karaya saboda ya san asalin ƙoƙarinta da yadda take da mutunci a gurin kowa kuma ya san an zalunci yarinyar saboda bata da gata bata da wanda zai kare haqqin ta sai Allah, suka gaishe shi cikin girmamawa da ladabi kafin fadila ta dake ta soma magana cikin muryar dake rawa tamkar za ta fashe da kuka tace "Dama malam, mun zo ne mu ji ko Nurayyah ta sami wata matsala ce a cikin jarrabawarta da ta sa ba ta sami scholarship ɗin ba bayan kowa ya san itace sawun farko da zata samu", Malam Sirajo ya zubawa teburinsa ido, fuskarsa ta bayyana tsantsar damuwa da bacin rai na abinda ya faru wanda yake jin ba shi da ikon canza shi, ya ja wani dogon numfashi mai nauyi dake cike da takaici kafin ya ɗago kai ya dubi Nurayyah cikin wata murya mai cike da tausayi da kuma rauni ya soma magana cikin sanyin jiki.
ya ce "Nima tun da naga an fitar da list ɗinnan na shiga damuwa sosai, bama ni kaɗai ba har sauran malamai da suka san ƙoƙarinki da hazakar ki sun damu matuƙa, a gaskiya babu inda kika faɗi a jarrabawarki, in fact you are the overall best student a ajinku gaba ɗaya saboda maki (marks) duka da kika samu sun fi na Faith Nbolu yawa, kuma kin ai kin sami gifts da yawa a best subject da sauran su, abu ne da bamu san yadda aka yi aka canza shi ba tunda shi wannan scholarship ɗin kai tsaye daga ofis ɗin Principal ya fito, kuma na tuna na taɓa ganin mahaifin Waleeda ya zo ya same shi a ofis ɗinsa makonni biyu da suka gabata tare da ita walidar".
Nurayyah ta lumshe idanuwanta cikin tsantsar ƙunci da baƙin ciki, zuciyarta tana wani irin zafi mai tsanani jin yadda aka tauye haƙƙinta na gumi da aka bayar ga wata can daban kawai don saboda mahaifinta wani jigo ne mai dukiya da iko a gari, ta kasa cewa komai saboda yadda wani abu mai nauyi ya tsaya mata a makwarwaron muryarta, ta juya da gudu ta bar ofis ɗin tana kuka mai cin rai, wanda fadila ma ba ta tsaya sake yiwa malamin wata magana ba ta bi bayanta da sauri cikin tsananin fargaba, Malam Sirajo ya bi bayansu da kallon tsantsar tausayi domin ya san an zalunci yarinyar zalunci mafi muni. Nurayyah dake kuka a waje kamar ranta zai fita, tana ganin fadila ta faɗa jikinta ta ƙanƙame ta da dukkan ƙarfinta tana wani irin kuka na fitar rai, cikin muryar kuka mai ban tausayi tace "Me nayi mata fadila? Me yasa take son ruguza farin cikina da burina na rayuwa? Menene laifina a nan duniya? Dan na fita kyau ni na ba kaina? Ko dan na fita ƙwaƙwalwa da basira ni na baiwa kaina? Shin laifi ne don talaka ya jajirce wajen neman ilimi tare da yaran masu kuɗi? Duk saboda wannan Waleeda ta tsane ni ba don na taɓa yi mata wani laifi ba".
fadila ta rungume ta ita ma tana zubda hawaye, tana ba ta haƙuri da kalamai masu sanyaya zuciya tana cewa "Please calm down my dear, kiyi haƙuri kuka ba zai magance komai ba", da ƙyar Nurayyah ta ɗan tsagaita da kukan, fadila ta zaunar da ita a kan wani dakali tana faɗin "Bara na samo miki ruwa ki wanke fuskarki sai muje gida ki huta kin ji?" Nurayyah ba ta iya magana ba sai dai ta gyaɗa kanta a sanyaye, fadila ta juya da sauri ta tafi nemo ruwan. Bayan tafiyarta da ɗan lokaci kaɗan, sai ga Waleeda da ƙawayenta sun zo gurin cikin takun isa da gadara, suka tsaya a gaban Nurayyah suka soma wata dariyar shaqiyanci da mugunta, Waleeda ta gatsine fuska tace "Kin gan ki yadda kika koɗe kika yi wani jajur dake saboda ordinary scholarship na banza? Kece kika damu da shi ƴar talakawa, dama baku da arzikin karatu a jinin ku uban waye yace kizo kiyi makarantar masu kuɗi? Meyasa baki je kinyi karatu irin na koyarwa a islamiya ba domin da shi kika fi dacewa tunda can ne ajinki".
Nurayyah ta ɗauke kanta gaba ɗaya ba ta yi magana ba saboda wani ƙunci da nauyi da zuciyarta ta yi mata, Waleeda ta ƙara matsowa gabanta tace "Kin san waye Babana a garin nan? Babban ɗan siyasa ne mai faɗa a ji, scholarship a wurin mu abin banza ne, har na alfarma na kyauta muna da su a gida, kin ga friends ɗinna nawa yanzu haka na saka Daddy ya ɗauki nauyin karatunsu a ƙasar waje daidai inda zanje yin nawa karatun nima, so na saka Daddy yazo ya karɓe scholarship ɗinnan ya biya Provost kuɗi masu yawa ya cire sunanki ya saka nawa saboda kawai na ƙuntata miki na nuna miki ke ba komai bace, babu inda zaki je zaki zauna anan cikin talauci kina kallo na, I just hate you duk sanda na dubi irin kyawun da kike da shi wanda da ni ya dace a matsayina na ƴar mai kuɗi, a hakan ma wai kina talaka, idan kika sami rayuwa tayi maki daɗi ban san yadda zaki koma ba, bana burin ganin kin sami cigaba a rayuwa, ki mutu a wulaqance kuma a talauce yanda kika zo duniya".
Waleeda ta ƙarasa maganar fuskarta ta sauya kamar zata yi kuka saboda tsantsar baƙin ciki da kishin yadda Nurayyah ta fita komai na halitta da basira, Nurayyah ta ci gaba da zama a dunkufe ta sunkuyar da kanta ƙasa tana jin baqaqen maganganun dake fitowa daga bakinta, Waleeda ta nuna ta da yatsa tace "Wallahi a garinnan ma ba zan barki ki ci gaba da karatu ba koda bana ƙasar, zan saka Uncle Hamza ya hana ki admission a kowace jami'a tunda shi ne mai bayarwa, zaki gane kin taɓo wadda ta fiki, banza shashasha talaka kawai, kuma wallahi da ace anan ƙasar zan zauna sai na cusgunawa rayuwarki na hana ki jin daɗi, kuma sai na saka kin auri ƙasƙastancen mutum because I will never allow you to succeed, ke da yaran da zaki haifa zaku rayu aciki wahala", ta yi tsaki mai sauti "Mtsww" sannan ta juya ta fice cike da ƙunci yayin da ƙawayenta suka kece da dariyar wulaƙanci suna bin Nurayyah da kallo kafin su bi bayanta.
Nurayyah ta bi su da kallo a sanyaye har suka ɓace wa ganinta a daidai lokacin da fadila ta dawo ɗauke da ruwa, ta mika mata ta wanke fuskarta sannan ta tashi tsaye jikinta duk a sanyaye, fadila ta dube ta cikin tausayi tace "Da ace ina son karatu a waje da zan ma Daddy magana ya biya mana tare muje, amma kiyi haƙuri mu ci gaba da karatun mu anan ƙasar, kinga Jaddi idan kika je kika barta a yanzu waye zai kula da ita?" Nurayyah ta ja numfashi idanunta cike da sabbin hawaye tace "Ina jin ma ba zan ci gaba da karatun jami'ar nan ba gaba ɗaya, wannan karatun da na yi zuwa yanzu Allah zai sanya masa albarka, iya secondary ɗin ya ishe ni tun da zan iya rubutu da karatu.
fadila ta ɓata rai sosai ta riƙe kafaɗarta tace "Ya zaki cire hope haka da wuri saboda an ƙwace miki scholarship? Ai ba nufin shikenan kin yafe karatun ki saboda wata Waleeda ba, kina da babban buri na zama likita meyasa lokaci ɗaya zaki fasa?" Nurayyah ba ta iya cewa komai ba sai ta soma tafiya saboda zuciyarta dake mata nauyi, fadila ta bi bayanta da sauri tana faɗin "Sam ba zai yiwu ba, dole tare zamu ci gaba da karatun nan koda a nan ƙasar ne, idan kuma kika ƙi wallahi nima ba zan yi ba". Nurayyah ta tsaya ta juyo ta yi mata wani kallo na tsantsar mamaki, ta dubi ƙwayar idanun fadila ta ga tabbas da gaske take yi ba da wasa ba, ta sauke kanta ƙasa a sanyaye ta ci gaba da tafiya yayin da fadila ke biye da ita su duka jikinsu a sanyaye cikin yanayi na damuwa.