...BASHI!

Page 7

by @sanazty

*...BASHI!*
   _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*K.W.A*

_Sadiya S. Adam🌸✍️_

                   Page 7

__________🖌️Miƙewa tsaye tayi, ganin yadda ya fara yin wani.
   "Daddy ka gani ko?" Ta faÉ—a tana kallon Muhasin É—in.
 "Ya ilahi, mene hakan?"
 "Ciwon shi ne ke Ć™oĆ™arin tashi haka yake yi Daddy." Ta furta a kiÉ—emi, tare da sake cewa "Ina zuwa bari naje na É—auko zam-zam."
  Da sauri ta juya sai kuma taji ya ce "Daddy.." 
Juyowa tayi tana kallon shi, ganin yadda ya dawo normal ya saka ta juya ido cikin jindaÉ—i sannan ta dawo ta zauna.

Muhasin ma zama ya yi yana faÉ—in "Daddy sai yau muke ganinka"
"Itama yanzu ta gama nata faÉ—an, shi ne kai kuma zaka É—ora daga inda ta tsaya."
 "Daddy muna cikin yanayi na tashin hankali kamata ya yi ace ka dawo since"
  "Muhasin baka san yanda aiki ya tsareni acan ba, shiyasa na kasa dawowa, domin ba s Ć™asa É—aya nake zaune ba, in yi nan in yi can haka nake ta faman nema maku abinda zaku zauna cikin aminci kuma bana son kuyi kuka da kuÉ—i"
  "Daddy ina amfanin kuÉ—in da bazasu kwantar maka da hankali ba, ba kuma zasu maka maganin damuwarka ba, mu ganinka a tare damu ya fiye mana kuÉ—aÉ—en da kake turo mana a ko wane wata."
  "Muhasin idan na dawo na zauna ku kanku sai kun ji kun tsaneni, ita fa soyayya da kuÉ—i ake yinta"
  "Daddy ni dai da zuciya nake soyayya domin gashi kuÉ—in ya kasa min maganin matsalata"
   "Amma ai ya yi ta mahaifiyarka da 'yan uwanka, domin da babu kuÉ—i ba zasuje asibiti mai tsada ba, kai kanka da sutura da motocin da kake hawa ba zaka hausu ba"
   "Daddy ni ban damu da arziĆ™i ba, da ace zan samu rayuwar farin ciki,ko babu arziĆ™i sai nafi jindaÉ—i"
   "Kana nufin yanzu ba rayuwar farin ciki kake ba?"
  "Daddy ni bana ganin wannan a matsayin farin ciki, domin ji nake gara ma na mutu da irin wannan baĆ™ar rayuwa da nake ciki, Daddy abu É—aya nake so shi ne waraka, amma kuÉ—in sun Ć™i su nema min. Da zan yi yawo da kaya yagaggu kuma ace ina da lafiya, babu wanda yake cutuwa a dalilina da sai na fi kowa farin ciki"
   "Baka san mene talauci ba, baka tashi cikinsa ba, shiyasa har kake faÉ—ar haka"
  "Ni kuma sai nake ganin babu amfanin  kuÉ—in da ba zasu yi min maganin matsalata ba"

Murmushi Daddy ya yi sannan ya ce "Aziza kina jin yadda muke daba da ɗanuwanki kuma kin ƙi kice komai"
  "Daddy ina ganin duk abinda ya faÉ—a gaskiya ne, domin kuwa gashi kuÉ—in sun Ć™i maganin matsalar, kullum wata masifar ce ke kunnowa cikin rayuwarmu, kuma mun kasa maganin matsalarmu. Kai kuma da ka zame mana hope sai gashi ka Ć™i zama garemu."

"Shikenan tunda kun yarda talauci yafi wani arziƙin, zan baka assignment, cikin wata 5 nake so kayi min shi"
  "Ina jinka, ni kuma zanyi zan dawo maka da sakamako mai kyau a cikin wara É—aya rak"
   "Good I like your confidence. Ina so a satin nan kayi tafiya zuwa wani Ć™auye, a wannan Ć™auyen akwai wani aminina babban Malami ne, ka faÉ—a mishi matsalarka zai maka magani acan, koda an gama maganin kafin ka cika wata É—aya a Ć™auyen, ina so ka zauna har tsawon wata biyar acan, to anan ne zaka gane cewa taluci da arziĆ™i akwai tazara mai yawan gaske a tsakaninsu. Zakayi soyayya kuma ba za a Ć™ara mutuwa a dalilinka ba, amma ka zauna da lafiyar ciki talauci kaji a abin yake" 

"Kana da tabbacin zan samu lafiya idan naje?"
  "Ya naga tun yanzu ka fara karaya?"
  "Ina so na samu tabbaci ne kafin in tafi"
  "Allah shi ne masanin gaibu, kawai abinda na sani shi ne, shi wannan Malamin babu cutar da baya iya warkarwa, Allah ya bashi wannan damar"
   "Shikenan, da Mommy ta Ć™arasa warwarewa zan tafi, saboda ba zan iya barinsu a haka ba, in naje ba zan samu kwanciyar hankali ba. Amma idan suka warke zanje da Ć™arfin gwiwata"
    "Na san halin Rukayya farin sani, ina so wannan ya zama sirri tsakaninmu kada ka yarda ka faÉ—a mata inda zakaje, haka kema" Ya furta yana kallon Aziza"
   "Daddy ba zamu faÉ—a ba, amma baka faÉ—a mana state da kuma village É—in da zai je ba"
  "Wannan kuma sirri ne tsakanina dashi, sai mun keÉ“e"
   "To ai ni dashi 5&6 ne, ko baka faÉ—a ba zai faÉ—a min"
   "Idan ma 7&8 ne ba zaki ji ba"
   
Sun ji daÉ—in tattaunawar da sukayi da Daddy a tsawon ranar, anan Aziza ta faÉ—a mishi taje Abuja ta samu transfer za a dawo da ita Kaduna ta cigaba da aiki.
   
Aziza macece budurwa mai kimanin shekaru ashirin da shidda a duniya, tun tana shekara 15 ta gama secondary school wanda tayi a ƙasar England tana gamawa ta jona Degree ɗinta, lokacin shi kuma Muhasin yana Master, lokacin daya ƙare Masters ita kuma kammala Degree sai ya nemi ya dawo Nigeria saboda ya yi aure, dan a lokacin yana da shekaru ashirin da bakwai, amma shi burinsa kawai ya ga ya yi aure ya kuma fara tara nashi iyalin.

Hakan ne ya saka itama Aziza ta ce shi zata biyo su dawo, tare kuma yake da Hafeez wanda amininsa ne tun a can suka haÉ—u lokacin da ya shiga aji É—aya na jami'ar Oxford.

A jirgi ya fara haɗuwa da Zainab wadda suka ƙulla alaqar soyayya da ita, kuma koda suƙa dawo bai yi ƙasa a gwiwa ba ya sanarwa da Mommy dan ta faɗawa Daddy dan a time ɗin ma baya ƙasar ya ce Eskimo wani aikin. Tana sanar dashi ya ce a'a a bari sai ya samu aiki tukun.

Lokacin itama Aziza ta fara soyayya da Hafeez saboda ta ƙara samun kusanci da Yayanta da take matuƙar ƙauna dan koda tayi aure ta san in Hafeez ta aura dole zata samu kusanci dashi, saboda tana matuƙar ƙaunarsa jin sa take a cikin jininta.

Ta ɓangaren Muhasin kuma ya saka Mommy a gaba kan ta sama masa aiki komin ƙanƙantarsa zai yi.
    Tayi masa nasiha sosai kan ya barwa Allah komai, domin gaggawa aikin shaiÉ—an ne.

Wata biyar da dawowarsu aka sama masu aiki kusan tare, sai dai shi ya samu Assistant Managing Director NNPC Kano Branch yayinda ita kuma ta samu aiki a Abuja a kamfanin C.A.C. Ai kuwa ta tubure sai dai a dawo da Muhasin Abuja ko kuma itama a kaita Kani, sai da Mommy tayi mata jan ido ta kuma haɗata da Daddy ya yi mata faɗa sosai sannan ta haƙura.

Wata guda da samun aikin aka masa baiko da Zainab, wanda a daren ranar ne matsaloli suka fara aikuwa, gidan ranar kasa bacci sukayi, fashe-fashe, ƙaran kukan mace, gicci babu wanda basu gani ba, haka suka takure a ɗakin Mommy.

Washe gari aka zo masu da mummunan labari, an yanka Zainab a ɗaki, kuma bayan an kaita asibiti an samu nasarar yi mata ɗinki saboda yankan bai taɓa jijiya ba, amma sai dai kayan cikinta da akayi scanning gaba ɗaya sun lalace, kwananta ɗaya a asibiti ta rasu.

Ya shiga damuwa da tashin hankali mara misaltuwa, sam bai san matsalarshi ce ta kashe Zainab ba, sai bayan daya fara soyayya da Amal itama kamar haka dai aka sameta an kasheta  akayi a cikin gidansu ta dare, ita kuma harshe aka yanka mata, anan ne ya fara zargin wani abu. Bai gama sarewa ba da kuma fidda rai daga rayuwa sai lokacin daya Ć™arayin soyayya da wata ma'aikaciyarsu mai suna Farha, ita ko sati basu rufa da fara soyayya ba itama aka kasheta, ita nata kisan ma yafi illa, domin cikinta aka yanka aka kuma fito da hanjin waje.

Lokacin ne ya fara samun nakasu a rayuwarsa har yaso zaucewa, a cikin wsta biyun nan aka sallemeshi daga aiki.

Muhasin irin mazan nan ne da aike kira black beauty, fatarsa bata da duhu sosai amma dai baƙine domin baya sahun farare. Yana da manyan sexy eyes, kuma farare tas wanda kallonki idan ya yi zaki ji kawai ya burgeki, yana da madaidaicin hanci, sannan mutun ne mai kwantaccen saje, yana da farin jinin 'yammata sosai, sai dai bayan komarshi Abuja da ya yi 'yammata biyu suka mutu sai kuma mata suka fara tsoronshi. Kun san Abuja ba gari ne da yake da cukowar mutane barkatai ba, shiyasa har aka gano shi.

Tun daga nan ya tsoraci soyayya, wanda mata uku da suka rasu bayan wannan biyar É—in gaba É—aya sune suka ce suna son yi,sai dai ita Amira ko data ce tana sonshi bai ma amince ba. Yayinda Safiyya ita baya da masaniya a kanta ma, dan har ya manta da itama.
   Sai kuma Sadiya da bai ma san an aura masa ba.

"Ita kanta Mommy wani lokacin tsoro yske bata.

Bare Fa'iza wadda take shekara 15 kuma take SS2 third semester, gaba ɗaya tafi kowa tsoronsa duk da cewar tana ƙaunarsa. Ita dama 'yar lelen Mommy ce, a gida Nigeria take karatunta, bata son sam tayi nisa da Mommy.

Shekara uku kenan cikin wannan tashin hankali da har wa yau basu san dalilinsa ba, sun yi na asibiti sun yi na gida amma abin yaƙi ci yaƙi cinyewa.

Har gara Aziza da yake tana da addini sosai, bata rabuwa da zam-zam wanda idan tayi addua data watsa masa cikin ikon Allah yake tashi.

           ***** ***** ******

Gida na alfarma, sama da ƙasa, tun daga farkon layin kake hango hasken gidan duk da cewar layin ko ma nace unguwar gaba ɗaya ta masu hannu da shuni ce, amma gidansu sai ya zama na da ban a cikin layinsu.

Securities biyu sanye da uniform sune suka wangale gate É—in, shi kuma ya danna kan motarsa ciki.

Sai daya isa kusa da main part ɗin sannan ya tsaya. Tana murɗa ƙofar ta buɗe ta fita.
  "Am sorry Najwa" Bata ko kulashi ba kawai ta wuce.

Murmushi ya yi sannan ya ce "Ke da zaki auri soldier amma kike da wannan zuciyar, naga wanda zai rarrashi wani, ni kam ba za a ɗauko sasanci ba." Ya yi murmushi sannan ya ƙara cewa ai nasan zaki sauko Najwa ba zakiyi fushi da number 5 ɗinki ba.

Babu kowa a babban parlour, dama ta san ba zata iske kowa ba, dan haka ta nufi sama, nan ma babu kowa. Kai tsaye ta nufi side É—in elder sister É—inta mai suna Anisa.

Tana zama ta ƙara turo baki.
  "What's wrong" Anisa tayi tambayar tana kallonta..
  "Sister ni dai gaskiya na gaji, zan faÉ—awa Habib ina son shi duk abinda zai faru ya faru"
    Anisa da take sakawa Ikram Pampers ta É—ago ta kalli Najwa ta ce "Like Serious"
  "Yes! Kar naje nayi sake, ga kin dai san yanda nake da kishi ko?"
   "To ke baki tsoron ya yi rejecting É—inki? Kuma kin san sai alaqarku ta samu rauni, and idan shi ne ya ce yana sonki, at least kina da kimarki, saÉ“anin idan kece wallahi ko da ya amince ba zakiyi wani daraja sosai ba"
   "Amma taya zai kasa ganewa, nabi duk wasu tactics amma abin yaĆ™i ci"
  "Matsalarki É—aya"
  "Me kenan?"
"Rashin haƙuri mana, da zafin kai, shi kuma namiji ɗan a lallaɓa ne"
  "Mace dai?"
"Mace ko? To shikenan, zaki yiwa kanki illa..."
  "No haba Sis ya da baki kuma"
  "Gaskiya nake faÉ—a miki"
  "Ni kam sai da safe, kai na yana wuta"
  Da ido kawai Anisa ta bita.

       **** **** ****

Ya kasa bacci sam, shi damuwar wani bata taɓa damunsa kamar haka ba.
Ya kasa gano dalilin daya saka shi tunanin abinda Umma ta faÉ—a lokacin daya juya zuwa mota.

_Mabuƙata ne!_ Shi ne abinda wani ɓangare na zuciyarsa ke faɗa masa.
"Wane irin taimako zan masu?" Ya faɗa yana miƙewa zaune daga kan round bed ɗinsa.
"Milayan! That's what she said"
  "I will try my best to make sure an sama mata Ć™oda, indai 1 Million ne ba zai gagara ba bi'iznillah.

Habib Isma'il shi ne cikakken sunansa, matashin sauryi mai tashe, wanda yake da kimanin shekaru 27 a duniya. Iyayensa na da rufin asiri, domin ba za a kirasu talakawa ba sai dai kuma su É—in ba masu kuÉ—i bane suma tsakiya.
Mahaifinsa yayi aiki  matsayin Malamin makarantar secondary har zuwa lokacin daya ajje aikinsa. Yayinda mahaifiyarsa dama bata taÉ“a aikin gwamnati ba.
Shi kaɗai iyayensa suka haifa shiyasa suke matuƙar ƙaunarsa.
Tun yana SS1 ya fara sha'awar waƙa kuma ya fara gwadawa har zuwa lokacin daya kammala anan ya faɗawa mahaifinsa ra'ayinsa na son zama mawaƙi, kuma babanshi ya mara masa baya. Ko a jami'a abinda ya karanta kenan kuma yana aji uku na jami'a ya fashe, aka sanshi aka kuma san waƙoƙinshi, sai dai bai taɓa yin video ba kasancewar video abune da sai an kashe kuɗi sosai.
A jami'arsu anan ya haÉ—u da Najwa, yana da tarin fans kasancewarsa sananne sai dai shi baya da girman kai, da kuma É—sgawa. Sai dai duk cikin fans É—in nashi yafi jituwa da ita Najwa saboda yanayin kamun kai da take dashi. Tun kafin ya san ita É—in É—iyar wani ce. 
Najwa ita ta fara kwaɗaita masa yin video ya ce ba yanzu ba sai a gaba. Ta ce idan wani abu yake nema ita zata bashi kama daga kuɗi zuwa lokaci amma fur yaƙi yarda.
Sai da ta kawo masa wata mawaƙi babba ta ce ta ɗauki nauyin video da ƙyar ya amince, wannan video daya yi shi ne ya saka ya samu kuɗaɗen da bai taɓa tunani ba.

A hankali ya ginawa iyayensa katafaren gida anan Na'ibawa inda a nan suke zaune a halin yanzu. Yayinda ita kuma Najwa suke zaune a Nassarawa GRA.