MAƘOFTAKA DA ALJANU

Chapter 6

by @deejasmah

MAƘOFTAKA DA ALJANU 

Khadeejah Bint Ismail (Deejasmah) & Ameenah Abubakar Ƴandoma 

CHAPTER 6
…Gidansu ya fara kira ya sanar masu sannan ya kira gidansu  Nana ya fada ba a jima ba sai ga  Inna Yabi tare da Iyami. Ba karamin tashin hankali suka shiga jin za a yi ma Nana daurin mahaifa. Nurse ce ta shigo ta fita da su ganin hayaniyarsu zata iya tayar da Nana da ke bacci, wadda suke so ta yi bacci mai isarta domin zuwa dare za su yi mata ɗaurin mahaifa.
Ba su jima ba sai ga Mahaifiyar Nana babban danta ya kawota. Bayan sun gaisa take tambayar mai jiki. "Da sauki Umma allurar da aka yi mata ce ake jira ta farka za a yi mata ɗaurin mahaifa" duk da dauriya irin ta mahaifiya sai da damuwa ta bayyana kwance a fuskar Umma, kasancewar Nana ita ce autarta. "Ubangiji ya bata lafiya." Da amin suka amsa.
Kasancewar Iyami ita ce ƙanwar Khaleed autar gidansu ita aka baro cikin dakin tare da Nana.
Daga gidansu Khaleed aka kawo abincin rana Umma bata bar asibitin ba sai la'asar liƙis, ba don ranta ya so ba. Ta so a ce Nana ta farka ko zata ji damuwarta amma tilas haka ta fita daga asibitin. Bata jima da tafiya ba Nana ta fara kokarin bude ido. Da Karfi Iyami ta kwalawa Inna Yabi Kira. A tare da Khaleed suka shigo dakin. Sannu ya ke ta jero mata ita kan ɗakin take ƙarewa kallo cike da mamaki.
"Inna Yabi Ina ne nan?" Nana ta fada cikin murya mai cike da rashin kuzari. 
"Sannu kinji! Asibiti ne Nana"
Jin abin da ta fada ya saka ta kallon Khaleed. Ɗaya mata kai ya yi alamun ta yi hakuri. Komawa ta yi ta kwanta ta na mamakin abin da ya kawota asibiti bayan ita dai a tunaninta tana cikin gidanta.

Shigowar likita ita ta saka Nana kallon ƙofar. "Ya mai jikin ina ke miki ciwo?" Likitan ya jefa mata tambayar.
"Daga kasan marata ke mini dan ciwo kadan" ta fada tare da dafe goshinta. Gaban Khaleed yanke wa ya yi ya fadi. "Likita! Kana ganin cikin jikinta kuwa lafiya lau, babu wani abu da ya sameta?" Ya karasa maganar cikin tashin hankali.
"Kwantar da hankalinka in Shaa Allah yanZu zamu yi mata aiki dama jira muke ta farka, musamman ma yanzu da ta ce mararta na dan yin ciwo"
Duk da rashin lafiyar da ke dawainiya da Nana, hakan bai hanata fahimtar abin da likitan da Khaleed su ke nufi ba. Ita kanta bata san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba. "Ciki! Tabbas ciki ne da ni. Alhamdulillah! Ya Allah na gode kai ne mai kyauta da kari ina mai kara godiya a gareka" ta karasa maganar zucin tana mai shafa shafaffen cikinta.

Nurse gudu biyu mata su suka dauki Nana aka tafi da ita, a ba jima ba suka gama yi mata aikin suka dawo da ita. Inna Yabi sai sannu take faman yi mata ruwan zafi aka bata ta sha daga nan bacci mai nauyi ya dauketa. Da Iyami da Khaleed ganin dare ya yi tare suka tafi gida ya rage daga Inna Yabi sai Nana da ke faman bacci.

Abinci Inna Yabi ta ci tabarmarta da ke gefen gadon Nana ta shimfida jim kadan bacci ya yi awon gaba da ita. 
Dare ya tsala baka jin sautin komai sai na karnuka. Juyi Nana ke fa faman yi a saman gadon, lokaci daya ta bude ido. Hasken Nefa ne ya kashe mata su ba shiri ta mayar da su ta rufe ta na mai kara budesu a hankali. Caraf idanuwanta suka sauka a kan Window. Murza idanunta tayi tana tunanin ko bacci ne ke sakata suna mata gizo, sai dai har yanzu mace take gani sak mai kama da ita tsaye a wurin taga ta kafeta da ido.
Zabura ta yi ta mike zaune. Kasancewar dakin akwai hasken Nepa  tana iya hango matar amma daga waje duhu ne sosai. Karfin gwiwa ta samu na fitowa daga saman gado, Inna Yabi ta kalla da ke kwance ta na sharar bacci bata san neke faruwa ba. Sando tamkar makaryaciya haka ta rika tafiya, har ta karasa bakin tagar. Jibgegiyar mage ta gani baƙa ƙirin ta na rarraba ido. A zabure Nana ta yo baya ta daki flacks din ruwan zafi karar faduwar sa ita ta tayar da Inna yabi da Ke bacci farkawa. "Subhanallah! Nana Firdausi lafiya kuwa, me ya kai ki bakin taga a cikin daren nan?" Ta karasa maganar tare da rirrike Nana da ilahirin jikinta ke faman kyarma. Gefen gado ta zaunar da ita ta na mata sannu. Ga dai magana tana son fadar abin da ta gani amma harshen ta ya yi mata nauyi. "Na sani gigin bacci ne zai kai ki bakin taga da tsakar daren nan, in ba haka ba ba a so mace tana kusantar inda taga take. Duk da dai na yi mamakin wanda ya bude tagar nan ni da hannuna na kulleta.  Ko da ya ke Nana koma kiyi baccin ki kinji" komawa ta yi ta kwanta a tsora ce. Har garin Allah ya waye bata sake bacci ba sai da ta yi sallar asuba.

Khaleed tunda safe ya kawo masu kayan kalaci sai dai har ya tafi Nana bacci take yi, duk da ya so a ce sunyi magana da ita. 
Ba a jima ba mahaifiyar Nana ta dawo tare da babbar yayarsu mace. 
Suna karasowa Nana ta farka nan suka gaggauta likita ya zo duba jikinta, tare da rubuta masu wasu magungunan. Iyami ita da mahaifiyar su wato mahaifiyar Khaleed a tare suka zo, ganin dakin ya fara cika dole suka fito harabar asibitin a nan suka yi sallar azahar har Khaleed ya iske su. Kai tsaye dakin da Nana take ya shiga, kwance take fuskar nan ta yi fari soll tamkar wadda jini ya yi ma karanci a jiki. Da fara'arsa ya shiga,  ya na tsokanarka. "Jannah maman Baby. Wannan Baby Kam ta zo da wahala ga shi nan sai wahalar min da mata take, ko haihuwar ki ta farko ba ki wahala ba kamar wannan" ya karasa maganar ya na dariya. Har ga Allah Nana ba karamin dadi take ji ba idan ta ji Khaleed ya kirata da wannan sunan, lokacin amarcinsu yake tuna mata. Iyami da ke gefe ganin suna bukatar a basu wuri fita ta yi ita ma tana murmushi.
"Hmm! wannan Baby har jikokin ta bata gajiya wurin wahalar da su ba, ka duba ka ga yadda bayin Allah kowa ya zo asibitin nan wutsiya zage"
"Yanzu dai abin da nake so ki kula da dokokin da likita ya gindaya miki, na san halinki sarai da rashin kaunar magani ga kuma kaunar yin ayyuka koda an hanaki. Shi ya sa ma na yanke shawarar da an sallame mu Iyami zata tattara ta dawo gidanmu da zama, duk wani aiki zata rika yi miki shi."
"Amma sai nake ganin kamar zamu takura mata!"
"Babu takurawa Iyami ce da kada ki damu" haka suka ci gaba da hira har lokacin tafiyar Khaleed ya yi. Daki ya rage saura Nana ita daya. Jingina da bango tayi ta rufe ido, ba arziki ta budesu gabanta na faduwa sakamakon banko kofar da akayi da karfi. Karasa mikewa zaune tayi ganin yarinya karama wadda ba zata wuce shekara hudu ba ta shigo daki. Kamannin yarinya fara ce sol hasketa Har kashe ido ya ke, kanta kwance ya ke an nade mata gashin kanta an mata gammo da shi a gaban goshi. Kwala-kwalan idanu gareta masu kama da na kyanwa, hancinta a naƙushe sannan shafe ya ke ba don kofofin da zaka iya hangowa ba zaka rantse da Allah ka ce bata da hanci.
Ganin yarinyar ta nufota gadan-gadan ya sakata dawowa bakin gado, sai dai kafin ta karaso tuni yarinya ta iso gabanta.
Sauran nutsuwa da karfin halin da ya rage mata ta tattaro. "Yarinya lafiya? Wa kike nema ina mahaifanki?"
Shuru yarinyar ta yi babu alamun zata amsa mata tambayoyin. Lokaci daya ta koma kallon cikinta da daka-dakan idanunta. Mummunar faduwar gaba ta sake ziyartar Nana a karo na ba adadi.
"Wa kike nema?" Nana ta sake maimaita mata tambayar.
Hannu yarinyar ta ɗaga ta na nuna cikin Nana. "Wannan nake nema" ta fada a cikin mummunar murya mara dadin amo
Nana Zabura tayi tana ja da baya cikin tashin hankali...

Meenat A. 'Yandoma