...BASHI!

Page 3

by @sanazty

*...BASHI!*
   _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*K.W.A*

_Sadiya S. Adam🌸✍️_

                   Page 3

__________🖌️ "Hankalina ya tashi a lokacin dana ga yarinyar nan tana ƙoƙarin guduwa, da ace ban ganta ba, da shikenan sai dai na wayi gari naga bata nan. Yanzu haka maganar da nake maka, wannan yarinyar bata je gurin jarabawa ashe bata cikinsu haka ta saka na ƙuƙuta na nemo bashi na bata dubu uku ashe dasu take son amfani ta gudu"
Malam Halliru wanda ya kasance shine mahaifin Sadiya, shi ne yake maganar tare da maƙocinsa a washe garin ranar da Sadiya tayi ƙoƙarin guduwa.

"Yaro ne ka haife shi baka haifi halinsa ba, amma gaskiya dole sai ka saka ido akan yaranka, da zan baka shawara ma da nace ka daure kayi haƙuri ka dawo da mahaifiyar yaran nan ku cigaba da zama, domin kai ba zaka iya riƙe 'ya'yan da kanka ba, dole suna buƙatar kulawar mahaifiyarsu"

"Malam Yakubu, wato idan na duba irin faÉ—i tashi da nake akan iyalina, da irin sakayyar da Lami tayi min, sai inji sam ba zan iya zama da ita ba a yanzu, ka duba yadda mutanen unguwa ke zagina, basu ganin darajata a yanzu, kai ne kaÉ—ai wanda ya fahimceni, dan haka na yanke hukuncin komawa Kano da zama tare dasu, idan ta samu miji sai na aurar da ita kawai na huta tunda karatun ma ta ajiye"

"Ni ina ganin kamar hakan ba shi ne maslaha ba"

"Ni dai shi ne maslaha a gareni, dan haka zan samo kuɗi daga nan zuwa ƙarshen mako kawai na bar garin nan, akwai ƙanena dake zaune a Kano tare da iyalansa, dama yana tayi min sha'awar na koma can na samu ɗan abin rufawa kai asiri"

Tsayuwar mota a gurin ce ta hanasu yin magana gaba É—ayansu. Da ido suka bi motar, a kuma lokacin ne Mommy ta fito tare da yaran gaba É—aya, sai kuma driver.

"A'a'ah ashe baƙin Abuja ne a garin namu, lale marhabun Rukayya kece a gidan"

"Ni ce Yaya"
"Sannunku da zuwa" Ya mayar da dubansa ga Malam Halliru ya ce "Ita ce ƙanwata da nake faɗa maka tana aure a Abuja"

"Allah sarki, to sannunku da zuwa, ya hanya?"

"Lafiya lau, ina yini, mun sameku lafiya?" Cewar Mommy

"Lafiya lau"

Su ma su Muhasin gaidashi sukayi, yana ƙara kallon irin unguwar da zai yi rayuwa a cikinta, geto area mai tarin kwatoci da bola.

"To Malam Yakubu bari na barka tunda naga kayi baƙi" Musabaha suka yi ya shige gidan sa.

A tsorace Sadiya ta ɗago ta kalleshi sai kuma tayi saurin mayar da kanta ƙasa ta cigaba da fifita wuta.

"Gama kizo nan" Ya faɗa rai ɓace.

A hankali ta ajje mafici tare da miƙewa ta ƙarasa kan tabarmar da Baba ya zauna.

"Ko shirya ko wane lokaci zan iya aurar dake tunda naga shi kika fi buƙata" Kai ta girgiza sannan ta ce "Baba, idan na fita ƙawayena magana suke min shiyasa na kasa zuwa nayi, dan Allah kayi haƙuri"

   "Wato saboda Ć™awayenki shi ne kika saka na baki kuÉ—i da nufin ki sayi kayan kartu amma kike Ć™oĆ™arin guduwa ko? To idan kin gudu ina zaki je? Zan miki aure kin ga idan na aurar dake naga gidan uban da zaki gudu, in kin komai hannun mijinki ai baki isa kiyi masa wannan iskancin ba, shashasha kawai."

Sadiya kuka kawai take, yayinda Ibrahim ya kafeta da idanuwa.

Shi kuma Baba tashi ya yi ya zura takalma ya sake ficewa.

       ***** ****** ******

"Ya aka yi tuntuni baku faÉ—a min wannan matsalar ba?" Malam Yakubu ya faÉ—a yana kallon Muhasin kafin ya mayar da kallonsa ga Mommy.

"To wallahi Malam kullum ina so nazo amma ka san halin mahaifin nasu, shiyasa na yanke hukunci kawo shi, tunda naga kai kana yin irin wannan addu'o'in sai kaga an samu waraka, ni ko zama ne ya yi anan zuwa wani lokaci"

"Muhasin matso nan kusa" Malam ya faɗa tare da kallon Muhasin ɗin. Shi kuma ya matsa kamar yadda aka umarceshi, Fa'iza ta riƙe Mommy sosai tamkar zata mayar da ita ciki

Goshinsa ya É—an buga masa, sannan ya yi wasu addu'o'i. 
Kallon Mommy ya yi ya ce "Rukayya matsalarshi babba ce, amma dai in sha Allah za a nemo maganinta ba abinda zai gagara"

"Malam a ina za a nemo? Dan Allah ka faÉ—a min abinda ke damun Muhasin?"

Kallon yaran ya yi, sannan ya ce "Ku tashi ku ƙarasa cikin gida zan yi magana da ita."
   Dukkansu jiki a sanyaye suka fita.

Ya mayar da hanklinsa kanta ya ce "Ga dukkan alamu aljana ce ta aureshi, kuma ita ke kisan duk wanda ya raɓeshi da nufin soyayya"

"Malam meye mafita?"

Shiru ya É—anyi kafin ya ce "Addu'a da kuma magani zan samu na haÉ—a masa, sannan kuma dole sai an masa aure ta haka ne matsalar zata kau"

"Malam duk yarinyar da ya ce yana so mutuwa take, to ina ga an masa aure?"

Shiru ya yi sannan ya ce "Akwai Sadiya"

"Sadiya!" Mommy ta maimaita sunan.

"Eh Sadiya zamu aura masa dan ganin mun daĆ™ile wannan matsalar, koda ta mutu to matsalar zata kau" 

"Amma Malam kana ganin idan mukayi haka bamu cutar da yarinyar ba, da kuma iyayenta?"

"Yarinyar bata da wani galihu, dan dai ba wanda ke son nashi ya mutu, amma ba dan haka ba da sai nace mutuwar wannan yarinya sai yafi akan rayuwarta, domin kuwa a yanzu mahaifinta cikin ƙunci ya ke saboda ita"

Take ya bata labarin komai daya faru, sannan ya ƙara da cewa "Ki bayar da maƙudan kuɗi a matsayin sadakinta ni kuma zan san yanda zan shawo kan mahaifinta ayi auren"

Shiru Mommy tayi na wasu daƙiƙu sannan ta kalli Yayan nata "A gaskiya bana son Muhasin ya yi aure har sai ya warke, shi ne kaɗai ɗana namiji, sai in ɗaukeshi in bawa wata talaka wadda ma aka gurɓata rayuwarta, gaskiya ni Malam na fi son 'ya'yana su samu gidan asali"

"Rukayya ni kike faɗawa gidan asali? Shin kema ba a talauci kika tashi ba, to'toh wato yanzu kin samu duniya shi ne har zaki iya kallon idanuna kina min maganar talaka bayan nima gani a cikin talaucin. Ko abinda mijin naki yake miki ai dan ya ganki a talauci ne da ace a gidan wani hamshaƙin mai kuɗi ya ganki ai ba zai riƙa wulaƙanta har haka"

"Kayi haƙuri Malam" Shi ne abinda ta iya faɗa, shi kuma cikin faɗa ya sake cewa "Wallahi ba dan matsalar 'ya'yana bace, da sai na gama wajijjigaki kafin na saurareki"

Shiru tayi kanta a ƙasa. Ya yi tsoki sannan ya ce "Yanzu me kike ganin za ayi?"

"To naji kace a bada kuÉ—i mai yawa a sadakinta, to kuma na faÉ—a maka yarinyar data rasu a yanzu bai ce yana sonta ba ita ce ma take son shi"

"Wannan dalili ne ya saka nace ayi masa aure ba tare da sun san aure za ayi ba daga shi har yarinyar, hakan zai saka matsalar ta gushe, amma zaku É—auki yarinyar ku tafi da ita ta zauna tare daku, amma kuma kar ku yarda ku sanar dasu cewar su ma'aurata ne, sati É—aya bayan biki insha Allah komai zai dai-daita"

Ajiyar zuciya Mommy ta sauke sannan ta ce "To Yaya nawa kake ganin za a bayar na sadakin?"

"Ki basu ko 500k ya isa, ni kuma na san yanda zanyi da mahaifin yarinyar idan yaso idan kun tafi da ita ko aikatau sai ta riƙa muku"

"Shikenan zan bayar dasu yanzu, amma idan cash ake buƙata dole sai naje banki"

"Zaki iya yin transfer ni sai na bashi da hannuna idan kun tafi, yanzu dai zuwa gobe insha Allah za a É—aura auren, idan muka fita sallar la'asar zan zauna nayi magana dashi"

"Shikenan Yaya, Allah dai ya shige mana gaba"

"Amin ya rabbi, kije ciki ku gaisa dasu ku samu kuci abinci"

Miƙewa tayi cikin ladabi ta bar ɗakin.

           **** **** ****

Safiyya dai tunda suka shigo ta kai idonta kan Muhasin, taji kawai ya kwanta mata. Shiyasa komai take yi cikin jin kunya yayinda shi bai ma san tana yi ba.

"Ashe Hadiza da Safiyya basu yi aure ba"

"Wallahi kuwa ai tun bikin Habibu ina jin baku sake zuwa ba"

"Eh gaskiya dan ko wanda aka yi kwanaki lokacin bamu nan ne"

"Ai ita Hadiza an saka rana, Safiyya ce dai har yanzu Allah bai kawo ba"

"Allah ya zaɓa masu mafi alkhairi"

"Amin.." Cewar Baba Zulai wadda itace uwar gida a gurin Malam Yakubu, wanda matansa uku ne sai tarin 'Ya'ya duk da talaucin da suke ciki amma kwantsin yara ne a gidan ko wacce haihuwa kawai take.

"Kai kuma kake wani sunne kai, to ni dai ba zan ce kayi min ba" Cewar Baba Hajara wadda ita ce ta biyu a gida.
   Dariya duka suka saka domin shi baya cikin mood É—in tsokana, dan hankalinsa a tashe yake.

Sun shiga É—akunan matan kafin daga bisani suka dawo tsakar gida inda aka shimfiÉ—a musu tabarmi. Ko ruwa sun kasa sha, Mommy ce kawai a cikinsu ta iya cin har abincin da aka kawo domin dama ita ta saba da cimar.

          ******* *******

"Anya kana ganin hakan zai zama mafita a gareni? Yarinyar nan dududu abin daya faru da ita ba a ko rufa sati biyu ba, tana buƙatar yin istibura'i kafin tsyi aure, domin tabbatar da sarkin mahaifarta"

"Malam Halliru abinda nake son ka gane shine, yarinyar fa ba yanzu zasu fara rayuwar aure da ita ba, hasalima sai yaje ƙasar waje yayi wani karatu na shekara biyu,kawai uwar ce ke son aurar dashi a yanzu ba a son kowa ya sani har shi, da uta kanta Sadiyar"

Shiru ya yi na É—an lokaci, shi kuma Malam Yakubu ya cigaba da cewa.
   "Dama ce a gareka, kai da watarana na cefane ke gagararka, amma yanzu ga kuÉ—i nan wanda har aure zaka iya yi idan kasa, ita kuwa Sadiya ta samu inda zata zauna cikin aminci, idan bata nan ka huta da surutsn mutanen gari ai"
   "Yana da kyau in yi shawara kafin zartar da hukunci"
  "To shikenan, a dai yi shawarar da wuri saboda"
   
Har ya miƙe sai kuma ya zauna.
    "Ina ganin kawai ayi uren su tafi, nima sai na fi samun sukuni a cikin unguwar nan, yanzu yaushe za a É—aura?"

"Zamu je can ƙauyen Gaci, akwai wani Malamina shi ne zai ɗaura auren.

"To bara na shiga gida na kintsa sai muje"
   "To shikenan, nima zan shirya É—in"

Yana shiga gida ya tarar da Ibrahim É—in da Sadiya zaune kan tabarma, ita Sadiyar ta tura kanta a cinya shi kuma Ibrahim yana 'yar gare.

Ɗago kai tayi, tana ganin shi ne ta ƙara dunƙule jikinta guri ɗaya. Sai kuma ya ji tausayinta ya kama shi.

Shiru ya É—an yi sai kuma kawai ya juya ya wuce É—akinsa.
  Cikin shiri suka ga ya fito, da alamu dai unguwa za suje a yadda taga yaci sabuwar shaddarsa.
   "Zan fita saura kuma in dawo in ga wani baya gidan. Musamman ma kai da kake da kunnen Ć™ashi." Ya Ć™arasa msganar yana kallon Ibrahim.

"A dawo lafiya" Sadiya ta furta a sanyaye.
  "Allah ya sa" Ya faÉ—a ba tare daya kalleta ba ya fice.

*1 hour later*

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ta furta tare da dafe ƙirjinta.
   "Adda ni gaskiya ina so na fita wasa" Ibrahim ya faÉ—a yana kallonta. Ita kuma hannunta na bisa Ć™irjinta ta dafe saboda yadda taji yana bugawa.
    "To yanzu ya za ayi? Ka san dai Baba ya ce kar muje ko ina ko?"
   "Ni gaskiya Adda wasa nake son zuwa"
   "Ka ga Ibrahim, kayi wasan ka yanda kake so a tsakar gidan nan, ka manta gobe litinin akwai makaranta, ba sai kaje kayi wasa da abokanka ba"
  "Ni ban son wasa ni kaÉ—ai" Ya Ć™ara faÉ—a yana dire Ć™afa.

Ajiyar zuciya ta sauke, taji wani sabon hawaye a idanunta.
  "Kayi haĆ™uri kaji, saboda Baba..."
  "Kar ma ya haĆ™ura, ka saka Ć™afarka ka fita ka ga yadda zan É“allaka a gidan nan" Suka ji muryar Baba.

Dukkansu kallon gurin sukayi, tare yake da Malam Halliru da kuma ita Mommy É—in.

"Bismilah, ke Sadiya maza É—auko tabarma"
  Da sauri ta shiga É—aki.

Mommy kallon g9dan kawai take, tana ganin a gidan nan har akwai masu rayuwa.
  Da farko gidan ma Ć™ofar a jingine take, sai labulen buhu. Tsakar gidan gaba É—aya Ć™asa ce, sai É—aki falle biyu, É—aya na Umma da yaran É—ayan kuma na Baba, babu kitchen sai dai wata rumfar langa-langa wadda anan aka ajje duwatsu uku, sai katanga É—aya. Shi kuma kewayen shima da langa-langa aka kewaye, sai kuma aka saka labulen buhu a matsayin Ć™ofa.

"Ku zauna, bismillah" Ya faɗa yana nuna tabarmar. Mommy ta zauna tana ƙara ƙarewa ƙaramin tsakar gidan nasu kallo.

Sadiya tazo ta ajje kofin silver wanda ta cikoshi da ruwan randa.
   Har zata miĆ™e ya ce "Dakata Sadiya" Ta É—an Ć™ara duĆ™awa.

Shiru ya É—anyi yana nazarinta kafin ya ce "Wannan mutane sun zo tafiya dake ne"
    A tsorace ta É—ago ta kalli Mommy dan shi dama Malam Yakubu ta sanshi.

"Za su sakaki a makaranta sannan idan kin samu miji za suyi miki aure acan, yanzu zaki tashi ki shirya ku tafi."
   Hawaye tuni ya É“alle mata a fuska ta kalleshi ta ce "Baba dan Allah kayi haĆ™uri, na maka alĆ™awarin duk abinda kace zan yi, dan Allah Baba karka saka su tafi dani"
   "Ke ban son iskanci, idan kin zauna anan so kike mu yi ta kallon juna, kina ganin tunda kika É—auka min wannan masifar har yau ban yi bacci awa uku ba, kullum da baĆ™in ciki nake kwana kuma nake tashi, dalla ki É“ace min da gani." Ya Ć™arasa maganar da tsawa, ita kuma da sauri ta tashi hankali a tashe.

Ɗaki ta faɗa, ta haye katifarsu ta dunƙule jikinta tana kuka, shima Ibrahim ya shigo ɗakin yana kuka.

"Malam ya kamata ka bita a hankali, domin abinda ya faru da ita ƙaddara ne"
  "Malam Yakubu wannan yara na zamani idan kace zaka lallaÉ“asu to iskaci zasu riĆ™a yi, gara nayi mata hakan"
   Ita dai Mommy kallonsu kawai take tana Ć™ara jin É“acin rai.

*I need more comments please*