11
by @gureenjoh
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO
✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)
@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad
ADABI WRITERS ASSOCIATION
#THE TRIO OF TALES
(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)
TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.
GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.
*SHAFI NA GOMA SHA ƊAYA*
"Babban Abin baƙin ciki ne idan kuka yi duba da tarin kudaden da ake fitarwa da sunan sayan wannan form na takara alhali dayawa sun san ba ci za su yi ba, waɗansu 'yan uwansu suna cikin wani hali, waɗansu iyayensu, waɗansu makotansu, waɗansu hakkokin wasu ne ma rataye a wuyoyinsu ba'a sauƙe musu ba. Mutumin da za'a je neman taimakon gina wani masallaci ko islamiyya wani ma ɗan uwansa na kusa kusa ne ke cikin matsanancin ciwo da bukatar wadannan kudi amma ya gwammace ya cire kalilan ya bayar ya ajiye saura don sayan duniya cikin zuciyarsa kuma ba alkhairi ba ne a kan hakan.
Wallahi Allah ya ce 'Lallai wadanda suka kafurta suna kashe dukokiyoyinsu ne domin su toshe da barin hanyar Allah, za su kashe dukiya mai yawa sa'annan daga baya su kasance masu nadama, sa'annan a kashe su kuma ba za su samu riba a duniya ba kuma su je lahira su samu tambayoyi iri daban daban'
Duk mai neman takara zai rufe ido don neman kuɗi ko ta wani irin hali ko hanya, suna yi kaman domin Al'umma ne alhali karya ne domin kawunansu suke yi da ribarsu wanda ba zai amfane su da komai ba a ranar gobe. Da mun san hatsarin da ke cikin mulkar al'umma da duk mun guje wa ko wani irin mulki ina ƙara jan hankalin shuwagabanni da su yi mulki kan gaskiya da amana su ji tsoron Allah su sani babu wani motsi nasu da ba za'a rubuta shi kuma a yi musu tambaya a kai ba ranar gobe."
Sossai ya ja hankali ya kuma yi nasiha kan zaɓen da yake ta karatowa ana ta rigimgimun jam'iyyu da 'yan takara, musamman ya sake jan hankalin mutane akan shugawabannin da suke ci a yanzu kuma suke da niyyar komawa ya nuna musu tunda da hankalulansu jikinsu wanda yayi musu sun sani wanda bai yi musu ba ma sun sani, a shekaru huɗun farkon nan ya kamata al'umma su san zafin kansu kuma su yi wayon tawaye ga duk wanda ya shafe su bai yi musu aikin komai ba, daga karshe yayi Adu'a aka tashi daga wurin wa'azin ranshi duk babu daaɗi saboda irin matsaltsalun da ake fuskanta a kan shuwagabanni a arewacin ƙasarmu.
Washegari da safe misalin ƙarfe goma ya samu ƙira daga secretary ɗin Excellency Bashir Dantani.
Ɗagawa yayi suka gaisa cikin mutunci kan ya sanar da shi akan Excellency na neman shi, Bashir Dantani gomna ne da ke ci a lokacin kuma yana kan tenure ɗinshi ne na ƙarshe ya dandani gardin mulki da rudin duniya yayi iya zaluncin da zai yi a bayan fage a yanzu kuma ya sayi kujerar Senator mai wakiltar arewa da fatan al'umma su sake zaɓarshi ya ƙara gaba, ya gama kwankwadar giyar mulki kuma babu abin da baya yi wurin ganin ya samu duk wata kujera da ya sa a gaba.
"Excellency na gayyatarka zama na musamman da shi a ofishinsa"
Ya gyara zama tare da rufe takardar da yake dubawa.
"Ba ni da wannan lokacin"
Yana kai nan ya katse ƙiran don babu wani ɗan siyasa da ya isa ya kai kanshi gabanshi ko ya duƙa mishi, idan yana buƙatar shi zai iya zuwa ya same shi a inda yake amma ba wai ya saka shi dole zuwa wurinshi ba.
Miƙewa gabaɗaya yayi ya shige ɗakinshi don shirin tafiya BUK akwai lectures da zai ba da.
Ta ɓangaren Diva ta yi kaman ta manta ta cigaba da harkokin gabanta, ta kan je ta duba su Pabloo, tabbatar mata da suka yi basu da wani matsala ya sa hankalinta kwanciya don kaman a gida suke babu abin da suka rasa, haka ɓangaren Zubash khadija na ta samun sauƙi amma ba hakan ba ne ya sa zubash ɗin chanzawa hasali ma kara kaimi tayi a kan harkokinta na samun kudi.
A bayan fage kuwa gabaɗaya Rayuwar Diva ta ta'alaka shi ga Shehi, duk wani motsinshi, tsarinsa da yadda yake tafiyar da jadawalin rayuwarsa kusan ta san komai da komai, ta san a ranar Litinin BUK yake shiga lectures a Arabic and Islamic department, tuesday da thursdays yana shiga Katsina inda nan ma yake visiting lecturer a arabic and Islamic department Alqalam university iyakaci ya tafi da safe ya dawo da rana Kasancewarsa azumin Alhamis da Litinin basa wuce sa baya taɓa kaiwa Magrib inda ba gida ba a irin ranakun, ranakun Laraba yana shiga dutse Jigawa a nan ma lecturing yake yi ɓangaren arabic and Islamic, juma'a, Asabar da Lahadi su ne ranakun kansa Dukda a cikin waɗan chan ranakun ma idan baya makarantun yana wurin wani wa'azi, taro ko karantarwa, yinin juma'a gabaɗaya a gida ya fi yawan yinsu don tun sha ɗaya yake fita masallacinshi har dare yana nan, Asabar da Lahadi kuma mafi yawan lokutansa na dalibansa ne. Duk sai da ta san komai hatta da 'yan gidansu a bincikenta, tana so ta mishi abin da zai matuƙar yi masa zafi amma bata son wani ya ɗaukar masa raunin.
Satin su Pabloo biyu aka sake su aka rufe case ɗin aka ma jefar da file ɗin kaman ba'a taɓa buɗe shi ba, (ƙasarmun kenan, daga lokacin da abu ya faru da zafinshi xa'a yi kaman za'a ɗauki mataki mai girma amma daga ya kwana biyu ya lafa sai komai ya wuce kowa ya koma rayuwarsa a manta da akwai waenda aka zalunta, hukumomi sun manta da ayyukansu sun dawo suna bautawa mulki da arziki. Allah ya yi mana mafita)
Tun dawowar su Pabloo basu gane kanta ba don bata fita da kowa, haka babu wanda ya san me take planning Dukda Shaly ta saka mata ido amma ta kasa gane kan Diva ɗin don ko magana bata cika yi musu ba sai ta zauna kawai lost ɗin thought zuciyarta bai daina karta ba Dukda raɗaɗin marin ya wuce tun ranar amma ya bar tabon da ya kasa mayar da Diva daidai, tunaninta kawai yadda za ta dauki fansa mai muni bata san cewa wannan fushi zai haifar da ɗa marar ido ba.
Satinta uku tana bibiyarsa, a yau tun karfe 10 ta shiga ɗakin taron da ta tabbatar zai zo, taro ne na hafizai waenda suka haddace alqur'ani su goma sha biyar, musamman a yanzu take yawo da Abaya a mota saboda irin hakan don yanzu wani Black Dubai Abaya ne jikinta ta zagaye fuskarta da gyale ta saka baƙin glasses rabin fuskarta, duk wanda ya santa da zai ganta ba zai gane ma Diva ba ce, ba ma zaka ce wannan ɗin 'yar daba ba ce, kaman ta sani bata jima da zama ba sai gasu sun shigo yana cikin manyan baƙin taron, aka rakashi har wurin zamansa ya zauna, an bude taron da Adu'a aka fara gabatar da jadawalin taron kunnenta ma airpods ne duk abin da suke cewa ba ji take ba.
Abu ɗaya ta san ta saurara yadda ake khatma ɗin, karatu ne yaran da ba su haura ashirin ashirin ba suke yi da ya tada tsikar jikinta lokaci guda, idanunta da suka juye ta runtse da ƙarfi tana sauraron yadda karatun ke ratsa zuciyarta, idan ta yi karatu to na sallah ne su ma ba sa wuce qulhuwa, falaki da nasi. Ba Za ta ce ma akwai Alqur'ani gidansu ba.
Zuciyarta ya cigaba da wani irin hautsinewa, a hankali ta buɗe idanunta ta kai kansa jin ana ambaton sunanshi zai ba da nasiha.
Karɓa yayi cikin natsatsiyar Muryarsa yayi sallama ya fara gabatar da wa'azin da ya tsuma kowa, yayi magana kan falalar Alqur'ani, yayi albishir wa iyayen mahaddatan cewa ubangiji yayi alkawarin ɗora su kan kujerun zinari a yi zagaye da su a ranar gobe sakamakon tsayawa da suka yi kan yaransu wurin zama mahaddatan, ya ja hankalin su mahadattan da yawan tilawa saboda shi qur'ani idan ka barshi na kwana daya zai barka ne na kwana goma, hakika ya girgiza hazo don wasu yaran sun kudiri niyyar dagewa, wasu iyayen da yaransu ba sa makaratun haddar sai boko zallah sun ji kwaɗayi da sha'awar wannan hidima da ubangiji yake yi wa mahaddata da iyayensu, ita kam ba za ta ce ga halin da ta tsinci kanta ba.
Ta dai ji ba zata iya cigaba da sauraro ba, fita ta yi da sauri ta nufi motarta ta shiga ta zauna tana sauƙe numfashi, wani irin zafi zuciyarta ke mata, runtse idanu tayi sai nasihar da yayi mata akan rayuwarta ya shiga dawo mata, rigar jikinta ta cire ta wullar tare da gyalen ta chusa hannu a gashinta tana hautsinawa, damke sitiyarin ta yi ta ɗora goshinta kai zuciyarta na wani irin ƙuna sai dai bata jin za ta zubar da hawaye don neman sassauci, gefenta kawai ta duba ta ɗauko wani kwaya ta haɗiye kan ta kunna motar ta fice daga harabar hall ɗin cikin matsiyacin gudu.
Ranar Lahadi biye da su take kaman kullum bayan isha'i ne, wurin wani taro ne ta ga sun shiga ta yi parking ta ɗauki glass tube da ta zuba kwayar (Ice) ciki saboda idan ta sha ta kan zama very aggitative, shi kaɗai ne ke sakata zama restless har sai ta aikata duk abin da ta kudurta a ranta, lighter ta kunna a ƙasan glass tube ɗin tana zukar ice ɗin da baki, ta jima zaune bayan ta gama bugar da kanta ta zaro Double chiffon Abaya Brown ta ɗora kan riga da wandon da ke jikinta, kunna motar tayi ta ƙarasa ciki ta zame hular kanta tayi rolling gyalen kan ta fito ta shiga wurin taron, a yau ta yi niyyar kawo karshen komai don ta gaji da bibiyar rayuwarsa haka.
Tana nan zaune tana gadinsa kafarta ɗaya take ta karkadawa idanunta sun ƙara girma kuma sun sauya, ta ci sa'a ya ɗaga wata waya mai muhimmanci ya tashi ya fita daga dakin taron, zuruf tayi ta fice itama ta zaga ta kofar da ya fita, ya koma ɗan baya inda babu ƙarar speaker don jin abin da na ɗaya ɓangaren ke cewa, cikin kamalarsa yake fitar da maganan yana nan tsaye hannunsa ɗaya a goye a baya, kaman an ce ya ɗaga idanu sai suka faɗa kanta tana tsaye babu wani tazara tsakaninsu sossai, Dukda ba tarr yake kallonta ba idanunsa sun kusa seconds goma a kanta kan ya fahimci ita ce dama ya raya a ranshi sai ta nemeshi.
Ta cire duka boturan Abayar yana iya kallon wandon jeans da farar rigar da suke ciki, a hankali ya bi hannunta da kallo wuka ne take riƙe da tsirararsa yana walkiya kanta babu ko gyale ko hula gashinta na ɗaure daga tsakiya, idanunsa ya ɗan sauƙar sai kuma ya kawar daga kanta gabaɗaya yana ta'awizi.
Sai ya nufi inda take tun kan ta nufo shi yana sauƙe wayan, dab ita ya tsaya, kamshinshi na gauraye numfashinta, abin da take so da burin gani a cikin idanunsa na tsoro ko shakkarta bata ga ko ɗaya ba sai ma ita da yake shirin karyawa alkadari, wuƙar ta damke tana datse hakorinta hannunta na rawa ba na tsoro ko shakka ba sai na zafin da ya tara na kusan wata guda don samun wannan opportunity na ɗaukar fansa a kansa, sai yayi murmushi mai sauti kaɗan.
"Yau ko ni ko kai!"
Ta faɗa a fili cikin wata kalar murya tana kallon cikin idanunsa da nata marasa tsoro.
Idanunsa babu firgici kwata kwata sai ma cewa da yayi cikin natsuwa da sanyi
"Da ma na san za ki zo."
Ya ƙarasa yana sake karantarta, idan bai ce ya ji bakin cikin ganinta a Buge ba yayi ƙarya, matasanmu suna lalata rayuwarsu a banza suna ɓata future ɗinsu yanzu ina amfanin wannan?
Sai kalamanshi suka ƙara tunzura zuciyarta, hannunta ta ɗaga rike da wukar tana nuna shi ko ɗar bai yi ba Dukda ya san tana iya cutar da shi ɗin kawai ita ɗin bata kai ya ji tsoro ko shakkarta ba ne, a lokaci ɗaya wani ɓari na zuciyarsa na mamakin irin karfin halinta, duk rayuwarshi tsawon shekarunshi ba zai ce akwai macen da ke iya sanya idanunta cikin nasa ba tare da zuciyarta ta girgiza ba, a idanun wannan ba ya ganin komai sai zarrah da rashin tsoro, tabbas ta gama kangarewa ko ma babu zuciyar gabaɗaya a ƙirjinta bare idanunsa su firgitata ko su sanya mata kwarjininsa kaman yadda suke sanyawa mata da mazan da za su yi arangama da shi kila kuma saboda bata cikin cikakkiyar hankalinta ne.
Cutarwa na gaske take shirin yi masa.
"Ka san me ka yi min? Ka yi abin da ba zan iya yafe maka ba, ka yi sanadin da nake jin muddin na kyaleka ban amsa sunan DIVA ba, a yadda na zuƙi Para ɗin nan yau ko ni ko kai na sake faɗa..!"
Fakonshi tayi ta kai wuƙar da iyaka zuciyarta na son cutar da shi cuta mafi muni da wani irin niyya da bata taɓa ɗora hakan a kan kowa ba na son dakatar da fitar numfashinsa saboda yanayinshi ƙara tunzura zuciyarta yake zuwa turiri.
********
Sai a tura shaidar biya ta
***
🖤Gureenjoh🖤