8
by @pherty001
Fadila ta shigo da sauri cike da murna gidan kai tsaye dakin Nurayyah ta nufa dauke da ambulan a hannunta, burin ta ya cika yau ta sanya Daddy ta ya samo wa Nurayyah admission a school ɗin da take karatu cos ita tun last year ta kona da ta ga Nurayyah da gaske taqi karatun, Fadila ta zauna a gefen katifar Nurayyah tana numfashi sama-sama cikin tsantsar murna tace, "Oh my God, Nurayyah! Look at this! I finally made it happen! Na matsa wa Daddy sosai a kan zancen karatunki, kuma yau gashi na karɓo miki Admission Letter! Nasan kin so kiyi Medicine a baya amma aka rusa miki mafarki, so I applied for Mass Communication for you a wannan karon tunda naga zaki dace da kwas ɗin matuƙa, please don't say no this time around, you deserve the best life has to offer Kuma Idan daddy yaji baki je ba he will not feel happy saboda na gaya mashi da gaske wannan karon zaki je!"
Nurayyah ta tashi ta karbi admission din tana kallo na makarantar Afit acan zata yi karatun Mass Com banda fadila ya zata samo mata wannan irin admission din bayan ta san ko surutu banza bata da shi, anyway ko bata so bazata nunawa fadila ba saboda yanda take qoqari take jajircewa akan ta dole zata yi karatun saboda fadila kawai, ta dube ta a sanyaye tare da qago murmushi yaqe tace " kin yi qoqari friend nagode sosai kuma kimin godiya a gurin Daddy" fadila ta gyada kai tana kallonta da murmushi tace " zaki je ko" Nurayyah ta gyaɗa kai tana kallonta batare da tayi magana ba sosai fadila taji daɗi kuma kafin taje gida sai da tayi ta qarfafa mata gwiwa akan ta manta komai tayi facing abinda ke gabanta kawai a yanzu da hakan zata yi succeeding in life me yiwuwa aikin likita ba alheri bane a gurin ta.
Bayan tafiyar fadila, Nurayyah ta zuba wa takardar ido, idanuwanta suka canza tana son yin kuka tana danne wa zuciyar ta shikenan bazata yi karatun doctor ba bazata zamo mai taimakon talakawa ba, bazata iya wato masu yanci da cin zarafi da ake masu a asibiti ba, tayi kuka a ranar har ta gode Allah kafin ta hakura da zata yi karatun hanyoyin taimakon talakawa yawa ne dasu ba dole sai ta likitanci ba akwai wurare da dama da ake cin zalun talaka kuma zata iya bin wannan hanyar dan taimakon su da wannan tunanin taji zuciyar ta na sanyi tare da amincewa da zata yi karatun.
Ranar da fadila ta kira ta akan ta shirya zasu shiga makarantar AFIT (Air Force Institute of Technology). Ta shirya cikin wata doguwar rigar atampa mai kyan launi, duk da cewa ba ta da tsada ko dinkin gayu ta zauna daram a jikinta tare da fito da cikar siffarta da diri mai kyau da Allah ya ba ta. Jaddi sai daɗi take ji a ranta, ta biyo ta har ƙofar gida tana ta zuba mata albarka da addu'o'in nasara gami da kariya. Suna zuwa kofar gida, motar gidan su fadila tana jiranta, an canzawa fadila mota zuwa Mercedes-Benz GLE 450 fara ƙal, fadila tana zaune a gaba sanye da wata tsadaddiyar abaya mai ɗaukar ido wadda ta sha aikin hannu na luxury hand-beaded embroidery, gashinta ya sha gyara, ko da Nurayyah ta bude motar tana zaune tana danna wayarta sabuwa iPhone 17 Pro Max dake ta walkiya a hannunta. Nurayyah ta kalli kanta ta kalli tsohuwar wayarta ta Tecno dake hannunta wadda taci screen sosai a haka take kallo da ita, ta ji wani irin daci da tsarguwa ya ratsa ta tun kafin su isa jami'ar.
Suna isa cikin harabar makarantar, bayan sun sun fito a mota fadila ta rakata har gurin da suke daukar lecture ta nuna mata yanda zata yi komai kafin ta fice da sauri tana faɗin "muna da lecture idan kin fito ki kirani " ta fice da sauri, Nurayyah ta tsaya a bakin corridor na Faculty ɗinsu tana kallon rukunin ajujuwan gaba ɗaya, saboda tsarguwa ta ƙi shiga cikin lecture room ɗinsu, ta ƙi tambayar kowa komai, sai yawo take yi ita kaɗai tana kare wa rayuwar mutane kallo cikin tsantsar mamaki da sha'awa dake dukan zuciyarta. Abubuwan da ta gani a ranar sune suka canza mata tunaninta na rayuwa, ta ga manyan motocin da ɗalibai mata tsaran ta suke hawa suna shigowa dasu makaranta, motoci ne irin su Lexus LX 600, Range Rover Velar, da Mercedes-Benz C-Class masu sildin glasses, ta ga yadda mata ke dressing irin na gayu kamar wanda take gani a TikTok da sauran su, ta gansu da manyan wayoyi, taga yanda wasu ke tafiya cikin nutsuwa wasu kuma ba kamun kai daga yanayin shigar su, taga yanda wasu ke wucewa da manyan handbags dinnan da take ganin tallar su a media irin su Gucci, Chanel, da Louis Vuitton, da sauran su, she see alots wani abun ma baya faduwa.
A karo na farko a rayuwarta, Nurayyah ta duba kanta bayan ta tsaya a gaban wata doguwar taga tana kallon kanta, tana da kyau na halitta mai girgiza kowane ɗa namiji, tana da diri mai ɗaukar hankali wanda ko da ace tana cikin tsofaffin kayan ba zai ɓoye ba, amma rashin dukiya ya sanya ta zama mabaraciya a gaban ƴaƴan masu kuɗi wanda rashin kuɗin ne ya janyo ake mata wulaqanci tun a secondary bary anan jami'a da ke hade da maza, bazata yarda a sake raina mata wayo ko asali ba, ta ji wani irin tsananin sha'awa na son shiga wannan rayuwar ta masu kuɗi itama taji yanda suke ji idan sun riqa babbar waya sun hau babbar mota kuma sun sanya kaya masu tsada, ta tsinci kanta cikin son yin kuɗi ta kowane hali, tana son ta ganta ta riƙe babbar waya ta bar amfani da wannan tsohuwar Tecno ɗin ta. Wannan sha'awa ta rayuwar qarya ta shige ta gaba ɗaya, har ta sanya karatun Mass Communication ɗin ma duka ya fita a kanta a wannan ranar, burinta guda ɗaya ne yanzu a jami'ar ta duba hanyar da zata yi ta zama mace mai dukiya, iko, da tsantsar daukaka a cikin AFIT (Air Force Institute of Technology).
Haka Nurayyah ta yini a school ɗin sukuku tana kallon kowa da kalar rayuwar da suke ciki, taƙi shiga ajin su wanda fadila ta nuna mata sanda suka zo kafin ta nufi nata, gaba ɗaya abubuwan da za a sha wahalar yi na registration, departmental clearance, da course enrollment duka baban fadila ya saka anyi mata ta hanyar kiran waya a school ɗin saboda babban mutum ne mai iko, a very influential figure wanda yake da mutane sosai a kowane sashe na jami'ar, hakan ya sanya Nurayyah bata wahala a komai ba shigowar ta Afit kamar wata ƴar gata,
Sanda fadila ta gama lectures ɗinta na ranar, ta fito cikin sauri da walwala tana dube-dube har ta hango Nurayyah zaune a kan wata kujerar sanyawa ta zamani dake harabar Faculty ɗinsu, fadila ta ƙaraso da farin ciki tana murmushi tace, "Hey babe! Ya kika ji jami'ar tamu ta yau? I hope you loved the environment!" Nurayyah ta ɗago fuskarta ta yatsina ta gaba ɗaya cikin sanyin jiki ba tare da ta iya cewa komai ba,
Fadila ta fuskanci akwai damuwa amma ta ƙetare zancen domin kada ta ɓata mata rai har suka shiga cikin mota suka bar harabar jami'ar, har suka iso unguwar su Nurayyah ɗin fadila ce ke ta faman surutu a cikin motar tana bata labarin yadda zata ji daɗin school ɗin idan ta saba tana faɗin, "Trust me babe, you're going to love Mass Com, it's so sophisticated and fun, just forget about the past, okay?" tana ƙoƙarin ganin ta mantar da ita damuwar baya amma Nurayyah jinta kawai take yi zuciyarta na wani irin zafi saboda tsarguwa.
Bayan wucewar fadila, Nurayyah ta tura kofa ta shiga gida a sanyaye, Jaddi dake zaune a tsakar gida tana jiran dawowarta taji daɗin ganin ta sosai ta tarbe ta tana mata oyoyo cikin farin ciki, amma ganin yanayin da jikarta ta dawo ciki ya saka jikin Jaddi yin sanyi matuƙa, ta tsaya tana kallonta cikin fargaba take tambayar ta ko lafiya, Nurayyah ta zauna dambashe a gaban kakarta ta fashe da kuka mai ban tausayi, ta shiga bata labarin komai na rayuwar makaranta da yadda ta ga kowa yana taƙama da dukiya da tsadaddun kaya da jaka na designer wanda kai tsaye tace "Jaddi bazan yi karatun ba gasky zan fada miki, babu talaka Irina acan, duk yawanci Yayan masu kuɗi ne, Jaddi Kinga yanda na wahala a secondary school saboda kasancewa ta talaka, yanzu bazan iya ba, saboda zan tsargu kuma zaa riqa kyamata a aji" jikin Jaddi ya ƙara yin sanyi sosai, ta matso kusa da ita ta soma rarrashin Nurayyah cikin tattausan sauti na lallashi tana nuna mata cewa ilimi ba na masu kuɗi kaɗai ba ne amma Nurayyah ta ƙi sauraron Jaddi saboda zuciyar ta ta riga ta kwadaita mata waccan rayuwar da take gani burgewa ce kuma take gani tafi dadi da kwanciyar hankali, hakan ya saka Jaddi damuwa sosai ta shiga tunani mai zurfi a ranar har zuwa washe gari da safe sanda fadila tazo ɗaukar ta a mota kamar yadda suka saba.
Nurayyah ta fito amma fafur tace bazata je ba, fadila ta tsaya da mamaki tana kallonta kafin ta soma tambayar ta dalilin da ya sa ta canza shawara lokaci ɗaya, ba tare da wani ɓoye-ɓoye ba ta gaya mata gaskiyar dake ranta tace "makarantar ire iren kuce bada ni ba fadila, bazan iya ba, bazan iya rayuwar wulaqanci da nayi a baya ba, bani da sutura mai kyau irin taku, bani da mota da waya irin naku kai bazan iya ba gsky kije kawai na yafe karatun na hakura" fadila ta tsaya tana kallon Nurayyah cikin tsantsar kulawa da ƙaunar da take mata, ta matso kusa da ita ta dafe hannunta tace "shikenan zanje na kawo maki wasu kayana ki riqa sakawa, ko kuma kizo muje daga can mu wuce kada mu makara ba sai naje na dawo ta nan ba, mota kuma kinga dama tare muke zuwa muke dawowa, and indai waya ce zan baki nawa sai in ma daddy magana ya siya min wata kinji" Nurayyah ta tsaya cur tana kallon fadila, idanuwanta suka cika da ƙwalla masu zafi da suka soma gangarowa a kuncinta, ta tabbata duk duniya bayan Jaddi bata da kamar fadila kuma babu wanda zai iya nuna mata wannan gata da asalin kauna dake cike da pure unconditional love ba tare da yaudara ba kamar fadila, har cikin ranta tana son fadila tana kaunar fadila kamar yanda take kaunar ta, Jaddi ita ma ta kasa daurewa cikin zubar da hawayen farin ciki tana ta yiwa fadila godiya da fatan alheri, ta qar da masu addu'a Allah ya basu mazaje nagari da zasu kula dasu.
Jiki a sanyaye Nurayyah taje tayi wanka ta shirya, suka yiwa Jaddi sai anjima sannan suka fita jikinsu duk a sanyaye, kai tsaye suna fita unguwar su fadila suka nufa, Malali GRA, gidan su fadila babban gida ne mai tsaro da kyau, gidan ba sabo bane a wurin Nurayyah saboda ta saba zuwa tun suna tare a makaranta, suna shiga cikin ɗakin fadila ta sami guri ta zauna fadila ta nufi luxury walk-in closet ta dinga ɗebowa Nurayyah atampa, leshi da abayoyi masu dama ko Nurayyah bata san adadin su ba, Nurayyah taji daɗi sosai a ranta wani sanyin dadi ya ratsa ta gaba ɗaya, ta karɓi ɗaya daga ciki ta sanya ta nufi gaban madubin dakin tana kallon kanta cikin less ɗin da ya zauna daram a jikinta ya fito da siffarta da kyanta na fitar da rai, fadila tayi dariya cike da farin ciki tana kallon ta tare da yaba kyawun da tayi tace, "Oh my God, Nurayyah! You look like a literal queen, this outfit was customized for you!" ita kanta Nurayyah tasan tayi kyau sosai fiye da kowane lokaci, bayan sun fito suka zuba sauran kayan a mota har da takalmi da luxury designer bags duka fadila ta bata, ta amsa sannan suka nufi makaranta cike da farinciki tana jin kanta kamar kowa yau.