...BASHI!

Page 6

by @sanazty

*...BASHI!*
   _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*K.W.A*

_Sadiya S. Adam🌸✍️_

                   Page 6

__________🖌️Kallon shi tayi cikin ɓacin rai sannan ta miƙe ta ce "Hafeez ba zan aikata abinda kake so na aikata ba, domin ni ba 'yar iska bace, kuma nayi slqawarin gidan mijina anan ne kaɗai zan kai budurcina" Tashi tayi da niyyar barin ɗakin nasa ya yi saurin riƙo gyalenta. Cikin ɓacin rai tayi ƙoƙarin fuzgewa amma ta kasa.
"Ka sakar min mayafi, ko kuma nayi maka ihun kwarto, 'yan gidanku suzo suga abinda kake ƙoƙarin aikatawa."
"Aziza karki manta akwai baiko a tsakaninmu, kuma niɓe wanda zan aureki, dan Allah ki bani dama ko ɗaya ce, na kasa jurewa ne"
  "Saboda zaka aureni shi nrƙe kake neman lalata min rayuwa?"
   "Ba fa lalatata zan yi ba, naga dama mun riga mun saba"
   "Romancing muke not sex dan haka ba zan yarda nayi sex da kai ba ba tare da mun yi aure ba"
   "Daddy yana dawowa za ayi bikinmu, kwana nawa ya rage"
   "Kayi haƙuri har zuwa kwanakin, domin ni yau nacewa Mommy zan koma Kaduna"
   "Flight ɗinki cewa kikayi sai 4.zai tashi, so har mun yi mu gama"

Da farko dai taƙi yarda amma a hankali ya fara ribatarta har ta yarda suka aikata alfasha.
   Kuka sosai take lokacin daya fito daga toilet.
  Ƙarasowa inda take ya yi tare da faɗin "Haba Sweetheart mene na kuka"
   "Hafeez tsoro nakeji" 
  Kan lips ɗinta ya yi mata peck sannan ya ce "Karki damu, dan dai na farko ne shiyasa kike jin wani iri"
    Ajiyar zuciya ta sauke, shi kuma ya saɓeta ya yi toilet da ita, nan ma sai daya sake ribatarta suka ɗan taɓa romance sannan sukayi wankan tsarki tare, dan shi da kansa ya gasata.

Shi ya shiryata, duk a lokacin ji take jikinta ya yi sanyi.

"Sweetheart ina matuƙar godiya, you are 25 amma a haka kika tsare min mutuncinki, domin nine na fara saninki a 'ya mace"
   Murmushi tayi sannan ta ce "Ina fatan kaima ni ce na fara saninka a namiji kuma ba zaka bawa wata mace dama ba"
    "Kece farko kuma kece ƙarshe" Ya furta yana sumbatar hannunta.

Har sai daya ga tashin jirginsu sannan ya tafi.

        ***** ***** *****

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shi ne kawai abinda Muhasin ke furtawa a ƙofar emergency.

Shigowar ƙanin mahaifinsu ya saka shi ƙarasawa da sauri inda yake.
   "Suna ina ne?" Uncle Ubaidu ya furta a kiɗime.
  "Suna ciki Uncle, an hana na shiga ne"
   "To ya jikin nasu?"
"Ban san halin da suke ciki ba har yanzu"
   "Ya ilahi Allah dai ya tashi kafaɗunsu"
   "Amin" Ya faɗa tare da zama kan kujera gami da dafe kan shi.

Suna zaune Doctor ya fito, da sauri duk suka miƙe suka ƙarasa inda yake.
   "Ku kwantar da hankalinku, gaba ɗaya mun samu nasarar ceto rayuwarsu, sai dai ita mahaifiyar taku har yanzu bata san inda kanta yake ba. Amma ita yarinyar da driver yanzu haka sun farfaɗo kuma zaku iya ganinsu."
    "Zamu iya shiga kenan?" Ya furta a ƙiɗime.
   "Eh zaku iya mana"
   Da sauri suka wuce ciki.

Fa'iza ya fara gani dan haka a jikin gadon nata ya tsaya.
  "Yaya Muhasin....Bana son na mutu Yaya, ina so nayi karatu" Ta faɗa tana hawaye. 
   "Ba zaki mutu ba, muna tare dake, tare zamu rayu gaba ɗaya"
   "Muhasin ya haka, ya kake kuka kai da zaka rarrasheta.
Hannu ya saka ya goge hawaye.

Wayarsa da ta fara ringing ya kalla ya ga sunan Aziza na yawo.
  Da suri ya ɗaga gami da karawa a kunne.
 "Idan har tafiya kayi baka min adalci ba Yaya, na san guduwa kayi tunda ka shaida min ba zaka sake fita ko ina ba"
  "Ki kwantar da hankalinki, ina asibiti Aziza"
   "Waye ba lafiya, mene ya sameka?"
"Ke dai kizo kawai, muna Habib"
  "Okay gani nan zuwa"

*1 Weeks Later*

"Inna dubi Sadiya, fatar ta har ta soma duhu, shikenan ina ji ina gani zan rasata, Inna bani da tsimi bani da dubara, me zan saya dan in nemo mata magani?"
"Allah yana tare damu, kuma shi ne zai bata lafiya"
"Amma Inna ina ganin gara mu myar da ita asibiti"
"Nima nayi tunanin hakan, amma da wani kuɗi kike ganin zu iya kai ta asibiti? Muma fa fama muke da abinda zamu ci"
"Inna gara muje mu roƙesu ko a bashi ne su karɓeta idan yaso daga baya sai mu san abinyi."
"Gashi kuma Malam baya nan bare ya samo abin hawa"
"Bari na fita na gani ko zan samu."

       ****** ***** *****

Kallon shi tayi sannan ta ce "Ni fa bana son ka riƙa yin wannan gudun Habib" Ta furta da muryar shagwaɓa.
   "To ai ina tafiya a 20 kin ce a ƙara, kuma yanzu ina tafiya a 90 kin ce ya yi yawa"
  "To ai gani nayi magrib tayi, kuma Daddy zai yi faɗa sosai baya son na ki dare"
   "Ki dai faɗa min gaskiya cewar Kamal zai yi faɗa" 
 "Ko dai kishi kake?"
 "Wane ni nayi kishi da soldier"
Dariya tayi, sannan ta ce "Da alamu dai wata rana sai an kada ka a soyayya indai kace zaka saka tsoro"
  "To ai kin ga ke ɗiyar senator kuma kina dating soldier to Habib a wa?"
   "Allah ya shiryeka Habib"
  "Amin, yauwa ina saukeki zan je gida nayi wanka na kuma tafi nima neman abar ƙauna"
  "Abar ƙaunar da har yau an kasa gano ta ko?"
  "To ai lalube muje tayi"
  "A dai daure samo ko gurguwa ce"
  "Gurguwa, okay so kike nayi auren wahala kenan, ai ni ba izgili ba amma ba zan ko iya soyayya da musaka ba bare har ya kaimu ga aure"
   "To ai masu ƙafafunmu ka tsaya ruwan ido, na kusa ce ka shiga sahun manema na kaƙi shiga"
   "Wane ni, kin ga ki daina wannan maganar, ni yanzu da Kamal zai zo da cewa zan yi ni driver ɗinki ne, dan idan nace ni friend ɗinki ne zai iya sakawa a yi min ɗaurin goro"

Dariya sosai Najwa tayi, a lokacin kuma suka gitta Inna dake tsaye bakin titi.
  "Wannan matar kamar naga ta tsayar damu?"Ya faɗa yana hangota ta madubi tana bin motar da ido.
   "Besty rabu da ita, yanzu fa ba a taimako, saboda duniyar gaba ɗaya ba gaskiya"
   "Kiyi haƙuri Najwa, kin ga babbar macece da ace budurwa ce to ba zan tsaya ba, amma kuma bai kamata na ga mace uwa anan tsaye na kasa taimakonta"
   "Ba fa 'yammatane kaɗai mugaye a yanzu ba"
  "Na san da haka, amma a yanzu da ake matsalar rashin man fetur za kiga wasu gidajen mai duk a rufe, to dole sai mun taimaki wasu mararsa ƙarfin domin kuwa wasu basu da kuɗin da zasuyi transport" Ya ƙarasa maganar yana reverse.
  "To kar dai ka manta da addu'a, idan ma muguwace abin ya ƙare mata ita kaɗai" 
   "To matsoraciya, ai kin san dai ban rabuwa da addu'a ko?" Ya furta lokacin da ya yi parking a saitin Umma tare da zuge glass ƙasa.

"Ina wuni" Umma ta rankwaɓa tana gaidashi.
  Da mamaki ya ce "Ina yini" Ya mayar da gaisuwar tare da faɗin lafiya kuwa?"
  "Eh dama taimako nake buƙata" Ta faɗa tana goge hawaye.

"Dan Allah ki faɗi abinda zaki faɗa sauri muke" Cewar Najwa.
  Kallonta Habib ya yi, sai kuma ta sauke kai. Ya mayar da kallonsa ga Umma.
  "Wane taimako ne?"
 "'Yata ce a gida rai hannun Allah, ina so na kaita asibiti amma bani da kuɗi, gashi duk abin hawar dana tsayar na roƙi ya kaita sai ya ce ba zai iya ɗauka a kyauta ba, naira ɗari da hamsin kaɗai ke hannuna kuma suna cewa dole sai mun bada ɗari huɗu"
  "Tana ina ne yarinyar?"
Da hannu Umma ta nuna layin nasu, unguwar burget da suka samu suka raɓa a gidan wata aminiyar Inna domin sun san koda sun koma Gaya dole su dawo Kano.

"Shigo muje sai a ɗauketa a kaita asibitin"
 Da hanzari ta kama murfin zata buɗe Najwa tayi saurin daktarwa "Haba Habib, ka basu ko 1k ce su hau abin hawa, amma taya zamu yarda da ita kai tsaye"
  "Najwa yaushe kika fara yi min musu?"
 Baki ta turo ba tare da ta ƙara cewa komai ba.

"Shigo Baba" Ya furta tare da buɗe mata ta ciki.

Suna is ƙofar gidan ta ce ya tsaya. Ta fita da sauri.

"Ga wani ruɓaɓɓan gida da aka kawo mu, ni kam gaskiya in ba dan kaine ba babu wanda zai saka na shigo wannan geto area ɗin"
   "Tunda har ina da wannan muhimmancin to kar in ƙara jin kin ce wani abu."
  "To am..." "Shhhhh" Ya dakatar da ita lokacin da aka fito da Sadiya, tana saɓe a kafaɗar Umma. Inna kuma na biye dasu.

Suna shiga motar Inna ta kalli Tabawa ta ce "To idan Malam ya dawo ki faɗa masa muna asibiti, sai ya nemi lambar Lami"
  "To shikenan, Allah yasa a dace"
  "Amin ya rabbi"

Yana lura da yadda Najwa ke da kumbure-kumbure shi kuma sai murmushi yake, dan ya san yau zasu kwashi 'yan kallo"
  "Wane asibiti za a kaita?"
   "Ko kawai a kaimu na gwamnati"
  Ɗan juyowa ya yi ya kalleta sai kuma ya cigaba da driver ƴana faɗin "Amma wane ciwo ne?"

"Ƙodarta duka biyun ance sun lalace, sai kuma ƙashin bayanta daya samu matsala" Inna ta faɗa, yayinda Umma ke matsar ƙwalla.
   "Ina ganin gara a kaiku Aminu Kano ima ganin zai fi, ko Najwa?"
   "Bata ko kalleshi ba, bare ya samu amsa.

Kai tsaye Aminu Kano ya kaisu, sai dai yasha wahala kafin a karɓeta a kuma yanki ƙati zuwa ɗakin da za a kwantar da ita.
   "Baba na gama muku komai, zasu kaiku can female ward, zuwa gobe Doctor zai zo a gwadata a san kuma abinyi"
    "Yaro Allah ya saka da alkhairi ya kuma baka lada"
   "Amin ya rabbi"

Yana juyawa yaji Umma na faɗin "Inna na san Sadiya mutuwa zatayi, ina muke da Milayan 6 da za a saka mata wata ƙodar. Har zai dawo ya masu magana sai kuma ya tuna kar suce ya zaƙe dan haka ya nufi inda ya ajje mota.

Yana shiga ya ce "Am sorry Najwa, kin san halin asibitin nan tunda anan kike aiki"
   "Na dai gama shanyuwa har ma na bushe, ka ajjeni a mota almost hour, wallahi ba dan a jiki k bar key ba da sai dai ka dawo ka ga bana nan"  
 "To ai da kin fito da tuni an gama komai, tunda ke sun sanki dole za suyi alfarma."
   "Akan me? Daga taimako sai in zaƙe, asibiti kawai suka ce ka taimaka ka kawo su fa"
  "Na zaƙe kenan"
"Ƙwarai kuwa"
   "Am sorry naga dai ranki a ɓace yake sosai"
  "Ni dai kayi dropping ɗina a gida am tired"
  "Okay"    

**** **** ****

"Daddy ka tafi ka barmu almost a year sai yau zaka waiwayemu"
   Kallonta ya yi, tare da yin murmushi ya ɗauki lemo ya yi sipping kafin ya ce "It seems like you are not happy, na ɗauka zakiyi murna da dawowana Aziza"
   "Daddy a cikin tasjin hankali muke fa, kuma muna ta kiranka ka dawo kaƙi ka dawo and..." Shiru tayi tana kallon gefensa cikin tsananin tashin hankali.

*Manage it please*