GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 29

by @nusybee143

Page 29




Kallonta kawai Haisam yake yi a wulaƙance har ta gama jero masa waɗannan tambayoyin, kafin ya sake kallonta ya ce"yanzu dare ya yi, kamar yadda na gaya miki ina buƙatar Hutu,duk lokacin da na samu dama sai na ba ki amsoshin tambayarki,amma kafin nan kar ki sake buga min ƙofa Please, respect yourself,good night"yana kai wa nan a maganarsa ya mayar da ƙofar ya rufe ba tare da ya sake sauraren abin da zata ce ba

Cikin dare Mubarak ya farka yana ta kuka yana kiran Mama,da ƙyar Haisam ya iya tashi yana lallaɓa shi,amma ya ƙi komawa baccin,sai kuka yake yi sosai,jikinsa ya ɗauki zafi zau,hankalin Haisam ya tashi sosai

Lokaci ɗaya kuma numfashinsa ya fara neman harɗewa,ƙirjinsa ya rinƙa ɗagawa sosai,dole ya shirya ya canja kaya,saɓa shi a daren ya fita da shi zuwa asibiti 

A can asibitin yana zuwa likitoci suka yi gaggawar karɓarshi,kai tsaye aka ba shi gado aka tura shi emergency saboda lokacin da Haisam ya isa asibitin Mubarak ya fara kakkafewa,hakan ya tayar da hankalin Haisam sosai

Ya kai aƙalla awa guda kafin likitan da ya karɓe shi ya fito, yana duban Haisam ya ce"officer biyo ni office za mu yi magana"babu musu Haisam ya miƙe jikinsa a sanyaye,ya bi bayan likitan suka nufi office ɗin likitan 

Sai da suka zauna likitan ya dube shi,a sanyaye ya ce "officer patient ɗin naka bai ci abinci ba,kuma gashi akwai alamun ba'a ba shi kulawa sosai game da ciwonsa,me yake faruwa ne?"

Kallonsa Haisam ya yi a sanyaye,da farko kasa magana ya yi,sai daga baya da ƙyar ya iya faɗin "wanne irin ciwo ne haka? I'm sorry yaron baƙo ne"

Likitan ya girgiza kai ya ce "yana da matsalar asthma,kuma ta taɓa masa huhu sosai,ta kai wani mataki wanda dole sai an saka masa idanu sosai 

A yanzu dai ba ya cikin matsala in sha Allah,amma ya kamata a ba shi kulawa sosai, saboda gudun matsalar daga baya"

Haisam ya yi shiru,gaba ɗaya kanshi a kulle,dama yaron nan yana da asthma ne ko kuma daga baya ya same ta?

Cikin jimami da tausayawa ya girgiza kai ya ce"Allah ya ba shi lafiya, shikenan,in sha Allah za'a ba shi kulawa sosai,na gode sosai doctor"doctor ya ba shi hannu suka yi musabaha sannan ya mike ya fice daga office ɗin cikin yanayin damuwa 

Washe gari wajen ƙarfe tara na safe aka ba wa Mubarak discharge letter, Haisam ya ɗauke shi yadda ya saba suna hira suka nufi gida 

Yana shiga sashen Nanny ya samu Amna a zaune,tana ganinsu ta taso da gudu ta rungume shi tana faɗin "Daddy ban ganka ba,na duba kuma ban ga ƙanina ba,ina kuka je?"

Janye ta ya yi gefe,ya ce"ba shi da lafiya Amna, idan kina yin magana da ƙarfi za ki saka masa ciwon kai,yau me kike yi har yanzu ba ki tafi makaranta ba?"

Yar dariya ta yi ta ce"Daddy ai yau da gobe Friday muna hutun mid-term holiday,babu school"Haisam ya jinjina kai, sannan ya ƙarasa kan kujera ya kwantar da Mubarak da yake ta bin su da kallo 

Nanny ce ta fito, cikin girmamawa take faɗin "barka da dawowa yallaɓai"

"Barka dai Hajiya,ya aikin,ya fama da yaran kuma?"

Nanny ta ce"alhamdulillah,ashe mutumina ba shi da lafiya haka?"Haisam ya ce"wallahi fa,ashe wai ciwonsa na asthma ne ya tashi,amma yanzu alhamdulillah da sauƙi"cikin tausayawa Nanny ta ce"ya Salam!

Allah ya ba shi lafiya ya tashi kafadunsa"Haisam ya ce"Ameen,bari na je,zan wuce wajen aiki ne "Nanny ta ce"to Allah ya bada Sa'a yallaɓai "ya ce "Ameen "ya fice daga sashen 

A gaggauce ya kammala komai ya fito cikin shigar suit baƙaƙe,sai addu'a yake yi Allah ya sa kar ya haɗu da Nimra, don ya makara,amma ina!

Yana fitowa suka yi kiciɓus,ya ja baya a firgice,daga baya ya ƙaƙaro murmushi yana faɗin "good morning Nimra "

Kallonsa kawai take yi tana nazartarsa, fuskarta a ɗaure ta ce"good morning,Ina zuwa haka?"

Kai tsaye ya ce"aiki mana!ko kin manta yau ina da zuwa wajen aiki?"

Gyara tsayuwa ta yi tana yi masa wani irin kallo ta ce"ka san da haka ai ka ƙi kwana a gida,gashi ka yi min alƙawarin za mu yi magana da kai, meyasa yanzu ka zama mai alƙawari da saɓawa ne?"

Sauke ajiyar zuciya ya yi ya ce"yaron da muka zo da shi ne babu lafiya, shiyasa na kai shi asibiti"

"Allah ya ba shi lafiya,ina fatan ka mayar da shi ga iyayensa,tunda ka ga ɗaukar alhaki ne barinsa a hannun wani a wannan halin,bayan ga iyayensa"

Kallonta ya yi fuska a ɗan ɗaure ya ce"yana nan,da wani abu ne?"

Taɓe baki ta yi ta ce"a'a,babu komai,kawai dai na yi mamaki ne, saboda Mamie ta ce har yanzu baka ce mata komai game da zaman yaron a gidan nan ba"

Haisam ya tsare ta da idanu ya ce"okay zuwa kika yi kika tambaye ta Kenan?"shiru ta yi kanta a gefe tana taɓe baki,ya yi ƙokarin sauke temper ɗin sa ya ce"bana son ki rinƙa yi min irin haka,tunda ni da kaina na ce zan gaya miki ki jira na gaya miki, meyasa kike yin abu tamkar wadda bata yi karatu bane?ko yaron nan akanki yake da zama ne?"

"I'm sorry "ta faɗa a daƙile,ya ce"sai na dawo, yanzu zan tafi aiki"yana kai wa nan ya kewaye ta ya wuce ya bar ta a wajen 

Bin shi ta yi da kallo fuska a ɗaure, kafin ta koma cikin gida tana taɓe baki,ranta a ɓace, don haka kawai take jin ta tsani yaron,kuma bata yarda da zamansa ba,tana jin akwai ayar tambaya 

Kai tsaye ta wuce sashen Hajiya Mamie, wadda itama take nata shirye shiryen don tafiya aiki,tana shiga sashen bata yi wata-wata ba ta faɗa ɗakin yayar tata tana huci 

Kallonta Hajiya Mariya ta yi, fuska a ɗaure ta ce"ya dai?

Ya za ki faɗo min daki haka kamar wata karamar yarinya?"

Nimra tana huci ta ce"Aunty ki tambaye shi inda ya samo yaron nan, bashi da niyyar gaya min, kuma wallahi zuciya ta fara raya min wata ya yiwa ciki ta haifar masa,don dai gashi kin ce ƴa ɗaya suka haifa shi da tsohuwar matarsa,gata nan Amna "

Shiru Hajiya Mariya ta yi ba tare da ta yi magana ba,sai cigaba da gyara daurin ɗankwalinta da ta yi,sai da ta gama ta juyo tana kallon Nimra da saura ƙiris ta fashe saboda takaici,hankali a kwance ta ce "ina fatan dai ba shirmen naki kika je kika yi masa ba ko?

Menene abin da zai dame ki akan ƙaramin yaron da har yanzu ba ki da tabbacin Wanene shi?"

Nimra cikin ɓacin rai ta ce "shine abin da yake damuna aunty,ya gaya min mana idan yana da gaskiya,ita kanta Amna bana jin zan iya riƙe ta ballantana wani yaro da aka samo a kwararo,tsintacciyar mage"

Hajiya Mariya ta ce"ai kuwa idan da irin wannan zuciyar za ki zauna da namiji ina mai tabbatar miki ba za ki taɓa cin riba ba, ita mace ma da aka santa da kissa? da ace hakan kika yi masa da tuni ba'a wuce wajen ba?kina tunanin wannan rigimar da kika ɓallo da ita zai biye miki ne ko zai ji tsoronki?

To ba'a yiwa namiji haka,ki gyara yadda za kiyi mu'amala da shi,kar ki manta matsayin sa na mijinki ma gobe,kuma har yanzu neman soyayyarshi kike yi bai kai ga amincewa ɗari bisa ɗari ba,har yanzu abubuwan da za su faranta masa za ki koyi yi,ba wanda zai baƙanta masa ba 

Idan kina da hankali kamata ya yi ki kwantar da kai akan batun yaron nan,ki ja shi a jiki,da kanshi zai sanar miki da ko wanene shi,ai nima ba son zama na yi da shi a gidan nan ba,amma da na kwantar da kai gashi nan ke shaida ce, yadda na mallake ubansa "

Nimra ta jinjina kai ta ce"I will try Aunty,da farko raina ne ya kai ƙololuwar ɓaci,amma yanzu na sauko,zan yi amfani da dabarunki in sha Allah"

"Better!"a cewar Hajiya Mariya, sannan ta ɗauki handbag ɗinta da labcoat ɗinta, ta dubi Nimra ta ce"sai na dawo"ta fice daga ɗakin 





*HAISAM*

Zama ya yi a office ɗin sa yana nazarin abubuwa da yawa,na farko labarin Roxy,bata kai ƙarshen labarin ba,amma daga yadda ya ga yanayinta har ya fara fargabar abin da zata ce masa a gaba, musamman game da iyayenta da danginta

Ga lamarin auren da ta yiwa kanta,ya yarda laifinta ya fi yawa,amma tun daga farko ya ga laifin iyayenta,sam sam bai kamata su nuna mata ƙarfi a wajen hana ta auren masoyinta da liƙa mata auren cousin brother ɗin nata ba

Sai maganar rayuwarta tare da Arnold,ta ba shi tausayi sosai, musamman yadda ta yarda da Arnold amma ya yaudare ta,kuma hakan ya karya mata zuciya sosai,a ƙarshe duk da yadda ya zama a gare ta ya kasance abin dogaronta,ya mutu ya bar ta 

Ko daga nan ta tsaya ya samu amsar dalilin da ya sa ta zama ƴar ta'adda, tunanin mace ba shi da tsawo sosai,kai ko da ace namijin ne mummunan halin da ta shiga daga wannan zuwa wannan zai iya sauya halayensa zuwa wani mutum dabam 

Yana nan zaune Musa ya shigo bayan ya yi masa izini,ya ɗaga kai yana kallon Musa,,Musa ya gaishe shi cikin girmamawa yana sara masa,cikin sanyin murya ya ce "ka haɗa min zama da team ɗin mu da muka yi operation na kama yarinyar nan"

"Sir wacce yarinya kenan?"

Haisam ya sauke numfashi ya ce "Shaheeda"

"Ko dai Roxy yallaɓai?"rai a ɗan ɓace ya ce" ba dai ka gane ba?

To sai ka yi min abin da na saka ka ko?"babu musu Musa ya sara masa, sannan ya fice daga office ɗin 

Bayan mintuna goma suka hallara gaba ɗaya su shidan, Haisam ya yi shiru yana nazarin ta inda zai fara 

Dakewa ya yi ya fara magana ganin gaba ɗaya sun ba shi attention,ya fara da faɗin "a ƙarshe dai ga Roxy ta shiga hannunmu,ina godiya da dukkan waɗanda suka taimaka min na kama ta

Sannan abu na gaba,a cikin mu shidan nan akwai wanda Roxy ta siya don ya faɗa mata sirrinmu, kuma ta yi nasara,ta siye shi ya fitar mana da sirri,a ƙarshe ta yi nasara akaina a karo na farko,sai dai a karo na biyu ban yi wautar sanar da kowa shirina ba,kuma cikin hukuncin Allah sai gashi na kama ta ba tare da wata matsala ba

Ban damu da sanin wanene baren a cikinmu ba, abu daya zan faɗa muku kawai, shine ko ma wanene ya kiyayi gobe, saboda muddin zai cigaba da fitar min da sirri to tabbas zan gano shi watarana,kuma abin da zai faru zai ba ku mamaki 

Na sallame ku"yana kai wa nan ya mike ba tare da ya sake kallonsu ba ya fice daga office ɗin 

Sai da ya kammala abubuwan da zai yi,da lissafe-lissafensa sannan ya miƙe ya fice daga office ɗin, kai tsaye ya faɗa mota ya nufi jail ɗin da aka rufe Roxy 

Yau ma dai kamar kullum sai da ya nuna ID card ɗinsa sannan aka shigar da shi,aka fito da Roxy wadda gaba ɗaya ta yi wani irin sanyi 

Kallonta ya yi sosai, cikin kwantar da murya ya ce"kuka kika yi?"

A hankali ta ɗago ta kalle shi, cikin sanyin murya ta ce"bani da dalilin kuka ne?"

Haisam ya ce"of course kina da dalilin yin kuka,amma sai nake ganin kamar kukan ba mafita bane ko?

Murmushi ya yi a sanyaye tana girgiza kai, sannan ta ce"Shi kadai ne makami na a yanzu,akwai lokacin da nake ƙyamatarshi, saboda na ɗauke shi a matsayin raunin da zai karya ni,amma a yanzu kuma shine maganina, shine babban makamin da nake da shi"

Haisam ya girgiza kai ya ce"Roxy bai cancanci ta karaya irin haka ba"

Kai tsaye ta ce"Roxy dama can a karye take,dakiya da gujewa rauni ne ya sa ake yi mata kallon jaruma "

Haisam ya ce"yanzu kuma bai kamata ta rungumi raunin nan ba kuwa, saboda....."

"Saboda me?

Rayuwarta ta tsaya ko?ai na sani,babu babbar asararriya a duniya number ɗaya kamar Roxy, saboda......"

"Zan iya samun cigaban labarin Roxy?"ya yi azamar katse ta da faɗin hakan yana kallonta,a ranshi yana danne yanayin da ta fara jefa shi 

Murmushi ta yi,ta ce "menene abin jan hankali a labarin Roxy ne har haka da ya kasa gundurarka?"

Gyara zama ya yi, shima yana murmushi ya ce"Tun da na buƙace shi ke ma kin san dole zai yi min amfani,ke dai ki cigaba kawai"babu musu ta jinjina kai ta ce" haka ne kuma,to ga cigaban labarin Roxy........"





#Nusy_bee