Page 2
by @sanazty
Page 2
__________🖌️Wani mahaukacin ƙara ta saki, duk riƙon addini irin na Aziza, zai yi wuya kaji ta tsorata tayi ihu sai dai ta ambaci sunan Allah amma a wannan gaɓar sai ta kasa jurewa.
Jikinta gaba É—aya tsuma yake, ta haÉ—a zufa sharkaf a jikinta, ta runtse idanunta sosai.
"Aziza lafiya?" Taji muryar Muhasin É—in, a tsorace ta buÉ—e ido tana kallonsa.
Halittunsa ne lafiya lau, cikin kiÉ—ima ta kalli inda ya yi wurgi da Fa'iza. Tana kwance a gurin amma kuma show glass na nan bai fashe ba.
Da sauri ta ƙarasa gareta tare da ɗagota.
"Am scared" Fa'iza ta faÉ—a idanunta a rufe.
"Fa'iza just calm down buÉ—e idanunki Aziza ce"
A hankali ta buɗe ido, tana duban Aziza ta kai dubanta ga Muhasin da yake tsaye kansu. Aikuwa ta ƙara ƙanƙame Aziza.
****** *****
"Na kasa gane abinda yake faruwa da Muhasin, gaba É—aya bama cikin kwanciyar hankali Malam."
Kallon Muhasin ɗin ya yi dake gefe, sannan ya kalleta ya ce "Insha Allahu zan yi istikara zan gano abinda ke damunsa, kafin mu ga taimakon da za ayi, kafin nan bari mu yi wani abu" Ya buga ƙasa ya kalli Muhasin ya ƙara buga ƙasa.
Aziza sai hararar Malamin take, ganin yadda yake wani abu tamkar boka.
"Hajiya tabbas akwai matsalolin dana hango a cikin rayuwar wannan yaro naki, amma dai ki kwantar da hankalinki, ki dawo zuwa gobe za kiji amsar ki"
"To Malam mene za a bayar na sadaka?"
"Ko nawa kika bayar na sadaka ya yi Hajiya.
Har ta buɗe jaka, Muhasin ya yi saurin takatar da ita. Sannan ya buɗe wallet ɗinsa ya ciro 15k ya miƙawa Malam.
Aziza ke driving shi kuma yana daga gefenta, sai Mommy na baya.
"Ni fa gaskiya ban fiya yarda da Malaman tsubbun nan ba, mushirikai ne, haka kurum su jefaka a bala'i"
"Kina nufin nima shirka nayi?"
"Ni ban faɗa ba Mommy, amma ni gaskiya tunda ya buga ƙasa naji hankalina bai kwanta dashi ba."
"To ni dai hankalina ya kwanta dashi, kuma shirka sai dai in ke keyinta"
"Aziza meyasa Mommy tana faÉ—a kina faÉ—a? Kin san dai ban son rashin kunya ko?"
Ranta a haÉ—e yake, ba kuma ta sake cewa komai ba.
***** *****
Idanunta jajir da hawaye ta É—ago zoben tana juyata a hannu. "Tabbas mamallakin zoben nan shine wanda ya ruguza rayuwata."
_Ko ban san garinsu ba, dolen zoben zata shaidashi, domin na san ya saka a hannuna ne dan wata rana ya gane ni. Tabbas dole na nemosa, domin ya biya bashin abinda ya É—auka._ Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta mayar da zoben a yatsanta na hagu.
Jin Baba yana kwaÉ—a mata kira ne ya saka ta goge hawayen idanunta sannan ta fita tsakar gida har a lokacin bata bar É—angyashi ba.
Har ƙasa ta duƙa tare da faɗin "Gani Baba"
"Naji labari a radio gobe zaku fara jarabawa ko?"
Shiru tayi, bata ce komai ba, har sai da ya ce "Ya naji kin yi shiru"
"Eh Baba!" Ta furta da muryar kuka.
"To me kike buƙata wanda baki saya ba?"
Kallonshi tayi, cike da tausayawa, ganin yadda ya damu da karatunta, amma kuma ita tuni ta ajje wannan a ranta tun ranar data fita thumb print taga ana nunata daga nan ta yanke ƙauna da karatu, hankalinta ya ɗunguma kan nemo wanda ya mata fyaɗe. Domin koda taje makarantar su, gani tayi ƙawayenta na nunata suna mata dariya, shiyasa ta juyo ba tare da tayi ba.
"Nawa ne zasu isa kiyi sayayyar?"
"Baba Math set ne ban saya ba, sai biro da Log book" Ta samu kan ta dayi masa wannan ƙaryar.
"Zan baki dubu uku zata isa ki saya ai ko?"
Kai ta gyaÉ—a alamar eh.
"To anjima zan samo in kawo miki, in yaso sai ki fita can shagon Ayuba ki saya na san ba za a rasa ba."
Kai ta gyaÉ—a tare da yi masa godiya, sannan ta mike ta koma É—aki.
Tsohon akwatin da take zuba kaya ta janyo, tare da fito da kayanta ta ɗebi kala biyu ta ƙulle a ɗankwali. Hankalin Sadiya ya yi gaba, burinta bai wuce ta nemo wannan mutumin ba, shekarunta na ƙuruciya basu hasaso mata illar abinda zatayi ba, sam bata tuno cewar ina zata dosa ba, ina zata zauna, waye zai bata abinci, ita idanunta ya rufe akan mutumin da bata san yanda ko kalar farcensa suke ba bare halittarsa gaba ɗaya. A taƙaice Sadiya ta shirya tafiya neman gaibu.
***** *****
ĆŠan lumshe ido ya yi sannan ya buÉ—e ya kalli Hafeez ya ce "Ina ji kamar na gudu kawai na tafi can wani gurin na cigaba da rayuwa"
"Idan kayi haka kuma baka yiwa Ć´an uwanka adalci ba, musamman ma Sweetheart É—ita Aziza ta damu da kai sosai, ita kanta na ga duk ta rame."
"Hafeez bani da zaɓi da ya wuce wannan, gani nake idan na bar kusa dasu sai sun fi samun nutsuwa da kwanciyar hankali"
"Ina ganin gara dai a samu wata mafitar amma ba guduwa ba."
"Amira na kwance har yanzu bama ta san waye a kanta ba, sam bana so inji ko inga mutuwar Amira, tuntuni na yanke ƙauna da soyayya da kuma aure, amma meyasa za a fara taɓa wanda suka ce suna sona ban amince ba?"
"Saboda sun ce suna sonka, kuma da alamu ba a so a raɓeka"
"Shiyasa nake ganin gara na É—an yi nesa da mutane kawai"
"Aikinka fa?"
"Ai dama tun dana fara rashin lafiyar nan ban koma ba, dan haka zan ajje aiki kawai"
"Meyasa? Haba Muhasin bai kamata ka bar garin nan ba"
"Zan yi magana da Mommy, gaskiya zan koma can wani guri da ban"
"Idan ma cikin dangine ka san dai dole za a samu wadda take sonka ko?"
"Ka daina wannan maganar"
"Dole ya yi, dan haka mu sam bamu yarda kaje ko ina ba, kana tare damu" Suka ji muryar Aziza.
Dukkansu juyawa sukayi, ita kuma ta ƙaraso, gami da watsa masa harara "Har wani kace zaka tafi ka barmu, to wallahi ƙafarmu ƙafarka ba zamu yarda ba."
"Yauwa Sweetheart nima abinda nake ta faÉ—a masa kenan."
_*Some Hours Later*_
Fa'iza na jingine da kafaÉ—ar Mommy yayinda ita kuma Aziza tana zaune kujera É—aya da Muhasin.
"Ya ce bai ga komai ba, bai san actual abinda ke damunka ba, amma dai zai baka wasu addu'oi, kuma mahaifinku yana tafe ji......." Bata ƙarasa maganar ba ganin yadda Maigadi ya shigo a kiɗime.
"Lafiya?" Mommy ta faɗa, ya yin da dukkansu suka miƙe tsaye.
"Hajiya mutane ne cunkus a waje, sun fi ɗari wasu ma makamai ne a hannunsu wai sai sun shigo sun kashe...." Sai kuma ya yi shiru ya kasa ƙarasa maganar.
"Kayi magana mana" Mommy ta faÉ—a lokacin da ta jiyo yadda ake bugun gate É—in gidan duk da suna nesa dashi.
"Wai ance wata yarinya ce ta rasu a sanadinsa"
"Amira...!" Aziza ta faÉ—a a kiÉ—ime tare da dafe kai.
Da sauri Muhasin ya ɗaga ƙafa zai fita "Mommy tayi saurin tarar gabansa.
"Ka san da wane irin makamai suka zo kuwa? Ba zan bari ka fita ba"
"Mommy mene ke faruwa dani ku faɗa min" Ya ƙarasa maganar yana doka tebur, idanunsa ɗauke da hawaye, tashin hankalin da yake ciki ba zai musaltu ba.
Da sauri Mommy taja mayafinta ta fita, kai tsaye kuma gate É—in ta nufa.
Ćłan aikin gidan daga boys quaters suma sun fito sun yi cirko-cirko.
"Hajiya bai kamata ki doshi gate É—in nan ke kaÉ—ai ba, gara dai a kira Ć´an sanda, domin wallahi kina buÉ—ewa wani zai iya buga miki abu, dan gaba É—aya makamai ne a hannunsu." Garba Driver ya yi maganar yana kallonta. A dai-dai lokacin Fa'iza, Aziza dashi kan shi Muhin suka fito.
"Koma ki É—auko min waya Aziza"
Da sauri ta juya. Sai da ta É—auko wayar ta dawo sannan ta koma kusa dashi ta tsaya.
"Hello...!"
Mommy tayi maganar a lokacin da ta kai wayar kunnenta. "Ƴallaɓai akwai matsala a gidana, yanzu haka ƙofar gidana cike yake da dandazon matasa sun zo su yaƙemu, ina so ka turo min yaranka domin a hanasu aikata ɓarna, na san daga inda kake kana jiyo ƙarar yadda suke bugu kamar zasu ɓalla gate"
Shiru na É—an wani lokaci tayi, kafin ta sake cewa "To shikenan, sai kun zo"
Tana sauke wayar ta kalli yaran nata, wanda suma ita suke kallo, ji tayi ƙwalla ta cika mata ido, gaba ɗaya tausayin Muhasin ne ya addabi zuciyarta, ta san yana haƙuri da danne zuciyarsa amma tabbas yana cikin tashin hankalin da kuɗi sun kasa yi musu magani.
***** *****
"Kai wane irin mahifine ga ƴaƴanka, ka san halin da yaronka yake ciki, amma sam ka kasa dawowa ka ganshi, so kake sai Muhasin ya mutu sannan kazo? Ban taɓa sanin auren maikuɗi babu wata riba sai bayan dana aureka, ƙila da talaka na aura ba zan ga irin wannan baƙar rayuwar ba. Ina amfanin kuɗin da kake samowa kawai ka turo mana, ba zaka iya zuwa ka zauna damu ba bare har ka san farin ciki ko damuwar mu. Tafiya kake har shekara amma idan kazo tsakaninmu da kai sati biyu ne" Hannu ta saka ta goge hawaye a lokacin da taji ana knocking.
Muhasin ne ya shigo, da ido kawai ta bi shi lokacin ta cigaba da cewa "Zan ɗauki Muhasin na kai shi can gurin dangina, su suna ƙaunarsa, kuma zai samu lafiya da yardar Allah, sannan kana dawowa sai ka tsinke igiyar aurena da kai" Tana gama faɗa ta ajje wayar.
"Mommy dan Allah ki sassauta zuciyarki, Mommy tun ina ƙarami nake ganin hawayenki har zuwa yanzu dana shekara ashirin da tara aduniya, sai yaushe hawayenki zai tsaya? Mommy na san abinda Daddy ke yi baya kyautawa amma tunda har kun yi haƙuri a baya ya kamata a yanzu ma ki haƙura, kin san fa kina da hawan jini, dan Allah ki rage damuwa"
"Ka san komai Muhasin, amma na gaji da zama dashi ne kawai. A baya na ɗauka nice kaɗai baya ƙauna shiyasa na zauna dashi, amma a yanzu dana gane har ku ƴaƴanshi bai damu daku ba shiyasa na shirya yanke alaqa dashi"
"Mommy tsufa ya zo maku, ya kamata kiyi haƙuri kamar yadda kikayi a baya koma fiye da haka" Hannu ya saka yana goge mata hawaye.
"Muhasin...!" Ta furta tana kallonsa da idanunta da suka fara canza launi saboda kukan da tayi.
"Ina so ka shirya jibi zan kai ka Gaya, can wurin babban Wanmu, Kawu Yakubu na san ba lallai ka gane shi ba, sannan ba lallai kaji daɗin rayuwar gidan ba, amma zan baka isassun kuɗin da zaka riƙa fita ka sayi abinci ka ƙoshi."
"To Mommy Allah ya kaimu, amma batun abinci kar ki ce naje na nema, a hankali zan saba da cimarsu."
"Shikenan, Allah ya yi maka albarka" "Amin Mommy, addu'arki da ƙaunar da kike nuna min a kullum ita ce ke ƙara min ƙwarin gwiwa."
Aziza dake bakin ƙofar ɗakin Mommy tana jin maganarsu gabanta ya faɗi, ta tsugunna a gurin tana hawaye. Tana jin fitowarsa ta miƙe tsaye tana kallonsa.
"Ba dai dan zan tafi shine kike kuka ba?"
Zumɓurar baki tayi, tare da saka yatsa ta goge hawayen idanunta. "Bana so ka tafi ka barmu Yaya"
"To ai zan dawo kuma ba ga waya ba, zamu riƙa yin waya dake"
"Yaya gaskiya ni dai bana so ka bar garin nan"
"Muje parlour muyi maganar." Ya faÉ—a tare da yin gaba ita kuma ta mara masa baya.
Suna zama ya kalleta ya ce "Ni kaina nafi son barin garin nan, domin yadda na zama tamkar mujiya, fita ta gagara, gara in tafi can inda ba wanda ya san ni, ba zan sakarwa ko wace mace fuskar da har zata ganni ta iya cewa tana sona, kin fahimceni"
"Amma anan É—in ma ai zaka samu lafiya, kuma ai Malam ya ce zai aiko da magani"
"Momma sai tafi samun nutsuwa haka ku kanku sai kun fi sakewa, a daina kiranku da ƙannen maye"
"Kai ba maye bane Yaya" Ta faɗa idanunta cike da ƙwalla.
"To mene na kukan, ai zan dawo gareku, kuma zaku riƙa zuwa"
Haka dai ya yi ta rarrashin ta yana mai bata baki har ta haƙura.
**** ***** ****
Kayanta na rungume a hannunta haka take takawa a hankali, har ta kusa zuwa zaure taji ance "Ke...!" Cikin matuƙar furgici ta saki ƙullun kayanta tare da juyawa.
KaÉ—an ya hana ta saki fitsari a lokacin da taga Baba ya dalleta da fitila.
Jikinta ya fara tsuma, sai kuma ta fashe da kuka, dan tabbas ta san yau zata sha duka.
"Sadiya guduwa za kiyi?"
Ya furta yana ƙarasawa gabanta.
Girgiza kai tayi tana hawaye, a lokacin daya kamota ya mayar da ita É—aki.
Ibrahim dai har a lokacin barcinsa yake. "Kwanta" Ya faÉ—a yana nuna mata shimfiÉ—arsu, a tsorace ta kwanta tare da runtse ido.
_Alqalamin Sadiya✍️_
[12/7/2023, 5:50 PM] Ummu Safiyya(reader): *...BASHI!*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
*K.W.A*
_Sadiya S. Adam🌸✍️_