Chapter One
by @suttie0
Zaune take a katafaren office ɗinta, tana duba sashen customer review a app na restaurant ɗinta da Tablet ɗinta ƙirar Samsung Galaxy S10+ a hannu. Sassanyan kamshin turaren wuta mai kwantar da hankalin mai jinsa yana tashi a hankali, ya ɗabaibaye lungu da saƙon ofishin. Haɗe da kamshin turarenta na Chanel Coco Madmoiselle dake tashi a hankali daga dogon rigar jikinta kimono-style datake sanye dashi, akan plain cream inner dress ɗinta ƴar ciki. Tayi nisa a karatun tana jin daɗin reviews da suke samu, tana kuma ɗaukan complains da suggestions daga customers. Hayaniya ta ɗan fara ji yana tashi daga wajen ofishin, amma ba daƙarfi sosai ba, sai taji ana ƙwanƙwasa ƙofarta.
"Excuse me Ma, your attention is needed please."
Ajiye Tab ɗin Imaani tayi, ta gyara cream Pashmina veil ɗinta dake kafaɗunta. Fuskarta naɗe yake da chiffon veil wanda ya dace da kayan jikinta, "I'll be there in a bit."
"Okay ma," aka amsa daga waje.
Kwanikan abinci (crockery) da tayi amfani dasu ta haɗa kafin takai owners kitchen dake haɗe da danƙareran ofishinta, da nufin idan ta dawo zata wankesu. Tana buɗe ƙofar ofishinta muryar mace taji daga General Dining Arean restaurant ɗin tana ɗaga murya da zage zage. Imaani tayi rolling manyan idanuwanta kafin ta ƙarasa wurin cikin kosawa da halin customers marasa kamun kai.
Ɗaya daga cikin waiters ɗinta ne a tsaye ya dage sai bada hakuri yakeyi ma wata mace, a ƙalla zatayi shekarunta ko ta fita da kaɗan, amma kaman ma kara tunzura matan yakeyi, wanda kayanta duk suka ɓaci da sauce ɗin abinci.
Receptionist ɗinta ne yafara ankara da zuwanta, "Yawwa ga General Manager ɗinmu ta iso, kiyi hakuri dan Allah tsautsayi ne."
"Bura uban tsautsayi ne, ko bashi da idanuwa ne dabai ganni a wurin ba." Matar ta faɗa a fusace, ta juya kan Imaani ta kalleta sama da ƙasa tana kissima wannan kalar kuma daga ina amma bala'i ya rufe mata ido. "Hala mahaukata da makafi kuke ɗauka aiki a wurinnan, wanda basu san hospitality da darajan customers ba."
Cikin natsuwa Imaani ta amsa ta, "Ba makafi ko mahaukata a restaurant ɗinnan kuma koda akwai su kuwa suna da darajan ayi musu afuwa da uzuri tunda ƴan Adam ne kuma ajizai ne."
Kafin matar ta furta wani abu wani customer da yake observing incident ɗin tundaga farko ya ce, "Itace fa ta bugeshi tana tafiya hankalinta yana kan waya shi kuma ya fito daga kitchen baima lura da tashinta ba daga kujera."
Wata mata ma tace, "Nima dai haka nagani, itace taci karo dashi ba shi ya bugeta ba."
Aiko matar ta ƙara tunzura, "Akan me zaku ce haka, tayaya kuka san abinda ya faru, naga dai kowa anan abinci yakeci inbanda sa ido a abunda ba ruwanku. Ko sabida ba jikinku aka yima wanka da abinci ba." Ta ƙarasa tana harare hararen rashin gaskiya.
Imaani tace, "Madam we are very sorry for the displeasure caused, and would like to compensate you by not charging for your meal. A restaurant dinnan muna aiki ne da professional ethics koda kuwa ba laifinmu bane accident ɗin ya faru. Have a good day."
Kaman ta tanka ma Imaani akan gatsen da tayi mata, amma tasan itace da jin kunya tunda ga shaidu kuma duk da haka ance basai ta biya uwar abincin da taci tare da ƙawarta a tsadadden wurin cin abincinnan ba. Tsaki taja ta fisge jakanta daga kan table, wanda ke shimfide da lallausan farin linen tablecloth, "Mufida tashi mu wuce, kawai mutum yazo ya kwashi datti da kayan takaici wai a haka ne restaurant din one in town."
Taɓe baki kawar tayi ta bita suka fice waje.
Sai a sannan Imaani tayi addressing matashin waiter ɗin da shima kayanshi a ɓace yake da abinci, "A rinƙa kula ana kiyayewa Abdul. A kuma ƙara haƙuri."
"Okay ma, bakomai In Sha Allah." Ya amsa yana haɗa kwanukan tangaran na abinci dake watse a ƙasa.
Receptionist ɗinne yasa masu shara su gyara inda abincin ya zuba.
Imaani ta juya zuwa office ɗinta sabida karfe 2:00 PM ya kusa, lokacin kaima Abbu lunch ofishinshi kenan. Akwai delivery men da zasu iya isar da saƙon amma saboda rana yayi, suna samun ƙarancin riders sabida lunch hour ne duk sun fita aiki, kuma tana son zuwa gyaran gashi a Saloon ɗinta, wanda yake area ɗin office ɗin Abbu, sai kawai ta miƙa mishi.
Ƙarasawa owner's kitchen ɗinta tayi wanda yake ɗauke da na'urori na zamani (state-of-the-art equipments). Wannan kitchen ɗin shi ake kira da Chef's Dream saboda babu abunda babu a ciki na abubuwan buƙatan girki da sarrafa abinci.
Wanke kwanukan data ɓata tayi, sai tayi wiping ɗinsu da kitchen clothe ta maida kowanne muhallinsa. Tana fitowa ta shafa handcream bayan ta wanke hannayenta ta gogesu, ta ɗauka wayanta, jakarta na Hermis Birkin da wasu files da suke buƙatan dubawa. Numbern driver, kuma mai kula da lafiyarta (Chauffeur) Mr. Samuel takira don ta sanar dashi fitowarta, ya tabbatar mata yana parking space isowarshi kenan ba da daɗewa ba.
Sallama tayi ma Supervisor na restaurant ɗin wanda ofishinshi ke kusa da nata, ta ƙaraso luxurious Dining Area ɗin, ma'aikata nata shige da fice cikin natsuwa ana serving clients, ƙamshin spices daga sassan duniya daban daban yana tashi yana tsinka yawun mai jin yunwa. Ƙarasa main kitchen ɗin tayi ta amsa lunch basket na Abbu that is ready to go.
Electronic sliding doors (kofofi masu aiki da wutan lantarki) na restaurant ɗin saka bude automatically bayan wasu sun shiga, ta fito haraban tana hango Mr. Samuel cikin professional kayan aikinshi (suit) a wurin silver motarta ƙirar Lexus RX 350 yana jiran isowarta.
"Barka da rana Mr. Samuel."
"Barkanki dai Madame." Ya amsa daɗan fara'a yana buɗe mata kofar motan ta wurin owner's corner.
Imaani na shiga motar sanyin AirCon ya rastata daga ɗan shiga ranan da tayi na taƙaitaccen lokaci.
Mr. Samuel ya kulle kofan ya zagayo driver's seat, "Where are we heading to Madame?"
"Abbu's office." Ta amsa tana duba schedule ɗin Saloon ɗinta ko akwai free time tunda improptu appointment ne. Ta samu akwai tsakanin 4:20 PM zuwa 5:30 PM wanda zai isheta wanke kai da gyarawa.
Mintuna 20 suka isa unguwar Kingsford Business Quarter dake garin Kaduna, wanda yawanci corporate businesses ne sukaci galaba a wuraren kaman dai Wall Street dake New York a ƙasar America. Motar da doshi wani tafkaken baƙin gate da ya fara rabewa automatically, basa buƙatan nuna ID dinsu sabida Lisence Plate Recognition na gates din ya karanta lambar motorsu as registered-to-enter, amma duk da haka Mr. Samuel yayi scrolling windownshi ya daga ma Security hannu saboda tsaro. Wannan tsarin yana daga cikin protocol na shiga koma waye ne kai kuwa sabida a tabbatar da kai dinne.
Wani haɗɗaɗen lafiyayyen building wanke ke maƙale da tambarin Dadan-Garba Chambers suka dosa, mai tsawo da faɗi yaci ya koshi da ma'aikata kama daga Lawyers, Partners, Paralegals, etc masu gudanar da aiki aciki. Ginin office ɗin reshe guda ne na Law Firm (Cibiyar lauyoyi), inda ake gabatarda fannukan Law, irinsu Corporate, Criminal, Property da Family Law.
Mr. Samuel ya tsaya a wurin shiga cikin building din (entrance), wanda yake ɗauke da sliding doors. Ya fito domin ya ɗauka lunch basket ɗin Abbu daga booth, sannan yayi ma Imaani rakiya kamar yadda aikinshi ya kunsa. Mai buɗe kofa (Doorman) dake tsaye a ƙofar ya ƙaraso ya buɗe mata kofar motan yana mata maraba da zuwa.
Imaani ta amsashi da sakkaken fuskar sanayya a tsakaninsu, cikin nastuwa take tafiya, ɗauke da hand bag ɗinta da haɗaɗɗen wayarta ƙirar Samsung Galaxy S25 Ultra. Mr. Samuel ya ƙarasa ya danna madannin elevator da zai ɗaukesu zuwa top floor inda private office ɗin Abbu yake.
Mintuna kaɗan suka isa floor ɗin, sassanyan kamshin turaren wuta da Ammi ke zaɓamma Abbu na office ya bankosu suna fita daga elevator din. Ɗaya daga cikin assistants ɗin Abbu, Adam, wani matashi ne dake zaune a table ɗinshi kusada office ɗin Abbu yayi mata sannu da zuwa.
Mr. Samuel ya ƙwanƙwasa kofar office din, daga ciki aka amsa da, "Come in." Sai ya mika ma Imaani basket din. Tayi mishi sallama ta sanar dashi nan ba da jimawa ba zai ajiyeta a Saloon.
Fuskarta ɗauke da murmushin ganin babanta tayi sallama ta shiga ƙayataccen office ɗin mai girma, wanda akayi designing da cool gray colors. Manyan tagogi daga bene zuwa rufi (floor-to-ceiling windows) ɗin yana nuna view ɗin unguwan daga waje, akwai ƙaton bookshelf a bangon dama wanda yake ɗauke da littattafen Law da framed awards. Ƙaton table na katako ya mamaye tsakiya, sai baƙin kujeran fata ya zauna a bayanshi. Akwai wasu kujerun guda biyu na baƙi (visitors) a gaban table ɗin, sai wani low glass table a tsakaninsu. Hasken rana yana shigowa ta tagogin masu duhu (tinted windows), ga ƙamshi mai dadi yana tashi da sanya nutsuwa.
Abbu ne zaune a wani lallausan kujeran couch a gefen hagu, ya ajiye files ɗinda yake dubawa kafin shigowan Imaani. Dukda shekarunshi na dosan 60 baiyi kamada masu irin shekarunnan ba sabida yana motsa jiki kuma abincinshi lafiyayye ne mai inganci da ƙara lafiya, wanda Ammi take approving mishi kafin yaci. Yana sanye da baƙin three-piece Brioni suit mai farin riga a ciki, ya ajiye baƙin neck-tie a gefe sabida lunch hour ne yana zaman jiran abincinshi. Ya ƙaraso ya sumbaci goshin Imaani da kulawa bayan ya amsa sallamarta.
"Kinbar yunwa zai kashe ɗan fillon Ammi Boɗɗo am."
A shagwaɓe Imaani tace, "Abbu its just half past 2:00pm fa, kuma ai ina hanya ne."
Abbu yayi murmushi, "Shikenan bazan faɗa mata kinbarni da yunwa ba."
"Toh Abbu komai ne saika faɗa mata, kasan faɗa zatayimun fa." Imaani ta faɗa tana ɗan turo baki.
Zaro ido yayi, "You want me to keep stuff away from my wife? In kwana a waje kenan."
Dariya Imaani tayi tana jin daɗin yadda Abbu ke nuna soyayyar da yakema Ammi akoda yaushe, baya shakkan kowa kuma hakan yana ƙuntata ma wasu daga cikin familynshi, suna cewa kudi da asiri sun rufe mishi ido.
Abbu ya numa ma Imaani wasu files a saman table bayan tayi serving ɗinshi, "Ki duba papers dinnan kigani, kayan da mukayi ordernsu weeks ago sun iso suna checkpoint a border. So you've got to sign the papers for approval kafin a kaisu shago."
Ƙarasawa tayi zuwa visitor's chair ta zauna kafin tafara duba papers din, "Abbu is my approval really necessary ba ka rigada kayi signing ba."
Abbu yace, "Common you have to actively participate in your own business from now onwards. Ai kin girma yanzu, I'm not always going to be around to take care of such."
Ƙwanƙwasa ƙofan office din akayi kafin Imaani tayi magana, Abbu ya bada izinin shigowa. Assistant ɗinshi Adam ne ya leƙo kanshi, "Sir baƙin sunƙaraso suna jira a Conference Room."
"Okay bani few minutes, gani nan isowa." Abbu ya faɗa.
"Okay sir." Adam ya amsa ya kulle ƙofan.
Abbu ya goge bakinshi da wet wipes yayi disposing a waste bin. Sai ya shiga bayin cikin office ɗin don yayi freshening up.
Daya fito ya kalli Imaani, "Boɗɗo am zan shiga meeting da wasu clients sai 4:00pm zanfito. Gida zaki wuce ko school?"
Sauke papern hannunta Imaani tayi ta kalleshi, "No zanbiya Saloon in gyara gashina sai inkoma gida."
"Okay tohm stay safe." Abbu ya ƙara sumbatar goshinta in a farewell manner ya fita.
Imaani tayi spending next hour ɗin tana signing tulin paperwork. Normally Abbu ne da Rafeeq suke kulada manyan aspects ɗin businesses ɗinta wanda yana daga cikin gadon ta amma tunda takai shekaru 22, ta fara Master's Programme dinta few months ago Abbu yace dole ta fara ɗaukan jagoran abubuwa da kanta har ta saba, ba kaman da ba da take participating inactively tana koyan aiki. Shiyasa aka bar mata ragaman restaurant dinta The Olive Room da Plaza dinta The Meridian inda Saloon dinta yake.
Bayan ta gama ta tattara papers ɗin ta barshi a nan kan table, saita ɗauka jakanta da wayarta da lunch basket ɗin Abbu. Tayi sallama da second assistant ɗin Abbu wanda ake kira Mas'ud tashiga elevator da zai kaita ƙasa. Kofar yana buɗewa bayan ta iso ground floor wani saurayi ne ya kusan cin karo da Imaani wacce tasa kai zata fito.
"Oh sorry, bansan akwai mutum aciki ba." Ya ja baya yana mata murmushin ban hakuri.
Imaani tayi rolling idanunta a zuciyarta tace ya za'ayi mutum yayi zaton babu kowa a elevatorn office kaman haka. Saurayin ya dinga kallon Imaani kaman yaga sabon halitta, dama ta saba da irin wannan reaction din, tayi gaba abinta tana jin idanunshi na binta.
***
Sai kusan Maghrib suka isa unguwarsu dake New Millennium City Kaduna, estate ɗinsu a farkon unguwan yake, hasken fitilun streetlight ya baɗe ko ina. Mr. Samuel ya tsaya a wani katafaren gida mai brown gate (ruwan kasa) ya danna horn. Security dake bakin gate ya danna madannin bude gate bayan ya ga motarsu ta CCTV dake maƙale a wajen gate ɗin. Cream color (ruwan madara) da brown (ruwan kasa) ne painting gidan tawaje, ko ina ka juya bishiyoyi da flowers ne a jere cikin tsari sai sakin ƙamshi sukeyi barin ma akwai flowern nan na Queen of the Night acikinsu. Tsarin gidan duplex ne (hawa biyu) haɗaɗɗe a tsakiya sai Chalet dake gefen hagu, yana ɗauke da ɗakuna uku da palour inda anan Rafeeq yake kuma anan ake sauke baƙi maza.
Daga gefen Chalet ɗin wani Bungalow (ginin hawa daya) ne inda nan masu aiki maza da securities ke zama. Gefen dama kuma Gazebo ne (wurin shan iska) da wani ƙaton Parking Lot inda ake ajiye duka motocin gidan dana escorts. Akwai garden ta baya da kitchen din waje sai private wurin shan iska da wasan yara na Shukrah mai ɗauke da swing (lilo) na manya da yara. Cikin gidan kuma a sama, section biyu ne ɗauke da ɗakuna shida, ɗaya na Abbu mai ɗaki ɗaya haɗe da palour. Akwai office dinshi na gida duk a cikin section ɗin. Sai ɗayan section ɗin yana ɗauke da wani palour na Ammi da ɗakuna biyar na Ammi, Imaani, Shukrah da Asmau sai spare bedroom. Ƙasa kuma ɗakuna huɗu ne, biyu na masu aiki sauran na baƙi mata sai parlour biyu, daya na baƙin Abbu, dayan kuma wanda yafi kowane girma saboda akwai dining area daga gefe, na zaman mutanen gida ne. Akwai Library na karatu, Gymnasium na motsa jiki da Laundry Room inda ake kula da kayan wanki, sai Kitchen wanda banbancinshi dana restaurant ɗin Imaani girma ne kawai tunda abincin duka gidan akeyi, amma babu abunda babu daga kayan buƙata na zamani.
A harabar kofar gidan (Porch) Mr. Samuel yayi parking. "Sai da safe Mr. Samuel." Imaani tayi mishi sallama ta kwashe tarkacenta kafin ya zagayo ya buɗe mata kofar motan.
"Goodnight Madame." Ya amsa kafin ya kulle ƙofarta ya shiga ya ƙarasa da motar inda ake ajiyewa.
Buɗe katon bulletproof ƙofar (maindoors) tayi ta shiga wani corridor mai ɗauke da wani haɗɗaɗen Console, ta isa faffaɗan palourn sai ƙamshin turaren wuta kakeji left and right ya kama ko ina sabida constantly ake sakawa. Babu kowa a parloun anata kiran sallahn Maghrib, ƙamshin abinci na tashi daga kitchen yana haɗewa da kamshin parlourn.
Ɗaya daga cikin masu aikin gidan mai suna Ƙarama ne ta fito daga kitchen da kayan wanki (laundry) da ta kwaso a chanya a hannu, kasancewan akwai kofar baya ta kitchen
"Sannu da zuwa Aunty." Ta gaisheda Imaani wanda har ta isa curved stairs ɗinda zai kaita sama.
"Kash Ƙarama!" Imaani ta faɗa sabida batason Ammi tasan tadawo wuraren Maghrib.
Murmushi Ƙarama ta sake, "Au, ai tana sama." Ta faɗa ta karasa corridor da zai kaita Laundry room.
Tsurewa cikin Imaani yayi jin Ammi na sama, kenan zasu iya kaciɓus a hanya.
"Adda!" Imaani taji an faɗa da ɗan karfi cikin wani ƙaramin murya bayan ta hau sama, a zuciyarta tace shikenan wallahi. Sai jin mutum tayi a jikinta ta riƙe ƙafafunta cikin murna, Imaani tayi baya kaman zata faɗi a corridor ɗin gaban stairs.
"Na shiga uku Shukrah." Ƙyalƙyalewa da dariya 8 year-old ɗin tayi innocently. Fara ce sol kaman Abbu, tasha kitso an zuba mata beads a dogon gashinta mai laushi sai karkaɗawa sukeyi. Murmushi Imaani tayi ta riƙeta suka karasa ɗakinta, Shukrah nata zuba mata surutun tayi missing ɗinta, kasancewan yau tadawo daga gidan Kakarsu mahaifiyar Ammi dake Malali.
Warware Pashmina ɗinta Imaani tayi kafin ta ajiye jakarta da folder tana biyema Shukrah.
"Oya muje ayi alwala it's time for prayers."
Shukrah tace, "Ai Halita tayimun yanzunnan kafin kidawo." Nanny ɗinta kenan.
"Toh jirani muyi jam'i sai muyi sallan tare." Tayi instructing ɗinta ta zauna a couch ɗin ƙayataccen ɗakinta.
Suna idarwa aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin, Imaani ta bada izinin shigowa. Josephine wanda itama tana ɗaya daga cikin masu aikin gidan ta sanar da ita Ammi na kiranta.
"Okay, ganinan zuwa." Ta amsa bayan ta ninke kayan sallahn dasukayi amfani dashi.
Imaani ta kama hannun Shukrah suka fita daga ɗakin suka ƙarasa haɗaɗɗen palourn Ammi. Anan suka tarar da ita cikin haɗaɗɗen material ɗinkin boubou, tasha kyau sai zuba kamshin signature turarenta Chanel No. 5 takeyi. Simple jewellery ne ta saka na zaman gida tana zaune a three-seater ɗin royal kujerun palourn suna tattaunawa da Baaba Salame wanda itace shugaban ma'aikatan gidan. Da sauri Shukrah ta saki hannun Imaani ta faɗa jikin Ammi tayi lamo abunta.
"Sannunku da zuwa uwar masu gida." Baaba Salame tayi mata iso kaman yanda ta saba.
Murmushi Imaani ta sake mata, "Sannunku da gida Mama."
"Yawwa ƴar albarka Allah Ya kara lafiya Ya kawo miji nagari musha biki." Ta amsa da dariya cikin raha.
Ɗauke kai Imaani tayi, don taƙi jinin ayi mata irin wannan maganan. Gani take kaman an gaji da ita ne a gidan idan ana kawo mata magana makamancin haka.
Ammi ma tayi dariya tace, "Nan ba da daɗewa ba kuwa Insha Allah."
Wani dan karamin guɗa Baaba Salame ta saki cikin farin ciki tana karkaɗe ma Imaani hannayenta wanda taƙi kallonta, kafin ta fita.
"Good evening Ammi, I'm sorry I came back late. Na duba wasu sakonni ne da aka kawo a Saloon bayan na gyara gashina." Imaani ta bayyana kaman an tambayeta kafin ta zauna a ɗaya gefen Ammi daga inda Shukrah take.
Hararanta Ammi tayi, "Ai duk wani salon kare kanki kinsani. Shi kayan dolene a dubashi yau ba sai gobe ba?"
Kwantawa tayi a kafaɗar Ammi, "I'm sorry Ammi zan kula next time."
"Ɗagani dalla malama, Samuel da yake biyemiki shi zan tuhuma. Sai yaushe James zai dawo? Shi nasan bazai biyemiki ki dawomin gida da Maghriba ba."
Pecking ɗinta Imaani tayi a kuncinta kafin ta mike tsaye, "Ammi kiyi hakuri dan Allah, bazan ƙaraba. Mr. James kuma sai next week zai dawo." Mr. James shima Chauffeur ɗinta ne suna exchanging shift da Mr. Samuel akai akai kamar yadda yake a tsarin aikinsu. "Ammi zanje inyi wanka kafin Dinner."
Bata ma tsaya jiran mai Ammi zata faɗa ba tayi sauri ta fita. Tana isa ɗakinta ta shiga tsaftataccen bathroom ɗinta mai fadi, kalan tiles din mai duhu ne wato ash color da ratsin brown. Kayan wanka da gyaran jiki jere suke a mazauninsu cikin tsari. Da sauri ta watsa ruwa jin kiraye kirayen sallan Isha', kafin tayi alwala ta fito. Shiryawa tayi cikin white and pink Marks & Spencer cotton pyjamas, T-shirt da dogon wando sai ta ɗora hulan bacci akanta tayi sallah.
Tana idarwa ta sauko ƙasa tasama masu aiki hannu suka jera abinci a 8-seater dining table. Abbu yadawo ba da daɗewa ba, tana cikin sallah taji motsin shigowan motocinshi tare da na Rafeeq. Kaman ta kira sunanshi kuwa taji kakkausan muryarshi mai kama da na Abbu inhar baka iya bambantasu ba, yayi sallama a cikin palourn. Juyawa tayi jin muryar Ammi na amsa mishi tana sauka daga stairs tare da Shukrah. Da gudu Shukrah ta ruga wurinshi ya cafketa ya ɗagata sama yana juyi da ita tana ƙyalƙyala mishi dariya. Sanye yake da casual wears, Henley T-shirt navy blue wanda ya ƙara fito da hasken shi na Fulani da baƙin lounge trousers. Dogo ne, kuma kyakkyawa ba karya. Gashin kanshi a kwance yake ba mai yawa sosai ba. Kamanninshi da Abbu is very obvious da har za'a iya kiransu wa da ƙanni ba uba da ɗa ba. Kasancewan shima yana motsa jiki akai akai kuma cimarshi mai inganci ne.
"Sannu da zuwa Hamma." Imaani ta gaisheshi.
"Yawwa sannu Boddo, mai muka samu yau?." Ya tambaya bayan ya zaunar da Shukrah a baby seater ɗinta kusa da inda yake zama a dining.
"Nikam bansani ba, ban wani jima da dawowa ba." Sai da ta faɗa tayi realising mistake dinta.
Ɗaga kanshi yayi ya sauke mata kakkaifan idanunshi, "A ina kika tsaya kuma mai kika tsaya yi?"
Ammi da ta zauna a wurin zamanta ta taɓe baki.
"Hamma wallahi a Saloon na tsaya, ankawo kaya ne kuma banason in fita gobe shiyasa kawai nayi sorting ɗinsu yau." Ta amsashi cikin kosawa (exasperatedly).
Kafin Rafeeq yayi magana sukaji muryan Abbu yana amsa gaisuwan Baaba Sa'ade, kafin ya ƙaraso dining jin Shukrah na kiranshi ba ƙaƙƙautawa. "Oh! Bingel am idan kinyi hakuri ai yau muna tare." Shafa kanta yayi ya sumbaci goshinta dana Imaani kafin ya zagaya wurin Ammi dake mishi murmushi, ya sumbaci kuncinta duka biyun sai shima ya zauna a head chair na dinning ɗin, Ammi na daga damanshi inda Imaani take, Rafeeq kuma na hagunshi tare da Shukrah.
Cikin soyayya da raha aka gaisa kafin a fara bama ciki haƙƙinsa. Da kulawa Rafeeq ke bama Shukrah abinci bayan Imaani tayi serving kowa daidai gwargwadon cimarsa. Creamy Pasta da Ceaser salad with grilled Salmon sukaci. Sai sabon hadin kwakwa da abarba (Piña Colada) a gefe.
Suna kammalawa suka koma cikin babban palourn gidan wanda yake ɗauke da settin royal chairs har biyu, masu aiki ne suka gyara wurin cin abinci aka sake baɗa turaren wuta. Abbu ya saka news channel, Rafeeq kuma ya fita don amsa kira a waya. Ammi ce ta sa Imaani ta bata bayani (run-down) din abubuwan da tayi yau a wurin aiki wanda ya shafi harkan kasuwancinsu.
Rafeeq ne yadawo ciki yayi ma Abbu magana, "Abbu Mummy tace inje in ɗauko Asma'u yanzu."
Wani abu ne ya ɗarsu a ƙirjin Imaani. Abbu yace, "What time is it now? It's too late tadawo yanzu tabari sai gobe."
Rasa abun cewa Rafeeq yayi sabida Mamanshi ta jaddada mishi lallai yazo a yau ya ɗauki Asma'u babu ɓata lokaci.
Ammi ta sa bakinta, "Barrister da kabari an ɗauko ta kawai, ai ba shi kadai zai fita ba."
Abbu yace, "No dare yayi and it's too late to travel to Unguwan Sarki at this time. Its past 9:00 PM yanzu, ɗaukan security kuma zai ja unnecessary attention ne.
Ganin Rafeeq na tsaye kaman baiji abinda Abbu ya faɗa ba sai ya sake tabbatar mishi, "I said ka kira kace sai gobe zata dawo. You will not travel this late at night."
Juyawa Rafeeq yayi don ya isar da saƙon da aka bashi.
Basu wani daɗe ba sabida Shukrah har tayi bacci a jikin Abbu kuma akwai aiki gobe tunda weekday ne. Ammi ta kira nanny ɗinta Halita don tayi mata shirin bacci. Imaani ma tayi musu saida safe kafin ta koma ɗakinta.
Wuraren 11:00 PM aka dinga danna ƙararrawan (doorbell) ƙofar ƙasa ba ƙaƙƙautawa. Abbu da kanshi ya sauko ƙasa ya bude don yasan dama za'a rina. Yana bude kofar ya ganta da karamin akwati a gefe, ta saka dogon riga irin casual wears dinnan ta ɗaura dankwali a kai koh arzikin gyale babu. Fara ce sol itama, mai matsakaicin tsawo siririya, tanada kyau sabida Allah Ya basu arzikin kyau a jininsu.
"Waya dawo dake?" Abbu ya tambaya cikin fada.
Kame kame ta fara yi don saida tacema Mummy ta bari sai da safe ko sammako ne tayi tadawo amma taƙi barinta.
"Um um dama dama.. Haidar ne zaizo unguwannan wurin wani abokinshi shine.. shine ya ajiye ne."
Kallonta kawai Abbu yakeyi. Wai saurayi ne zai dawo da ƴarshi gida saboda rashin kamun kai. Sai yaushe Hajara zatayi hankali ne a rayuwarta? Idan kuma wani tsautsayin ya faɗa kan ƴarshi me zatace? Inda Jiddah ta fita hankali kenan.
"Ki koma kice ya maidake inda ya dauko ki, ai ba shi ya kaiki ba." Ya faɗa a fusace.
Ƙwalla ta fara mishi, "Abbu please kayi hakuri, wallahi saida nacema Mummy tabari-"
"Common shut up! Har kinsan kishiga motar saurayi da tsohon darennan ya dawo dake gidan babanki?" Ya faɗa cikin murya mai amo.
Muryar Ammi sukaji tana saukowa ƙasa, "Abbu kayi hakuri, tunda ta riga ta dawo lafiya, Alhamdulillah. Abar komai sai da safe sai ayi addressing. Dare yayi kar a tada mutanen gidan."
Ran Asma'u ya ɓaci dukda tasan da badan zuwan Ammi ba da kashinta ne zai bushe a wurin Abbu da tsohon darennan. Amma bawai taso tsoma baki da Ammi tayi tsakaninta da ubanta bane!
Juyawa Abbu yayi ya koma sama bayan ya mata kallon zaki san mai zai biyo baya.
Ammi ta tsaya taga shigowarta ciki dan tasan zata iya tashin masu aiki su ɗaukar mata akwatin ciki.
Ilai kuwa don dabadan nauyin idan Ammi ba, wanda shi kaɗai ke hanata yi mata rashin kunya kai tsaye so da yawa, to da ta tashe mai aiki ta dauka akwatinnan sama kuma ta gyara mata ɗakin kafin ta kwanta.
Murya a daƙile ta gaida Ammi taja akwatinta tayi gaba.
Da sakakken fuska Ammi ta amsa, kafin ta kulle kofan itama ta koma ta kwanta.
***
Assalamalaikum guys, keep me in your duas please 💜
PS: Share, share share!