Page 5
by @sanazty
*...BASHI!*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
*K.W.A*
_Sadiya S. Adam🌸✍️_
Page 5
__________🖌️"Kidney kuma? To wace irin bugawa ce wannan da har zai ja mata matsala a spinal cord? Na shiga uku. To Doctor ya batun yanka data samu a wuyanta?" Mommy ta faɗa tare da fashewa da kuka.
"Ba kuka zaki yi ba Hajiya, mafita ya kamata a samu wurin ceto yarinyar nan, domin gaskiya idan ba ayi aikin nan ba za ta iya rasa rayuwarta. Maganar yanka a wuya kuma ai dama babu yanka a wuyanta, goshinta ne kawai ya fashe."
Cikin tashin hankali Muhasin da Mommy suka kalli juna, dan sun san dai tabbas sun ga yanka a wuyanta, amma kuma ya ce babu.
"Lafiyarta ƙalau dana ɗauko ta daga gidan iyayenta, kuma yanzu ace ta samu matsala a ƙoda har duka biyu, sannan kuma ga rashin takawa, me zan faɗawa mahaifinta?"
"Doctor yanzu mene abin yi?" Cewar Muhasin.
"Anan zamuyi iya bakin ƙoƙarin mu, amma abu ne da yake buƙatar kuɗi, ƙoda kaɗai zaku iya samunta a miliyan 8 zuwa gobe, shi kuma spinal cord ka san dai baya gyaruwa."
"Miliyan 8" Ya maimaita tare da kallon Mommy.
Da sauri ta tashi ta fita. Shi kuma ya kalli Doctor ya ce "Zan yi magana da ita sai kaji feedback"
"To babu damuwa, ina sauararku"
"Kana ji Malam,ni dai ban san ya zanyi da yarinyar nan ba, gaba ɗaya sun yi rugu-rugu da rayuwarta, duk da kwana biyu Muhasin bai yi komai ba amma ni dai hankalina a tashe yake, yanzu haka muna asibiti"
Daga ɗayan ɓangaren Malam Yakubu ya ce "To ai dama yarinyar a matsayin hadaya ce, dan haka komai zai iya faruwa"
"Duk da ka faɗa min, amma hankalina ya tashi, yanzu haka tana asibiti fa, kuma ance gaba ɗaya ƙodarta ta lalace sai an saka mata, sannan ance ba za ta ƙara taka ƙafafuwanta ba"
"Kin ga ki kwantar da hankalinki, yanzu haka case ake jiya an shiga har gidan su yarinyar an yiwa mahaifinta yankan rago, to hankali duk ba a kwance ba, yanzu haka zaman makoki ake."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
"Karki ɗaga hankalinki, zuwa anjima zan kiraki yanzu ba a nutse nake ba."
Tana sauke wayar ta jingina da bango. Hankalinta gaba ɗaya a tashe yake.
Fa'iza ce ta faɗo mata, dan haka tayi saurin kiranta.
"Mommy...?"
"Kina ina ne?"
"Ina gidan su Hibba"
"To karki koma gida, ki bari zan kiraki idan mun koma"
"Mene ya faru?"
"Babu komai, kin dai san matsalar gidanmu, kuma gaba ɗaya bamu nan munje unguwa, so idan na dawo I'll let you know"
"Alright! Allah ya dawo daku lafiya"
"Amin."
_Dole in bar garin nan, dole inyi nesa da mutane, domin na san komai yana faruwa ne a dalilina, yanzu abin har ya fara shafar wanda basu ji ba basu gani ba, abin ya fara dawowa kan 'yan aikin gidanmu, ba zan iya zama ina ganin mutane na rasa rayukansu ta dalilina ba._
"Muhasin..." Jin an kira sunansa ya saka ya ɗago.
Zama tayi a gefensa sannan ta ce "Ya kuka yi da Doctor?"
"Na biya kuɗin gado da magungunan da aka yi amfani dasu. Amma kuma ya ce min dole sai an sakawa waccan yarinyar ƙoda"
"To ina zamu samo wata ƙoda fisabilillah"
"Sune zasu nemo, suna buƙatar kuɗi ne kawai"
"Har nawa?"
"Almost 10M"
"What...? Ina muke da wannan kuɗin?"
"Nima na rasa mafita, ya ce idan har ba ayi da gaggawa ba zata iya rasa rayuwarta"
"Gaskiya sai dai na kira iyayenta su san abin yi"
"Mommy im har wannan gidan nan ne gidan su yarinyar nan, to gaskiya basu da wannan kuɗi, kina ganin yadda suke a ƙuntace fa. And a gurinmu ta samu wannan ciwo dan haka muke da alhakin ɗaukar nauyin nemo mata magani"
"Wannan ba hujja bane, tunda bamu muka ɗaura mata ciwo ba"
"Mommy kawai ki sanarwa Daddy saboda idan yarinyar nan ta rasu ba zamu fita ba"
"Mommy dani dake fa gaba ɗaya mun ga an yanki yarinyar nan a wuya, amma abin mamaki sai gashi anan babu komai, shin baki tunanin matsalata ce ta shafeta?"
"Ai dama na san sai ka faɗi haka, shikenan ko wace ƙaddara sai kace kaine silarta"
"Ai naga lokacin da na shigo kin hanani shiga, kuma irin abinda ya faru da ita shi ne ya faru da Zainab macen dana fara so a rayuwata, ita cewa akayi kayan cikinta gaba ɗaya sun lalace, kwana 10 cif tayi a asibiti ta rasu."
"To wannan ɗin ma ko cewa kayi kana sonta?"
"Ni ko sunanta ban sani ba, sannan tun ranar da muka dawo daga Gaya wannan shi ne gani na biyu da nayi mata"
"To ka san da haka shi ne kake son mayar da laifin kan ka"
Shiru ya yi dan ji ya yi zuciyarsa na raɗaɗi.
***** ***** *****
Kuka sosai Umma takeyi, dan ko 'yan gaisuwa bata iya amsawa, duk da basu tare da Baba amma tabbas taji mutuwarsa.
Dhigowar wata budurwa ya saka duk ɗakin aka yi fara amsa gaisuwar da takeyi.
Ta matso kusa da Umma tayi mata gaisuwa, ita kuma kai kawai ta gyaɗa.
"Ibrahim ko?" Ta faɗa tana shafa kanashi, ita kuma Umma ta ɗago tana kallonta a ɗan tsorace dan bata taɓa ganin fuskar ba, kuma ta ganta sam batayi kama da wanda zasu zo mata gaisuwa ba.
"Ibrahim ya jikin Sadiya?"
Jin haka ya sak Umma miƙewa tare da faɗin "Ke kuma wacece a ina kika sanmu?"
"Lafiyarki kuwa Lami"
"Inna ni sam ban yarda da wannan ba, ta wani zo tana min maganar ya jikin Sadiya, to ma mene haɗinmu da ita"
"Wa kenan?" Ladi tayi tambayar.
"Gata nan wadda ta shigo tayi gaisuwa yanzu." Ta ƙarasa tana nunata da yatsa.
"Waye ya shigo, mu ai bamu ga kowa ba?"
"Haba Umma gata nan a zaune kusa da Habiba"
Ai jin haka ya saka Habiba ta ɗan zabura sannan ta kalli gurin tana faɗin "Nan ɗin da babu kowa."
Kallon budurwar tayi taga tana mata murmushi, aikuwa a take a gurin ta zube.
***** ***** *****
"Ba zan samu dawowa ba yanzu akwai aikin dake gabana"
"Amma Daddy matsaloli sai faruwa suke ya kamata ka dawo ka ga halin da gidan nan ke ciki"
"Aziza idan na dawo muka zauna nan, waye zai nemo abincin da zaku ci,bare har ku samu damar yin karatu, komai ina yine domin na rufa muku asiri"
"Daddy gaskiya ya kamata ka duba lamarin nan, and we need almost 10M saboda yarinyar dake kwance asibiti"
"Aziza kina da hankali kuwa? Ina naga wannan maƙudan kuɗaɗe idan ba kadarorina zan sayar ba, kuma ma kawai sai in turo har wannan uban kuɗi ayi wa bare aiki, va zai yuwu ba, ku mayarwa da iyayenta sune ke da alhakin su nemo mata lafiya"
"Amma Dad..." Ƙit taji ya kashe. Ranta a ɓace ta kalli Mommy.
"Gaskiya ba daidai bane abinda Daddy keyi haba dan Allah"
"Ba zai biya ba ko?"
"Haka ya ce, kuma yaƙi dawowa"
"To ni kam ban san ya zamuyi ba, ga Mommy ta fita tun ɗazu"
"Ina tunanin asibitin taje ta duba yarinyar"
"Ina ta jin haushin yarinyar nan amma yanzu wallahi tausayi take bani."
Muhasin miƙewa ya yi, Fa'iza ta ɗan kalleshi a tsorace.
Aziza ma da sauri ta miƙe tana ƙoƙarin tarar gabanshi.
"Ina zakaje kuma?"
"Zan je asibitin"
"A'a Yaya ka bari ta dawo sai muje"
"Aziza hankalina ya kasa kwanciya"
"Na sani amma kayi haƙuri."
***** ***** ******
"Idan aka kaita can Dala sai tafi samun kulawa, daga nan kuma ka biya kaje a sanarwa iyayenta dan a samu mai jinyarta" Mommy ta ƙarasa maganar tana faɗawa Likitin da ta bawa maƙudan kuɗi ta saka aka yiwa Sadiya transfer zuwa asibitin ƙashi na Dala dake can kano.
"A matsayinmu na likitoci da zamu ɗauketa da motar asibiti mu kaita can, bamu da damar zuwa ko ina sai dai mu dawo nan, da ace ma a Kano iyayen suke da sai naje amma gaskiya hakan ba mai yuwuwa bane"
"Shikenan zan yi magana dasu a waya."
"Yauwa"
**** ***** *****
Malam ya kalleta ya ce "Ki cigaba da addu'a Lami, insha Allah komai zai zo da sauƙi"
"Ina Sadiya? Ina aka kai min ƴata ne?"
"In sha Allahu Sadiya zata bayyana, ƙoƙarin da nake fa na ganin naje gidan Malam Yakubu domin shi ne maƙocinsa, to kuma naga 'yan sanda suma suna ta bincike akai shiyasa kawai na ɗan dakata da nawa."
"Inna ni zan je na tambayeshi" Kina wannan ciwon ina zaki..." Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Suka ji Baffa ya kwaɗa salati a sakar gidan.
A ruɗe suka fita, har ta manta da ciwon dake jikinta.. "Malam lafiya kuwa? Ka razana mu wallahi, ka san jiya aka shafe makoki yau kana rafka irin wannan salatin ai sai mu ruɗe."
"Ai nima ban san nayi ba Asabe. Yanzu aka kirani ake sanar min an kai Sadiya can asibitin ƙashi dake dala"
"Wace Sadiya kuma? Sannan daga ina aka kawo ta?"
"To ina zan sani, a waya aka kirani aka sanar dani"
"Mun shiga uku" Umma ta faɗa tare da zubewa a gurin ta fara tir,ar kuka.
**** **** ****
"Ke....!" Sakin butar hannunta tayi ta shiga ɗaki da gudu.
"Lafiya Safiyya? Kin wani faɗo mana ɗaki a haukace"
"Inna wallahi ji nayi an min magana a ƙofar banɗaki..." Bata ma ƙarasa faɗa ba kawai sai ganin mace tayi a gabanta, fuskarta kaca-kaca da jini, ga zaƙo-zaƙon haƙora da kuma wani dogon gashi.
Kafin tayi magana tuni ta cafki wuyanta, tare da fizgo jijiyar gurin.
Kakari kawai Safiyya keyi, idanunta gaba ɗaya sun juye.
"Safiyya? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Inna ta furta hankali tashe tare da fita tsakar gidan tana kuwwa.
Malam cikin tashin hankaƙi ya nemo ɗan sahu aka tafi da ita asibiti, sai dai duk wani gwaje-gwaje da aka bata baya nuna komai. Hakan ba ƙaramin ɗaga hanklin Malam ya yi ba.
Har safe ana abu ɗaya, bata gane wanda ke kanta, ba kuma ta iya komai face wannan kakarin.
"Ki tambayar min ɗanki shin ya ce yana son Safiyya ɗiyata, domin alamu suna nuna ciwonta bana asibiti bane, gata nan rai hannun Allah" Yana gama faɗa ya kashe wayar, tare da ƙudirin inda matsalar daga gurin Muhasin ne ba zai lamunta ba.
****** *******
"Mommy what's wrong?" Cewar Fa'iza.
"Wai ɗiyarsa ce ke kwance an rasa mene yake damunta, shi ne yake so na tambayi Muhasin."
"God forbid me zai yi da wannan talakar kuma 'yar ƙauye, su je can su nemi wanda dai suke zargi."
Aziza data fito ta zauna, kallon Fa'iza tayi sannan ta ce "Ai idan aka ce wani abu ya sameta ba zan musa ba, dan ni nayi mamaki da har ta daɗe haka lafiya"
"Kenan kin san wani abu?"
"Ba ma ni kaɗai ba Mommy, dukkaninmu akwai abinda muka sani game da hakan. Domin ranar da muka je Gaya, yarinyar tana ta rawar kai, har ma ta ce ya bata number, sai dai bai bata ba, ya ce ta karɓi tawa. Kuma ko da ta karɓa ɗin basu taɓa waya ba, domin dama ya ce duk sanda ta kira ince baya nan, kuma haka na riƙa yi, kawai dai ta yuwu abinda ya faru da Amira ne ya faru da ita"
"Ya ilahi? Wai mene ke son faruwa damu?"
"Ƙaddara ce kawai Mommy, mu barwa Allah komai mu kuma cigaba da addu'a."
"Ina so kar Muhasin yaji komai game da wannan, domin na waccan 'yar aikin ma fushi yake dani"
"Mommy koni ban ji daɗin abin nan ba, me 200k zatayi musu? Ko kuɗin magani ba lallai ta gama saya ba, bare har akai ga aiki. Momny mutanen dake neman almost 10M amma an haɗasu da 200k"
"Aziza idan ba sata kike so nayi ba, ta ina An fara nemo wannan kuɗaɗen?"
"Amma Mommy ya kamata ace ko 3M ne atleast ki basu"
"Kenan sai na jaɗa da sayar da Motocinmu da kuma gwala-gwala, kin ga ban son wannan banzar maganar, ni abinda naga ya kamata shi ne nayi"
Aziza bata ƙara cewa komai ba dan ta rasa abin faɗa ma.
Ganin zaman ba mai yuwu bane, kawai ta miƙe ta nufi side ɗin Muhasin.
"Mommy wai meyasa kwana biyun nan faɗa kawai kike?"
"Fa'iza dole nayi faɗa, inji da ku inji da mahaifinku, shi yana ɓatan rai kuma kuma faɗa min"
Hawayene ya fito daga idanuwanta, da sauri Fa'iza ta miƙe ta koma kujerar da Mommy take. "Kiyi haƙuri Mommy, insha Allah ba zamu sake ɓata miki rai ba"
Hannu Fa'iza ta saka tana gogewa Mommy hawaye.
Tana tura ƙofar ta tarar dashi can ƙarshen gado a zaune, ya haɗe jikinsa guri ɗaya.
A kan sidw drawer ta zauna tana kallon shi kafin ta ce "Yaya lafiya ɗai ko?"
"Jikina ne bana jindaɗi Aziza"
"Sannu Yaya, Allah ya sawwaƙe"
"Amin ya rabbi."
"Aziza.." Ya furta sunan nata a sanyaye.
Kallonshi take cike da tausayawa kafin ta ce "Ina jinka Yaya"
"Nayi tunanin tafiya na barku ba tare da kun sani ba, amma kuma sai nake ganin kamar na muku rashin adalci"
"Akan me zaka tafi, zama tare damu yafi maka daɗi tunda ko babu komai mun san matsalarka kuma zamu riƙa tausarka"
"Tsoro nake, na ganin mutane suna ta mutuwa a dalilina, Aziza yau nake tunanin visa ɗina zata fito, amma kuma sai naga gara kawai na zauna anan ba zan ƙara fita ko parlour ba, na haƙura da duk wani jindaɗi na rayuwa, da ace mutane su riƙa mutuwa dalilina gara kawai nayi zamana a bedroom ɗin nan, kome nake buƙata zan kiraku a waya ku kawo min"
Haka fa ba shi ne mafita ba, ni zan yi ƙoƙari wajen nemo mata magani, amma ba zaka iya rayuwa a ɗakin nan ba tare da ka fita ba"
"Zan iya, komai kamawa take. Hankalina ya matuƙar tashi, domin na tabbatar matsalata ce ta samu wannan ƴar aikin har ta mutu"
"Ta mutu?" Aziza ta tambaya a tsorace.
"Haka nake tunani domin Mommy ta ce ta mayar da ita gidansu, ni kuma zargina ya bani yarinyar nan mutuwa tayi."
Dafe kai Aziza tayi sannan ta ɗago ta kalleshi "Idan ma har rasuwa tayi babu wanda zai tsallake lokacin shi Yaya, tabbas kayi ƙoƙari kuma kana kan yi, amma wannan ƙaddarar data kutso rayuwarmu babu mai iya mana maganinta face Allah. Muna addu'a kuma zamu cigaba dayi, zancen ka bar ƙasar nan ma bai taso ba, muna tare da kai har zuwa lokacin da komai zai warware"
"Ko da kuna tare dani, ni kuma alƙawari na ɗauka kan cewa ba zan ƙara zuwa ko nan da can ba"
Ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon fuskarsa da tayi jajir duk da cewa shi ɗin ba fari bane can.
***** *****
Salati kawai suke lokacin da suka ga ana ta danna mata ƙirji, Innarta ban da kuka babu abinda take.
Shi kuwa Malam Yakubu addu'a yake ta yi a fili, a haka har suka ga Likitan ya ja zanen da aka rufeta zuwa ciki, ya rufeta rufa.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shi ne abinda faɗa tare da zubewa ƙasa, Goggo ta riƙota tana faɗin sai haƙuri.
"Likita kana nufin Safiyya ta rasu?"
"Sai dai muyi haƙuri"
"Ya Allahu, Innalillhi wa inna ilaihi raji'un" Ya fura yana duban gawar Safiyya da aka rufe ruf.
*Bayan Kwana Biyu*
Ƙofar gidan Driver ya yi parkin. Mommy ta kalli Fa'iza ta ce "Muje ko?"
Fa'iza ta fara buɗe murfin motar ta fita.
Yana cikin mazan dake zaune a ƙofar gidan ya miƙe kuwa cikiɓ bambami ya fara faɗin "Ku tafi, ku bar min ƙofar gidana, ɗanki maye ne, shi ne ya cinye min ƴata, nayi dana sani da har na karɓeku a lokacin da kuka zo."
Mommy da Fa'iza gaba ɗaya sun kasa koda ƙara taku ɗaya daga inda suke.
Malam Bala da wasu mutanen suka rikeshi tare da faɗin "Ka daure Malam, kar kayi furucin da zai saka rai ya ɓaci, idan hankali ya gushe..."
"Ka ga Malam Bala ku ƙyaleni, na rantse da Allah wannan matar ba zata shigar min gida ba. Tun a farko nayi sake ne, ban san haka zata faru ba."
"Amma kowa ya san Hajiya Rukayya 'yar uwarka ce"
"A'a babu wani 'yan uwantaka, ni bani da alaqa dasu, ɗan uwanta na can Amurka ai ita ta sani, shi ne ɗan uwanta bani ba, ni mutuncin maƙotaka ta haɗa iyayenmu kafin daga bisani ta samu ta auri mai kuɗi ta ɗauki Wanta ta bashi jari ya wuce amurka amma ni bani bane ɗan uwanta, ganin iyayenmu duk sun rasu shiyasa na ɗauketa a matsayin 'yar uwa ganin a yanzu bata da wani dangi anan, gaba ɗaya ahalinta tun lokacin data tubure ta ce zata auri mijin nata suka ce babu su babu ita, wannan dalilin ne ya saka tunda tayi aure babu wanda ke waiwayarta itama bata isa taje ba domin ta san irin ƙasar data watsa musu a ido"
"Duk wannan bai taso ba Malam Yakubu, dan Allah kayi haƙuri ka barsu tunda har suka zo maka gaisuwa ja bari su yi"
Gaba ɗaya hayaniya ta kaure a gurin, rantsuwa yake da Allah sai ya makasu kotu tunda ɗanta ya cinye masa 'ya.
Hatta matan dake cikin gida wasu duk sun fito waje saBoda hayaniyar da suka ji ta kaure a wajen.
"Baiwar Allah tunda abin yaƙi ci yaƙi cinyewa kawai ki koma, in yaso daga baya sai ki dawo kiyi masa gaisuwa."
Ɗaya daga cikin mutanen ne ke yiwa su Mommy wannan maganar.
"Aikuwa na rantse da Allah idan suka dawo sai na karya ƙafafunsu"
Mommy da Fa'iza gaba ɗaya rai a ɓace suka shiga motar. Domin Mommy ma kuka take sosai.
Tafiya suke babu mai cewa komai, sai shi driver ɗin Malam Hamza yake ɗan basu baki.
"Mommy wannan wace irin rayuwace, ni kaina ina tsoron Yaya bana son a barni gida ni dashi shiyasa ma na biyoku, tunda ita Aziza taje Abuja, to amma Mommy shi Yaya wane laifi ya yi? Ba shi ne ya halicci kansa ba, sannan idan maye ne shi da mu zai fara cinyewa, amma Mommy ya kamata ki bamu labarinki, tunda 'yan uwan Daddy da basu ƙaunarmu su kaɗai muka sani"
"Fa'iza kullum ina son baku labarina, amma ganin baku labarin babu amfani yake sawa ina fasawa. Ahalina basu min adalci ba, saboda ni na san ban yi laifin da zasu tsaneni ba"
"Mommy duk da haka ya kamata a yanzu ki daure ki bamu"
"Shikenan, idan mun kom...." Maganarta tsayawa tayi cak ta ɗauki salati ganin motar ta ƙwacewa Hamza.
Bata tsaya kan titi ba, ta yanki daji, sai data bawa bishiya wani mugun karo, wanda har gaban sai daya lamuƙe, yayinda Fa'iza aka yi wurgi da ita da murfin ƙofar side ɗin da take.
*Kuyi following ɗina a Tiktok @SaNaz deeyah Writer*
*A Youtube kuma kuyi searching Inspire by SaNaz deeyah*