Chapter Two
by @suttie0
Kiran sallan Subhi a masallacin dake ƙofar gidansu ne ya tada Imaani daga bacci. Batayi mamakin jin mutum a jikinta ba saboda haka ɗabi’an Shukrah yake, indai Halita ta kwantar da ita a ɗakinta toh la shakka idan ta tashi cikin dare ɗakin Imaani take dawowa koh na Ammi idan Abbu baya gari.
Saukkowa tayi daga gadonta ta nufi bayi tayi alwala, da ta dawo da tashe Shukrah ta kaita bayi tayi mata alwala. Da ƙyar Imaani ta tsayar da ita saboda layi da magagi da takeyi daga tsaye. Suna fitowa Imaani ta shafa musu turaren da suke sallah dashi, farin miski ne wato Misk al-Abyad. Wannan training ɗin Ammi ne tun Imaani na karama kamar yadda Shukrah take a yanzu.
Bayan sun idar da sallah sukayi adhkar sai Shukrah ta koma bacci bayan sun gama, Imaani kuma ta buɗe bedside drawer dinta ta dauka Qur'aninta. Ta nufi parlourn Ammi inda suke bitan karatu tare a kowace safiya har zuwa lokacin fitowar rana. Kasancewan Annabi SAW ya kwaɗaitar damu falalan wannan lokacin da albarkar dake cikinta.
Suna cikin bitan karatun Abbu da Rafeeq suka dawo daga masallaci sukayi joining ɗinsu. Zazzaƙar muryarsu na fita cikin ƙira'a mai daɗin sauraro. Haka al'adar gidan yake a kowace saafiya, da weekends kuma mazan na makarantar asuba a masallaci, da yamma kuma akwai malamin dare dake zuwa bayan Isha’ yana koyar da duka matan gidan har masu aiki duk da weekends dindai.
Suna cikin karatun Abbu yayi realising Asma'u bata zo ba, saida suka kai ƙarshen aayah sannan yayi magana.
“Ina Asma’u take?”
Ammi ce ta amsa shi, “Nashiga ɗakinta na tarar tana Sallah ɗazu, koh bata gama adhkar bane har yanzu?” Tayi tambayar da ba mai bada amsanta.
Cikin mamaki Rafeeq yace, “Dama tadawo ne?”
Abbu bai amsa shi ba ya kalli Imaani, “Boɗɗo je ki kirata.”
Ko yashe tadawo? Haka Imaani ke saƙawa a ranta ta nufi ɗakin Asma’u dake ta farkon corridorn ɗakunansu.
Ƙwanƙwasawa tayi bata jira an amsa ba ta buɗe ƙofar. Kwance ta ganta akan gado tayi kane kane tana sharɓar bacci. Cikin takaici Imaani take kallonta, akan abunda zai amfaneta ma sai anyi fama da ita. Ji tayi kaman ta juya, sai kawai ta ƙarasa cikin ɗakin wanda banbancinshi da nata arrangements din kayan ɗakinne da color. Na Imaani pastel colors ne na different shades of pink, na Asma’u kuma bold red colors ne da ratsin fari. Ƙara gode ma Allah tayi da iyayensu basu takurasu akan sharing ɗaki ba tun suna kanana.
Imaani ta ɗan bubbuga gefen gadonta sau biyu taji shuru, ta matsa ta kara bubbugawa.
Kawai sai jin wani dogon tsaki tayi, “Haba sai an ishe mutum da sassafennan. Ko baccin kirki bansamu ba-”
Katseta Imaani tayi,“Abbu yana jiranki a sama.” Ta juya ta fita, dan yanzunnan sai ta fusata. Zubar da girmanta zatayi idan ta tsaya maida mata magana. Wato Asma'un na sane da shigowarta shiyasa tayi banza da ita da farko.
Tana komawa ta tarar Abbu yana addu’o’in da ya saba yi idan sun kammala karatu. Zaunawa tayi aka karasa ta ita. A wannan lokacinne idan kanada buƙata ko neman shawara ko matsala sai ka fada domin ayi addressing ɗinshi. Wannan duk yana daga cikin al’adun gidan masu burgewa, idan baka samu damar faɗa ba a lokacin sai kuma da daddare idan sungama cin Dinner.
Gaisuwa suka gabatar ma juna, Ammi kuma ta tafi kitchenette dake sama a palourn Abbu don haɗa mishi morning tea ɗinshi, kafin ma’aikatan su fara shirin fita aiki bayan breakfast. Rafeeq ne sai Abbu masu fita. Ammi kuma bata daɗe ba da dawowa daga kammala wani project ɗinta a Kano na NGO ɗinda take gudanarwa, so tana hutu ne kafin su fara sabon aiki.
Kitchen Imaani taje na ƙasa dan ta haɗama Rafeeq daily Flat White Coffee nashi da morning drink nata na Morroccan Mint Tea. Ta samu har masu aikin sun sa mata ruwan zafi a heater, already suna haraman breakfast ɗin duka gidan ne. Gaisawa sukayi dasu Baaba Salame da sauran, bata ɓata lokaci wurin haɗawa ba don bacci takeji sosai, tana gamawa ta jera mugs ɗin a tray ta fito.
Rafeeq ta tarar a Palour riƙe da Shukrah a ƙafarshi ta kwanta tana mishi bitar karatun Qur'ani a lokacin saboda bata daɗe da tashi daga bacci ba. Shukrah badai sonjiki ba.
Ajiye tray ɗin Imaani tayi, Shukrah ta dasa aya ta gaida Imaani. Cikin baby voice ɗinta tace, "Good morning Adda, kintashi lafiya."
Kafin Imaani ta ɗauki mug ɗinta amsa Shukrah tayi tana shafa mata kai tenderly, "Good morning Shuk, Alhamdulillah natashi lafiya. Nasan kema kintashi lafiya."
Ɗaga mata kai Shukrah tayi koma ta kwanta jikin Rafeeq ta cigaba da karatunta.
Imaani ta kalli Rafeeq tace, "Hammah I'm feeling really sleepy today. Ga coffee dinka, saika dawo."
Kallonta Rafeeq yaɗanyi da light brown eyes ɗinshi kafin ya ɗaga mata hannu saboda bayason a ƙara katse Shukrah.
Komawa ɗakinta Imaani tayi ta gabatar da sallan Duha (walha) kasancewan few minutes to 7:00 AM ne kuma rana yafito, sai ta koma bacci tunda ba fita zatayi ba yau. Shukrah ma suna hutun makaranta so Halita wanka zatai mata ta shiryata bayan sungama cin Breakfast.
Sai wurin 11:51 AM Imaani ta tashi daga bacci, ta gyara gadonta, ta kunna burner tasa bakhoor kafin ta shiga bathroom ɗinta da ba’a daɗe da wankewa ba. Wurin sink ta karasa ta matsa toothpaste a electronic toothbrush ɗinta ta sanya a bakinta.
Kallon fuskarta tayi ta cikin mirrorn gabanta. Tunani ta faɗa, daga tasowarta, girmanta har zuwa shekarunta na yanzu, zata iya cewa rayuwarta cike take da ƙalubale, tsangwama da kyara daga strangers harma daga wasu family members dan kawai saboda yanayin halittarta.
Hakan kuma baisa ta bijirema Allah ba ko a tunani, ko nuna rashin godiyarta a gareShi. Idan Allah Ya nufeka da babban rabo, jarabawarka ba irin ta kowa bane.
Alhamdulillahi, Ya hallicce ta da gaɓɓai masu motsi dana tafiya, zata iya ci da sha da biyan buƙatunta na bayangida da kanta ba saida taimako ba kamar yadda yake cikin jarabawar wasu baayinSa.
Kyakkyawa ce ita mai manyan idanuwa na almond-shaped eyes, siririn hanci da cikar laɓɓa, full lips in all the right places. Ga cikar gashin gira da suma a kanta mai laushi da santsi, cika da tsawo har kasan kafadunta kaman irin na ƴan Somali.
Tanada tsawo madaidaici irin average-height batada ƙiba saidai cikar halitta a inda ya kamata. Fatar jikinta light brown ne da rastin fari a wurare mabanbanta da ya kawata fatarta cikin burgewa. Wannan shi ake kira da Vitiligo.
Fararen tabon vitiligo sun bazu a sassa daban daban na jikinta cikin tsarin da Allah Ya kaddara, tamkar zanen da Mahalicci Ya zana da launuka biyu. Sunfara daga gefen idonta, suka shafi kuncinta da wuyanta, sannan suka gangaro zuwa kafaɗunta. A wasu wurare kuma sun bayyana a ƙafafunta da ankles ɗinta tamkar ɗigon farin haske akan fatarta mai launin ruwan kasa.
Dukda bambancin skin colournta komai a tattare da ita yayi daidai. Hatta tabon kansu sunzama wani bangare na kyawunta, basu kasance abinda ya ɗauke mata kyau ba, sai dai wani abinda yayi differentiating ɗinta da kowa.
Tofar da kumfar bakinta tayi, ta kuskure ta maida brush ɗin muhallinsa. Ta mika hannu ta dauka shower cap daga towel hanger dan ta rufe gashinta dashi.
Wanka ta shiga da sassanyan Bioderma Atoderm Shower Oil ɗinta mai kamshi da gyara fata, kuma anyi formulating ɗinshi ne domin masu irin yanayin fatarta kasancewan sunada normal skin amma zai iya zama dry koh irritated depending on yadda kake kula dakanka.
Tana gamawa ta ɗora bathrobe ɗinta mai laushi kafin ta fito daga bayin. Ta kashe burner, ƙamshin Bakhoor ɗin Gidan Ƙamshi by Suttie ya karaɗe ɗakin sai ta ƙarasa ƙayataccen walk-in closet ɗinta domin ta shirya bayan ta fesa body spray na Oriflame Love Nature sai ta shafa cream ɗinta na Bioderma Atoderm Intensive Baume.
Cikin wani atamfar Vlisco mai light blue da black pattern, ɗinkin riga da skirt ta fito, sanye da safar kafa na Marks and Spencer cotton everyday socks. Minimal jewellery na Mikimoto pearl studs da necklace ɗinshi tasa, sai bracelet da anklet na Tiffany & Co.
Ankira sallan Zuhr sai kawai ta gabatar da sallah bayan ta shafa miskinta na sallah. Sai ta karasa rantsatsen dressing mirror ɗinta mai ɗauke da different types of perfumes sama da shabiyar. Imaani ma’abociyar kamshi ne a koda yaushe, especially idan tana gida. Tanada fragrances ma kowani occasion kaman bauta kuma bata taɓa tsallakewa, dukda haka tana ƙoƙarin kiyaye dokar shari’a domin ta fita hakki.
Ɗankwalinta ta ɗaura simple style mai steps amma a kwance wanda shine yawancin irin ɗaurin da takeyi dan yana ƙawata fuskarta. Shafa farin Khumrahnta tayi mai sassanyar ƙamshi daga Gidan Ƙamshi by Suttie, ta fesa turarukanta na zaman gida Lattafa Musk Mood da Chanel Coco Madmoiselle.
Saukowa tayi daga curved stairs ɗin wanda ka nade a gefen palourn, design ɗinshi irin na ƙasashen ƙetare ne wanda zaka iya hango cikin palourn idan kana saukowa. A tsaftace palourn yake kaman kullum, kamshin turaren wuta yana tashi.
Ƙarasawa dining table tayi inda aka ajiye mata abincinta, ta ɗan saki murmushi dan wannan aikin Baaba Salame ne, inhar taga Imaani bata fita zuwa makaranta ba ko wurin aiki to la shakka sai ta jera mata abinci a dining table.
Potatoe Chips with Fried Eggs da Liver Sauce ne. Sai kunun gyada da freshly squeezed orange juice. Ajiye wayarta tayi akan table ɗin kafin taja kujera ta zauna sai ta ɗiba daidai cimarta, tasa kunun a mug sannan ta fara ci.
Bayan ta gama ta ƙarasa wash hand basin dake gefen dining arean ta kuskure bakinta da TheraBreath Fresh Breath Oral Rinse. Tare da Ƙarama wacce ta fito daga kitchen sukayi clearing kayan abincin.
Wucewa library Imaani tayi domin tasamu abinda zai ɗebe mata kewa, tana sane da aikinda ta taho dasu daga restaurant jiya, wanda suke buƙatan dubawa amma ta share saboda tanasan tadan huta, sai ta dubasu anjima kafin Rafeeq ya hayayyako mata akan procrastination idan yajira ta kawo mishi kuma bata dubasu ba.
***
A ƙaramar hukumar Song dake garin Adamawa, a nan iyalan Alhaji Sunusi Dadan-Garba sukayi rayuwarsu. Bafulatani ne shi haifaffen garin Song, wadda ƙaramar hukuma ce dake jihar Adamawa. Nan ne asalinshi tun daga kakanninshi har zuwa kanshi. Iyayenshi a garin Song sukayi rayuwa shima kuma anan yayi rayuwarshi har zuwa aurenshi na fari da bafulatanan matarshi jajir mai suna Aminatu.
Saboda matsayinshi na bafulatani ba sirki yana daga cikin norms and traditions ɗinshi da ya aure ƴar uwarshi bafulatana. Kasancewan baiyi karatun boko ba saboda a lokacin bai yaɗu kamar yanzu ba. Waɗanda suka fita cirani ne kawai suke da opportunity ɗin samun western education, amma sauran yawanci manoma ne walau na dabbobi ko na hatsi kamar Alhaji Sunusi wandake haɗa duka biyun yana nomawa.
Aminatu matar Sunusi wanda ake kira Kawu Lamiɗo ta haifar masa ƴaƴa huɗu maza; Ahmadu, Kabiru, Usman da Aliyu. A wurin haihuwar Aliyu ne Allah yayi mata rasuwa bayan tayi zaman aure da Kawu Lamiɗo for 11 years. Kamar yadda yake a al’ada, bada jimawa ba aka ɗaura ma Kawu Lamiɗo Khadija wacca itama dai ƴar garin Song ce. Itace ta raini Aliyu har yaye kuma ta riƙe sauran ƴaƴan da Aminatu ta bari.
Khadija wacce ake kira Nenne ta haifar ma Kawu Lamiɗo ƴaƴa bakwai, mace da namiji alternatively ta haifa har zuwa last born ɗinta mace. Ya zamana first born ɗinta Hafsatu ce, sai Naziru, Kamila, Shettima, Jamila, Sunusi (Babangida) sai kuma last born Aminatu mai sunan marigayiya.
Haka rayuwa ta cigaba da gudanar musu, Ahmadu dai yayi karatun boko haɗe dana allo kamar yadda yake a al’ada bayan wanzuwan musulunci, kuma yayi kokarin sa kannanshi akan hanya dukda ba duka suka yadda da ilimin yahudawa ba as they do say back then. Matan ma ansamu sunyi primary har wasu sunfara sec. school kafin a aurar dasu bayan sunyi saukansu na makarantar allo.
Baffa Ahmadu kamar yadda ake kiranshi bai aure ƴar garinsu na Song ba, tsallakawa yayi yaje har garin Jimeta ya haɗu da kyakkyawar bafulatar matarshi, Faɗimatu, ƙanwar abokinshi ce na makaranta. A makaranta suka fara haɗuwa tun tana mitsitsiyarta kafin tashin balaga kasancewar tana zuwa ma Hammanta Saminu visiting.
To daga nan ne fa Baffanmu ya ƙyasa ya kama aka samishi ita a lalle tana da shekaru 17 shikuma yanada shekaru 24.
A garin Jimeta suka fara zama saboda anan ne Baffa yasamu aikinshi na lecturing a department of Mathematics na Federal College of Education Yola that is located between Yola and Jimeta bayan ya kammala Master’s ɗinshi under Mathematics ɗindai daya karanta as a degree course.
Already Faɗimatu da ƴaƴanta ke kira Daada tanada iliminta na boko har ta fara sec. school kafin ayi mata aure bayan tayi saukanta na allo, sai ta karasa sec. school a dakinta.
Daada ta haifarma Baffa Ahmadu ƴaƴa tara tana kammala secondary kamar dana jira sukeyi ta gama su fara zuwa. Ibrahim Mu’azzam (Abbu) shine ɗanta na fari, sai Abubakar Siddiq (Abba) wanda tsakaninsu da Abbu watanni sha ɗaya ne so sun taso tare komai nasu tarene. Sai kuma mace takwarar Nene, Khadija amma ana kiranta da Kubra, sai twins Hassan and Hussain sauran kuma mata ne Ammatullahi, Aisha, Surayya da Juwairiyya.
Kasancewan Baffa Ahmadu gogaggen ɗan boko ne, bayan haihuwan Kubra ya tarkato iyalanshi ya dawo dasu garin Kaduna domin yana so ya cigaba da faɗaɗa karatunshi na boko, sai ya ɗora da PhD dinshi a Ahmadu Bello University dake garin Zaria.
Bayan ya kammala yasamu aiki a National Mathematical Centre dake Abuja. Ganin irin cigaban da yake samu daga amfanin ilimin boko tuni ƴan uwanshi maza Kabiru, Usman da Aliyu manyan kenan suka dora daga inda suka tsaya a baya. Sun samu ɗaukaka daidai gwargwado, kuma time to time suna komawa gida can Song inda Nenne ta cigaba da zama da sauran ƴan uwansu mata da sukayi aure a ciki da wajen Song.
Mazan kuma waɗanda Nene ta haifa wasu na Jimeta wasu kuma suna nan Song sun cigaba da jagorantan aikin gonannakinsu dana yan uwansu tun bayan rasuwar Kawu Lamiɗo watanni kadan bayan ya aurar da autarshi Aminatu.
Baffa Kabiru wanda ya karanta Business Administration yayi aure a garin Mubi yana kammala university, ya zauna da matarshi Maijidda a mubi kafin shima ya dawo Kaduna da zama saboda aikinshi a Abuja shima. Baffa Usman da Baffa Aliyu anan Song sukayi aure kafin su dawo Yola da aiki, amma daga baya Aliyu ya koma Jimeta da zama. Adda Hafsatu tayi aure a Yola a wurin Baffa Ahmadu kafin yabar Yola, ta aura abokinshi ɗan garin Yola kafin su koma Abuja da zama. Baffa Ahmadu ya kuma aurar da ƙanwarsu Kamila anan Kaduna da sukayi relocating to bayan ya daukota itama.
Baffa Naziru da Baffa Shettima suma anan Song sukayi aure, amma a Mubi suke zama da iyalansu. Baffa Babangida (Sunusi) da Jamila anan Song suke zama tare da Nenne, Adda Aminatu auta kuma na aure a garin Hong dake kusa da Song, sai ya kasance sauran ƴan uwan basu bar gida a baya ba don suna zuwa tunda Nene taƙi bin kowa.
***
Sauke wayar hannunshi yayi yana lumshe idonshi, ya jinginarda kanshi baya. Zaune yake a cikin motarshi ƙirar Mercedes-Benz S-Class a back seat tare da Chauffeur dinshi Horace dake seat din gaba. Tashinshi kenan daga office yau bayan la'asar ya kama hanyar gidan iyayenshi dake Gwamna road.
Dama yana jiran tsammanin kiran Daada bayan dawowar Asma'u jiya da daddare, Hajara tariga ta rantse saita haɗashi da iyayenshi tunda tasan bazata taɓa samun buƙatarta ta biya ba. She is hell bent on frustrating him at any chance she gets.
Mintuna kaɗan suka isa baƙin gates din ƙayataccen family residence din Proffessor Ahmadu Sunusi Dadan-Garba, family house ne wanda yafi nashi girma kasancewan anan ne ake saukarda ƴan uwa da baƙi daga Song, kuma duk wata meeting da yanke hukunci daya shafi ahalinsu toh anan ake wanzarwa.
Suna shiga drivern Abbu, David yayi parking a daidai ƙofar shiga gidan wanda aka ƙawata da babbar water fountain da saika zagaya kafin ka ƙarasa harabar ka shiga cikin gidan.
Bude ƙofar motan David yayi ma Abbu cikin girmamawa. Saukowa Abbu yayi a natse kafin yaɗan yi tafiya ya danna doorbell dake jikin ƙofar. Buɗewa akayi ta ciki Mama Ladi wacce itace shugaban masu aikin Daada kuma wacce ta kula dasu Abbu da ƙannanshi a lokuta da dama tundaga tasowarsu har i zuwa yau idan sunkawo ziyara.
Abbu ya gaisa da ita ta amsa ta sanar mishi Baffa da Daada suna palourn Baffa na sama. Ƙarasawa stairs ɗin Abbu yayi wanda zai kaishi sama har wani corridor kafin ya isa faffaɗan palorn Baffa dake ƙawace da kayan zamani cikin tsari kamar dai yanda yake a gidanshi.
A zaune ya tarar da Daada akan Turkish rug ɗinda ke shimfide ta jingina da tumtum tana ɗaukan yankakken fruits dake gabanta ɗaya bayan ɗaya tana kaiwa bakinta cike da izza kamar wata matar basarake.
Baffa kuma na zaune kusa da ita yana jingine da ɗaya daga cikin set ɗin royal chairs dake palorn yana duba wani littafin addini dake hannunshi. Saukewa yayi ganin babban ɗanshi ya shigo cikin shirin kayanshi na zuwa aiki wato Briono three-piece suit, buttons din suit jacket ɗin a sake yake kuma yayi loosening neck tie ɗinshi kaɗan. Ya amsa sallamanshi kafin ya miƙa mishi hannu sukayi musabaha.
Gaishe da mahaifiyarshi Abbu yayi bayan ya zauna a gefenta amma ta line of vision dinta. "Jam waali, Daada?" (Kuna lafiya Daada?)
"Jam woni." Ta amsa mishi a taƙaice. Baffa ya cigaba da duba littafinshi yabar uwar da ɗanta.
Shuru Abbu yayi kaman na jiran tsammani, in da sabo ai ya saba da haka a duk lokacinda yayi laifi ko ƙannanshi suka ɓata mata rai. Tanada fara'a ga duk wanda taso amma inhar bata sanka tofa tana da wuyar sha'ani. Sai Allah Ya sa mata san Hajara fiyeda Jiddah kasancewan ita ɗin orthodox fulfulde ce masu son nasu fiye da kowa kafin suso wani. Ƙarin abun kuma Hajara itace matar ɗanta na farko, ɗanta na fari kuma ƴar uwarsa, sannan uwar manyan ƴaƴanshi, ai sai abun ya haɗe dakyau ta yanda bazata so ganin ko jin laifinta ba.
"Dalilin meyene yasa kace baza'a ɗauko Asma’u jiya ba sai yau? Ƴarka cefa ita ba ta wani ba Ibrahim."
Ran Abbu ya ɓaci amma bai bari tagane ba, sunkuyar da kanshi yayi cikin banhaƙuri, "Ki gafarceni Daada, darene yayi dayawa kuma naga ba a baƙon wuri take ba da bazata iya bari sai washe gari a ɗauko ta ba, a wurin mahaifiyarta take."
"Bayan Maghrib ai ba dare bane, idan kaso ta dawo dakanka zaka sa a ɗaukota naga?" Daada ta ɗaga mishi kakkaifan girarta ɗaya mai barbaɗin furfura. Wato Hajara sai ta ɓoye abinda tayi, bata faɗa mata ta turo Asma'u da saurayi jiya wurin tsakar dare ba.
Abba ya ƙara bata hakuri kasancewan bayasan ya ja da maganarta, "Kiyi haƙuri Daada, baza'a ƙara hakaba In Sha Allah."
Dukda haka saida Daada ta kara da, "Ruwanka ne kuma wannan, ka riƙeta karka riƙeta kai kasani. Naka dai nakane ba'a canzama tuwo suna."
Sai a sannan Baffa ya saka musu baki, "Faɗi wannan ba magana bace, shi da ƴarshi ai ba wanda zai iya shiga tsakaninsu. Nasha faɗa miki ki dena ɗaukar ko wane magana kina zama akai."
"Baffa magana daga bakin uwarta wani bincike kuma yake buƙata?" Ta amsa mishi da tambaya.
Baffa yace, "Duk baikai haka ba dai, tunda ba baƙon wuri take ba ai zata iya kwanan ta koma gida washegari." Ya ajiye littafin hannunshi ya juwa ya kalli Abbu, "Lokacin sallah yayi, mu tafi masallaci kafin ka wuce gida koh?"
Dukda Abbu yanada plan ɗin zuwa night drive da Ammi kasancewan yanada tafiya agabanshi wanda zai iya daɗewa kafin yadawo so he wants to spend some time with her saboda itama bata wani daɗe da dawowa daga tafiya ba. Amma for peace to reign zai zauna har bayan Isha' yayi dinner dasu domin ya ƙara pacifying Daada yaji kuma idan akwai wata maganar da zata mai dan he could sense she wasn't done with him.
Amma ko da wasa baiyi hasashe ko zaton irin next maganan da ta kawo mishi ba.
***
What do y'all think so far?
Can you guess mai Hajiya Daada zata faɗama Abbu kuwa?
Badai abunda kuke tunani bane fa😂 bazaki iya ganema matarnan ba, ni kaina shakkarta nakeyi.