JODAH

11

by @sadisakhna


 

 

______👑 *JODA* 👑_____ 

 

              

 

 

 

Na  

 

*Sadi-sakhna* 

 

Ƴar mutan Jama'are 

 

 

 

 

 

 

 

THE TRIO OF TALES  

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)  

 

@sadisakhna on Arewapen 

@SAKHNA03 On Wattpad 

*** on Whatsapp 

 

 

LITTAFI NA 1 

 

 

 

*Harƙa ta (11)*👑 

 

 

 

 

 

Bayan wasu shekaru.................... 

 

 

Lokaci ya tafi a kwana a tashi, babu abinda yake tsayawa a yanda yake,ciki kuwa harda rayuwata. Naƙara girma shekaru dakuma wayo. Nakoyi abubuwa da dama ciki harda karatu da rubutu wanda har yau babu wanda yasani. Kuma nakoyane ta hannun abokina Hamad,wanda tun ina guje masa har dole na haƙura nake kulashi,abotar tamu tayi tafiya mai nisa sanadiyya shima mutum ne mai son sabon abu. Sannan a yanda na kuladashi bayason mulki da wani matsayi na duniya sosai,yanasone yayi rayuwa ta hanyar tafiye tafiye dakuma yawon buɗe ido. 

  

Lokacin dana nemi ya koyamin karatu da rubutu bai Fasih ba,sai ma yaji daɗin hakan,domin a kullum cewa yakemin Allah yabani baiwa da dama a rayuwa. A sirrance muka gudanar da koyarwar cikin bishiyoyin dasuke wajen rafi,bamu bata wani lokaci ba na ƙware sosai,wannan abu yaxamo wani mataki na nasara dana cimma wanda bazan manta dashi ba,kuma nakejinsa a raina sosai. 

 

Izuwa yanzu nakware a wajen haɗa magani saninin tsirrai masu amfani ga lafiya dakuma kulada ƙananun marasa lafiya,da farko nafara duba marasa lafiya amma da labari yafita cewa ni baiwa ce sai hakan yakawo naƙasu da aikinnawa,domin babu wanda yake yarda yabani jikinsa kokuma ya karbi magani na idan akace nice na haɗa. Ganin hakan yasa na daina shiga wajen masu jinyar indai bawai kwandon maganin zan rike mata ba. Shima bayin wajen suyita hantarata da masu zaman jinyar. Wanda nasan kuma ba komai bane illa suna hassada da fasahata da kuma matsayin da suke tsoro karna taka nafisu.  

 

Yanzu aikina gabaɗaya ya koma ɗebo magani a jeji,hakan yayimin daɗi sosai,domin da wannan damar nayi amfani wajen koyon karatu a gurin hamad ɗin.  

 

 

Baba Almahdi bayanan yatafi Dalaur masar wata shida kenan daya wuce, akan binciken wata cuta data bullo,kasancewar yana ɗaya daga cikin manyan likitoci a duniya yasa aka gayyaceshi gagarumin aikin. 

 

Tun safe na tashi inata sauri na gama ayyukana na niƙa maganin da ummu hajar tabani,yanzu wani lokacin basai naje can ɗakin magungunan ba,nakan iya tsinkowa idan tafaɗamin na cututtukan da akeso na busar dasu na niƙa mata saina kai kawai garin a cikin kwalba. A ɗakinmu akwai inda nake ajiye shirgina na kayan aiki. Kuma mu uku ne a ɗakin,daya Addah Aneesa sai Addah Rahilah amma yanzu mu biyune ita Rahilah tayi aure da wani bawa Sairayinta wanda shima anan Jami'ar yake aiki bangaren Ɗakin litattafai na karatu. Amma ko yaushe anan muke wuni da ita kasancewar aikin bawa babu ƴanci ballantana kasamu lokacin iyalinka yanda kake so,saidai yana iya ƙoƙarinsa wajen bata kulawa itama kuma tana sonsa sosai. 

 

Tun zuwana yanxu shekara biyu kenan da kusan rabi,muna zaman amana dukkan su sunayimin kallon ƙanwarsu kuma ƴar uwarsu,babu ma ya Rahilah dayake ita tanada surutu. Addah Aneesa ce idan ba wani abu bata fiye zama muyi hira ba. Itama kuma dan halittarta ce batada yawan magana.  

 

Ina cikin nikan akan dutsi wanda aka aikin niƙan dashi,hankali na yatafi kan abinda nake sauri nagama naje. Sam ban kulada shigowar Addah Rahilah ba wacce take tafiya tana tura cikin jikinta daya fara tsufa, zama tayi a bakin gadonmu na kara tana kallon abinda nakeyi.  

 

 

"Malamar jinya hala hankalin ki baya kan abinda kikeyi,naga garin maganin yaƙare akan dutsen amma sai gurzawa kikeyi har yanzu" 

 

Zabura nayi na ɗago na kalleta tana tacin goruba,gabaɗaya banga shigowarta ba sai muryarta naji. Gyara zamana nayi ina inda inda kafin nace. 

 

"Addah Rahilah yau ne za'a bikin yaye dalibai" 

 

"Uhmm saikuma mai wannan wani sabon abune?" 

 

"Yallabai hamad yana cikinsu zai tafi" 

 

Naƙarisa maganar cikin karyewar murya,da alama zai yanzu ta ɗago sanadiyyar damuwar tawa,domin babu wanda yakaita sanin tsakanina dashi,mun shaƙu sosai kullum zancena saina haɗa dashi. Nakoyi abubuwa da dama dabazan taba misaltasu daga gareshi ba. Shiɗin ɗayane tamkar da dubu acikin ƴaƴan masu mulki. 

 

"Innalillhi ke dan Allah dagaske dama yallabai Hamad na cikin waɗanda za'a yaye bana,amma ba shekara biyar bane,naga bai wuce shekara uku da zuwa ba" 

 

"Ehhh daga gida aka buƙaci a yaye dashi saboda zai fara zaman majalisa a can na gidan sarauta,suma karatun ake musu to zai ɗora daga na nan" 

 

"Ehh nagane,to yanzu yaxakiyi kenan,bazakije bane kike zaune,an kusa fara taron fa" 

 

"To yazanyi Addah Rahilah,bangama aikin da ummu hajar tasakani ba,kuma kinsanta kullum zancen ta shine na dunga saka rayuwar marar lafiya a kullum kafin wani uzurin ya biyo baya" 

 

 

"Uhmmm kaman hakan yadamu su marasa lafiyan,ina nan saboda kina baiwa suke hantararki dole tasa kika daina shiga ɗakin jinyar,saboda hassadarsu kar ace baiwa ta koyi abu zata fisu" 

 

Cikin ƙanƙanin lokaci ta harzuƙa,domin tunda cikin yafara tsufa na kulada ita abu kaɗanne yakesa ta hau tayi fushi,kuma daga tayi fushin zatace kanta yana ciwo kokuma tanajin hajijiya. A yanda na nazarceta akwai wani abu a tattare da ita wanda ba daidai ba. Amma babu wanda nafaɗawa saboda gudun saka wani a damuwa. 

 

"Ahah Addah rahila kibar wannan maganar,babu wani bawa daya isa yahana wani samun abinda shi ya nufeshi da samu. Dan haka ki kwantar da hankalin ki,idan inada rabon samun ilimi ko ba akan wannan ba da sannu zan sameshi. Nakusa gamawa ai yanzu zanje,kuma dama baza'a barni nashiga ba domin ni bana cikin bayi masu kulada taro, saisun gama kafin inya fito zai tafi naganshi" 

 

Nayi mata bayani saboda kar tacigaba da ɗaga hankalin ta. 

 

Hakan kuwa akayi bayan na shirya a gurguje naje ɗin saida na jira a wajen na tsawon daƙiƙa talatin kafin na kalla mutane sun fara fitowa daga ɗakin taron. 

 

Rarraba ido nakeyi har zuwa dana hangoshi yana fitowa,na manta da sanin junan namu sirrine,tsawon lokaci muna boyewa babu wanda yasani. Yau daya kasance na ƙarshe na barar dakomai saboda ɗokin ganinsa da kuma tunawa bankwana zamuyi. Domin ɗaga murya nayi iya ƙarfina nace  

 

"Yallabai Hamad!!!" 

 

Ina mai ɗaga masa hannu,shima ɗagamin hannu yayi ya taho da sauri yana maida min ɗaga hannun danake masa. Shi murmushi nikuma murmushi,nice nafara narai narai da ido dana kallah Bawansa wanda shima mun ɗan saba Kanata yana saka masa kayansa a bayan keken doki.  

 

Ganin ina sunne kai babu abinda nake cewa yasa yafa magana. 

 

"Duk surutunnaki abokiya yau babu shi,keda yakamata kiyishi dayawa naji wanda zan dunga tunawa idan na tafi?" 

 

Ha ilau nakasa cewa komai sai sunkuyar dakai,ko dan muna cikin mutanene. Da kyar na daure nace. 

 

"Wai dagaske yanzu tafiya zakayi?" 

 

"Gashi kuwa kinga zahiri,nima ke kanki kinsan bazan tabason hakan ba. Kafin na haɗu dake tun ranar farko naji wajennan ya gundureni,amma daga ranar da muka fara abota sai naji wajen yazamemin yalwatacce mai ɗauke da lambuna na farinciki,har ya zamto bana sha'awar abinda zai rabani da wajen. Hakan yasa lokaci yaketa gudu batareda na ankara ba sai cin karo nayi da ƙarewarsa. Ƙira yaxo daga gida wanda bazan iya ƙin amsawa ba. Zan koma nahiyata joda banida tabbacin zamu sake haɗuwa amma ina roƙonki daki dunga tuna duk wasu sakanni,daƙiƙai da kuma sa'o'i damukayi a tare. A zamana dake joda na ƙaru da abubuwa da dama,wanda hakan yasa na ƙara yarda da maganar koda karene karka taba wulaƙantashi,domin wataƙila yanada wata baiwa dakai bakasanta ba kokuma bakada ita. To inaga kuma mutum domin kawai kana tinƙaho yana ƙanka..........." 

 

 

Rushewa nayi dakuka mai tsuma ruhin duk mai jinsa,inaaa kunnuwana sun kai maƙura bazasu iya cigaba dajin waɗannan kalamannasa ba masu nauyi a cikin ƙirji. Dakyar labban bakina wanda suke rawa suka samun damar furta. 

 

"Kafara ko zaka farako.....ko aboki wannan kalamannaka masu saka mutum ya kasa ƙin saurarenka shin meyasa ka tunkaro rayuwata ka tura da karfi ka shiga,idan kasan irin wannan rayuwar zamuyi ta har abada yallabai hamad uhmm?" 

 

Inna sheshsheka shima naga idanuwansa sun cika tabb ta ƙwalla jin nawa furucin. Haƙiƙa nasan bakaramar dauriya yake ba. Ciro zobe ɗaya na azurfa yayi daga jikin hannunsa ya miƙamin. Saka hannu nayi na karba ina kallonta. 

 

 

"Ki rike wannan Joda,ki rikeshi har ƙarshen rayuwarki,nasan banyi miki adalci ba danayi miki irin wannan bankwanan,amma ina roƙonki da kada ki manta dani. Wannan zobe yazamo cikon abotarmu. Nizan wuce nahiyata nabarki lafiya" 

 

 

Har bayan yayi nisa saina tuna kuskure ɗaya danayi wanda shine rashin yi masa tambaya a gameda inda yafito. Saurin yunƙurawa nayi zanbi bayansa na tambayeshi,amma sai naji an fincikoni da baya. Na juya bankai ga kallon waye ba niji an Wankeni da wani lafiyayyen mari da saida dukkan jijiyoyin dasuke barin kuncinnawa na dama suka amsa tasssss. 

 

 

Saurin dafe wajen nayi kafin na ɗaga ido domin naga waye. 

 

Gimbiya meerah ce a tsaye tana huci kaman baƙar zakanya,batada ƙarfin hannun dazatayi irin wannan marin. Wata gwabjejiyar baƙar baiwa ce a gefenta itace tayimini wannan marin na bazata.  Miƙa min hannu tayi tanamin wani irin kallon,gabaɗaya jikinta har rawa yakeyi. Fatar bakinta ma rawar takeyi,daƙyar ta buɗe bakin kana tace. 

 

 

"Bani zoben daya baki.........ƙazamin hannunki yayi kaɗan yataba abu mai daraja kamarsa!" 

 

Saurin zubewa nayi a kan gwiyoyina ina mai kallon ƙasa,indai har duk abinda ya auku tsakani na da hamad akan idonta yafaru,to lallai ya tabbata na tabka babban kuskure. Bakina kasa furta neman gafara yayi a gareta saboda fargabar,jin furucinta nayi mai kamada na dafin maciji yaci gaba da gudana. 

 

 

"Bijima idan bazata bada zoben ba to ku sare hannun da zoben yake ku miƙomin shi da karfi sannnan kuyi mata dukan dasai takasa tashi" 

 

Ganin matar ta nufo kaina yasa nayi saurin mika mata zoben jikina yana rawa,amma duk da haka bata tsaya ba saida takaimin duka a ciki mai matuƙar ƙarfi,duk da na kalli dukan ya taho amma banida ƙarfin tareshi har kaiga isa marata giffff. Take kuwa wani wani matsanancin ciwo ya ziyarce ni har cikin ƙwaƙwalwata,ina jin wasu dukan suna cigaba da sauƙa a sauran sassa najikina, ciwonsu da azabarsu ya nunkuwa akan wanda tayimin na farko.  

 

Kan kaceme cikin ƙankanin lokaci har mutane sun fara taruwa a wajen,xuwa lokacin sai tumurFasihni take a cikin rairayin wajen tana dukana kaman ta samu abokin kokuwa. Muryar ummi Asma'u naji tana tambayar mai yake faruwa. Buɗar bakin gimbiya meerah sai tace wai satar zobe nayi mata,tana nemansa kawai saita ganshi a waje na. Babu wanda ya yayarda da zancenta,amma kuma babu wanda zai Fasih mata,saboda ita ɗin ƴar mulkice nikuma baiwa. Ina ji ina gani kowa yafara watsewa tamkar babu wanda akayiwa rashin adalci. 

 

Wacce aka ƙira da Bijimar ce ta kalleni lokacin dana ɗaga fuskata wacce ta kumbura suntum saboda duka. Dantsenta ta nuna min tana murmushin mugunta. Dukan datayimin mai cimin rai ba kaman jina danayi kamar marar amfani,wai macece ƴar uwata tayi amfani da karfinta wajen yimin irin wannan tozarcin,inaga kuma idan wasu daban maza a wani waje suka kawomin farmaki. Nayi tunanin idan nayi ilimi zan tsira,lokaci guda sai naji ashe da saurana a babin gwagwarmayar rayuwa. Masu kuɗi da masu mulki suna amfani da kuɗi ko mulki su saka a basu kariya,to ni kuma fah damai zanyi amfani wajen kare kaina. Zuciyata ta bani amsa da .......Ƙarfi nah!!! 

 

Ganin kowa yana shirin barin wajen yasa nima tattara saƙina zan tashi. Wata kara na saki danaji wani matsanancin zafi a mata ta tamkar ana yankani. 

 

Ummu Asma'u ce tajuyo daidai lokacin da Addah Aneesa itama ta ƙariso wajen,masu kai rahoto sun kai mata. 

 

Saurin ƙarisowa inda nake tayi ta niyyar ɗagani na tashi. Lokaci ɗaya nida ita muka kalli abinda yakebin kafafuna.....jinine!! 

 

Firgicewa nayi nama rasa mai zance,lokaci guda na shiga tambayar kaina shin mai yake damuna?. 

 

 

"Ranki ya daɗe Jinine fah yake zuba a jikinta mu tafi da ita Sansanin mu a haka?" 

 

Nasan tabiyu tayi maganar,tanaso tajine ko za'a kaini ɗakin jinya. 

 

"To akwai inda zaki kaita bayan can,sanin kanki ne bamuda ɗakin jinya na bayi anan,ki kaita ku haɗamata ruwan ɗumi da dumduma jikinta,wataƙila al'adarta ne yazo" 

 

 

Nida Addah Aneesa da mamaki muka kalleta har ta bar wajen,domin ita kanta shidace nasha haɗa mata gari na shayi wanda zai sakata samun daɗin bacci. Kokuma magani na ciwon baya danake haɗa man ƴaƴan bishiya,har turakarta nake kaimata tayi ta murna. Amma gani a mawuyacin hali babu wanda zai kalleni saboda ni baiwa ce. Kuma hakan bai zama wani sabon abu ba ko zalunci saboda an ɗauki hakan bakomai ba. Runtse idona nayi dana kalli mutum na ƙarshe a wajen ya tafi,an barmu dagani sai Addah Aneesa wacce take riƙe dani. Wani abu naji ya tokaremin maƙoshina,sannan kuma hakan yasa nakoyi wani babban darrusa a yauɗin. Karfin kwakwalwa bashine kaɗai ba. Sannan ka fara amfanar da baiwarka ga wanda suke kusada kai,kokuma wanda suka nemi taimakon ka tukunna. Daga yau bazan kara Amfani da baiwata akan kowa ba sai ga wanda ya nema kokuma ya cancanta,amma ba kowa ba. Sannan zanbj kowanne hanya danasan zanbi wajen ganin nasamu ilimin da zasusha mamakina. Nasan bawai mugunta ne yasa taki taimakona,saidai illah hakan dokane da wasu mutane can da suka wuce suka kafa ta. 

 

Ikon Allah ne kaɗai yakaimu sansanimu lafiya,wahala kam nashata da bazata bayyanu ba. Muna zuwa Addah Aneesa ta tafasa min ruwan mai zafi ta gasamin jikina. Kuma babu ƙarya naji daɗin hakan sosai.  

 

Bayan mun gama ina kwance akan gado na yunƙura nace. 

 

"Addah Aneesa dan Allah ki taimakeni kije wajen ummu hajar kice tabani garin shayin mata masu ciwon mara,sannan tabani garin na'a na'a dakuma habbatussauda akwai ban daɗe dayin aiki akansu ba. Daga yanzu ma yakamata na fara ajiye wasu magungunan anan saboda wanda suke a zaune a nan ɗin suma mutanene kuma suna buƙatar magani,idan ka mutu ina amfanin kare dokar" 

 

"Hmmmm sai yanzu kika san hakan kenan,itan ma kinada tabbacin zata baki ɗin idan tasan wa kanki zaki yi amfani dashi?" 

 

 

"Banida tabbacin amma idan da sauran amfanin daxanyi mata to lallai zata bani in tanason kasancewata a raye. Ɗazu kaman naji ummi Asma'u tace wai al'ada nafara,sai yanzu hakan yazomin kaina,wataƙila dukan datayimin yasa shi zuwa" 

 

Yar dariya addah Aneesa tayi kafin tace. 

 

"Ko bata dukaki bama zaizo ai naga kinyi jinkirin yi da wuri ma,domin wasu tun a shekara tara,goma,sha ɗaya a yayi yawa sha biyu suke farawa. Ke gashi har kinyi sha biyar fah. Wata ƙila a kulle yake dukan nata yasa ta buɗemiki shi. Sannu su Joda an zama babbar mace" 

 

Nidai kallonta kawai nake ina narai narai da ido,nikaɗai nasan wahalar danasha a yauɗin,ga rashin abokinnawa ga rashin zoben daya bani ga kuma dukan danasha da kuma tozarci duk ni kaɗai ka ƙashin raina. Wannan ai dole yakowamin darrusa da dama idan har inada hankali. Bakomai hakan bazai sake faruwa ba Insha'allahu. Na ƙuduri niyyar gyarawa. Badai ƙarfi take taƙama dashi dole nima na tashi na nemi nawa wato na kai dana zuciya koda kuwa baxan iya samun na damtse bama. 

 

 

 

Sadi-sakhna ce ✍🏼 

 

Comment  

Like  

Share  

Follow