...BASHI!

Page 1

by @sanazty

Kuyi following ɗina anan Arewabooks domin samun Novels ɗina masu daɗin gaske. Na gode

*BASHI...!*
    _Wattpad@ SaNaz_deeyah_

*K.W.A*📚

_Ga masu buƙatar ayi musu talla, za su iya tuntuɓata a wannan number ***_

_Sadiya S. Adam🌸✍️_

_Bismillahir rahmanir rahim_

                     Page 01
_________🖌️"Sadiya...!
 A tsorace ta miƙe domin jin kiran tamkar a cikin mafarki. 
  Kafin ta kai ga ƙofa tuni Umma ta danno kai.

"Ke baki da aiki sai bacci ko? Ba ma zaki bari a yi Isha'i ba"

"Wallahi Umma bacci kawai ya ɗebeni ban sani ba" Ta furta tare da rufe baki da hannu saboda hamma da tazo mata a lokacin.

"Kin ga itace da aka sayo gaba ɗaya ɗanye ne, da yake jiya an maka ruwa, ina tunanin jiƙaƙƙu ya samo min, ko zaki je gidan Tabawa ki sayo?"

 "Umma ina Ibrahim ba sai yaje ba, kin san Baba baya son mu riƙa fitar dare."
    "To wa ma ya san inda ya nufa, yana can yawon sa"
    "Umma dan Allah ki daina barinsa yana yawo, kin san dai duniyar nan babu gaskiya sai da tsaro."
   "Insha Allah, Ibrahim ɗin ne baya jin maganata ban san meyasa ba, taurin kai ne dashi"
   "Bari ya dawo, sai na saita shi wallahi, Umma ai maganar fatar baki bata fiya gyara yaro ba, in ba samu kika yi ki ka zane shi ba, ba zai yi hankali ba."
  Karɓar kuɗin tayi sannan ta ɗauki gyalenta ta fita.

**** 

Sauri kawai take, dan ganin hadari ya haɗo a garin, gashi har garin ya yi duhu, kuma babu fitila a hannunta, da ƙyar take iya ganin gabanta.
   Bata da wani buri daya wuce ta ganta a gida dan sam bata so ruwa ya taɓa ta.

Jin kamar taci karo da mutum ne ya saka taji gabanta ya faɗi.
    "Subhanallahi...!" Ta furta, daga nan kuma bata ƙara sanin inda kanta yake ba.

_Washe Gari_
08:30am

Tana kwance akan ƴar ƙaramar katifarta, hawaye na bin gefen idanuwanta.
    Umma ta shigo ɗauke da kwano, ta ajje a ƙasa tare da faɗin "Sadiya tashi kici abinci"
     "Na ƙoshi" Ta furta a can ƙasan maƙoshinta.

"Kin san muddin Babanku ya shigo ya ganki a wannan halin ni dake ranmu ba zai mana daɗi ba, domin ƙarya nayi masa nace kina gidan ƙanwata Ladi."
   Shiru bata bayar da amsa ba, har sai da Umma ta sake cewa "Ina kika kwana jiya?"
    Gabanta ya faɗi, taji kanta ya sara tamkar zai dare biyu.
   
"Tambayarki nake fa" Wannan karon a hasale tayi maganar.
   Kuka sosai Sadiya ta fashe dashi, tare da runtse idanunta da suke mata zafi tamkar an watsa targu a cikinsu.
   "Tunda ba zaki faɗa ba, ki tashi ki wanko baki kici abinci"
   Miƙewa tayi zaune a hankali, dan har a lokacin gabanta raɗaɗi yake da azabar zafi, daurewa kawai take.

"Idan ni mahaifiyarki baki faɗa min abinda ke damunki ba waye zaki faɗawa? Sadiya yanzu har akwai abinda za ki iya ɓoye min?"

"Umma ban san mene ya sameni ba, ni kawai na tashi na ganni a wani guri ne..." Ta ƙarasa maganar tana fashewa da wani kuka na takaici da dana sanin fitar da tayi a daren jiya.

_Fyaɗe aka yi miki._ Shi ne abinda zuciyarta ke ƙara nanatawa.
   _Ban san waye ba, ban kuma san dalilinsa na aikata haka a gareni ba, ni a sanina bani da wani abokin hamayya, bani da izgili kuma bana wulaƙanta kowa, to waye ya yi min fyaɗe? Kuma mene dalilinsa na lalata rayuwata a lokacin da zan fara more ƙuruciyata?_

   "Ki faɗa min me aka miki?" Shi ne abinda taji Umma ta furta cikin tsawa, wanda hakan ne ya dawo da ita daga tunani data faɗa, a take ta tariyo abinda ya faru da ita a daren jiya.

Tun bayan da taji kamar ta bugi mutum taji an shaƙa mata abu a hanci, daga wannan lokacin kuma, bata sake sanin komai ba, sai dai ta tashi ta ganta a gado babu komai jikinta, kuma bata iya motsa komai face idonta. 
   Ta ɗauki kusan awa ɗaya tana kuka kafin ta samo ƙarfin tashi, anan taga bedsheet ɗin kaca-kaca da jini.

   Da ƙyar ta iya ɗaukar riga tana kuma sakawa taji ana knocking, sam ta kasa tashi ta buɗe, har sai da taji kamar ana magana sannan ta samu ta miƙe tana ɗangyasa ƙafa ta buɗe.

"Hajiya room service ne, zamu gyara ɗakin"
    Da jajayen idanunta take kallonsa, kafin bakinta ya iya furta "Ina ne nan? Waye ya kawo ni?"
   "Oh baki ma sani ba kenan. Kin ga Malama ban son rainin hankali ki tattara ki fita, kuɗin da aka biya na ɗakin nan sun ƙare."

Tana ji tana gani ta fita, anan ma ta gane hotel ne inda take, haka ta hayo napep tayo gida, tana jin zugi a gabanta.

Sai da ɗan napep ya sauketa, sannan ta shiga gida ta ɗauko masa kuɗi a cikin kuɗaɗen da take tarawa a lokacin suna gab da fara WEAC to tana so ta tara kuɗin da za tayi hidimar Candy ban da wanda su Umma za suyi mata. 

Har ta biya mai napep ta koma cikin gidan Umma bata fito daga kewaye ba. Sai data shiga ɗaki ta kwanta tana ta tunanin wanda ya ruguza rayuwarta sannan Umma ta faɗo, bata kuma kulata ba ta juya ta ɗauka abinci.

"Ban taɓa yawon banza ba, na tsare mutuncina tun daga yarinta har zuwa girmana, har nayi aure wasu iyayen dani suke kwatance wajen yiwa ƴaƴansu faɗa, meyasa haka ta kasance dake?"
    Kuka sosai Umma take tana faɗin maganganu, yayinda Sadiya ma kukan take.

Umma da kanta ta ɗora ruwan zafi, ta kuma kai Sadiya kewaye ta mata gashi.
      Bayan ta canza kaya ta zauna ta cigaba da aikin rera kuka.
    "Sadiya...!" Umma ta furta sunan a sanyaye.
   Da ido Sadiya ta bi ta, dan bata da abin cewa.
      "Ina so wannan ya zama sirri, ko mahaifinki kada ki faɗawa dan Allah"
   Kai ta gyaɗa tana ƙara goge hawayen takaici.

            *** *** ***

"Ina kika kwana jiya?" Shi ne tambayar da Baba ya watso mata, ta kasa koda haɗa ido dashi.
   "Magana nake miki kin sunne kai kamar wata munafuka" Ya yi maganar da tsawa.

"Ba...ba...ba..." Shi ne abinda Sadiya ke faɗa cikin sarƙewar murya domin ko sunan shi ta kasa furtawa saboda tsananin firgici.

Tun asali suna tsoron mahaifin nasu daga ita har shi Ibrahim, dan in ka ga Ibrahim ya fita yawo to ya tabbatar mahaifin nasu ya yi nisa da unguwar.

"Sadiya idan baki faɗa min ba, yanzu zan lakaɗa miki duka, kin ga anan bakinki zai buɗe"

Umma sai lokaci ta shigo ɗakin ta tarar da wannan tarzoma tsakanin Sadiya da mahaifinta.

"Malam lafiya kuwa?"

Juyawa ya yi ya kalleta, tare da miƙewa tsaye.
   "Ina so ta faɗa min gaskiyar inda ta kwana, dan ban gaskata abinda kika faɗa min ba, sai kuma gashi tana kame-kame."

"Amma ai na faɗa maka cewar gidan Ladi taje ko? Kana tunanin ƙarya nayi maka?"

Shiru ya yi na wucin gadi, kafin ya ce "Ke Sadiya tashi kije ki kirawo Ibrahim yana dakalin ƙofar gida, zan haɗaku gaba ɗaya muyi magana."

Da ƙyar take miƙewa, ya tsaya ya ƙura mata idanu.

Tana gama miƙewa kuwa jini ya biyota har ƙafarta.

"Mene haka?" Ya furta cikin tashin hankali yana kuma nuna gurin.

"Babu komai fa ciwo ne taji" Umma ta faɗa cikin sarƙewar murya.

Kuka Baba ya fara, yana faɗin "Lami kin cuceni, yanzu da wane ido zan kalli mutanen gari da suke ganin kima da darajat..." Bai ma ƙarasa faɗa ba ya kai ƙasa.

Gaba ɗaya suka rafka salati, a gigice Sadiya ta ɗaga ƙafa zata fita jini ya ɗebeta ta suma a gun.

                      ** *** **

Lumshe ido ya yi sannan ya buɗe, ya kai dubansa kan laptop dake ajiye kan cinyarsa. 

Miƙewa ya yi, sai kuma ya koma ya zauna, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke a lokacin da yaji wani irin bugun zuciya.

Aziza da ta fito daga side ɗin Mommy shi ta tsaya tana kallo daga nesa, dan a yadda ta ganshi kamar ba cikin hayyacinsa yake ba.
 
Da ɗan sassarfa ta ƙarasa gabansa, tare da riƙe hannunsa, kallonta ya yi, a lokacin wani hawaye ya sauka a kuncinsa, da sauri ya kuma miƙewa.

"Zauna...!" Ta furta a sanyaye, tare da taimaka masa ya zauna.

"Addu'a...!" Ta furta idanunta cikin nashi, a lokacin da taga kamar yanayinsa ya fara canzawa"

"Ina zuwa, kayi addu'a please Yaya" Ta faɗa tana kallonsa.

Ganin yadda jikinsa ya fara rawa, da yadda tsigar jikinsa ta fara tashi ya saka tayi saurin miƙewa ta nufi bedroom ɗinta.

Zam-zam ta ɗebo hankalinta a tashe ta tofa addu'a sannan ta koma parlour

Ruwan ta watsa masa, wani ƙara ya yi, a lokaci guda ya murgina har ya bugu da center table ɗin. 

Kuka ta saka tare da rufe guskarta da tafukan hannunta.

Ganin ya buɗe ido ya saka tayi saurin miƙewa, bama ta damu ta goge hawayen ba, haka ta ƙarasa gabansa. 
"Yaya...!" Ta furta a sanyaye, idanunta a kanshi suke.

"Mutuwa...!" Ya furta da ƙyar.

"Na san ko yaushe haka kake faɗa, amma ka sani, ko wace cuta da maganinta, kuma insha Allah zaka samu lafiya.

"Muhasin lafiya kuwa?" suka ji muryar Mommy.

Aziza ta miƙe da sauri ta ƙarasa gurin Mommy, cikin tashin hankali.

Fa'iza kallon Muhasin tayi sannan ta kalli Mommy cikin damuwa ta ce "Mommy tsoro nake, ni dai ki mayar dani boarding school na ƙarasa karatuna, ko kuma ki kaini Abuja gidan Uncle" Muryarta kamar za tayi kuka.

"Calm down, ba abinda zai faru, mu ƙarasa"

Kai ta girgiza sannan ta juya da gudu ta koma ciki, Muhasin ya kasa yiwa kowa magana a cikinsu.

A sanyaye Mommy ta ƙarasa gabansa, tare da cewa "Muhasin kana yin wannan addu'o'in kuwa?"

Kai ya gyaɗa. Aziza ta sauke ajiyar zuciya tare da zaunawa kusa dashi.

"Mommy...!" Ya furta da deep voice ɗinsa, wannan manyan idanun nashi tuni sun canza kala sun koma jajir.

"Bana shaye-shaye, kuma ban taɓa neman mata ba. Bana yaudara kuma zai yi wuya na wulaƙanta wani, amma wannan halin dana shiga, ina ji a jikina inama ace mutuwa nayi kawai, hakan sai ya fi min sauƙi Mommy" Ya furta yana hawaye.

Aziza ta kalleshi ta ce "Ciwonka ba dawwamamme bane, kuma in dai kuɗin da muke dasu zasu nemo magani to tabbas zamu sama maka lafiya da yardar Allah."

               *** *** ***

"Kuɗi ba zasu taɓa dawo min da martabata ba, kuɗi ba zasu taɓa dawo da budurcin da ta rasa ba, amma a kansu gashi kin ruguza rayuwar ƴarki. Yanzu haka za ayi ta nuna ni a gari" Baba ya furta yana hawayen takaici.

Umma ta saka haɓar zane ta goge hawaye, sannan ta ce "Da ace na faɗa maka gaskiya tun a jiya na san ba zaka zargeni ba. Amma ka sani duk son kuɗina, ba zan iya sayar da martabar ƴar dana haifa ba."

"To mene kikayi a yanzu? Kin ce min ta tafi gidan ƙanwarki, amma ga halin da take ciki" Ya faɗa yana nuna Sadiya dake kwance a gado bata ma san meke faruwa ba.

"Malam wallahi aikenta nayi sayen icce, kuma na san ka hana a aiketa in duhu ya fara shiyasa nayi maka ƙarya da haka, amma wallahi ni ban tura Sadiya yawon banza ba"

"Ba zan taɓa yarda da abinda kika faɗa ba, haka zalika ba zan taɓa yafe miki ba. Kuma kada ki dawo min gida kije na sakeki" Ya furta tare da juyawa.

"Malam saki, innalillahi wa inna ilaihi raji'un" 
Kuka da Umma ke yi shi ne ya ta da Sadiya daga baccin wahala. Itama kukan ta dasa, duk da bata san dalilin kukan Umma ba, amma itama raɗaɗin da ke ranta ne ya taso.

       *** **** ***

"Baffa na sha yi mata magana akan ta daina aika yarana ko ina duba da yadda yanayin gari babu cikakken tsaro. Na sha faɗa mata duk abinda ake buƙata a saya ido na ganin ido da zarar magariba tayi kar su fita ko ƙofar gida. Abin mamaki dana dawo gaba ɗaya har ƙaramin basu nan, ga yaran nan ka tambayesu"

Ibrahim da bai wuce kimanin shekaru takwas ba, ya yiwa Baba ƙyar yana zumɓurar baki, dan duniya babu abinda ya fi masa daɗi irin wasan dare, shiyasa Umma ko ta hanashi sai ya samu ya fita, duk da wani lokacin in Sadiya ta lura tana kamoshi ta zane amma hakan bai saka ya daina ba.

Gashi yanzu Baba ya saki Umma kuma ya hana ta tafi dasu, dan a washe garin ranar aka sallamo Sadiya daga asibiti kuma ya ce dole gida zasu zauna. Yau kwana biyu da faruwar abin shi ne Baffa(Mahaifin Umma) yazo da kan shi biko.

"Yanzu dai kayi haƙuri, ka mayar da matarka ku cigaba da zama cikin rufin asiri. Ga yara kai ma ba zaka iya ba, musamman ita macen, dole tana buƙatar mahaifiyarta a kusa, tunda naga ɗangyashi take har yanzu, ga shekarunta 16 har yanzu bata wuce kulawar mahaifiyarta ba."

"Ɗanki fa aka yi mata, na tabbatar Sadiya ba zata iya gasa ɗinkin nan yadda ya kamata" Umma ta faɗa tana matsar hawaye.

"Ko ma bata gasa shi yadda ya kamata, a haka zai warke insha Allah"

Ya kai dubansa ga Baffa ya ce "Kayi haƙuri Baffa, amma gaskiya a yanzu ba zan iya mayar da Lami ba"

Yunƙurawa Sadiya tayi, sai kuma ta kasa. Kuka ta saka cikin ƙunar rai.

Tana ji tana gani haka Umma ta miƙe.
"Baba dan Allah kayi haƙuri ka bar Umma ta zauna" Shi ne abinda suke faɗa cikin kuka.
 Amma sam yaƙi ko kallonsu dan ma kar su bashi tausayi, dan baya jin zai iya mayar da ita a yadda yake jin ciwon lalata ɗiyarsa Sadiya.

                     *** ***

A hankali ta buɗe idanunta jin abu yana ɗiga a fuskarta.

Hannu ta saka ta kunna side lump, sannan ta miƙe zaune. 
   Taɓa gurin da ruwan ya zuba tayi sannan ta kalli hannunta, sai ganin jini tayi.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Ta furta cikin tashin hankali gami da sauka daga kan gadon.

Gabanta faɗuwa yake lokacin data kalli agogonta dake side drawer taga ƙarfe biyu da rabi na dare.

A tsorace ta sake waigawa, kawai sai ganin wata mummunar halitta tayi ta dumfarota gami da kai zaƙo-zaƙon hannunta ga fuskarta, tayi ƙoƙarin ta kauce amma sai da ta kai mata yakushi wanda zafinsa ne ya saka ta ƙwalla mahaukacin ƙara.

A take a gurin ta sume.

_Washe Gari_
*11:20am* 

Yana fitowa daga side ɗinsa, dukkansu suka kalleshi, hakan ya saka ya ɗan ji faɗuwar gaba.

Fa'iza ta miƙe da sauri ta rungumeshi "Bro am scared, But I so much love you, am sorry for what i did to you yesterday"

Kanta ya shafa tare da faɗin "Never mind, I love you too" Ya kama hannunta suka ƙarasa cikin parlour.

Har ƙasa ya durƙusa ya gaida Momma, sannan Aziza ma ta gaidashi.

"Momm..." Tayi saurin ɗaga masa hannu tare da faɗin "Wacece Amira?"

"Amira...!" 

"Eh ka faɗa min wacece ita? Muhasin meyasa ba zaka haƙura da soyayya ba, za kayi aure amma dole sai ka warke, yanzu yarinyar nan tana mutuwa itace mace ta 8 da kayi soyayya da ita ta mutu, dan me ba zaka haƙura ba? meyasa?"

Bata ko jira abinda zai faɗa ba ta wuce cikin ɓacin rai.

Ya kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi daga inda yake. Aziza ta taso ta kalleshi cikin kwantar da murya ta ce "It's alright ka zauna Yaya"

"Aziza dama Amira bata janye daga soyayyata ba?"

"Baka da laifi akan Amira Yaya, domin I warned her amma ta ce ita ba zata daina sonka ba, impact ba ma ta yarda kana da larura ba, ita tunaninta kamar ina hanata sonka ne"

"Amma ita ai ban ce ina sonta ba, hakan na nufin ko bance ina son mace ba in dai tana sona zata mutu? Ko dai aljana ta aureni?"

"Something like that, but if ace aljana ta aureka ba zaka riƙa canza halitta ba, kuma ba kisa zatayi ba sai dai ta hana aure, there will be something behind, am confused gaskiya."

Ji tayi ya yi shaƙuwa, kawai sai gani sukayi ya zube anan.

A gigice Fa'iza ta ɓuya bayan Aziza.

"Run to your room" Aziza ta furta tana kallon Fa'iza. Ai tana juyawa ya cafkota. Ta ƙwalla ƙara.

Aziza a tsorace take kallon yadda gashin jikinsa ya mimmiƙe, idanunsa ya zama wani green ga Fa'iza ya cakuma kamar ba mutum ya damƙa ba.

"Please dan Allah kar ka cut...." Bata ƙarasa faɗa ba taga ya wurga Fa'iza tamkar ƙwallo ta bugi show glass har ya fashe.

Gani tayi ya dumfaro inda take.


*Yanzu ma aka fara, kar a biyoku BASHIN ɗaukar darasin cikin labarin nan.*


```Alqalamin Sadiya....🌸✍️```