7
by @pherty001
Suna fitowa ta babban gate ɗin makarantar, tuni motar gidan su fadila tana fake a gefen titi tana jiran isowarsu, direban ya fito da sauri cikin natsuwa da ladabi ya buɗe musu kofa ya lura a wannan karon babu alamun zalamar farin ciki ko murna ta kammala karatun sakandare da ya ga sauran ɗalibai suna yi a tare dasu kamar ma wadanda suka sha kuka da ya dubi idanun su, suka shiga motar suka zauna, maimakon su riqa jimamin rabuwa da friend's da murnar ban-kwana da kowa yake yi a ranar da aka kammala karatu, kowaccensu ta fuskanci tagar motar zuciyarta a cunkushe da wani irin daci da nauyi mai tsanani, tafiyar ta kasance shiru babu sautin komai sai kukan sanyaya na'urar gidan motar da yake ratsa jikinsu amma ba zai iya sanyaya zafin dake ruruwa a tsakiyar ƙirjin Nurayyah ba, har direban ya shafe nisan dake tsakanin makarantar da unguwar su Nurayyah ya zo ya faka motar a daidai kofar gidansu.
Nurayyah ta juyo a sanyaye ta dubi fadila da idanuwanta suka canza tace "Sai an jima nagode", kafin ta fita daga motar ba tare da ta jira amsar fadila ba, ta tura kofar gidan nasu ta shiga ciki da wani irin sanyin jiki da kasala, a tsakar gidan ta sami Jaddi tsugune tana zubawa kajinta abinci a ƙasa kamar yadda ta saba yi a kowace rana, Nurayyah ta ƙago wani murmushin yaƙe mai cike da rauni domin ta ɓoye kuncin dake ranta, ta matso kusa da ita cikin muryar can ciki da ba ta saba jin ta da ita ba tace "Ke da kajin nan naki biyar da shida (5&6), ban taɓa ganin mutum da ya shaƙu da kaji irin ki ba Jaddi", ta faɗi hakan ne kawai don ta kaucewa tambayoyin da ta san zasu biyo baya.
Sai dai Jaddi ba ta bi ta kan maganar kajin ba ko kaɗan, ta bar abinda take yi ta ɗago kanta da sauri tana ƙoƙarin sanya idanunta cikin na Nurayyah domin ta karanci ainihin yanayin da jikarta take ciki tunda taji muryarta a dishe tasan akwai abu da yake faruwa, Nurayyah ta ƙi yarda ta kalli jaddi, ta kauce da fuskarta tana kallon kajin dake tsifar abinci a ƙasa tana ci gaba da ƙago murmushin yaqe, Jaddi ta ajiye kwanon abincin kajin ta miƙe tsaye tana gyara zaman zanin jikinta dake neman faɗuwa saboda tsufala tace "Ba kya son kallo na Nurayyah saboda kina tsoron kada na gane halin da kike ciki, gaya min waye ya taɓa min ke a makarantar? Wane irin kuka kika yi haka da har idanuwanki suka kumbura suka yi jajur tamkar wuta?"
Jin waɗannan kalaman na Jaddi ya sanya Nurayyah soma ƙoƙarin haɗiye wani sabon kuka da yake ƙoƙarin taso mata tun daga can ƙasan maƙogwaron muryarta, ta dubi Jaddi da ta riga ta kafe ta da idanuwa masu cike da zargi da fargaba tace "Ba komai Jaddi, kawai kaina ne yake ɗan ciwo tun ɗazu a aji", Jaddi ta girgiza kanta cikin sauri ta girgiza kanta tace "Wannan ƙarya ce Nurayyah nafi kowa sanin halin ki ko ciwon yatsa kike da yanzu kina kwance bare ciwon kai zaki tsaya a gabana har kina gayamin, ban manta ba nasan cewa yau ranar karɓar sakamakon jarrabawarku ce ta ƙarshe ban manta ranar ba kuma da zaki fita kin gayamin, kuma shi kika tafi karɓa, gaya min gaskiya, ba ki sami wannan bizar (visa) da tallafin karatu da zaki je ƙasar waje ba ko kuma jarrabawar ce baki ci ba?"
A daidai wannan lokacin ne juriyar Nurayyah ta rushe gaba ɗaya, hawaye masu zafi da radadi suka shiga gangarowa a kan kuncinta ba ƙassaba, ta ja wani dogon numfashi mai haɗe da majina tana share hawayen da bayan hannunta cikin tsantsar kuncin zuciya, ta yi ƙoƙarin magana amma kukan da take tura shi ƙasa ya toshe mata muryarta ya hana ta magana gaba ɗaya, ganin haka ya sanya hankalin Jaddi tashi matuƙa, ta riƙo hannun jikar tata da yake rawa da sauri suka bar tsakar gurin suka nufi kan daddumar shinfidarta dake cikin ɗaki, ta zaunar da Nurayyah a kai sannan ita ma ta zauna a gefenta tana kallonta cikin tsantsar tausayi da raunin zuciya tace "Na sani sarai ba zaki taɓa faɗuwa jarrabawa ba sai dai wani ikon Allah saboda kowa ya san ƙoƙarinki da hazakarki a kowane darasi, idan kuma maganar wannan biza da gurbin karatu ne yake sa kike zub da hawayenki haka ba kiyi min adalci ba Nurayyah, menene amfani na a duniyar nan idan har zan zama ina kallo ba zan iya saka miki murmushi a fuskarki ba? Kawai a shirya a siyar da wannan babban gidan nawa gaba ɗaya, a haɗa da gidan mahaifinki da muka bayar da haya a siyar da shi ma, mu haɗa kuɗin gaba ɗaya a ba ki kije karatun jami'ar da kike so a kowace irin ƙasa kike sha'awar zuwa a faɗin duniyar nan idan har kuɗin zasu isa".
Nurayyah ta girgiza kanta cikin wani irin matsanancin kuka mai ban tausayi, ta dubi Jaddi tace "Jaddi, Waleeda ta ƙwace min farin cikina na rayuwa saboda kawai na fito daga gidan talakawa kuma ina da kyau da basira da na fita, biza ɗinnan haƙƙina ne wahala da nayi karatu kuma na rubuta jarrabawa na ci, ta sanya mahaifinta babban ɗan siyasa ya zo ya ƙwace ta wurin Principal aka ba ta ita, ba don ba su da kuɗin da zasu iya biya mata ta tafi ba, a'a sai don kawai ba ta son ganin farinciki, murmushi ko nasara a kan fuskata saboda hassada", ta ci gaba da kukan da ya ƙara sa jikinta rawa gaba ɗaya.
Ran Jaddi ya ɓaci sosai a wannan karon da jin rashin adalci da cin mutunci na Waleeda da mahaifinta, fuskarta ta canza ta miƙe tsaye cikin bacin rai tace "To wallahi ba za a bar wannan zancen haka ba, zan kai ƙararta da mahaifinta har gaban kotu, tabbas kotu zata tilasta musu su dawo miki da bizar ki da haƙƙinki da aka ƙwace aka ba ta cikin rashin gaskiya".
Nurayyah ta riƙo zanin Jaddi tana kuka tace "Jaddi ko kin je kotun nan kika shigar da ƙara, zaki ɓata lokacinki da kuɗinki ne a banza ba tare da an miki adalci ba, kin manta yadda aka yi wa mahaifina Abba a kotu lokacin da yake raye duk da cewa shi ne mai gaskiya amma saboda ba ɗan siyasa bane aka murɗe shari'ar aka ba masu gwamnati, kin sani bamu da kowa sai Allah bayan shi waye zai tsaya mana? Haka za a sake miki irin na Abbana Jaddi, kawai mu haƙura mu bar wa Allah, ba abinda masu kuɗin ƙasar nan suka sani sai ƙwace farin ciki da gumin talaka da nuna iko a kan rayuwarsu, shi talaka kwata kwata ba abin so ba ne a cikin al'ummar nan, ba shi da wata daraja ko kariya a gaban hukuma matuƙar ba shi da dukiya kuma baya siyasa".
Jaddi ta yi shiru na wani lokaci mai tsawo, fuskarta ta haɗe cikin wani irin ɓacin rai da takaici mai nauyi yayin da kalaman Nurayyah suka dawo mata da tsofaffin miƙon dake ƙasan zuciyarta, ta juya a sanyaye tana duban jikar tata da idanuwanta suka canza saboda kuka kafin tace mata cikin muryar rarrashi "Je ki watsa ruwa a jikin naki kizo kici abinci, ki daina sa damuwa a ranki kin ji Nurayyah, ki bar kukan nan haka, idan baki je wata ƙasa kinyi wannan karatun ba ai ba a isa a hana ki yi a cikin ƙasarki ba, Allah yana kallon kowa kuma zai bayyana gaskiya burin ki zai cika zakiyi karatu irin wanda kike sk", Nurayyah ta ɗago kai ta dube ta a sanyaye, kamar ta gaya mata sauran maganganu da Waleeda ta gaya mata na cewa ko a ƙasar nan ba za ta barta ta sami gurbin karatu a jami'ar koyar da ilimin asibiti ba saboda uncle ɗin ta shi yake bayar da admission a school ɗin, ganin yadda jikin Jaddi ya riga ya yi sanyi ya sa ta fasa gaya mata sauran kalaman, ta miƙe ta nufi ɓangaren ɗakinta cikin wani irin sanyin jiki da sanyin gwiwa, ta bar Jaddi zaune a wurin cikin matsanancin takaici da tunani mai zurfi dake addabar zuciyarta na yadda rayuwar maras galihu take a kullum.
Bayan shekara biyu.
Rayuwa ta sauya wa Nurayyah gaba ɗaya cikin waɗannan shekaru biyu da suka biyo baya, rayuwarta ta juye zuwa ga tsantsar duhu da ƙunci da ba shi da iyaka, tsawon lokacin nan tana killace a cikin gida ta shiga cikin wani irin matsanancin yanayi na ciwon fargaba da tunani (depression) wanda ya sanya ta rame ta yi fari kamar ba ita ba, kullum tana ɗaki a kwance ko kuma idan fadila tazo suka matsa.mata da Jaddi ta fito ta zauna babu fara'a ko wani farinciki a tare da ita tun bayan waɗannan shekaru kuma babu yadda ba'a yi da ita akan ta shiga wata makaranta ba taqi saboda tayi loosing interest akan karatun gani take kamar da gaske Walida take idan taje neman karatun zaa hana mata admission meyasa to zata je? Kullum da ƙunci Walida take barci take tashi kuma take yini ta kasa manta yarinyar da abinda tayi mata, bata da wani tunani ko wani buri a yanxu na ganin tayi kuɗi kafin ta shiga wata jami'a ta karanta fannin da bata da future akan cos babu karatun da take so kamar na medicine an kashe mata wannan burin kuma ta hakura sai dai bazata qara yarda taje wata makaranta a wacce ake wa kallon talaka a sake cutar da ita ko danne mata haqqi, sai dai ta yaya ina zata sami kuɗin bayan tasan yadda suke, ire iren waɗannan tunani kullum sune aikin ta ta sami kudi itama ta zama kamar yar masu kudi a daina wulaqantar da ita ko gori da kyamarta idan ta shiga wata makaranta, wani lokaci haka zata ajiye waya tayi ta kallo tana shiga yanar gizo sosai tana kallon yanda masu kudi suke rayuwa, tana kallon yanda suke dressing , tafiya da komai nasu tana ji ina ma itace ita or itama da da tayi kudi haka zata zama irin su haka zata iya tafiyar su daniya dressing din su da sauransu.
A cikin waɗannan shekaru biyu kuka da addu'a su ne kaɗai abokan tafiyar Nurayyah a kullum, yayin da Jaddi ita ma tayi sanyi saboda tsantsar damuwar da take kallon jikarta take ciki, kusan kullum Jaddi ta ga Nurayyah tana kuka hankalinta tashi yake taje tana rarrashin ta "Nurayyah dan girman Allah ki saki ranki ki bar kukan nan haka, shekaru biyu kina abu ɗaya, idan har kika biye wa wannan damuwar zaki iya kashe kanki sannan ki bar ni ni kaɗai wanda Nima bazan jima ba zan biki kin san irin son da nake maki, ki yarda da ƙaddara ki tashi mu nemi wata makarantar daban kamar yanda Fadila ta faɗa ki manta da wata Walida da rayuwar ta karatun da ba'a bi ta hanyar da ta dace ba bazai yi albarka ba nasha gayamiki Allah baya barci kuma baya yafe wanda yayi zalunci", Nurayyah sai dai ta girgiza kanta tana kuka ba tare da ta yi magana ba, fadila ta nuna asalin amana da kyakkyawar abota a tsakanin ta da Nurayyah, kuma sosai tana iya qoqarin ta na ganin Nurayyah ta cire damuwar ta manta baya amma sam Nurayyah taqi ta hakura wani lokaci har zuba mata ido take tana mamakin taurin kai irin na Nurayyah Walida na can na rayuwar ta kila ta manta da Nurayyah amma Nurayyah ta kasa hakuri da mantawa da Walida, kullum idan aka zo batun makarantar sai ta hau kuka ta ce ta fasa, ta gwammace ta zauna a gida cikin wannan kuncin da ta sake fita waje a wulaƙantar da ita a gaban mutane saboda tana talaka kamar yanda Walida ta faɗa, wannan yanayi ya sa fadila ita ma ta tsinci kanta cikin damuwa domin karatun ma duka ya fita a ranta saboda ganin yadda aminiyarta take cikin wani hali na rayuwa.