...BASHI!

Page 4

by @sanazty

*...BASHI!*
   _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*K.W.A*

_Sadiya S. Adam🌸✍️_

                   Page 4

__________🖌️"Yaya ka bani number ɗinka" Safiyya ta faɗa da zumuɗi.
    Aziza kallonta tayi a ɗan tsorace, sai kuma tayi murmushin yaƙe ta ce "Oh wato ba zaki ce na baki number ɗina ba sai tashi ko?"
   "A'a Aunty Aziza kema fa ina so na karɓi taki, kawai dai..." Sai tayi shiru kuma.
  Fa'iza kuwa kallon banza kawai ta watsa mata.

"Wayata ko sim card babu, amma ki karɓi ta Aziza sai mu riƙa gaisawa"
   "To shikenan" Ta furta tare da miƙawa Aziza wayarta ƙirar Android Pop 2.

Tana saka mata number ɗin ta miƙe tare da faɗin "Bari naje na dawo, na ɗan barku kar na cikaku da surutu"
   Tana fita Fa'iza ta ce "Wannan kucakar wai tana da gots ɗin ta ce Yaya ya bata number.
   "Ni fa bama wannan bane a raina, ganin yadda ta zaƙe ne ya saka na fara tsoron kar abinda ya faru da Amira itama ya faru da ita."
   "Stop saying that! Insha Allah norhing will happen to her, da izinin Allah Amira ce last person da zata mutu a kaina"
    "Low your voice Yaya" Fa'iza ta furta a ɗan furgice.
   
     ***** ****** *****

Kuka sosai take, kayanta na bakkont ta rungume bakkon tamau kamr wani zai ƙwace mata.
   Ibtahim ya ƙaraso da sauri tare da faɗin "Ni dai Baba sai dai na tafi da ita" Sai kuma ya fashe da kuka.

Cikin ƙuɓar rai Baba ya kalleta ya ce "Wallahi idan baki bar kukan nan ba, sai na lakaɗa miki duka kuma ki tafi da kumburarrar fuska."
   Jin haka ya saka ta ɗan rage sautin kukan tare da faɗin "Ina so muyi sallama da Umma"
   "Ba zakiyi ba, munafuka, ita Ummar na faɗa mata, amma wallahi babu inda zan bari ki tafi, ai dama tunda kika fara yunƙurin guduwa na san akwai abinda ke ranki, kuma ki daina kuka kar ma mu fita waje mutane suyi tunanin sayar dake nayi"

"Malam Halliru ba ayi wa yaro haka." Ya mayar da kallonsa ga Sadiya ya ce "Kin ga ki kwantar da hankalinki Sadiya, kinga wannan da kike gani ƙanwata ce, kuma zata tafi dake ne ta sakaki a makaranta ki ƙarasa karatunki, idan an kwana biyu mutane sun manta da abinda ya faru, zata dawo dake, sannan Ummar taki ni da kaina zan kawo miki ita idan an kwana biyu kin ji" Kai ta gyaɗa tana matsar hawaye.

"Yauwa wanke fuskarki kin ji, ki daina kuka, kin ga kin ɓatawa Babanki rai, ga ƙaninki ma kin saka kuka, ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru." Kai ta gyaɗa, sannan ta ajje bakkon ta nufi inda buta take ta ɗauka.

_Wai wannan 'yar ƙauyen ace ita ce matar Muhasin, it's a shame wallahi._ Mommy ta furta a zuci, tana kallon Sadiya da take wanke fuska da ruwa.

A cikin mota suka tarar da su Muhasin ɗin, dan already har sun shiga.
    "Shiga ciki" Mommy ta faɗa tana kallon Sadiya.

Sai da ta juya ta kalli Babanta da kuma ƙannenta sannan ta buɗe murfin motar, amma ta kasa, sai da Malam Yakubu ya buɗe mata sannan ta shiga, bai rufe ba saboda Mommy zata shiga.

"Who is she?" Fa'iza ta faɗa tana kallonta a sheƙe.
  "How will I know" Aziza ta faɗa, shi kuwa Muhasin juyowa ya yi ya kalleta sannam ya juya.
  "Ke kuma wacece?" Aziza ta kalleta tana kallonta.
  "Sadiya..!" Ta furta a sanyaye.
   "Kin ga mu ba sunanki muke buƙata ba, mene ya shigo dake..." Ganin Mommy ya saka duk sukayi shiru.

"Mommy wannan villager ɗin da ita zamu tafi, ni wallahi perfume ɗin da tayi using gaba ɗaya ya isheni wani wari"
   Dara-daran idanunta ta bita dashi, dan taji abinda suka ce.

Tana ji Mommy na faɗin ita ɗin sabuwar ƴar aikin da ta ɗauka ne, tana jin yadda suke zaginta da kushe halittarta da bata da wata makusa. Basu san tana jin duk abinda suke faɗa ba, domin Sadiya tun tasowarta macece mai son karatun shiyasa ko a makaranta tana daga cikin best student.

Wasu hawaye masu zafi ne suka samu damar zubo mata, kenan Baba aikatau ya kaita da ya ce karatu za taje tayi.
   _Ya rabbi, ka sani bada son raina aka yi min fyaɗe ba, ban kuma san waye ko dalilinsa na aikata haka ba, Allah ina roƙonka daka ƙwatar min haƙƙina, ka kuma tozarta koma waye daya wulaƙanta rayuwata da kuma raba kan ahalina, muna riƙe talaucinmu, muna tattala rayuwarmu, amma komai ya tarwatse a yanzu._ Ta furta a zuci. Idanuwanta tuni sun yi jajir.

            *** **** ***

"Nan shi ne ɗakin ki, da safe zaki ji sauran bayani daga Mommy" Aziza ta faɗa. Ita dai Sadiya da ido ta bita har ta bar ɗakin.

Kallon katifar tayi, tare da zama akai. "Na shiga uku" Ta faɗa tare da saka kanta a gwiwa ta fashe da kuka.
    
"Lafiya kike kuka?" Da sauri ta ɗago kai ta kalli wadda ta shigo da kula a hannunta.
   A gabanta ta ajje tare da kallonta. "Ya sunanki?"
   "Sadiya?" 
"Karki damu, wannan shine karonki na farko da aiki ko?"
   Kai ta gyaɗa alamun eh.
  "Karki damu, insha Allah zan taimaka miki wurin yin wasu abubuwan, yanzu dai ga abinci kici, sai ki samu ki kwanta na san kin sha hanya."
Kai kawai ta gyaɗa, ita kuma ta miƙe. Har ta kusa ƙofa ta juyo ta ce "Sunana Fatima.

Tana fita si kuma Aziza ta shigo.
"A'a waye ya kawo miki abinci?"
"Wata ce"
"Wata wa? Wadda muka zo da ita?"
"A'a ni ta ce min sunanta Fatima"

Aziza sakin robar takeaway tayi sannan ta dafe ƙirji "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da sauri ta juya ta bar ɗakin.

Sadiya kasa zama tayi, dan bata fahimci komai ba. Tare da Mommy da Muhasin suka dawo.
  "A ina ta kawo abincin kuma me ta ce miki?"
  "Ta ce naci abinci sai na kwanta na huta. Kuma ta ce za ta taimaka min"
   "Ya ilahi...!"
A tsorace take kallonsu, taga duk tashin ya bayyana a fuskarsu.

"Babu komai kawai, ku wuce mu tafi, ke kuma karki ci wannan abinci, ga wanda zaki ci, saboda wannan ɗumame ne na jiya."

"But Mommy!"
"Hold on Muhasin, ku wuce kawai muje"
Har suka bar ɗakin Sadiya bata zauna ba. Dan ita sam ta kasa gane tsoron na mene.
  "Ko dai step mother ɗin su ce?"
Baki ta taɓe sannan ta zauna ta buɗe flask ɗin.

Lafiyayyar friedrice taji mai da hanta.
Robar takeaway ɗin ta buɗe white rice and stew sai kaza a ciki.
  Ajiyar zuciya ta sauke, tana tunanin wanɓe zata ci.

"Mommy yarinyar nan a mayar da ita gidan su, dan ina ganin gara a ɗauko ƴan aiki ko guda biyu daga Abuja, wanda sun san situation ɗinmu kuma zasu iya zama damu."
   "Muhasin kai baka fini sanin abinda ya dace da nayi ba, dan haka ka ƙyaleni kurum"

Aziza ta gyara zama ta ce "Amma ina ganin maganar da Yaya Muhasin ya faɗa gaskiya ne, domin ni a ganina ai wannan itama bata wuce a kula da ita ba, ba fa zata iya aikin gidan nan ita kaɗai ba, kina ganinta kin san bata fi sa'ar Fa'iza ba"
   Muhasin ya ƙara da faɗin "Nima abinda na gani kenan, me yarinyar nan za ta iya dan Allah, haba ni wallahi bana son wani ya raɓemu matsala tazo ta sameshi ace mune da laifi."
   Tsaki Mommy tayi tare da faɗin "Sai kuyi, domin ni ba zan tsaya biyewa ahirmenku ba"
 Tashi tayi ta bar ɗakin, Aziza ta kalleshi ta ce "Ni yarinyar ma tausayi take bani kamar tana cikin damuwa"
  "Koma dai mene ni bana son matsala shiyasa ma sam yanzu bana son ganin ko wace mace indai ba ku ba"
   "Insha Allah komai zai zo da sauƙi"
 
*2 days later*

"Ni Daddy ban sani ba, Mommy ta ce dai yanzu transfer ma za a yi min, domin mun dawo nan gaba ɗaya da zama." Fa'iza ta faɗa tana fitowa cikin parlour.

"Daddy wallahi Abuja babu daɗin zama ni gara Kaduna ɗin ma, saboda akwai ƴan uwa da kuma friends"

Zama tayi kan kujera sannan ta cigaba da cewa "Daddy ni dai gaskiya 50k ya yi min kaɗan wallahi, har abayas nake son saya fa"
  Kallon banza Aziza ta watsa mata, sannan ta cigaba da danna laptop.
  "Love you" 
Tana cire wayar a kunne ta kalli Aziza ta ce "To kuma mene na hararata"
  "Kin dai san aiki nake bana son kizo nan ki takura min"
  Taɓe baki tayi tare da faɗin "Naji" Ta furta tana taɓe baki.

Mommy data fito daga side ɗinta ta zauna tare da faɗin "Meyasa indai kuka haɗu sai kun yi faɗa."
  "Mommy daga ina waya da Daddy shikenan fa ta wani fara hararata"
    "To yanzu dai va wannan ba, ina waccan yarinyar nan?"
   "Tana kitchen na saka ta haɗa min fruit salad"
   "Aziza meye amfanin Mariya da Hajara dana saka su zo jiya, ita wannan ku daina saka ta aiki"

Fa'iza sakin baki tayi ta kalli Mommy ta ce "To ita mene amfaninta a gida?"
   "Ni dai na faɗa muku ku daina saka ta aikin komai"
   "Amma Momm..."
"Rufa min baki Aziza dan na san ke dama ko wace magana nayi kina son musa min"
  "Yi haƙuri Mommy" 

       **** ***** *****

"Na rantse da Allah ba zan yarda ba sai ka faɗa min inda ka kai min 'yata" Umma ta faɗa rai a ɓace a kuma lokacin ta fuzgo Ibrahim suka fito daga gidan.

"Wane irin hauka ne haka, oh kin zo ki tara min mutane ne?"
   "Koma mene zaka faɗa ka faɗa, me tayi maka ita ta aikata laifin? Kawai sai ka tsani yarinya, ka kuma ɗauketa ka kaita can wani gurin, ka hukuntani su kuma in baka iya riƙonsu ai ni zan iya, to na rantse da sake ba zai yuwu ba, kuma Ibrahim ma ba zi ƙara ko kwana ɗaya a gidan nan ba"
  Yara da matan unguwa gaba ɗaya sun taru, Malam Yakubu ya ƙaraso tare da faɗin "Haba Lami bai kamata ba"
   "Dama ai zaka ce haka baƙin azzalumi, ai dama ance da kai aka haɗa baki wajen ɗauke Sadiya, to na rantse da Allah muddin baku dawo min da ita ba, sai na kaiku ƙara"

Shiru Malam Yakubu ya yi, jin tana neman kunce masu zane a kasuwa.
  "Dan Allah ki tafi yanzu ma ki kai kotu, ki gani waye a wahale? 'Ya daitawa ce, kuma nine ke da haƙƙi a kanta"
   "Haƙƙi ko, to wallahi baka isa ba" Jan Ibrahim ta yi suka wuce.
   Baba na ƙoƙarin bin ta Malam Bala wanda gidan shi ke daga gefe ya yi saurin riƙo hannunsa "Ka barta kawai, har zuwa lokacin da zata huce"

     ****** ****** ******

Sai data sake juya zoben a hannunta sannan ta mayar.
   Zama tayi gefen katifar, a ranta ta ce "Allah sarki yanzu class mate ɗina suna can suna jarabawar WAEC" Ta furta a fili, sannan ta yi murmushi ta ce "Allah sarki Kausar na san ta ji ni shiru, yanzu shikenan ba lallai mu sake haɗuwa ba" Ta ƙarasa maganar tana goge hawaye.

"Sadiya...!" Taji an ambaci sunanta da ƙarfi. Ɗan juyawa tayi a tsorace sannan ta sauke ajiyar zuciya dan a tunaninta gizo ne.
  Jin an taɓa kafaɗarta ya saka ta juya, ganin wata mummunar halitta ya saka ta kaɗa ƙara tare da miƙewa ta maƙale a bango.
   Tafi mintuna biyu a haka sannan ta sake jin sunanta ya karaɗe ɗakin.

"Umma...! Umma!! Umma!!!" Shine da take ta faɗa cikin tashin hankali.

Aziza da take jiyo ihun Sadiya da sauri ta miƙe, Mommy tayi saurin dakatar da ita.
  "Amma naji tana ihu ne"
  "Eh nace karki je, ki barta kawai"
   "But Mommy why?" Ta furta kamar za tayi kuka.

"Ƙanwar uwarki ce? To kada ki sake kije in ba haka ba sai na saɓa miki"
    "Kenan kin ɗauko ne da wata manufar?"
   "Ni ba macuciya bace, amma zan iya komai saboda lafiyar ɗana"
  "Itama 'yar wani ce Mommy" Aziza ta faɗa tana goge wahaye.

Ta ɓangaren Sadiya kuwa a tashin hankali take sosai. Ji tayi ana ta buga ƙofar toilet ta runtse idanunta taƙi ta buɗe.
    "Sadiya... Ki buɗe ido... Ni ce Fatima... Nazo ne na baki wani labari...." A hsnkali ake maganar, ita kuma tana faɗin "A'a"
   "Ki buɗe ido Sadiya...." Taji kamar ana hura mata iska a fuska.
  Tana buɗe ido taga mace da zaƙo-zaƙon haƙora jini na zuba a jiki, sai kuma idanunta suma ƙwala-ƙwala kuma jajir.
  A take a gurin ta sulale ta suma.

       ****** ***** ******

Kallon mutumin ya yi jikunsa ya fara jin ba daɗi.
   "Visa ɗin zan iya samu kwana kusa?"
  "Insha Allah, da ta fito zan kiraka"
  Kai ya ɗaga sannan ya miƙe ya fita.

Tana tsaye daga jikin motarsa, tana taunar chewing gum.
  
"Barka da fitowa haɗaɗɗe"
  Kamar ba zai mata magana ba, dan har yaje kusa da motar sannan ya juyo ya kalleta 
   "Ki ɗan matsa ina son ɗaukar motana"
  
Murmushi tayi, ta ƙaraso gabanshi tana kaɗa mukullin motar.
   "Yanzu ka fahimci cewar motar tana ƙarƙashin ikona"
 "Amma how comes?"
"Kana fitowa ka wuce a gogice baka zare ba, shi ne na jare na kuma tsaya jiranka"
  "Ina godiya sosai"
"Ni ba godiyarka nake so ba, so nake ka biyani kawai"
"To nawa kike so na baki?"

"Haba ɗan samari, ni bana son kuɗi"
"To me kike so?"
"Zan faɗa maka" Ta buɗe jaka ta ɗauko kati tare da faɗin "Ga kati na, zaka iya nemana, mu haɗu da ƙarfe 8 na dare a Habib Hotel"
   "Hotel kuma? Why not mu haɗu a ko Galaxy ne?"
  "No bana zama irin wannan public guri,i need privacy"
  Shiru ya yi, sannan ya kalleta ya ce "Ba zan iya zuwa ba"
  "In har baka zo ba, to baka min adalci ba"
  "Ba zanje hotel ba gaskiya"
  Hannu ya saka zai karɓi wayar, sai kuma ta janye.
   "To kazo gidanmu"
 "To wai mene kike son sanar dani ne?"
  "Wani sirri"
"Sirri name kenan?"
 "Si kazo zaka ji, ai na san kana son sanin waye kai?"
"Ban fahimceki ba"
Miƙa masa key ɗin tayi yaƙi karɓa.
  "Ki faɗa min abinda kike nufi"
Kawai gani ya yi taja hannunta ta damƙa masa.

Juyawa tayi cikin rangwaɗa ta bar guri. Shi kuma da ido kawai yake bin ta. "Ya ilahi, wannan wace irin macece haka"
   "Hmmm!" Ya yi ajiyar zuciya tare da girgiza kai, ya kuma buɗe mota ya shiga.

          ***** ***** *****

"Mommy ni gaskiya zan je naga halin da waccan yarinyar take ciki"
   "Ba zaki je ba"
"Akan me? Kina ji yadda take ihu fa, haba Mommy" Ta furta tare da fashewa da kuka.

Itama Mommy kuka ta fara, tana faɗin "Kun san dai ba zan taɓa yin abinda zan cutar da wani ba"
    "Amma ai haka kika ce, duk son da zaki yiwa wani bai kai wanda zaki yiwa ƴaƴanki ba, itama ɗayar wani ce, kuma na tabbatar iyayenta na matuƙar ƙaunarta" Ta faɗa tana goge hawaye.

"Lafiya kuwa?" Suka ga Muhasin ɗin ba tare da sun san ya shigo ba.
    Dukkansu babu wanda ya iya cewa komai.
   Jin wani gigitaccen ƙara ya saka ya kalli gurin.
   "Ihun mene haka?" Ya faɗa yana kallonsu.

Babu wanda ya yi magana dan haka da sauri Muhasin ya nufi side ɗin.
   "Dakata Muhasin!"
Shima Mommy ta dakatar dashi, aikuwa ya tsaya tare da juyowa ya kalleta a tsorace.

"Karkaje inda take"
"Meyasa?"
"Ba sai kaji dalili ba"
"Mommy ba zan yarda a yi kisan a gabana ba" Yana gama faɗa ya miƙe da sauri, su kuma suka rufa masa baya.

Yana shiga ya tsaya cak, jikinsa na kyarma, lokacin da suka ga Sadiya a kwance an yanka mata wuya.
   "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Aziza ta faɗa tare da suma a gurin.

           **** **** ****

"Lafiya ƙalau muka yi sallar asuba sashi, mukayi sallama y shiga gida nima na shiga nawa gidan, to waye za ace daga gabannin asuba zuwa yanzu ya shiga gidansa har ya masa yankan rago irin haka." Malam Yakubu ya faɗa, yana daga gefe tare da sauran gungun mutane da suka taru a ƙofar gidan Malam Halliru.

Asp Ahmad Indabawa ya matso kusa da dattajawan unguwar tare da gabtar da kan shi a gurinsu, sannan ya ƙara da cewa "Shin baya da mata ne? Shi kaɗai yake rayuwa a gidan?"
   "Eh to, a baya yana da mata, amma da wani al'amari ya gitta sai suka rabu da matar, wanda yaran nashi a hannunsa suke, daga bisani kuma yau ku san sati kenan yana rayuwa shi kaɗai." Malam Yakubu ya yi maganar dan shi ne mafi kusa da Malam Halliru.
  "A kwanan nan, babu wani wanda suka samu saɓani dashi?"
  "Gaskiya babu, sai matarsa da tayi hayaniya dashi akan yaran har ma tayi iƙirarin kai shi kotu, kuma mutane da dama za su shaida haka, domin anan waje sukayi hayaniyar amma ita ɗinma tana gidansu kuma gidan yana da nisa da nan"
  "Za a rakani domin zan so muyi magana da ita."

"Oh rayuwa kenan, Allah sarki Malam Halliru baya da abokin faɗa, yana da tsare mutunci da kima na kansa da iyalinsa amma ƙarshensa ya kasance a haka, aka yiwa ɗiyarsa fyaɗe, yanzu kuma aka samu wani azzalumin ya yi masa yankan rago"
   "Ni fa da duku-dukun dfiyar nan naga wata budurwa ta fito daga gidan, fuskarta sanye da niƙabi shiyasa ban gane wace ba."
   "Amma Isma'il ya kamata kayiwa 'yan sanda wannan bayanin"
  "Taɓ wallahi ba ajin mutuwar sarki a bakina, domin kuwa yanzu idan suka fara tuhumata, sai na gwammace kiɗa da karatu."
   
        ***** ***** *****

Doctor na fitowa suka miƙe da sauri, tare da ƙarasa inda yake.
   "Doctor ya jikin nasu?"
  "Gaba ɗaya da sauƙi, ku kwantar da hankalinku, ita wadda ta suman shock ne ya jawo hakan, taga abinda ya furgitata, yanzu haka ma allurar da akayi ta bacci itace ta saka bata farka ba, saboda muna so ƙwalwarta ta samu hutu"
    "Ɗayar fa?" Muhasin ya faɗa a sanyaye.
  "Ku biyoni office ɗina, zan maku bayani akan ta" Kallon Mommy ya yi, wadda gaba ɗaya a sanyaye take.

Doctor na wucewa suka rufa masa baya da sauri.
  A office ɗin duk sun zauna, sai dai hankalinsu yaƙi kwanciya ganin yadda yaƙi cewa komai.
   "Doctor ko dai ta mutu?" Muhasin ya faɗa hankali a tashe.

"Bata mutu ba, amma tana cikin mawuyacin hali."
  "Wane hali ne, dan Allah Doctor ka daina tsayawa kayi mana bayani yadda zamu fahimta.

"A gaskiya ba lallai ta ƙara takawa da ƙafafuwanta ba, saboda buguwar da tayi ya saka spinal cord ɗinta ya yi collapse, sannan kuma gaba ɗaya ƙodar(kidney) dake jikinta duka biyun sun samu matsala, dole a canza cikin gaggawa ko kuma ta rasa rayuwarta baki ɗaya.

*Masu sauraro kun ji fa, me zaku ce game da wannan? Ina jiran jin ta bakunanku*

Sadeey ce✍️